Kanwar Maza 1&2 Complete Hausa Novel

Author :  Ayshacool Category :  Love

Chapter   51 / 61

150K to 153K   out of 182.7K words

mama ta ce "Ashe ka zo, na je sayo mata magani ne a waje"

Adam ya ce "Eh na zo, ban jima ba, amma ku din ga kai takardar pharmacy zasu baku ba wani abu".

Mama ta ce "A'a basu da shi ne, ai yakamata muma mu din ga taSukawa, masu shagunan ne ma basu fito ba, saboda ha?ar?arin da take kuka da shi, ya sanya na fita dubawa".

Adam ya karSi takardar hannun mama, ya Wau hotonta, ya kalli mama ya ce "In anjima Bashir zai zo, zai taho da maganin sannan ya kai ku wurin X-ray Win".

Mama ta girgiza kai ta ce "A'a, mun gode Wawainiyar ta yi yawa, hakan ma Allah ya saka da alkhairi yayi maka albarka, ka bari kawai wannan zamu yi ba zai gagara ba da yardar Allah"

"Nima Wan ki ne, ba zan ji daWi ba idan ki ka nuna ba kya son na yi muku abu"

Tsidik ruma ta sanya baki ta ce "A'a bama so, yaya Abubakar zai zo su kai ni, idan ma wayo kake yi mini na fika wayo in gaya maka" ta yi maganar tana harare-harare.

Da ido Waya yayi mata wani irin kallo, mama kuma ta yi mata da?uwa ta ce "Ke bana ciki da rashin hankalinki, sa'anki ne ko wani ya saka baki da ke? Kin ma taSa yi masa godiyar Wawainiyar da yake da ke?"

Ruma ta yi shiru tana basarwa, kar mama ta cigaba da yi mata faWa a gabansa ya rainata.

Huzaifa ne yayi sallama da kwandon kayan abinci, suka amsa masa bayansa kuma Gwaggo ce da lawisa.

Nan suka zauna suna gaggaisawa, Huzaifa ya ?arasa ya karSi Mahmud a hannun takawa ya ri?e hannun jaririn ya ce "Mai sunan babanmu, kana lafiya?" Yayi maganar kamar jaririn zai amsa masa.

Takawa kuwa bin su yake da ido, lawisa ma ta bi Huzaifa tana cewa ya bata ta Wauke shi.

Adam ya tashi yayi musu sallama ya fice, tabbas ranar da zai karSi jaririn nan akwai daru, mussaman a wurin uwar ri?onsa rumaisa, yarinyar da ta riga ta fara shi kai bango saboda halinta.

***
"Ammi kin yi shiru baki ce mana komai ba"

Ammi ta ce "To Nusaiba me zan ce muku?"

Iman ta ce "Ammi kina Soye mana abun da yake faruwa, amma gaba Waya yanayinki da na takawa a 'yan kwanakin nan ya tabattar da akwai wani abu a Soye, bama jin daWin yanayin nan sam".

Nusaiba ta ce "Ni fa ina daf da sanarwa Anty laila, wata?ila ki gaya mata meke damunku ku ka ?i gaya mana"

Ammi ta numfasa ta ce "Kar ki kuskura ki haWa ni da laila, koma menene dole zaku ji, amma ba yanzu ba"

"Yanzu Ammi haka zamu cigaba da kallonku a haka, ba fa haka muka saba rayuwa a tsakaninku ba, taya zamu yi adopting hakan lokaci guda, ammi walwalarki ce fa tamu" Nusaiba tayi maganar kamar za ta yi kuka.

Iman kuwa tuni idonta ya tara hawaye ta ce 'Ammi ko dai nice, idan saboda ni ne, ki kai ni Gombe can family house Win ku, zan zauna, kuma duk wanda ki ka zaSa mini zan aure shi, amma dan Allah ki cigaba da walwala muna ganin murmushin ki"

Tausayin Iman ya kama Ammi, ya kamo hannun iman ta ce "Haba iman Wina, ki na tunanin akwai wani ?alubale da zai ta so na rabu da ke ne? Kar ki kuma wannan maganar, wani abu ne yake faruwa daban, amma komai zai daidaita in sha Allah".

