Kanwar Maza 1&2 Complete Hausa Novel

Author :  Ayshacool Category :  Love

Chapter   38 / 61

111K to 114K   out of 182.7K words

mini wani abu, yi ha?uri iman, Ammi ban san iman ba ce ki bata ha?uri"

Nusaiba ce ta kalli su Fauziyya da suka yi tsaye suna kallon abun da yake faruwa, ta ce "Anty Samha ba wani abu, zaku iya tafiya".

Samha ta ce "Ba zamu tafin ba, a kan ki muke ko yayanki ne ke kaWai".

Ammi ta Wago iman tana yi mata sannu, iman ta jinjina mata kai.

Ammi ta ce "Ina maganinsa yake? shegiyar gardama irin ta sa Wauko in shafa masa" A hankali iman ta yin?ura, ta je ta saka mukulli, ta buWe wata drower, ta Wauko wata jarka cike da wani mai.

?urii Fauziyya ta yi, tana kallon in da iman ta Wauko maganin.

Adam yayi zuruu da ido yana bin su da kallo, can ya sauke idonsa a kan su samha, cikin tsawa ya ce "Get out" sai da suka razana, kan su yi wani yin?uri ya sake daka musu wata tsawar, cikin rige-rige suka yi waje da gudu.

Ammi cikin damuwa ta ce "Takawa, meye ya Sata maka rai haka ne?"

Kamar mai shirin zaucewa ya hau surutai, "Ni na ce ina son sarautarsu ne? Su barni in ji da abin da ya dameni mana, me na yi masa? Idan ya kuma takura mini zan kashe shi, zan shanye jininsa gara ma ki gargaWe shi ya fita a hanyata".

Cikin tsawa Ammi ta ce "Adam! Kar na sake jin ka furta wannan maganar, wan ubanka ne fa, ban hanaka zancen shan jinin nan ba, sai ka ce maye?"

Nusaiba ta ce "Ammi ba a hankalinsa yake faWar shan jinin nan ba, ki yi masa a hankali".
iman shammace shi, ta shafa masa maganin a fuska, a take ya yi atishawa, sai kuma a hankali ya sulale ya kwanta a ?asa ya hau bacci.

Hawaye Ammi ta shiga zubarwa, iman da Nusaiba suka yo kanta gaba Waya "Haba Ammi, idan ki ka yi kuka mu kuma mu yi yaya, dan Allah ammi ki daina ki yi masa addu'a" Iman tayi maganar hawaye na cika idanunta.

"Iman, ciwon da nake tunanin ya rabu da shi, yana neman ya dawo daga rai ya Saci sai ya hau maganganu, ya fita hayyacinsa, ina zan saka kaina, saboda tsabar neman magani na fara tsoron kar in faWa hannun mushirikai na rasa imanina, sanadin ciwon nan har jita-jita aka din ga yaWawa wai maye ne fa, da wanne zan ji?".

Nusaiba ta ce "Dan Allah ammi ki daina damuwa, Addu'arki fa ba ta tafiya a banza, zai warke in sha Allah "Astagfirullah, Allah ya yaye maka Adam, duk wani hope Wina a kanka yake, ban ce wani ne ya yi maka bs, Allah ne ya Wora maka, ina fatan ya yaye maka"

Suna tsaka da maganar ya fara surutai "Sidi, ku je ku dubo mini yarinyar nan, na gaji a kan me zata din ga zuwar mini a bacci ko in din ga jin kukan ta a kunnena, anya mutum ce? ku je ku duba mini ni bani da lokaci" kamar sun je cinema haka suka zuba masa ido, can kuma ya toshe kunne yana faWin "Ki daina yi mini kuka, bana son kuka, meye ala?ata da ke ne?"

Kallon kallo aka shiga yi tsakanin ammi da su Nusaiba.

A hankali nusaiba ta ce "Yaya maganar wa ka ke yi ne?"

Tun da Nusaiba ta yi magana bai sake cewa komai ba, yayi shiru bacci yayi awon gaba da shi.

