Kanwar Maza 1&2 Complete Hausa Novel

Author :  Ayshacool Category :  Love

Chapter   29 / 61

84K to 87K   out of 182.7K words

yake jin muryar tana yi masa gizo, gashi tun daga ranar yau kwanaki huWu kenan, bai sake arba da wani abu da ya shafe ta ba.
Haryanzu zuciyarsa ta kasa nutsuwa da cewar ruma mutum ce, duk da sidi ya tabbatar masa da binciken da ya yi a kan ta da makarantar da take zuwa, wanda makarantar yayi niyyar zuwa, amma suka haWu a hanya.
Tunawar da ya yi cewa yana da tafiya Abuja jibi zai je wata ganawa ta musamman da wasu lawyoyi, tuna hakan ya sanya shi dawowa nutuswarsa, ya bar tunanin ruma ya tashi ya fice.

Gidansu ya tafi, ya je ya samu Ammi dan sanar mata da batun tafiyar sa. Cikin damuwa Ammi ta ce "Ina fatan ba a kan mutanen ne zaka yi tafiyar ba, ka je ka cigaba da bin diddiginsu su illataka ba?"

Takawa ya ce "A'a Ammi, tattaunawa ce da wasu lauyoyi, kwanaki uku kawai zan yi na dawo"

"To Allah ya kaimu, ka kula sosai takawa, ka ri?e azkar sannan ka sanya Allah a ranka, kar saboda kana da matsala da wani ka sako shi a gaba da niyyar fansa, ka saka Allah a cikin lamuranka"

"In sha Allah ammi"

"Allah Ubangiji ya tsare, zaka ci Abincin dare a nan ne, ko kuma gida zaka tafi?"

"Ina da ayyuka a gida Ammi, ku ci abincinku kawai".

"To Shikenan, Allah ya tsare"

Ya amsa da Amin, ya tashi ya fita.

Yana daf da kaiwa in da motarsa take, motar Mummy ta yi parking. Ta buWe ?ofar motar ta fito ta nufi Adam tana wani irin murmushi.

"Manya gatan wasa, a gidan ka wuni ashe, kwana biyu ba ka shigowa mu gaisa"

"Na yi busy ne" ya bata amsa a ta?aice.

"Ashe Abuja za ka tafi, to Allah ya tsare"

?an turus ya yi yana tunani, ya aka yi ta sani? Amma kasancewar ba ya son yin doguwar magana, mussaman da ita, ya sanya bai tsaya bin diddiginta ba, ya buWe motarsa ya shiga.

***
Sarai ruma ta warke, mama ta sake haWa mata kayanta, sai dai dare ya raba, ruma ta na cikin net Win ta tana ta bacci, mama kuma ta zubawa jakar da ta haWawa ruma kayanta, haka nan ta ji ba ta son tafiyar da ruma za ta yi, kuma ba ta ji za ta iya hana tafiyar ba, ba ta taSa rabuwa da ruma na lokaci mai tsawo ba sai wannan karon, gaba Waya jikin mama a sanyaye yake, ba ta da wani kuzari, zuciyarta na raya mata ko ta hana tafiyar da ruma, amma daga ?asan zuciyarta ba ta ji ta yarda da wannan shawarar ba.

Tun asuba ruma ta fesa wanka, sai murna take ba ta taSa tafiya mai nisa da wayonta ba, mussaman barin Kano, mama dai jiki a sanyaye take taya ruma shiryawa, tana yi tana mata nasiha, a kan ta nutsu har su je su dawo, ban da gantali da neman magana.

?arfe goma na safe, suka kammala shiryawa, Aliyu ya Wau jakar kayan, suka tafi, ruma sai Wagawa mama hannu take tana murmushi, yayin da mama ko murmushin ta kasa, ruma ta Wauko wayarta ta wurin Yasir, ta saka a jakarta.
Gaba Waya su kansu sauran yayyen na ta, jikinsu a sanyaye yake, kamar su ce a fasa tafiyar da ita, daga ?arshe da ta gallabe su, suka ce Allah ya raka taki gona.

?angaren takawa ma, yau ta kasance ranar da zai tafi Abuja, ya biya gida ya yi wa Ammi sallama, sannan ya Wauki mai kaishi airport, ya dawo da motar. Sai dai tun a daren jiya yake jin ba ya son tafiyar, duk da ba yau ya fara tafiye-tafiye ba, amma yana jin sa wani iri, kamar akwai wani abu mai muhimmanci da zai yi nesa da shi, yana tsaye yana gyara agogon hannunsa, Ammi sai kallonsa take yi.

