Author : KHADEEJA CANDY Category : Romance
aka yi aikin idon da ka taba fada min cewar ka yi yar'uwarka alkawari”
Hurriya ta dago ga kalli Hamad ta mika masa hannayenta so take ya taba ta a karo na biyu ta ji idan da gaske dan'uwanta ne. Hamad ya kama hannun yar'uwarsa da ya fi Marmari fiye da kowa ya rike. Sai ta fashe da sabon kuka.
“Ni dai ina so ko da waninka ne aka kawo min a matsayin kai, zan karba kai ne kadai ka rage min farincikina ya cika, ni kadai ce na yarda baka mutu ba Hamad, amman duk haka ganinsa nake kamar ba gaske ba”
“Tun a ranar da da Captain yace min za'ayi wani aiki da yake son ayi tare da ni amman ba zai kawo aikin ba sai a lokacin da zan fara koyon aikin a wannan asibitin sai na kagara na ga haka, da na zo na ga fuskarki sai na ji kamar wata rayuwa ce ta same ni da ba zahiri ba, kuma ya hana ni magana a ranar har sai yau... Kuka nake Captain ya cutar da ni”
“Ban cutar da kowa ba a nan, ni kawai taimako na yi, kuma ba zan amsawa kowa tambaya ba sai a gaban iyaye”
Captain ya fadawa Hamad a tsawace, kamin ya rika fuskar Hurriya ya share mata hawayenta.
“Ya isa haka, yau aka bude idonki i thought hakan zai saka farinciki ba kuka ba, karki janyo min wata matsala please”
Ya rumgumeta a kirjinsa, ita kuma kamar ya karawa kukanta fetir haka ta ji sai ta kara fashewa da kukan sosai.
“Ina son na tafi gida ina son na ga iyayena idan suna raye...”
“Hakan ba zai yiyu ba, sai an dauki permission daga makarantarka hakan kuma ba zai yiyu ba sai da hujja, dole ka kwantar da hankali kamin mu yi tunanin abun da zai fi”
“Ba zan kwantar da hankali ba, 8na bukatar ganin Amma, babu ruwanka da rayuwata you lie to me azzalumi kawai, ka kira min Amma zan yi magana da ita”
Captain ya daka masa tsawa a karo na biyu.
“Ba zaka bar garin nan ba sai da izini, kuma ba zan kirata ba...! And control yourself Hamad na hadeye ka a zuciya Wallahi”
Yadda Hamad din yake ta fada ya kara tabbatarwa da Hurriya lallai dan'uwanta sai dai akwai abun da ita da shi ba su sani ba, waya kawo shi a garin nan? Meya saka ce ya mutu? Ta ya ya hadu da Captain? Kuma me yasa Captain ya boye mata gskiyar har zuwa yau? Ta dago kai ta kalleshi tana jin idonta yana wani dauri kamar zai like.
“Kira min Amma...”
“Toh zan kirata, amman yanzu ki min hakuri mu tafi masaukinmu kim ga Mama Rukayya da Momy Ikilima ma suna waje suna jiranmu! Sai mu magana a masauki zai fi kin ji”
Magana yake mata ta siffar rarashi yana shafa gashinta, sai ta girgiza masa kai ta lake kafadarta daya.
“Aa dan Allah ka kira Amma”
“Okay”
Ya ciro wayarsa ya danna number surukarsa ya aikata mata da kira. Wayar bata dade tana ringing ba Amma ta dauka tana sallama sai da ya amsa sallamar ya gaisa da ita sannan ya mikawa Hurriya wayar. Hurriya ta karba tana kuka
“Hello Amma...”
Hamad yayi saurin kara kunnensa a jikin wayar yana sauraren muryar mahaifiyarsa sai ya fashe da kuka.
“Lafiya Hurriya idon be bude bane?”
“Amma wata gaskiya zan fada miki mai kama da karya, Amma Hamad ne yana raye yana tsaye a gefena yanzu na yi magana da shi kuka ma yake yi Amma Hamad dinki yana raye...”
Amma ta yi shiru for some seconds sannan ta amsa.
“To ba Jamal wayar...”
“Amma baki yarda da ni ba?”
“Na yarda ba shi wayar..”
Hurriya ta mikawa Captain wayar sai Hamad yayi karaf ya karbe ya kara a kunnensa.
“Amma... Amma.. Amma...”
Nan ma Amma bata ce komai ba, domin ba muryar Captain ta ji ba, kuma ba muryar wanda ta sani ba ne, sai dai hankalinta ya tashi sosai tana jin kamar yarta ta samu matsala ne.
“Amma ki ce wani abu dan Allah Hamad ne...”
