Kanwar Maza 1&2 Complete Hausa Novel

Author :  Ayshacool Category :  Love

Chapter   44 / 61

129K to 132K   out of 182.7K words

kalli matar cikin mamaki za ta yi magana ta fasa, ta kwantar da yaron, ta mi?e ta kamawa matar suka sauke ?orran.
Ta koma ta zauna ta na cigaba da kallon jaririnta, matar ta din ga auna nono, ba tare da kuma tankawa rumaisa ba, can rumaisa ta ce "Dan Allah baiwar Allah ki taimaka mini da ruwa da nono na bawa yaron nan, ni ko ba zaki bani ba, shi ki bashi dan Allah".

Matar ta yi murmushi ta ce "Ai na zata ba zaki kulani ba, na tashi na yi tafiyata".

Ta mi?awa rumaisa battar ruwa, ta karSa ta Wago jaririn za ta bashi, matar ta karSe shi ta bashi ruwan, sannan ta buWe wata ?warya ta tsiyayo madara fresh ba a daWe da tasota ba, ta fara bashi, aikuwa duk da bashi da lafiya, haka ya din ga karSa yana sha, kamar zai cinye da mazubin.

Rumaisa sai murmushi take, ganin ya samu ruwa da abun da zai ci.

Matar ta kalli ruma ta ce "Ba dan halinki ba bari na san miki ruwa ki sha, ruma manyan gari, ruma kaya da yani, gwagwarmaya na gaba ba ta zo ba kuma ba ta wuce ba".

"Wai ke a ina ki sanni?" Ruma ta tambayi matar.

Matar ta yi murmushi ta ce "Ke waye bai sanki ba, karSi ruwan ki sha, kar kuma ki manta ki kula da amanar da aka baki, Allah ya taimake ki baki mini rashin kunya ba, Kodayake jikin ta ?aura yayi la'asar, wallahi da a dajin nan zan barki, amma ki ka taimaka mini, sha ruwan na rage miki hanya " rumaisa ba ta gama gane me matar ke cewa ba, ta karSi abun ruwa ta kafa kai, sai dai ma?warwa biyu ruwan ya ?are ba ta ?oshi ba.
Lumshe ido rumaisa ta fara yi, tana jin yadda kanta yake ?ara nauyi, ta karSi yaronta daga hannun matar ta rungume, sai sunkuyar da kai take, kamar ta yi shaye-shaye saboda ji take kamar zata fita daga hayyacinta.

"Ke!ke! Baiwar Allah me ki ke yi a gefen titi haka?" Rumaisa ji ta yi kamar ta farka daga bacci, ta buWe idonta sosai, irin zaman da tayi ta rungume yaron a haka take, sai dai a wani wurin ta ganta daban, jeji ne wurin sai dai tana zaune a gefen titi, kwalta WoWar.

"Me ki ke yi a nan, ina zaki je?"

Ta Waga kai ta kalleshi amma ta ba ta kula shi ba.

"Ko dai mahaukaciya ce ne? Wannan yaron na waye, ni da na zaci tsohuwa ce ashe yarinya ce, daga ina ki ke Wan waye a hannunki?"

"?ana ne" ta bashi amsa.

Mutumin ya ce "A'a ba dai Wanki ba, ina hijjabinki, ina ne gidanku?".

"Kai dan Allah ka ?yaleni haba" tayi maganar tana neman wurin kwanciya.

"Karki kwanta da jaririn nan a wurin nan, ki gaya mini in da zaki in kai ki".

Ta kalleshi ta ce "Ka san Worayi?".

"A'a wanne gari ne?"

"Tun da baka sani ba Shikenan, na gode sosai" gani yayi kamar maganar da rumaisa take yi, haukacewa ta yi ba a hayyacinta take ba. Wata dan?areriyar mota ce ta yi parking a wurin da mutumin yake tsaye a kan rumaisa, da tuni mutane suka fara taruwa a wurin.

