Kanwar Maza 1&2 Complete Hausa Novel

Author :  Ayshacool Category :  Love

Chapter   21 / 61

60K to 63K   out of 182.7K words

ake nema su biyu, ga garin a tsaye yake cak, sai dai Allah ya iya mana kawai, ita kanta mama ba ?aramin ?o?ari take ba, yakamata ace zuwa yanzu ta fara hutawa, ta sha wahala domin mu rayu mu zama mutane".

Abubakar ya ce "Haka ne, amma komai lokaci ne, daga cikin godiyar da nake yiwa Allah shi ne kasancewar dukkaninmu Allah sa babu wani wanda yake fita ya Wauko mata magana a waje, ko ba komai hankalinta a kwance yake "

"Sai wannan abar" mai sunan Baba yayi maganar yana nuna ruma, da tayi pretending kamar bacci take.

"Ba wani Waukar magana, guda nawa take"

"Kai ba zaka gane ba, da ta je ta karya 'yar mutane a makaranta, sai da aka kusa korarta, har wurin 'yan sanda aka kaita"

Abubakar ya waro ido ya ce "Autar"

"Hmm kai ba ka nan, ba ka san wainar da ake toyawa ba kawai, wannan yarinyar ba ta da kai sam, kullum cikin nemo magana take ana ta abin da za a ci"

"To a daina faWa, gara ayi ta mata addu'a "

Mai sunan Baba ya ce "Ai Addu'ar ce kamar ba ta kamata, duk gidan nan babu mai ibada kamar mama, kuma babu wanda zai yi mata addu'a ta karSu sama da wadda take mata, amma haryanzu shiru, kullum rashin jin ta gaba yake yi, ni tausayi take bani wasu lokutan, tana da zaSe-zaSen abinci, and we can't provide what she wants, kuma ba ta san babu ba, sai ta zauna tana kuka, wai an bata kunu ba suga, ko ba za ta ci tuwo ba, could you imagine?"

Abubakar yayi murmushi ya ce"Allah dai ya yassare mana, in sha Allah za su huta, ita da mama"

Ruma da ta yi bakamm ta na jin su, wani irin tausayinsu ne ya kama ta, wato duk wannan zare idon da hantarar da mai sunan Baba yake yi mata, yana son ta har yana tausayinta haka.

Tana wannan tunane-tunanen har baccin gaske ya yi awon gaba da ita, sai magariba ta tashi, Yaya Abubakar ya tsefe mata kai tas ya taje, dama ya saba yi mata tsifa idan har yana gari.

Duk in da suka gilma sai tayi ta kallonsu cike da jin tausayinsu, tabbas tun da ta buWi ido a duniya, yayyen nan na ta maza kowa ?o?arinsa ya ga ya kawo abin da za a rufa kai asiri, haka mama kullum cikin faWi tashi take.
Ta zubo abincin dare ta zauna tana kallon yadda kowa ke ta walwala kamar ba su da wata damuwa, ta zubawa su Mai sunan Baba ido, da suka zuba Abinci kwano Waya, tausayin Abubakar ya kamata, da tuna yadda yake gaya wa Wan uwansa ya kwan biyu bai ci abinci ba, kuma ya sha garri ba ruwa balle suga, kuma ba wanda ya gayawa.
Ta kalli Abincin gabanta, Usman ya sayo kifi ya Wora mata a kan abinci, kifin da shi bai ci ba, bai kuma bawa kowa ba sai ita, gefe ga ?ullin lemon fata da Aliyu ya shigo da shi, shi ma bai sha ba ita ya bawa.
A hankali ta ture abincin, ta shiga Waki ta zauna tayi shiru, sai kuka wani irin ?auna da tausayin yayyen nata ya kamata.

Babu tsammani ta ga mama ta hasketa da fitila.

"Kukan me ki ke yi a duhu haka, ga abincin ki ba ki ci ba?"

Da sauri ta girgiza kai ta ce "Ba kuka nake ba"

"To me ki ke yi idan ba kuka ba, ?arya nake kenan?"