***
Idan da sabo ruma ta saba, dan haka yanzu baccinta take cike da mafarkan su Mama da yayyenta, sai dai babban abin da yake addabarta bai wuce ganin mutumin nan da ta tsana a cikin mafarkinta ba, wanda hakan ba ?aramin haushi yake bata.

Yanzu ma mafarki take yi, tana zaune tana kuka a cikin dajin nan, takawa ya Sullo sanye da wasu ba?a?en kaya, ya ratso mutanen da suke wurin, ba wanda yake iya ganinsa sai ita, ya zo ya tsaya a kanta, ya mi?a mata hannu ya ce "Taso mu tafi"

Ta waiwaya tana dubawa ko akwai wanda yake ganin sa, "ba zaki taso mu tafi ba kin tsaya kina kalle-kalle?"

Cikin tsiwa ta ce "Eh ba za'a taso ba Win ni na gayyace ka?" Tayi maganar a fili, tana buWe ido, tsaki tayi tana ?o?arin gyara kwanciyarta ta ce "Aikin banza, ko me yake kawo shi mafarki na oho, idan na kuma ganinka a baccina, sai na yi maka rashin mutunci, dan wallahi sai na rama abin da ka yi mini"

"Ke da waye ne baby rumaisa"ta ji muryar anty aisha.

Ruma ta sake buWe ido ta ce "Ba kowa".

"Haba dai ba kowa, tun Wazu ki ke surutu fa kina masifa a cikin bacci, har wancan yake cewa zai taka ?afarki ki tashi,"

Duk da duhu ne, Ruma ta zare ido ta ce "Haba dai, me nake cewa?"

Aisha ta ce "Ina ta fama da kaina ban ri?e ba, amma dai faWa ki ke da wani a bacci"

Ruma tayi ajiyar zuciya ta ce "Wani mara kirki ne yake zuwar mini, taimako Waya Allah zai yi masa, shine na mutu a wurin nan, amma muddin na fita ko ni ko shi, sai ya gane bashi da wayo"

Anty Aisha ta ce "Subhanallah, me yayi zafi haka?".

"Baki san rashin mutuncin da yayi mini ba, nonona ya taSa mini, kuma mama ta ce duk wanda ya taSa nan wurin na zama 'yar iska cikin shege ne zai fito mini"

"Ya salam, ke ya aka yi ya kai hannunsa nan wurin?"

"Sa wa yayi aka Waukoni, wai zai yi mini warning, ya sha?o hijjabina ya taSa wurin, ni kuwa na din ga bin diddigi sai da na gano gidansu, na je na rubuta masa wasi?ar rashin mutunci na ce a bashi"

"Kai ruma lallai jan wuya ke ce, irin wannan ?arfin hali haka?"

"Rabu da shi, ai wallahi ya bari na fita daga wurin nan zai gane kurensa, Anty Aisha wai ke a wani gari kike?"

"Zan gaya miki ruma, na san zuwa yanzu labari ya samu mijina da dangina abin da ya faru da ni, sai dai ban ga alamar kuWin fansa suke so ba,. Tun da sun ?i yin waya su faWi abin da za s bayar idan.... Ba ta ?arasa maganar ba ta ri?e ?ugunta ta ce "Washhh"

A Wan rikice ruma ta ce "Sannu Anty Aisha, kwanta a kan cinyata ki mi?e ?afar to".

"A'a kar na hanaki bacci baby ruma, yi kwanciyarki".

Ruma ta ce "A'a ai ba zan iya komawa ba kwanta".

A hankali Aisha ta ja jikinta ta kwanta a kan ?afafuwan rumaisa, Ruma ta ce "Bari na yi miki tsifa, kin san ni nake yi wa mama tsifa har kitso na iya" Aisha ba ta hana ruma ba, ta dinga jagwalgwala mata gashi, sai dai duk da mawuyacin halin da take ciki, ruma dariya take bata, dan sam ruma ba ta da rufi.