"Bawan Allah lafiya, meyake faruwa ne?".

Ya kalli na cikin motar ya ce "Wallahi kaga yanzu nake dawowa, na biyo hanya ns ga wannan yarinyar da jariri, ta ma dai ?i bari na ga yaron, amma kamar dai mahaukaciya ce".

"A'a dawanau ce ni ba mahaukaciya ba, kai haka ake tainako ?ishirwa nake ji, amma ko ruwa bai bani ba yake ce mini mahaukaciya".

Na cikin motar ya Wauko ruwan roba, ya fito ya bawa rumaisa, ta karSa ta ta?ar?are ta shanye shi a ma?warwa uku tayi jifa da jarkar.

Ya kalli rumaisa a tsanake ya ce "Na ji kin ambaci dawanau, ke 'yar kano ce?"

"Eh, dawanau asibitin mahaukata ne, dan Allah idan ka san kano ka kaini, kar jaririna ya mutu, bashi da lafiya" tayi maganar cikin magiya.

Ya ce "Ok babu damuwa, amma Meyasa na ganki a haka? Ina hijjabinki kalleki futu-futu fa, ga raunuka a jikinki, kalli kanki yana zubar da jini, jikinki babu hijjabi, ?afarki babu takalmi, dole ayi zaton ko baki da hankali".

"Kwana kusan sittin fa a dajin nan, saceni aka yi, dan Allah ka tashi ka mayar da ni gida" salallami mutanen wurin suka Wauka.

A take ya ciro id card Win sa, ya nunawa mutanen, shi jami'in tsaro ne, dan haka ya ce zai tafi da rumaisa babban asibiti na cikin garin katsina.

Rumaisa ta ce ita fa ba ta so a kaita ko ina sai gida, ya fuskanci yarinyar kafaffiya ce, dan haka ya ?yaleta ya ce ta taso sai ya Wauki wakilcin mutum Waya su tafi, su tsaya su yi reporting wa police, su wuce da ita asibiti.

Sai dai duk yadda rumaisa ta so ta tashi ta kasa, saboda ji ta yi ?affuwanta kamar ba nata ba, ?arshe sai Waukarta aka yi aka saka a motar suka tafi.

Sai dai fa fafur ta hana kowa jaririn nan, yana ?an?ame a jikinta, jin abubuwan take kamar a mafarki, Allah ya kuSutar da su, ta din ga jera hamdala ga Ubangiji.

Sai dai rumaisa na sanya ran an kama hanyar kano ne, ta gansu a asibiti, aka zo da wheel chair, aka Worata a kai, nurses zasu karSi jariri ta ce ba ta san zance ba.
Emergency aka shiga da su, aka yi ta lallaSa rumaisa ta bayar da jariri ta ?i, ta ce idan aka matsa mata, ko da rarrafe sai ta gudu daga asibitin.

Kasancewar mutumin da ya tsinceta shi ma ba Wan gari bane ba, idanya barta babu wanda zai kula da ita, ya sanya a ka bawa rumaisa Wan taimakon gaggawa, ya Wau rumaisa tare da rakitar 'yan sanda biyu, suka taho kano.
Suna tafe a hanya rumaisa tana ta surutai, masu kama da na fita a hayyaci, ta ce wanna ta ce wancan, ita dai gata nan kamar mai barci kuma kamar zautacciya.

Ba su suka iso kano ba sai bayan tara na dare, suka biya suka kuma report ga police na kano, aka yi rubuce-rubuce, sannan suka wuce da rumaisa asibiti.

Suna zuwa aka karSi su rumaisa, da tuni hankalinta baya jikinta, tun a hanya aka sai abin ci aka bata, amma ta?i ci, ba ta ma da nutsuwar da zata ci Abincin.

Aka zare jaririn hannunta, da a yanzu numfashi ma yake neman ya gagare shi, da yawa sai da wasu suka yi hawaye, ganin halin da jaririn Wanyen haihuwa yake ciki, cibiyarsa ta ya?une tayi ba?i, jikinsa duk ?azanta, aka samo kaya aka saka masa aka wice da shi nursery domin bashi taimakon gaggawa.