"A'a mama ni fa ba kuka nake yi ba"

"To meya hana ki cin abinci ki ka dawo Waki ki na kuka?"

Ta girgiza kai ta ce "ba komai"

"Wai ba ance miki batun auren nan wasa bane ba, shi ne ki ka cigaba da takura kanki, ba zaki tashi ki je ki ci abincin ba?"

"Ba magana ake yi miki ba, ko sai na zo kan ki?" Ta jiyo muryar Yaya Umar daga tsakar gida. Jiki na rawa ta taso ta fito.

Cikin haWe rai ya ce "zauna ki cinye abincin nan, sai wani ciwon ya kama ki ki cazawa mutane"

?o?arin kai abincin bakinta take, amma ta kasa kuka ya kuma ?wace mata.

Aliyu ne ya dubeta ya ce "Ko Abincin ne ba kya so, ki ke yiwa mutane kuka? Me zaki ci?"

"A'a zan ci"

"To kukan me ki ke yi?"

"Ku ?yaleni dan Allah, na ?oshi ne" tayi maganar tana share hawaye.

Abubakar ya ce "Ikon Allah, taso dawo nan kusa da ni, zo ki saka hannu mu ci namu abincin tare" ba ta son Sata masa rai, dan haka ta tashi ta je kusa da shi ta zauna, ya dinga Webo abincin yana bata a baki tana karSa yana rarrashinta ba tare da sanin dalilin kukan nata ba, sai dai ba rarrashin da yake yi mata ne ya sanya ta yi shiru ba, hararar da mai sunan Baba ya jefeta da ita ne, ta sanyata haWiye kukan da take yi.

Haka ya dinga lallaSa ruma, da kansa ya gyara mata wurin da zata kwanta, ya saka mata net, har da yi mata addu'a, hakan ya ?ara sanya tsananin tausayinsa a ranta.
Sai da ya tabattar ta Wan nutsu, sannan ya tashi ya fita, Mai sunan baba kuwa sai tsaki yake yi, yana hararar Abubakar, ya san da ya yi wani yin?uri na yiwa ruma tsawa, zasu yi faWa.

Mama har ta manta da batun ruma, ta na shirin kwanciya, ta sake jin sheshshe?ar ruman a cikin net Winta.

Mama ta kuma haskta da fitila ta ce "Ke dan ubanki fito daga cikin net Win nan, ki zo ki gaya mini abin da aka yi miki?"

Ruma tayi saurin goge fuskarta tayi kamar bacci take yi.

A hasale mama ta ce "Ba zaki fito ba sai na zo?" Ruma ta janyo jikinta ta fito, ta zo gaban mama ta zauna, amma ta kasa magana.

"Gaya mini menene kuma? Ko wani ne yayi miki wani abun?"

Ruma ta girgiza kai, "to kukan me ki ke yi wa mutane, ki gaya mini ko na le?a na kira miki dodon naki"

"Kiyi ha?uri, zan gaya miki amma kar ki ce na gaya miki"

Mama ta ce "Ina jinki" nan ruma ta kwashe komai ta gaya wa mama, sannan ta Wora da cewa "Mama Allah ya bamu kuWi, ya horewa su Yaya ya sa kar su daina zuwa makaranta, kuma ni ba sai an canza mini makaranta ba, Allah ya bamu kuWi su daina shan wahala, yayana ya kwana biyu bai ci abinci ba mama, wai an kore shi daga kamfani bai gaya miki ba" ta ?arasa maganar tana kuka.

Jikin mama yayi sanyi ainun, duk wauta sa rashin tunani irin na ruma ashe ta na da hankali wasu lokutan, biri ya yi kama da mutum, Abubakar ya rame amam ya?i gaya mata meke faruwa.