Ya kalleta ya ce "Ammi, ya dai na ga kina ta kallona?"

"Haka kawai bana son ka tafi ne, ji na yi kamar na ce ka fasa".

Murmushi ya yi ya ce "Ammi kenan, sai ka ce zan bar gari, saudiyya fa sai da ns kwana ashirin da takwas, kwanaki uku fa zan yi kacal na dawo, ki yi mini addu'a, idan su Nusaiba sun dawo daga makaranta, ace musu na tafi"
Ammi ta jinjina kai ta ce "Allah ya tsare" ya Wau jakarsa ya fice.

Huzaifa da Yasir, sai da suka raka su Aliyu tasha, suka hau mota, Ruma sai Waga musu hannu take, ta na yi musu gwalo, wai ba za a tafi da su ba.

Tun da suka baro tashar suka nufo gida, jikin Yasir yake a sanyaye, Huzaifa na ta magana, amma ya kasa amsa masa.

"Wai lafiya na ji ka yi shiru?"

"Huzaifa, ji na yi ban yarda da motar nan da su ruma suka hau ba"

Ya kalli Yasir cikin mamaki ya ce "Saboda me?"

"Mutanen da suke cikin motar ne ba su yi mini ba sam, ni duk wani iri nake ji a jikina!!!

Ayshercool
08081012143


*Na gamaku da zatin Allah kar wanda ya haWa mini document Win littafina, mallakina ne, nike da alhakin amfani da abina yadda nake so, kar wanda ya juya mini abin ta kowacce siga, duk wanda ya haWa mini document Win littafi ya fitar ban yafe masa ba! Kuma ina fatan Allah ya bi mini hakkina!*
*Paid book ne, 500 ne via 0009450228, Aisha Adam jaiz bank, sai a tura shaidar biya ta 08081012143, wanda suke ba a Nigeria ba kuma, za su iya saya a arewabooks*





Ta yi shiru ba ta ce komai ba, Aliyu ya ce "Magana ake miki, ihun me ki ke yi wa mutane?"
Ta Wan Wago ta kalleshi, idanunta sun yi ja saboda gajiyar tafiya ga bacci da bai isheta ba ga kuma razana da ta yi.

"Mafarki na yi na tsorata"

"Kuma shine ba zaki yi addu'a ba,waye ma ya ce ki kwanta ki yi bacci da la'asar Win nan?"

Gwaggo ta ce "Daina yi mata faWa, wannan ba laifin kowa bane laifin babarku ne, bana tunanin ta na nemawa yarinyar nan maganin tsari, wata?ila aljanu ne ko kuma mayu suka tsorata ta, bana raba Waya biyu suke bibiyarta"

Ruma ta waro ido ta ce "Mayu kuma, ni fa wani mutum nake gani, ki daina tsorata ni"

"Ahaf sai kuma ki yi, ko dai maye ne, ko kuma aljani shi ya sa ki ke ganinsa, kurwarki ya ke son lashews" shiru ruma ta yi tana tunani a kan mafarkin da ta yi.

"Aikuwa sai dai ya ci kansa, ba dai ni ba"

"Tashi kiyi sallar magariba, a samo mini gaushi, na turara miki tsakin kuka da tazargade haWi da turaren mayu, koma menene zai barki, ai kaf zuriyarmu kurwarmu tafi ?arfin maye, aljan kuwa sai dai yayi ya barmu"

Aliyu ya girgiza kai mutanen karkara sun yarda da camfi, kuma ba ka isa ka sauya musu ra'ayinsu ba.

Takawa kuwa a hankali ya gama watstsakewa a kan gadon ba tare da ya motsa ba, a hankali ya furta "Wai me na yi miki ne haka ki ka sakani a gaba, wace irin jaraba ce wannan duk in da na motsa yarinya Waya nake gani, wannan idan har ba aljana ba wata?ila tana da wani mugun nufi a kaina, Allah ya shiga tsakanina da ke".

Rurin da wayarsa ke yi ne, ya sanya ya mi?a hannu a hankali ya janyo wayarsa ya duba, magariba ta riga ta yi, ya tarar da missed call rututu, wanda na Ammi duk ya fi yawa sai na Jabir.