“Ba Hamad ba dai.... Ko waye kai dan Allah ka bawa Jamal wayar...”
Hamad ya dauke wayar a kunnesa ya mikawa Captain sannan ya nufi kofa zai fice hawaye na sauko masa, Hurriya ta yi saurin sakowa daga kan gadon tana kiranshi.
“Dan Allah karka tafi, dan Allah karka tafi Hamad inda da gaske kai din ne karka tafi dan Allah...”
“Jamal matarka bata da lafiya ne?”
Amma ta tambaya Captain ya sauke ajiyar zuciya.
“Lafiyarta kalau, kuma an yi aikin idon ya bude Alhamdulillah an yi nasara”
“To me yasa take min zan cen Hamad? Ko idonta ya fara ganin fatalwa ne yanzu kuma...”
“Da gaske ne Amma Hamad yana raye, akwai abun da baku sani ba, akwai abun da na boye muku sai a yanxu nake jin lokaci yayi da ya kamata ku san komai...”
“Kai ma baka da hankali ko Jamal? Dana Hamad ya dade da rasuwa...”
“Be rasu ba Amma Hamad yana raye....”
Ta katse wayar ji take kamar wasa suke son yi da hankalinta ko kuma dukansu ba su da lafiya ko kuma dai yana biyewa matarsa ne wata kila ta tabu.
“Ka ga abun da ka janyo ko? Ka kashe kowa a gurina kuma ka kashe a gurinsu...”
“Ban kasheka a gurinsu ba, ba ni na yi wannan ba step mother dinka ce ka tuna wannan? Ban fadawa kowa kana raye ko a mace ba, amman kai na fada maka suna a mace ne saboda ka rayu...”
Captain na kai aya kiran Appa ya shigo wayar Captain cikin girmamawa da mutuntawa ya amsa kiran.
“Lafiya kalau ya matarka?”
“Alhamdulillah an yi aiki cikin nasara Appa ido ya bude...”
“Alhamdulillah maa sha Allah ina take bata wayar..”
A madadin ta karba sai Hamad ya sake karbewa.
“Appa...”
Appa yayi shiru kamin ya amsa.
“Na'am waye wannan...”
“Hamad ne Appa Hamad ne...”
“Hamad na mu?”
“Eh Wallahi ni ne Appa wallahi ni ne ba fatalwa ba ne ban mutu ba”
“Me ka fada min na yarda kai ne? A ina ka hadu da Hurriya? Ina ka san Captain...”
“Ina karkashin kulawarsa ne Appa, ina tare da Captain kusan ko da yaushe, amman ku ya fada min kun mutu...”
“To ba shi wayar zan yi magana da shi....”
Hamad ya aje wayar akan gado domin bakin cikin abun da Captain yayi masa ba zai barshi ya sake hada hannu da shi ba. Captain ya kalli wayar sannan ya danne zuciyarsa domin ya san babba baya zama kamar yaro, kuma dole zai yi ma Hamad uzuri na halin da yake ciki a yanzu.
“Hello Appa..”
Iyami ce ta kirani tana kuka tana fada min wata magana da bata kama hankalinta ba, ni ma kuma bata kama nawa hankalin ba, shiyasa na kiraka sai kuma na ji makamancin abun da take fada min me yake faruwa.
“Labari ne mai tsawo Appa ba zai yiyu a waya ba, dole sai an zauna hakan kuma ba zai yiyu ba sai an dauki permission daga makarantarsu Hamad gudun lalacewar karatunsa”
“Hamad kake kira fa Captain...”
“Hamad Appa Hamad yana raye... Amman yanzu kamin uzuri zan tafi masaukinmu idan Hurriya ta natsu zamu yi magana... Zan kiraka na fada maka yadda komai zai gudana.”
Hankali namiji be taba zama iri daya da na mace ba hakan ya saka Appa ya saurare shi.
“Toh ina jira..”
Captain ya kashe wayar ya kalli Hurriya dake kallon Hamad kamar zata cinye shi tana hawaye.
“Kukan nan ya isa haka, ni da na san haka abun zai zama ba zan bayyana miki shi ba”
“Ni kuma sai na yi ta zama har zuwa lokacin da zaka bayyana ni bayan na ga yar'uwarta?”
Hamad ya fada a tsawace, Captain ko gefe da yake be kalla ba ya kama matarsa.
“Mu tafi Mama Rukayya suna reception suna jiranmu, daga can zan yi clearing kudin asibitin sai mu tafi masauki mu yi magana hakan yayi miki...”
Ta daga mishi kai.
“Hamad zai tafi tare da mu ko?”
Ya daga mata kai yana shafa fuskarta hawayen dake zubar mata yake jinsu har a ransa.