"Ammi wai muma 'ya'yanki baki yadda da mu ba, muma munafukai ne kenan yaya takawa ne kawai mai iya ri?e sirrinki?" Nusaiba ta yi maganar har cikin zuciyarta.

Duk da halin da Ammi ke ciki, sai da Nusaiba ta bata dariya, ta girgiza kai ta ce "Ba abun da ku ke tunani bane ba Nusaiba, wata yarinya aka tsinto a katsina da jariri" sai kuma ta yi shiru.

"Ammi to meye haWin hakan da damuwar da kuke ciki?"

Ammi ta ce "?an takawa ne"

Nusaiba cikin rashin fahimta ta ce "Wane takawan? Ta ina za a tsinto yaro a katsina kuma ya zama Wan sa?"

"?an sa ne" Ammi ta basu amsa.

Iman ta ce 'Amma Ammi, ta yaya?"

"?an Aisha ne, ta kawo Wan kwalinta da gwala-gwalanta"

Nusaiba ta Wan dafe goshi a rikice ta ce "Ammi kin hargitsani ban gane ba, ta yaya Anty Aisha da take Saudiyya za'a tsinto Wan ta da Wan kwalinta a Nigeria kuma a katsina, anya ba ?arya yarinyar take yi ba, ko wani abun ake shiryawa ba"

Hawaye ya cika idon ammi, ta Wauki wayarta, ta buWe ta nemo hoton jaririn ta mi?a musu.

Cikin tsananin mamaki suke kallon hoton, babu in da yaron ya bar Adam saboda kamanni.

Iman ta ce "Ammi, ni fa haryanzu ban gane ba, a ssudiyyan ta haihu ko kuma yaushe ta dawo Nigeria har aka tsinci jaririnta, ita tana ina?"

Nan Ammi ta warware musu komai, kamar yadda takawa yayi mata bayani.

Nusaiba ta dafe kai ta fashe da kuka ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Ammi yanzu mai za'a cewa mai girma turaki, tayaya za'a warware wannan lamari? Anty Aisha a hannun 'yan bindiga tsawon wannan lokaci babu wanda ya sani? Kuma Ammi ki ke Soyewa, idan zancen ya Sullo ta wani wurin daban fa, kar ki manta ba'a san da cikin nan ba, kuma cewa aka yi zata ?aro karatu, aka yi ta surutu a kai, tayaya za a dawo ace ba ?aro karatu ta tafi ba, har ta je ta dawo an saceta ya haihu sai Wa da Wankwalinta da gwala-gwalanta, ana ma da tabbacin tana raye?"

Gaban Ammi ne ya sake faWuwa, jin abubuwan da Nusaiba ta faWa, take hawaye ya fara gangarowa daga cikin idon Ammi.

Iman ta ce "Anty Nusaiba, komai da muhallinsa, kan ?alubalen ya zo, za a nema masa mafita, wannan maganganun naki zasu sake jefa ammi cikin damuwa"

Iman ta dubi Ammi a tsanake, ta fara goge mata hawayen fuskarta ta ce "Ammina, ki yi ha?uri ki kwantar da hankalinki, duk wani surutu da ?azafi da zs ayi mana, ba zai kai wanda aka yi mana a baya ba, na san da tashin hankali, amma ammi ba zaki taSa yanke hukuncin da zai cutar da wani ba balle mu. Ki na ji ammi ?addarar haihuwar yaron nan ce ya sanya anty aisha dawowa ?asar nan, kuma suka Soye miki, duk da yadda suke biyayya ga umarninki, kar ki Sata ranki ammi,? kin san addu'a da ki ke yi mana ce ta zama katanga daga dukkanin sharri. In sha Allah mai girma turaki zai fuskance ki. An tambayi yarinyar ina Anty Aisha take?".

Ammi ta yi ajiyar zuciya ta ce "Haryanzu fama ake ba ta yi magana ba tukuna".

"To shikenan, in sha Allah za ta yi magana, Sai a bi komai a hankali Allah ya sa tana lafiya, shi kuma jaririn Allah ya raya shi" iman ta sake Waukar wayar Ammi, tana kallon hoton jaririn.
Nusaiba ta ce "Ba wai tayar muku da hankali zan yi ba, amma kar ku manta masarautar nan ba a iya samun bala'i ba, idan aka sako mutum a gaba da baki da surutu sai zaman garin nan ya nemi ya gagare shi".