Ammi ya fara kira, bugu Waya ta Waga cikin damuwa ta ce "Ina ka shiga ka ajiye wayarka nake ta nemanka ba ka Wagawa?"

Ya Wan gyara muryarsa ya ce "Ammi na ajiye duka wayoyin ne na fita, shi ya sa".

"Amma bai kamata ka ajiye wayoyi ka fita ba, ka saka hankalina ya Waga sosai, amma ya na ji muryarka a haka, ba ka da lafiya ne?"

Yayi Murmushin ?arfin hali ya ce "Haba Ammi, lafiyata ?alau mura ce ta kamani, da na motsa sai ki ce bani da lafiya?"

"To ai dole sai ina yi ina bin diddigi, tun da ba cikakkiyar lafiya gareka ba, Ubangiji Allah ya tsare"

"Amin Ammi, na gode" ya katse wayarz ya tashi a hankali, ya ji jikin da sau?i yanzu ba kamar Wazu ba, ya lallaSa ya shiga banWaki yayi alwala, ya dawo ya yi salla.


***
Har zuwa dare, ruma ta ?i sakin jikinta, kamar ba ita ce mai shegen surutun nan ba ta bi ta takure a wuri Waya kamar mara kuzari, gaba Waya ji take jikinta babu ?wari. Yaya Aliyu ne suke ta hira da Gwaggo, da wasu daga cikin samarin gidan da suka shigo, duk yadda suka so su yi wa ruma wasa ta kulasu ta?i, ta koma gefe ta takure ta sha kunu.
Cikin damuwa Gwaggo ta ce "Rumaisatuna, wai menene gaba Waya kin ?i sakin jikinki sai ka ce wata ba?uwa, me yake faruwa ne?"

Sheshshe?a ruma ta fara sheshshe?ar kuka.

Gaba Waya hankalinsu ya dawo kanta.

"Menene, me ki ke so?" Ta yi shiru ba ta ce komai ba.

Aliyu ya ce "Ba magana ake miki ba?"

"Gida" ta faWa tana rushewa da kuka.

"To dan ubanki nan a titi kike ba a gida ba?" Aliyu yayi Maganar a hasale dan daga tahowarsu zuwa yanzu, ruma ta kai shi bango.

"Ni mama nake son gani, ka kira mini ita a waya". Gwaggo ta ce "To shikenan, yi shiru a kira miki ita. Ka ga illolin rashin zumunci ko? Yanzu da ana zuwa da ita, yaushe zata yi kuka dan tana cikinmu, ai duk abu Waya ne, amma kalli yanzu kallon ba?i take yi mana, yi maza ka kira mata ita ko ta daina kukan".

Takaici ya rufe Aliyu, kamar ya tashi ya naWawa ruma duka, sai iskanci take kamar wadda aka kawo yaye, ya kira mama a wayarsa, ya jefawa ruma jikinta.

Mama na Waga wayar ruma ta saka kuka, cikin kiWima mama ta ce "Lafiya kuwa ruma, menene?"

"Mama gida, ni ba zan iya bacci ba"

Mama ta ce "Haba ruma, ai sai ki Waga mini hankali, ba kun sauka lafiya ba ko wani abun aka yi miki?"

"Ba ayi mini komai ba, ni kawai gida a kusa da ke zan kwana, kuma ina son in ga su Yasir da Abdallah da yaya usy".

"Ke dai ki na da shirme, to da aure aka yi miki fa, dangin mahaifinku ne fa nan ma gida ne ruma, duk abin da ki ke so za su yi miki, dan Allah ki daina Waga musu hankali"

"To ni gaskiya ki ce a dawo da ni gida gobe, ni so nake na ganki dan Allah".

Mama ta ce "Ke ki mayar da hankalin ki, bana son sakarci fa, meye haka ne ruma, kawai daga zuwa ba?unta ki tayar musu da hankali, ko sai na haWaki da babana?"

Da sauri ruma ta ce "A'a".

"To ki nutsu ki daina yi musu kuka"

Ruma tana share hawaye, wasu na gangarowa???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? ta ce "To, na daina".

"Yauwwa, sannan ki yi fitsari kan ki kwanta, kar ki yi musu fitsarin kwance kin san dai kashedin da na yi miki ko?"