"Anty Aisha ina son in ga kina dariya, daWi nake ji, tun da ki ka zo wurin nan na rage damuwa duk da ina missing Win gidanmu, in sha Allah idan Allah ya ?addara muka bar nan, ko a wane gari ki ke zan zo gidanki".

Tayi murmushi ta ce "Nima haka ruma, tun da na zo wurin nan, kawai nake jin ki a raina, nake kuma sarawa jarumtarki, sai dai babu lallai na bar wurin nan a raye haka jikina yake bani"

"?aga mini cinyata tun da ba zaki daina wannan maganar ba" ruma ta faWa rai a Sace.

"Haba ruma, ni Win ki tsaya ki ji mai zan gaya miki, idan ma na mutu lokacina ne yayi kuma zan yi shahada". Ruma ta ture kan Aisha daga kan cinyarta ta tashi ta ce "Sai ki je ki yi ta shahadar ai, ba zan sake kulaki ba"

Kowa yayi bacci, sai masu gadi da su ruma ne idonsu biyu, da wani ne yake wannan surutun cikin daren nan, da yanzu ya sha tijara ?ila a haWa masa da duka ma, amma kasancewar rumaisa ce take magana ba wanda ya kulata, dan yanzu da an taSata zata hau kwarmato, idan kuma ba a isa ayu mata wani abun ba kamar tayi musu asiri.

?ayan ya kalli ruma da ta tashi zata canza wuri daga kusa da Aisha, ya ce "yau kun yi faWa da uwar taki ne?"

"To meya dameka ne, ka cigaba da gadinka mana, sa ido sana'ar banza".

"Ni ki ke cewa sa ido sana'ar banza, dan kin ga ana ?yaleki?"

"Ai wallahi ko me zan yi, baku isa ku yi mini wani abu ba, addu'a nake banka muku ta ko ina, in gaya maka, ka san wani abu kuwa?"

"Bana son ji, wuce ki nemi wurin kwanciya".

Ruma ta ?arasa wurin da suke zaune sun kunna wuta, wasu suna shaye-shaye, ta zaune a gefansu ta ce ta yi ?asa da muryarta ta ce"Ka san meya haWani da anty aisha muka yi faWa kuwa? Cewa take yi wai zata mutu ta tafi ta barni, shine ta bani haushi"

"To ina ruwana? Sauran da suka mutu meyasa baki damu ba?"

Ta Wan yi shiru sannan ta ce "Tana sona ne wallahi, nima kuma ina sonta, dan Allah ku saketa, ko ku kai ta asibiti ba ta da lafiya"

Ya ce "Wallahi na yadda addu'a ki ke yi mana, ko kuma daga can gidanku ake yi, ban da haka ba a taSa kawo Wan iskan mutum mara tsoro irin ki ba".

"A'a nifa ba 'yar iska bace, so nake ku kasheni, amma kun ?i ya zan yi, kalli yadda na koma kamar 'yar jari bola, wataran a gidamu mama sai ta yi mini wanka sau biyu a rana, amma yau ban san adadin kwanakin da na shafe ban yi wanka ba, tun ina warin har na daina".

"To ai ko ni ma sai na yi miki wankan, akwai kogi a gaba"

Aisha tana daga can nesa, amma ko ?ifta ido ba ta yi a kan ruma, dan kar wani abu ya faru, ruma tayi zaman dirshen sai zuba take, duk da ba ta san mai ruman take cewa ba, amma hirarta kawai take yi da su hankali kwance.

Ba ta sake bi ta kan Anty Aisha ba, har aka yi sallar asuba, ruma ta yi salla tayi kwanciyarta bacci.

***

"Mummy, wallahi na san in da maganin nan yake, a Wakin iman yake, kuma na sake tabattar da takawa yana nan da wannan ciwon mai kama da na aljanu, mai kuma kama da na hauka"

Mummy ta kalli Fauziyya a tsanake ta ce "Fauziyya, bana son shirme da ?arya fa".