Iman ta ce "Haka ne, amma in sha Allah babu abun da ya gagari Allah, Addu'a zamu du?ufa babu dare babu rana. Amma Ammi yaushe zamu je asibitin mu ga yaron muma?".

Ammi ta ce "Ba yanzu ba, ku Wan bani lokaci, bana son mutanen gidan nan su fuskanci wani abu tukuna"

Haka suka cigaba da tattaunawa, sai dai Nusaiba ta kasa magana domin kuwa ta riga ta gama karaya.

****
?aton katafaren office ne, mai Wauke da duk wani kayan alatu na jin daWi da more rayuwa, Senator Usman wakili na zauna a Waya daga jerin kujerun office Win, sai kuma ba?onsa da yake zaune a kan kujerar da take fuskantar sa.

"Kana Waya daga cikin makusantan wancan yaron, da ya dage kai da fata sai ya ga bayana, sai dai kuma kwana biyu na ji shi shiru, duk na gama duk wani shiri da zan yi maganinsa, ko kuma akwai wani abu da yake ?ullawa da ban kai ga sani ba, kar yayi mini bazata".

"Ranka ya daWe shi Wain banza ja da ikon masu ?asa? Ku ne fa ?asar nan yadda ku ka dama haka ake sha, shi da duk masu goya masa bayan gayyar rashin sanin ciwon kai ce, dan tabbas manyan ?asar nan akwai masu goya masa baya, wanda nake kyautata zaton 'yan adawarka ne".

Wakili yayi murmushi ya ce "Ba abokan adawata bane ba, domin abokan adawata muna aiki tare ne, mabiya kawai muke rainawa hankali".

"Haka ne YallaSai, amma a yanzu haka dai, bana tunanin wani shiri yake yi, dan a 'yan kwanakin nan akwai abun da ya Wauke masa hankali, ko office bai fiye zuwa ba, ya ce bashi da lafiya, amma babu tabbas a maganar ta sa"

Wakili yayi murmushi ya ce "Yaro bai san wuta ba sai ya taka, shikenan ka cigaba da sanya mini ido a kan sa, da kawo mini rahoton duk abun da yake ciki, sannan zamu cigaba da shirye-shiryen tsayar da khalifa takarar gwamna, shi ma ba zamu baro ya Sata masa suna ba".

"Amma ranka ya daWe, na ji wancan satin majalisa ta naWa kwamiti, domin bincikar gaskiyar abun da hukumar dss suke zarginka da shi, ya za'ayi da wannan"

Wata iri dariya wakili yayi ya ce "Duk saSatta juyatta ne na siyasa, domin juya tunanin talaka baibai, ka san shi talakan Nigeria idan har zai ci ya ?oshi, duk abun da zaka Wora shi a kai zai bi a haka, babbar damuwar Wan Nigeria ya ci ya ?oshi ne, daga haka ba shi da wata damuwa da yadda abubuwa suke wakana, suma Dss Win muna nan zamu yi abun da ya dace a kan su"

Mutumin ya jinjina kai ya ce "Yanzu ranka ya daWe wannan kwamitin da aka naWa na binciken shi ma plan ne?"

Kamar mara imani haka wakili ya sake ?ya?yacewa da dariya ya ce "Ka je ka cigaba da yi mini aiki, nima zan yi amfani ?arfin kujerata da faWi a ji na ?asar nan, na cika maka naka burin".

Risunawa mutumin ya yi yana jinjinawa wakili yana faWin "Allah ya ida nufi, wakili na kowa"

Yayi maganar yana kamabama wakili, yayin da shi kuma yake ta SaSSaka dariya.

***
Kamar yadda Adam ya faWa, da azahar bashir ya zo, zai kai rumaisa wurin X-ray, amma mai sunan baba ya ce bai yarda ba, su zasu kaita kar son banzan na su yayi yawa.

Bashir cikin mutuntawa ya ce "Haba YallaSai, rumaisa fa ta zama ?anwarmu mu ma, ko ma in ce maka 'yar mu, duk abun da muka yi mata bamu faWi ba, ka duba girman aikin alkhairin da ta yi mana, ai tafi ?arfin abun da muke yi mata a wurin mu, dan Allah kar ka damu, wallahi ba son banza bane, idan dai har kuWi ne, akwaisu adam ba shi da matsalar su, ku kwantar da hankalinku, dan Allah ka bari a kaita".