"Eh"

"To ki nutsu, sai da safe ki gaida gwaggon"

Usman ya karSi wayar a hannun mama ya ce "Ke ruma, maman nono za ta baki da zaki din ga kuka ke mama, to idan ma shayar da ke take yau an yayeki"

Cikin shagwaSa ta ce "Yaya ussy".

Ya amsa da"Na'am ?anwar maza".

"Yaya usy ina son in ganka".

"To idan kin gannin lada za a baki? Zan gayawa Ali, idan kin samu miji a nan mun bar musu ke, su aurar da ke".

Aliyu ya fizge wayarsa ya ce "Ba katin banza ne da ni ba, kar Allah ya sa ki daina kukan, dama akwai karnuka da suke yawo a garin da daddare, idan baki nutsu ba, a ?ofar gida zaki kwana".

Gwaggo ce kawai ta din ga rarrashin ruma, ta gyara mata kan gadonta na ?arfe ta kwanta.
Tsananin gajiyar mota, da ba?unta ya sanya bacci kwashe ruma.

?angaren mama ma, hakan take, kewar ruma take sosai, tun yamma su Huzaifa suka fuskanci hakan suke tsokanar mama suna mata dariya, wai yau an Wauke mama 'yar gudaliyar ifrituwarta, duk ta damu.

Mama ta din ga basarwa, irin ko a jikinta Win nan, amma tun da ta ji kukan ruma hankalinta ya ?ara tashi, cikin dare kuwa kasa bacci tayi, sai kallon wurin shimfiWar ruma take yi. Sai yanzu take jin ina ma ba ta bayar da ruma an tafi da ita ba, dan gaba Waya hankalinta ya ?i kwanciya.

***
Samha ce zaune a wani katafaren office, tare da Khalifa wakili, sai juyi yake a kan kujera yana kallonta yana mata murmushi, ita kuwa ta yi tsuru-tsuru kamar Sera ya kwan a gadon kyanwa.

"Ki kwantar da hankalinki mana, babu wani abun damuwa a ciki fa"

"Khalifa, dan Allah kamar yadda muka yi yarjejeniya, tare da yin al?awari a fari, dan Allah kar ka cutar da Adam, ni yanzu haka ma fa a tsorace nake"

Yayi wata makirar dariya ya ce "Lallai kin damu da shi da yawa, kar ki ji komai fa, kin fara naki Sangaren, saura Waya Sangaren suma za su yi nasu role Win "

"Amma haryanzu ba ka gaya mini su waye Waya Sangaren ba, kuma aikin me zasu yi ba su, bayan da fari ce mini kai deal Win ni da kaine kawai".

"Saken da ki ka yi na rashin ba da amsa da wuri ya sanya third party joining deal Win, kuma na ga za su taimaka sosai, shi ya sa na haWaku ku duka a tafiyar, amma ki kwantar da hankalinki ba wata matsala"
Ta yi ajiyar zuciya ta ce "Shikenan, ni zan wuce sai ka ji ni".

Ya ce "To a sauka lafiya, zamu yi magana" bayan fitar Samha Khalifa yayi wata uwar dariya ya ce "Yaro man kaza, zaki gane baki da wayo"

?angaren samha ma bayan fitarta jinjina kai ta yi ta ce "Yaro bai san wuta ba sai ya taka, da na yi achieving abin da nake so, zan nuna maka wacece mace, zaka gane ba ka da wayo, kuma zan gano wanda ka sako a cikin sabgar nan bayan ni, zan baka mamaki".

****
Ko da garin Allah ya waye ma, aka yi alwala aka yi salla, ruma ta gaida wanda ta ga zata iya gaisarwa, ta koma ta yi shiru abun ta.

Lawisa ta dubi ruma ta ce "Sannu, kina bu?atar wani abun ne?"

Ruma a ranta ta ce "Wannan yarinyar kin isheni wlh" a zahiri kuwa ruma ta shareta, dan ita ji take kamar a kan wuta take, ba ta son zaman gidan nan.

Aka yi abin karin kumallo, kunun tsamiya da wainar gero, ga kunun na daka ne, sai ?amshi yake, sai dai tun da Aliyu ya ga an kawo kunu, kuma kunun babu suga yake kallon ruma ya ga, wani action za ta yi, za ta sha ne ta yi kara ko halin za ta nuna.