Mama ta yi ajiyar zuciya ta ce "Ruma, kin ga wannan yana Waya daga dalilan da yasa nake miki faWa a kan nutsuwa, ke gaki a gida amma sai abin da ki ke so shi zaki ci, kin ga yadda suke ta wahala da ?o?arin faranta mana, dan Allah ki daina rashin ji kin ji, ki yi ta yi muku addu'a, nima ina yi, yanzu ki je ki kwanta, gobe in Allah ya kaimu kin san zaki tahfiz". Ruma ta jima ta kwant???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?a, sai dai bayan kwanciyarta mama ta kasa barci, sai tunanin yadda za ta Sullowa al'amuran.

*****
Kirarin da Waya daga cikin hadiman Ammi ke ta rangaWawa ne, wadda suke kira da Baba uwani, ya tabattar wa da su Iman da ke zazzaune a falo, takawa zai shigo, nan suka din ga kintsawa, ban da Iman da ta rashe a jikin Ammi, suna hira.
Sai dai Adam tare da Jabir suka shigo, hakan ya sanya Iman jan mayafi ta rufe kan ta.
Cikin girmamawa suka gaida Ammi, Jabir ya kalli Iman ya ce "Ke ba ki san girma ya zo ba ne?, Look at you, you are now a big girl duk kin bi kin danne mana Ammi"

"To idan ba ta danne ni ba wa zata danne? ?yaleta 'yar auta ce ai"

Jabir ya yi wani murmushi sannan ya ce "Ammi, biyo takawa na yi, na kawo miki ?ararsa, ko ke zai ji maganar ki"

Adam ya harari Jabir, amma Jabir ya maze ya cigaba da magana.

"Ammi kin san halin ?asarmu sarai, kin san yadda abubuwa ke gudana, duk da kasancewar sa shima wani ne, amma gaba da gabanta ta yaya zai sako Senator wakili da mutanensa a gaba, ai duk wanda ya kwana ya tashi, ya san mutane ne masu Waurin gindi, dan me zai tsananta?"

Ammi ta Wan numfasa ta ce "Ban ?i ta taka ba Jabir, amma abin nan na ga duk sabgar aikinku ce, ni ba komai nake ganewa ba, amma nima ina yawan yi masa magana a kan ya san in da zai din ga kai kansa"

"Yanzu haka Ammi, wai akwa ibom zai je, na rasa abin da zai kai shi wata akwa ibom"

Ammi ta kalli takawa, da ya kashingiWa ya lumshe ido, kamar ba a kansa ake tattaunawa ba, ta yi murmushi ta ce "Rabu da shi Jabir, zan yi magana da shi"

"Ai gara dai Ammi" ya mayar da kallonsa kan Iman ya ce "Iman, Wan sama mini abin sha mai sanyi mana, zan je garden in Wan yi wani aiki"

Haushi ne ya kama Iman, ga masu aiki amma bai saka kowa aikin ba sai ita, ga Ammi a zaune balle ta ce ba zata yi ba.
Haka ta tashi ta tafi kitchen dan haWa masa wani abun.

Adam kuwa Wakinsa ya wuce, ya je ya nemi wuri ya kwanta, dan ya ji kansa ya fara yi masa ciwo, tun wayewar garin yau.

A garden ta tarar da Jabir, tun da ta Sullo ya kafeta da idanunsa, da hakan sai da ya ?ona mata rai, ta yi tsaki.
Tana zuwa ta dire masa jug da kofi, za ta juya.
"?an tsaya mana" ta tsaya cak, sannan ta waiwayo ta kalle shi.

"A tunaninki haka kawai na ce ki zo ki sameni a garden, magana zamu yi".

Cikin yanayinta mai kama da shagwaSa ta ce "Ni uncle J karatu fa zan yi, ina da exams"

Tashi yayi ya zagaya kusa da ita yana kallonta.

"Maganata ba ta da muhimmanci kenan?"

Ta Wan ja da baya ta ce "To ina jin ka"

"Iman me na yi miki ne ki ka tsaneni, ki ke guduna kwanan nan?" Shiru ta yi ba ta bashi amsa ba. Sai gani yayi kamar ta Wan razana tana kallon wuri Waya.

Waiwaya ya yi domin ya ga mai take kallo, Mahmud ya gani a tsaye yana kallonta, gaba Waya ta ruWe.