Mai sunan baba ya ce "Wanda ku ke yi mana, da wanda ku ka riga ku ka yi mana ma mun gode sosai, Allah ya saka da alkhairi, amma muma a matsayin mu na ahalinta yakamata mu tagaza".

Bashir ya Wan langaSe kai ya ce "Zaku ja mini magana a wurin uban gidana, ga kuma uwa uba Ammi, ba za ta taSa jin daWi ba, sun Wora ni a kan kula da komai, dan Allah ku yi ha?uri wallahi baku da wata damuwa a kan hakan, Waukar Wawainiyarta ba yana nufin gazawarku bane ba, yana nufin nuna godiyarmu da jin daWinmu ne a gareku, da yaba karamcinku, duk da mun san ba biyanku zamu yi ba".

Abubakar ne ya ce "Shikenan Wan uwa babu damuwa, Allah ya saka da alkhairi".

Bashir ya ce "Yauwa Wan uwa Amin, ku gama kintsawa sai a fito da ita ga mota can a waje" yana gama maganar ya fita.

Mai suanan baba ya ce "Malam wannan wane irin abu ne, shikenan sai mu zuba musu ido suna Wawainiya da mu, bana son nan gaba su yi amfani da wannan damar, su ce zasu juyamu ka san ba zai yiwu ba".

Abubakar ya ce "Haba dai, in sha Allah babu abun da zasu yi".

Sai da rumaisa ta tabattar da mama ta goya Mahmud, wanda take wa la?abi da Sabir, ta ce saboda ha?urin yaron take kiransa da sabir, tun da suka baro daji bai fiye kuka ba, ba kamar Wan wata malamarsu ba jarababbe mai kukan masifa.
Suka Wunguma suka tafi kai rumaisa x-ray, mama na ta fatan Ubangiji Allah ya sa lafiya babu wata matsala.

***
Adam ya idar da salla yana zaune a kan sallaya, yayi shiru ya rasa abun da yake yi masa daWi, babu tsammani ya ji an turo ?ofar bedroom Win sa.
Jabir ya gani, ya shigo bakinsa Wauke da sallama.
Ya amsa masa a ciki, yau ya manta bai yi wa masu gadi warning na kar su bar kowa ya shigo ba, koma yayi musu ya san basu isa su hana Jabir shigowa wurinsa ba.

"Adam, wai ina ka shiga ne a kwanakin nan, na zo gidan nan ba adadi, bana samunka idan na je can gida ma baka nan, ina ka shiga haka?".

"Ina nan" ya faWa a ta?aice.

"A'a, Wan tsaya meyake faruwa ne, ka wani rame, ga fuskarka duk ta kumbura har idonka, menene?"

Tashi Adam yayi ya ninke sallayar, ba tare da ya kula Jabir ba.

"Adam magana fa nake yi maka, ka wani shareni, ni ne fa nake yi maka magana, meya sameka haka?"

"Idan ka tashi tafiya, ka sanarwa masu gadi, kar wanda ya sake zuwa wurina" yayi maganar yana ?o?arin hawa gadonsa ya kwanta.

Ture shi jabir yayi ya tsaya a gabansa ya kalleshi ya ce "Kalleni, da Jabir kake magana, har akwai wani abu da kake Soye mini a rayuwa? Muna Soyewa juna wani abu ne?".

Adam ya dafe kansa ya zauna, yana ajiyar zuciya, ya dubi Jabir ya ce "J, gaya maka matsalata ba shi ne maganinta ba, ka yi mini addu'a kawai".

"Mu kan tattauna abubuwan da suke damunmu a tsakanin mu, ko da bamu da mafita, sai dai hakan yana ?ara mana yarda da juna da jin matsalar Wayanmu ta dukkaninmu ne, dan haka babu bu?atar Soye mini komai".

Adam ya kama hannun Jabir, suka zauna a tare, ya kalli Jabir ya ce "Ha?i?a ka tuna mini abun da na kusa mantawa, tabbas damuwar Wayanmu, ta dukkaninmu ce, duk da ina ta Soye abun, ban bari kowa ya sani ba, amma a kowane lokaci na san dole komai zai fito, amma a yanzu ku Waga mini ?afa please ".