Ta kalli kofin kunun, ta kalli Aliyu, amma ya kawar da kansa, ya na shan nasa.

Lawalli da yake yayan lawisa ya ce "Rumaisa ki sha kunun mana"

"Bana shan kunu" ta faWa a raunace.

Ya ce "Au mutan birni ba cimarku ba ce ba, Gwaggo dafa mata shayi, bari na sayo madara a shago, a sayo miki burodi"
Dariya ruma ta yi ta ce "Meye kuma burodi, buredi ake cewa ai" karo na farko da tun da ta zo ta yi dariya, gaba Waya hausar ta su wani iri take jin ta.

Shima ya yi dariyar ya ce "To shikenan buredi bakanuwa".

Ta ce "Banda buredi, shayin kawai zan ci wainar geron"

Aliyu ya galla mata harara, ta basar kamar ba ya ganshi ba.

Haka kuwa aka yi, sai da aka samo shayi sannan ruma ta karya.

Gwaggo ta ce lawisa ta zagaya da ruma sashen matan yayyenta su gaisa, su ga ruma.

Jiki na rawa lawisa ta amsa, ta jagoranci ruma zuwa Sangarorin gidan.
Ruma ta sha mamakin waWanda ta din ga gani a matsayin ma'aurata, duk yara da su.

Sai dai Mutanen gidan akwai su da kirki, hannu bibbiyu suka din ga karSar ruma, suna yi mata barka da zuwa.

A hanyar komawarsu sashen gwaggo ruma ta ce wa lawisa "Wai duk wannan sirikan gwaggo ne?"

Cikin jin daWin ruma ta kulata lawisa ta ce "Eh" ruma ta jinjina kai.

Bayan sun koma sashin gwaggo, lawisa ta Wau ni?a za ta kai, ruma ta ce za ta bita. Suna tafe a hankali ruma ta fara sakin jiki da lawisa, ta din ga kallon garin, yayi kyau sosai, 'yan garin ma'abota noma ne.
Duk wanda ya ga Lawisa da ruma sai ya tambaye ta wacece ruma, ta ce musu 'yar uwatta ce. Abin yayi ta bawa ruma mamaki, ita a gida unguwarsu wa ma ya damu da wani, da za a din ga tambayarka waye wannan.

Ko da suka dawo gida ma, ruma a hankali take sakin jiki da lawisa, suka fara aiki tare suna Wan taSa hira.

Wajen sha Waya na safe, lawalli ya Wauki Aliyu a babur Win sa suka tafi can wani ?auye, in da a nan wasu daga cikin gonakin nasu suke, wurin gidan wani kawunsu da suke kira da baba Habu.

Ruma ta zazzage kayan da ta zo da su tana sake ninkewa, bayan ta gama ta Wauko wayar nan ta ta, ta fara kallon hotunan ta.
Lawisa ta zauna a kusa da ita tana le?awa. Gwaggo ce ta kira lawisa, ta tashi ita kuma ruma ta cigaba da kallon wayar.

Hotuna ne da videos da ta din ga yi ciki har da wani sashe na wannan jakar ta bullet da Waya daga cikin mutanen nan ya rataya, sannan a hotunan akwai in da gefen fuskar Waya daga cikinsu ta fito.
Ruma ya ajiye wayar tana tunin wasu abubuwa da suka dabai baye mata kai ta kasa gane kansu.
Bindiga dai jami'an tsaro ne suke ta'amalli da ita, amma ta yaya za ayi ace da saninsu ana shiga da fita da su ba tare da sun tsawatar ba?' ajiye wayar ta yi, tana son ?ara nutsawa cikin tunani, amma kwanyarta ta gaza bata komai.

"Ruma zaki je rafi, muje ki ga ruwa da duwatsu".

Gwaggo ta ce "Ke kar ki kaita ki wahalar da ita mana"

Ruma ta ce "A'a gwaggo zan je" tayi maganar tana mi?ewa tsaye, ta saka hijjabi suka sake fita.

Wani Wan madaidaicin rafi suka je, 'yan mata wasu na wanki a gefe, wasu kuma suna Wiban ruwa. Ruma ta samu na yi, ta din ga Waukar hoto, ta din ga tsalle-tsalle a wurin, yanayin ya burgeta.

Kan wani Wan dutse ta hau, can nesa ta hango wani wuri ba?i?irin kamar an yi gobara. Ta

29 / 61