Ita kanta rumaisan sai ka kai zuciyarka nesa zaka iya taSata, saboda yanayin da take ciki na ?azanta da dauWa, ba yadda ba su yi ba su kwance Wan kwalin ?ugunta, amma aka kasa, ?arshe suka ?yaleta suka fara kokawar ceto rayuwarta, ita kanta sai da aka saka mata oxygen, saboda sama-sama take numfashi, aka Webi jininta aka tafi yi mata gwaje-gwaje.

***
Kusan mintuna uku tana zaune a dining tana ta juya cokali a cikin kofin shayin, amma ta kasa Wagawa ta sha ko da sau Waya, sai zancen zuci take. Jin an dafa ta ne ya sanya ta Wago a hankali ta kalli ammi, a take ta fara ?a?aro murmushin da bai wuce iya leSenta ba.
Ammi ta ja kujerar kusa da ta iman, ta zauna ta ce "Autana, ko ban tambayeki ba na san abun da ki ke ji, kuma na san ke mai juriya ce, dan haka kar ki saka maganganun da wambai yayi a ranki, ki manta da komai, ki mayar da hankali a kan karatunki, da kin kamma sakandare, zan turaki Mexico wurin laila, ki nutsu ki yi karatunki a wurinta, kuma in sha Allah zan sama miki miji na gari, mai tsoron Allah wanda zai ri?e mini ke tsakani da Allah"

Iman ta rungume Ammi ta ce "Ni dai a'a ammi, zan zauna a tare da ke, bana son mu rabu, zan cigaba jure komai in rayu a kusa da ke".

Ammi ta yi murmushi ta ce "Duk abun mutum dai dole sai aure ya rabamu, watarana sai mutum ya tafi gidan miji"

Iman ta ce "Sai mu tafi tare, duk wanda zai aureni, sai ya yi wa ammina nata Wakin".

Yana sanye da farar jallabiya, ya Wora rigar sa?i ta sarauta, da farar hula, yana tsaye yana kallonsu, ya Wan yi gyaran murya, hakan ya sa suka Wago suna kallonsa.

Ammi ta ce "Ina zuwa haka?"

Ya gyara agogon hannunsa ya ce "Zan je gidan turaki ne in gaishe shi".

"Amma ina fatan ba wani abun zaka je ka gaya masa ba, ka tayar masa da hankali?"

Takawa ya girgiza kai alamar a'a, iman ta ce "Yaya a dawo lafiya".

"Allah ya sa, ki kula ki sha magungunan ki a kan lokaci".

Ta jinjina kai ta ce "In sha Allah" daga haka ya fice daga falon.

"Ammina, bari na je na sha magani na Wan kwanta".

Ammi ta ce "To babu laifi, amma dan Allah kar a je a zauna ana tunani, idan na gani ba zan ji daWi ba".

Iman ta yi murmushi ta ce "Ba zan yi ba in sha Allah, in dai kina nan Ammi wane tunani zan yi?" Tayi maganar tana mi?ewa tsaye tana yi wa Ammi murmushi.

Ko da ta je Wakinta, ta tarar da baba uwani tana ta yi mata bincike bincike.

"Baba uwani" ta kira sunanta a razane ta waiwayo ta kalli iman ta ce "A'a uwar Wakina kin shigo?"

Iman ta ce "Eh, amma me ki ke nema ne?".

"A'a babu abun da nake nema, baki gani ba, gyara Wakin nake yi, ke da ba lafiya ba, kaye-kaye nake yi miki ai".

"Amma baba uwani na sha gaya miki, gyaran Waki ba aikinki bane ba, ya zaki din ga wahalar da kanki da yawa haka, kiyi wancan aiki kuma ki zo ki yi wannan".