"Zo nan" Mahmud ya faWa cikin isa yana kallonta.

Jabir ya ce "Kamar yaya ta zo, haka ake yi?"

"Ban saka da kai ba, kar ka Sata mini rai"

Jiki na tsuma, Iman ta sunkuyar da kai ta nufi in da Mahmud ya ke.

"Amma Mahmud kamar ba ka ikon nuna wa iman wannan isar, tun da dai ba wani abu a tsakanin ku"

"Jabir, kafi kowa sanin waye ni, idan ba ka kiyayeni ba, za a ji kaina da kai, ba ruwana da abin da ku ka laSe a lambu kuna yi, abin da ya dameni shi zan yi"

Waro ido Iman ta yi, jin abin da Mahmud ya faWa, sai dai ko kusa ba ta ga fuskar da zata kare kanta ba, haka zalika ba ta da zaSin da ya wuce ta bi umarnin Mahmud.

Ya tasata a gaba har sashin su na Mummy, da Mummy da Fuziyya da ru?ayya duk suna falon sai kuma Samha da dama tun tasowarta kusan kullum tana gidan su.

"On your knees" yayi maganar cikin tsawa. Cikin mamaki iman ta yi abin da ya ce, tana son jin laifin da ta yi.

"Ke saboda baki da mutunci, Mummy ta aika a kiraki amma ki ce ba zaki zo ba aiki ki ke yi wa Ammi, Mummy sa'arki ce?"

Cikin rashin fahimta iman ta ce "Ni kuma? Wallahi ba wanda ya zo ya kirani"

Mummy ta ce "Au iman ru?ayya ?arya za ta yi miki kenan, ai da ka ?yaleta, dama ta daWe tana nuna mini ba ni na haifeta ba, dama ba wani abun ne ya sa na ce a kirata ba, dogwayen riguna ne na saya musu, nace ta zo ta karSi nata".

"Wallahi Mummy ban haWu da Ru?ayya ba jiya, ru?ayya a ina muka haWu?"

Ru?ayya ta ce "Ni zaki rainawa hankali, kina falo fa kina kallo a lokacin ki ka ce mini ba zaki zo ba"

Samha ta girgiza kai ta ce "Yaya Mahmud, ta ina zaka yi tsammanin tarbiyya a wurin 'yar da ba jinin sarauta ba, 'yar karere 'yar ri?o"

Haka suka din ga jifan iman da miyagun maganganu.

Tun da ta taso, ta buWi ido a gidan Galadima, take fuskantar ?alubale sharri gami da makircin hajiya Jamila wato Mummy, makira ce ta gaske.
Suka ?are mata cin mutunci, Fauziyya ta watso mata dogwayen rigunan a jiki, Mahmud ya ce ta yi godiya ta Wauka ta bar sashen.
Ba yadda ta iya, ta aikata abin da ya ce ta tashi ta fita gwiwa a sanyaye.

Mummy tayi murmushi, a ranta ta ce bari mu gani, yarinyar nan zata gayawa wancan mahaukacin ne ya zo yayi hayagaga ko kuwa? Idan har ya zo yayi mana tashin hankali, zan tabattarwa da Samha akwai ala?a a tsakanin iman da Adam, ko kuma in cigaba da amfani da wannan damar, wurin rura wutar ?iyayya tsakanin Mahmud da shi, ina ba?antawa matar nan.

*****
Mama tayi ta faWi tashi, ta tarawa Abubakar kayan abinci na komawa makaranta, wanda sam shi bai san ma tana yi ba, tun da ya dawo yake ta buga-buga yana tara Wan abin da zai tafi da shi, ranar da zai koma mama ta tambaye shi babu wata matsala, ya ce mata eh ai yana da komai.
Mama ta yi murmushi, ta nuna masa watto bagco ta ce ya Wauko, ya duba. Ya Wauko ya duba, kayan abinci ne da ta tara masa.

Ya ce "Mama na gaya miki fa ina da komai, Meyasa zaki takura kan ki?"