“Toh...”
Ya dauki mayafinta ya rufe mata kai sannan ya kama hannunta suka fito daga dakin.
NIGERIA....
Appa ya saka hularsa yana amsawa Yasir.
“Eh can zan tafi gurin Iyami na yi magana da ita, saboda na ji tana ta kuka abun ne da daure kai na rasa gane kan gadon labarin..”
“Ni ma na ji abun wani iri, maybe akwai abun da Captain din yake boyewa ko kuma Hurriya ta samu matsala ne? Yake biye mata...”
Yasir ya fada with confused.
“Amman na ji wata murya yake cewa Appa ni ne Hamad ne har da rantsuwa ni abun ya daure min kai... Shiyasa nake son na tafi gurin mahaifiyarta”
“Okay Aappa Allah ya tsare”
“Amin sai na dawo...”
A tare suka fito bangaren Appa ya shiga motarsa, Yasir kuma na nufi bangaren Hajiya Kaltume domin labarta musu halin da ake ciki. Shigarsa bangaren ta yi daidai ta cire mayafin da Hajiya Kaltume take tana sauke gajiya. Tana kallon fuskar danta ta san ba kalau ba, domin mamaki ne da daure kai a fuskarsa sai dai bata ce masa komai ba har sai da ya zauna.
“Lafiya.?”
“Wani abu ne mai daure kai Hajiya... Yanzu muna tare da Appa a gida muna duba kasafin kudin da suka shiga da fita na wannan watan bangaren Motocin Appa, sai Amma ta kira tana kuka wai Hurriya ta kirata da number Captain tana mata zancen Hamad, Appa ma be gane kan maganar ba sai da ya kira Captain din da kanshi sai wani ya karba yana cewa shi ne Hamad, Appa dai yayi magana da yaron kamin Captain ya karba ya ce idan sun koma masauki zai kira Appa su yi magana kuma shi Captain din ya fada ma Appa cewar Hamad ne, but labari mai dadi dai idon Hurriya ya bude”
“Hamad......!”
Hajiya Kaltume ta fada da karfi kamar zata rusa dakin.
“Karya ne ba dai Hamad ba, Hamad din da ya mutu? Hamad din da aka kashe? Yaushe zai rayu? Wane irin Hamad kuma? Wannan karya ne, an riga da an kashe Hamad ba zai dawo ba, wannan wai duk na minene Yasir? Duk na ganin bayana ne? Duk na son a ga karshena ne? An hana ni zaman lafiya da mijina, an fitine ni har sai da Alhaji ya sake ni, yanzu kuma zai maida Iyami, idon Hurriya ya bude, ta yi aure ta auri babban mutum, sannan n fasa auren tawa yar, mahaifinku ya juya min baya, na gagara neman lafiyata na gagara zaman dakina kullum bana gurin wannan boka bana gurin wannan malamin, amman har yanzu shiru, yanzu fa na dawo daga wani gurin, sai kuma ka zo min da labarin wai Hamad yana raye? Yaron sa aka kashe tuntuni? Yaushe zai rayu? Hamad ya mutu wani ne dai ya dawo yana son a kai ni gidan yari, burin Iyami ya cika... Shikenan tawa ta kare”
Cikin rashin fahimta da mamaki Yasir yake kallon mahaifiyarsa, be da dalilin daga hankalinta saboda Hamad ya dawo ba har da zancen gidan yare, above all ta gama fada masa tana bin malamai da bokaye.
“Ta ina dawowar Hamad zata saka a kaiki gidan yari idan ma gaskiya ne?”
Tana tambayarta ne a daidai lokacin da Ruma da Khairy suka sauko domin har dakunansu suna jin muryar Hajiya Kaltume saboda yadda take daga murya.
“Saboda ni na saka aka sace Hamad... Ni na saka aka dauke shi tare da Umm Ruman, Hurriya na ce su dauka sai aka yi kuskure aka dauki Hamad... Amman ban ce su kashe shi ba, Danja ne ya aikata hakan ba da umarnina ba..?”
“Waye kuma Danja?”
“Wanda na saka ya sace Hamad, a gidan Hajiya Fatee na hadu da shi.. Ni na saka shi aikin saboda ina son a karbe kudin Iyami ne da Alhaji ya bata lokacin da ya sake ta ya damka mata kudi da gida ga sarkar zinari ya siyawa Hurriya wannan ya saka na aikata... Iyami ta hana ni jindadi ta hana ni zaman lafiya ta saka na rasa komai daga zuwa aiki ta aure min miji sanadinta na rasa Salma ni na kashe yata da kaina... Iyami na ce a halbe sai aka halbe Salma ta cikin madunin Tsafi nan ma ni na saka mai aikin Nafisa ta kai ni duk saboda Iyami ne... Shikenan na lalace rayuwa ta ta kare...”