"To imanuwa idan ban yi miki ba wa zan yi wa, kuma gashi ba cikakkiyar lafiya ce da ke ba, na san sai ki ce zaki yi da kanki ma".

Iman ta girgiza kai ta ce "Kar ki damu baba uwani, ki yi tafiyarki kawai, za a gyara Wakin ma ai babu datti, ina son in Wan kwanta ne".

"To Shikenan babu laifi, ki huta lafiya"

Iman ta bi bayanta da kallo, daga bisani kuma ta je ta nemi wuri ta kwanta.

***
Cikin ?osawa take wayar, cikin yanayi mai kama da faWa-faWa "gaskiya Khalifa na gaji da gafara sa ban ga ?aho ba, ai yakamata ace zuwa yanzu result ya fito".

"Ke duk result Win da ki ka gani bai yi miki ba, wanne ki ke jira? Meyasa kin fiye wutar ciki ne?"

Samha ta ce "Au haka ma zaka ce, ni na kasa gane wannan yawon da hankali, ni fa na fara jin tsoro".

Dariya Khalifa ya yi ya ce "Haba jaruma, wane irin tsoro kuma? Ai mun yi kaso mafi yawa na aikin, sauran ke zaki yi wa kanki fighting, ki bi komai a hankali, idan ki ka yi gaggawa aiki zai iya kwaSe miki, dan ni babu ruwana. Nan ba da daWewa ba, zaki ji labari mai Wan karen daWi".

Ta yi ajiyar zuciya ta ce "Shikenan, Allah ya sa". Ta ajiye wayar ta yi shiru tana tunanin maganganunsa.

"Anty Samha, Anty Samha!"

Waiwayowa Samha ta yi ta kalli yarinyar a Wan hasale ta ce "Lafiya ki ke yi mini wannan kiran haka?"

"Anty Samha kin gan mu, zuwa muka yi baki yi murna ba?".

"Na ji, jeki wasanki, idan na fito ma gaisa"

Yarinyar ta Wan Sata fuska ta ce "Shikenan, naga uncle takawa ya zo, bari na je na gishe shi".

Da sauri Samha ta ce "Jannah, bana son shirme da gaske ki ke yi ko kuwa?".

"Wallahi da gaske, ga motarsa can da hadimansa, yana wurin Baba suna gaisawa"

"Shikenan, na ji jeki maza" janna na fita samha ta tashi ta canza kaya, ta hau feshe-feshen turare.


Takawa yana jin daWin mu'amala da turaki, dattijon akwai nutsuwa da kuma dattaku, ba shi da hayaniya sam balle faWa.
Sun daWe suna hira, sai da takawa ya fara shirin tafiya sannan turaki ya ce "Amm..wato akwai maganganu da muka ji suna ta yawo a kanka, a cikin masarautar nan, sai dai bamu yanke maka hukunci ba. Maganganu ne marasa daWi da maimaita su ma bashi da wata fa'ida, amma duk da haka zamu jadadda, a din ga kula a ?ara kiyaye martabar addini da kuma al'ada, ba zamu so zancen nan ya je kunnen mai martaba ba, mussaman yadda ake ji da kai, yake sonka, muna ta ?o?arin da?ile jita-jitar, mun sani shaye-shaye ba halinka bane ba, dan da kana yi, zamu gane, amma a cigaba da kiyayewa tare da ri?e addu'a".

Adam yayi wata irin nannauyar ajiyar zuciya ya Wan risuna ya ce "Za'a kiyaye in Allah ya yarda, Allah ya ?ara maka lafiya, zamu wuce".

"To madalla, Allah ya tsare ka isar da gaisuwata ga mahaifiyarka, ka ce kwana biyu bamu ga aiken mutan daji ba ma'abota nagge" yayi maganar a nutse cikin sigar barkwanci.

Takawa ya Wan murmusa, tare da du?awa daga nan ya tashi ya fita.

A falo ya tarar ana ta shirya abinci, Janna ta ?araso gabansa ta risuna ta ce "Barka da wannan lokaci uncle".