"Haba mummy, kamar wata ?aramar yarinya, kin ga yadda ya sha?e iman a Wakinta kuwa, ya Wage mata riga baki ga ba"

Mummy ta yi murmushi ta ce "Kin tabattar kin ga in da maganin yake? Idan kin tabattar ina son gaya wa uwani ta kawo mini shi, dan da maganin wannan malamin yace zai mini aikin da zai kawo ?arshen hankali a jikin adam, kin ga ba shi ba sarauta kenan"

"Wallahi mummy na gani, sai dai akwai mukulli a drower mudubinta ne"

"Fine, kafin nan, ina son ayi raising issue na cewar yayi yin?urin yi wa iman fyaWe, wani sashin kuma ace an kama shi shi da ita, hakan zai ?ara Sata sunansa, da yi wa zuriyar binta ba?in jini a cikin masarautar nan"

Fauziyya ta Wan yi jimm sannan ta ce "Anya Mummy, decision Win nan naki bai yi tsauri ba kuwa?"

"Ban gane tsauri ba, duk wannan fafutukar ba dan ku nake yi ba, ki shiga hankalinki fa"

"Am sorry, ba zan sake ba duk hukuncin da ki ka yanke dai-dai ne"

Mummy ta yi ?wafa ta tashi ta fice.

***
Habiba ?awar ruma kullum sai ta je layinsu ruma, ta tambaya ko an ga rumaisa, dan tsoron zuwa gidan su ruma take saboda yayyen ruma, tsoro suke bata, ita a da can ma idan ba dole ba ba zuwa take yi ba, balle yanzu da suke cikin damuwa da tashin hankali.
A ?ofar gidan su ruma take tsaye tana le?e.

"Me ki ke dubawa ne?" Ta ji muryar usman.

Da sauri ta waiwaya tana kallonsa.

"Me ki ke yi a nan?" Ya maimaita.

Habiba ta ce"So nake na ji ko zan ji yo muryar ruma ta dawo"

Cikin sanyin jiki usman ya ce "Ruma ba ta dawo ba Habiba, na san kina yi mata addu'a, to ki cigaba kar ki daina dan Allah".

Hawaye ya cika idon habiba za ta yi kuka, usman ya ce "Kar ki yi kuka kin ji, maza tafi gida kar a neme ki kin ji"

Haka nan ta juya ta tafi gida.

***
Ruma kuwa sai da rana ta take, sannan ta tashi daga baccin da take yi,ta tashi zaune ta Waga kai suka yi ido huWu da Aisha, amma rumaisa ta kawar da kanta gefe ta?i kula Aisha.
Sai dai a kallo Wayan da ruma tayi mata, ta hango damuwa a fuskar aishan.

Gaishe da mutanen wurin tayi, ta koma gefe ta tattara duwatsu ta hau 'yar carafke.

"Sannu rumaisa, ke rayuwarki baki da wata damuwa, yau ba kya jin yunwar ne?" Cewar wanda suke kira da sha tara.

"To kun bani abincin ne?"

"Ga abinci nan barde ya kawo miki kina bacci"

"Nifa na gaji da buredin nan ba yau ba gobe... Au ashe waina ce yau" tayi maganar tana murmushi, yayin da mutane suke kallon tsabar samun wuri da ruma ta yi.

Ta koma gefe da nufin ta fara ci, suka yi ido huWu da Aisha ta zubo mata ido,haka nan ruma ta ji jikinta yayi sanyi, dan haka ta tashi ta je gaban Aisha ta zauna ta ce "zo mu ci"

Aisha ta?i magana, kawai ta zubawa ruma ido.

"Mu ci mana" ruma ta sake maganar tana kallon idon aisha, amma ga mamakinta taga hawaye a kwance a cikin idonta.

"To Meyasa kuma zaki yi kuka?" Ruma tayi maganar kamar ita ma ta yi kukan.

"Meyasa ki ke fushi da ni ruma? Na ji daWin kwanciyar da na yi a kan ?afafuwanki, har na ji ina son yin bacci, amma ki ka tashi ki ka barni" tayi maganar cikin damuwa.