"A'a ni ban takura kaina ba, Ubangiji Allah ya bada sa'a ya taimaka" yayi ta yiwa mama godiya, mai sunan Baba ya raka shi tasha, ya bashi dubu biyar, amma sai da suka kai ruwa rana Sannan ya karSa.

Ruma ce ta fito daga wanka, ta tsaya a gaban mudubi daga ita sai pant, tana kallon kanta.
Mama ta kalleta ta ce "Meye haka ne ki ke tsaye tsirara ki nemi kaya ki saka"

Ruma ta juyo ta kalli mama cikin damuwa ta ce "Mama kalleni"

"Na ganki meyafaru?"

"To ba abin da ki ka gani?"

"Ni banga komai ba"

"Mama wai baki ga ?irjina kamar ya kumbura ba?"

Mama tayi murmushi ta ce "Na gani"

"Mama to ya kike dariya, ba alamomin ciwon Cancer bane?"

Mama ta ce "A'uzubil'ahi, ba wannan bane ?irga dangi ki ka fara"

Cikin rashin fahimta ruma ta ce "Wane dangin na ?irga, ni ina zan iya ?irga danginmu?"

"Ba wannan ake nufi ba, girma ki ka fara zaki zama budurwa, fitowa za su yi"

Ruma ta haWe rai ta ce "Ni bana son su fito"

Mama tayi dariya ta ce 'Saboda me?"

"Da nace ina son su fito a daina ce mini ?waila, Yaya Aliyu ya ce gara na yi zamana a haka, ai suma basu da shi"

"To ke namiji ce, da zaki zauna a haka nan gaba da kanki zaki zo kina nema daga baya, ke da a da ki ka ce zaki sayo na sayarwa ki saka"

"To ai yanzu na fasa, gara kar ya fito, idan ya fito fa ba zan din ga yawo ba riga ba"

Mama ta ?arewa ruma kallo, alamomin girma duk sun fara bayyana a jikinta, mama ta numfasa ta ce "Yanzun ma ai na hanaki yawo babu riga"

Ruma ta Wau vest Win ta ta saka, ta ce "Mama kalli fa, kalli yadda vest Win fa tayi mini, to wai tsayi zai cigaba da yi? Ko kuwa?"

"Nima ban sani ba, sai ki bari in sun fito, sai ki ga yadda za su yi, ki dai kula da kanki, ban da wasan banza da maza ko mace, duk wanda yayi miki wasan banza ko ya kai hannunsa jikinki, idan kin zo ki gaya mini, wannan wurin ba wurin wasa bane, gaba Waya jikinki ma al'aura ne abin alkintawa ne".

"Ni mutum ya taSani ma, ba sai na sumar da shi ba"

"Ni dai bana son rashin hankali, ki kula da kanki, zuwa gaba in ga mai yakamata ayi, idan rigar mama yakamata a saya, sai a sayo ki farawa sakawa".

Ruma ta ce "TaS, haka kurum a din ga yi mini kallon 'yar iska"

Mama zata yi magana, usman? yayi sallama ya shigo, ba ta amsa sallamar ba ta ce "Yaya usy, kalleni me ka gani?"

Ya ce "A ina?"

"Au dan ubanki gaya masa zaki kin fara nono, ni yau na ga ta kaina, Innalillahi wa Innalillahi raji'un"
Jin abin da mama ta ce ya sanya Usman ja da baya ya bar Wakin.

(Masu nema daga farko, ku din ga dubawa watpad ko arewabooks)

Ayshercool
08081012143
[01/08, 5:33 pm] JAKADIYAR AREWA: ? ? ? ? ? ? ? ? ?ANWAR MAZA
? ? ? ? ? ? ? ??

*Na Aisha Adam (Ayshercool)*

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES




P19

*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

*SHI YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR? DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA? TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ?URAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN FATA NE, KO INFECTION? KO KUMA SO KI KE FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHE?I KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI,
SANNAN YAN UWA KUSANI DUK SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO*

*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu.*

=?I? *Supplements suna da yawa

21 / 61