Jabir ya jinjina kai ya ce "Shikenan" ya fice ya bar Adam, da ganin s yadda ya fita Adam ya san bai ji daWin abun da yayi masa ba, sai dai shima dole ce babu yadda ya iya.

Sai daf da magariba sannan Bashir suka dawo da rumaisa daga wurin X-ray, yanzu tana iya taka ?afafuwan ta sannu a hankali.

Sai bayan sallar magariba, sannan Bashir ya yi musu sallama, mama ta yi ta masa godiya da sanya albarka.

Daga nan asibitin bai wuce ko ina ba, sai gidan Adam, ya tarar da shi ya dawo daga masallaci sannan, lokacin an yi sallar isha'i.
Bayan sun gaisa Bashi ya ce "Yauwwa, mun je an yi mata hoton, likita zai ganta gobe in Allah ya kaimu, sannan ya duba idan da yiwuwar a sallameta"

Adam ya Wago ya kalleshi ya ce "Babu in da za a sallameta sai ta faWi in da matata take, ko na sanya a tsareta"

Bashir ya girgiza kai ya ce "No, Adams, a hankali zamu bi ta, duk da muna cigaba da Sata lokaci, kuma can katsinan ma, babu wani cikakken bayani, dan haka na yanke shawarar zamu je da police, kai tun da ban san meye a tsakaninku ba, kamar wasu ma?iyan juna kai da ita, za mu je da masu uniform, wata?ila su ta yi musu bayani, yadda ake ciki sai mu san abun yi".

"Zuwa yaushe kenan?"

'Zan yi magana da Hassan, sai muje ko zuwa gobe in Allah ya kaimu da safe ne".

"Wannan shi ne chance na ?arshe, idan har ba ta yi magana ba, zan saka ta yi ta ?arfin tsiya!".

Ayshercool.



*Littafin kuWi ne, ? 500 via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143*

*Paid book ne, ? 500 via 0009450228, aisha adam jaiz bank, sai a tura shaidar biya ta 08081012143, masu bu?atar special kuma, suna iya zuwa arewabooks su yi searching.*



Bashir ya ce "A'a, ba sai an kai ga amfani da ?arfin tsiya ba, zata yi magana a hankali, ?uriciya ke damunta, amma duk da haka kamar akwai wata 'yar tsama tsakaninka da ita, yanayin abubuwan da take yi maka, kamar da gayyya take yi maka".

Adam ya Wan yi guntun tsaki ya ce "Manta da ita kawai, sai gobe in Allah ya kaimu, X-ray Win na ta babu wata matsala?"

Bashir ya ce "Ai na gaya maka sai gobe in Allah ya kaimu likitan zai duba".

"Allah ya kaimu"

Bashir ya amsa da "Amin".

**
Nusaiba tun da ta ji abun da yake faruwa, ta rasa nutsuwarta, ko abincin kirki ba ta iya ci. Yanzu haka tana tsaka da tunanin da ta saba ta ji Iman ta dafata "Anty Nusaiba" Nusaiba ta Wan zabura sannan ta sauke numfashi ba tare da ta ce komai ba.

"Anty Nusaiba tunanin me ki ke yi haka ne?"

"Bari kawai Iman, tun da Ammi ta gaya mana zancen nan, na kasa nutsuwa ina tausaya mana idan zancen nan ya fita, kin san yadda aka samu a gaba da ma a masarautar nan, ?iris ake jira wani abu ya faru, to ga wannan babbar magana gaba Waya na kasa nutsuwa, idan har ba Anty Aisha aka gano ba, wallahi muna cikin tashin hankali".

"Haka ne, amma babu abun da ya gagari addu'a anty nusaiba, kuma babu ta yadda muka isa mu kaucewa ?addara, in sha Allah babu abun da zai faru".

"Iman, na san kina dakewa ne kina ?o?arin kwantar mini da hankali, amma kar ki manta abun da aka gaya wa mutane a kan barinta ?asar nan, kin san yadda aka sako yaya Adam a gaba, yanzu idan maganar nan ta fasu, babu irin sharrin da ba za ayi masa ba ba shi ba har Ammi da mu baki Waya. Shiyasa ni tun farko ban so hukuncin da ammi ta yanke ba, tun da komai mu?addari ne" ta

51 / 61