Ita ma ruma cikin damuwar ta ce "Ba ke ce ki ke cewa zaki mutu ba, na gaya miki kuma bana so".

"To na daina, amma ki matso kusa da ni in kwanta a kan ?afarki, ko zan Wan ji daWin kwanciyar, kwana na yi ina ciwon baya da ciwon mara, ?afafuwana kamar ana sara mini su"

"To mu ci wainar, sai ki kwanta"

Ta girgiza wa ruma kai, ta karkata da ?yar ta kwanta a kan cinyar ruma, sannan ta kalli ruma ta ce "Har na ji daWi, mu daina faWa dan Allah ?awata, gurin nan yana bani tsoro, da sakani cikin damuwa ke kaWaice ?warin gwiwata, idan na ganki nake jin daWi, kuma ko ina cikin damuwar barkwancinki na sakani nishaWi".

Murmushi ruma ta yi ta ce "Ni wallahi idan ki ka ce baby ruman nan, sai na ji kamar na fara rarrafe da shan hannu, kamar wata jaririyar zanin goyo, wai da mama baby take ce mini da har a yanzu sai na din ga fitsari a wando, zan zuba taSar wallahi".

Cikin dariya Aisha ta ce "Ki gauraya da mai sunan baba ba" tare suka cigaba da dariya, kamar babu abin da yake damunsu duk su biyun. Can aisha ta ce "Wai ina Wan kunnenki, na ga kunnenki babu yari".

Ruma ta haWiye lomar wainar da ke bakinta ta ce "Ai ni ina ga sai salla salla nake saka Wan kunne, nifa kamar su Huzaifa haka nake yawona, dan da za a barni, zan iya yawo da gajeren wando a cikin unguwa, in je ayi mini askina"

Aisha ta girgiza kai ta ce "Ruma idan na biye miki, sai ki saka na fara na?uda yanzu" ta saka hannu ta ciro Wan kunnayen kunnenta, ta sakawa ruma.

Ruma ta yamutsa fuska ta ce "Ni fa bana son Wan kunne, idan suka dameni tsaf zan ciresu na watsar"

"Ruma kin san kuWin abin da na saka miki a kunnenki kuwa? Gold ne tafiyayye daga dubai, dan Allah kar ki yar".

"To ni me zan da shi?" Ruma ta tambaye ta tana shafa kunnenta.

"Bar miki na yi, ga wannan ma, ta mi?awa ruma Wan kwalin kayanta, ta ?ulle wani abu a ciki ta ce "Sar?ar Wan kunnen ce, da zobuna da kuma sar?ar ?afa".

"To su kuma me za ayi da su?" Aisha ta Wan yi shiru, daga bisani kuma ta ce? "Ajiya ce na baki, zan karSa, idan kuma ban karSa ba na bar miki"

"To ni yanzu wannan ajiyar taki, a kaina zan Waurata ko kuma ?uguna zan Waurawa, dan tsaf zan manta ya kama gabansa na kama nawa"

"Amana ce fa, ki kula da su sosai" ruma ta takurawa aisha sai da ta Wan ci wainar nan, amma kallo Waya zaka yi wa aisha ka san bata da lafiya, amma sai ?arfin hali take tana biyewa rumaisa.

A 'yan kwanakin nan kusan kullum, akwai kalar mutanen da suke zuwa wurin nan, wasu idan sun zo su Wauki manyan jakunkuna.
Yau ma wasu ne suka zo a babura kusan huWu, amma su waWan nan sanye da ba?a?en coat, suma fuskokinsu a rufe, ruma ba ta damu da su ba, ta mayar da hankalinta kan aisha, tana fatan kar ?arar baburan nan nasu ya tasheta.

Bayan mutanen sun tattauna da waWanda suka sace ruma, kai tsaye aka nuno musu in da su ruma ke zaune, suka tunkari su rumaisa.

Tsayawa ruma ta yi taga ikon Allah,wurin wa aka zo, wurinta ko kuma wurin Aisha....

Ayshercool


*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR? DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*
*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ?URAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHE?I KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI*
*SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE

38 / 61