"Barkanki dai janna, kwana biyu bana ganinki, ya makaranta?"

"Lafiya ?alau"

Ya ce "Masha Allah". Yana Waga kai ya yi tozali da matar da ya tsana a duniya, mahaifiyar su Jamil, wato mama, bai san ya aka yi suka san ya zo ba, dan ta ?ofar baya ya shiga sashen turaki, ya nemi ayi masa iso.

Ta washe baki ta ce "Takawarka lafiya toron giwa, gaba salamun baya salamun, galadima magajin galadima, da haka za a wuce ban san an zo ba? Ai yakamata mu gaisa ko".

"Ai ban zaci idonki biyu ba, barka da wannan lokaci" yayi maganar yana Wan risunar da kansa ?asa.

Kan ta amsa samha ta fito tana murmushi "Takawa, yau kai ne a gidan namu? Zaka tafi babu ko sallama da mun yi faWa da kai kuwa" wasu irin matsatsun kaya ne a jikinta riga da skirt, ilahirin surar jikinta ko ina a matse.

"Ku yi mini afuwa, dama ina da niyyar shigowa".

Mama ta ce 'Amma na ga kamar kana shirin tafiya, da ka yi Wan waken zagayen, ga abinci nan na saka a kawo maka ai".

"Ayi mini afuwa sauri nake ne, ana jirana, zan sake yin zuwa na musamman na barku lafiya" bai ma tsaya ba balle ya ji mai za su sake cewa ba ya fice.

***
?an ?ura mata ido yayi, bacci take kamar babu rai a jikinta, yanzu babban fatansa ya san daga in da take a nemo 'yan uwanta, su zo su san abun yi a wanke mata wannan dattin na jikinta, ko ita ma ta samu ta ji daWin jikin nata.

A hankali ta buWe idonta, ta Wan motsa jikinta da yake ta yi mata azabar ciwo.

Ya ce "Alhamdilillah, kin farka?"

Ta yi masa ?uri da ido tana kallonsa.

Ya dur?usa a gaban gadon ya ce "Ki bani lambar wayar wani a gidanku, a sanar musu kin dawo".

A hankali ta buWe baki ta ce "Haka muka yi da kai?"

Ya ce "Me fa?".

"Ina Wana?" Ta tambaye shi.

"Yana sashin jarirai ana kulawa da shi, kin san ya galabaita".

Rumaisa ta ce "Lallai baka sanni ba, ni fa a kan yaron nan, sai na tayarwa da kowa hankali, a bani Wana"
Zai yi magana wayarsa ta fara ringing, ya ciro wayar daga aljihunsa, ya kalli screen Win wayar ya ce "Jarababbe, na san na shiga uku da masifarka yau".

Ya Waga wayar ya saka a kunnensa ya ce "Ya?".

"Abun da ya kamata ka ce mini kenan?".

Bashir ya ?ara nutsuwa ya ce "Sorry man, na san na yi maka laifi, am sorry for that, wani emmrgency case ne ya faru, na bayar da taimakon da zan iya, yanzu haka ina Asibiti wata yarinya na tsinto a katsina ta kuSuta daga hannun 'yan bindiga".

"Ina ruwana, ta ina hakan ya shafe ni? Ni abun da ka yi mini ka kyauta kenan? Na rantse da Allah muka haWu sai ka gane baka da wayo".

Ruma ta yi ?uri da ido tana sauraren muryar da ko daga maye ta farfaWo, ba ta manta mai ita ba.

Ayshercool
08081012143


*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR? DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*
*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ?URAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHE?I KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI*
*SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*

*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*

=?I? *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*

*1.? Supplements na gyaran jiki ciki da waje*

*2.?? Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*

*3.? Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*

*4.? Supplements na karawa fata kyau da sheki? glowing skin*

*5.?? Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*

*6.?? Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*

*7.?? Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*

*8.? Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*

*9.? Supplements na karin ni'ima

44 / 61