Kama ganin yadda take maganar yana murza jikinta zaka san bata a cikin hayyacinta. Khairy da Yasir ne mamaki ya cika su, Ruma kam kuka ta fashe da shi domin ta san asalin gaskiyar.
“Hajiya... Wannan maganar ba a cikin hayyacinki kike yinsu ba...”
Yasir ya fada tana tasowa daga inda yake zaune ya dafa mahaifiyarsa ta kai kasa tana kokarin cire riga.
“Ni na saka aka dauke shi Wallahi... Ni na ce a sace Hurriya su kuma suka dauke shi ina ta murna asirina yana rufe sai kuma ka ce min wai Hamad ya dawo? Gidan yari zan tafi kenan? Gidan yari zani Yasir?”
Ya rike rigarta yana kuka, ya dago ya kalli kenansa.
“Akwai wanda ya san wani abu a cikinku...”
Cikin kuka Ruma ta ce.
“Eh gaskiya ta fada, ita ta saka aka sace Hamad, kuma Hamad da ni duk mun ji muryarta lokacin da take magana da su, Har yake cewa Hajiya me na yi kika ce a kawo mu nan? Idan na dawo sai na fadawa Appa, sai ta fara fada tana cewa ya ji muryarta zai tona mata asiri, bayan ta kashe wayar ne suka buga mishi karfe akai kan ya fashe yana ta jini, Hamad yana ta ihu yana kiran sunan mutane har da ni, suka fitar da shi daga dakin suka bar ni daga nan ban san me ya faru ba...”
“Innalillahi Wa'inna'ilaihirraji'u ײ”
Yasir ya furta har sau biyu sannan ya mike tsaye ya rike bakinsa. Khairy kuma ta fadi zaune tana kuka domin bata taba jin wannan ba sai yau. Hajiya Kaltume kuma bata fasa tonawa kanta asirin abun da ta yi ba, tana ta firgar rigar jikinta da zanenta.
“Hajiya me yasa baki ki tunanin makomarki ba da ta mu kamin ki aikata? Wane irin abun kunya ne wannan? Har yaushe zuciya zata bushe ki aikata hakan ga dan mijinki dan be miki komao ba, be tare miki komai ba? Idan ma kishi kike da mahaifiyarsa shi meye nasa a ciki? Gashi har kina fadar sanadinki Salma ta mutu...”
Hajiya Kaltume ta kyalkyale da dariya ta buga kafa. Ta janyo jakarta ta ciro maganin da ta dawo da shi ta zube a gurin.
“Ai ba Shikenan ba, ni na saka Khairy ta dauke gilasan da suke dakinka na Hurriya, ni na yi ma Hurriya da Appanta farraqu, aka saka masa tsanar Hurriya, ni na saka aka saki Iyami Yasir ni na yi mata wannan asirin kuma na ce a kwantar da ita ciwo, kuma na ce ayi mata asiri kar wani ya ganta ya aureta, yanzu wannan maganin shi kuma bokan ya fada min idan na yi amfani da shi Alhaji zai zo Jiki na rawa ya maida aurensa, kuma Fadeel zai dawo ya auri Khairy... Kawata Hajiya Fatee ita take kai ni ko'ina ita ma kuma tana can da ciki cikin haihuwa wanda ta saka malam ya danne, na biyawa Malam makka saboda na jidadin aiki, na mallaka Alhaji sai abun da nace yake min... Tabbas na aikata Hamad kuma ni na dauke shi ni ce nan na aikata, kuma na yi shiga gaban Alhaji da Sapna na kawar masa da ita a zuciya ya fita maganarta na shashantar da ita a zuciyarsa...”
Kusan duk wani abu da Hajiya Kaltume ta aikata tun cancan da har zuwa yau sai da ta fadawa yaransa da wanda suka sani da wanda ba su sani ba. Yasir sai ambaton Allah yake be taba tunanin mahaifiyarsa ta yi nisa haka ba sai yau be taba tunanin ita ce sanadin barin Amma a gidan ba sai yau, be san ita ta shiga tsakanin Hurriya da Appa ba sai yau, be san ita ta aikatawa Hamad haka ba sai yau. Ya rasa ta ina zai fara ya rasa ina zai saka kansa ya samu sassaucin rayuwa.
“Ku shiga da ita cikin daki ku rufe karku bari ta fito”
Ya fada sannan ya share hawayensa yana jin kamar ace ya mutu kamin yau. Ruma ta kalleshi tana kuka.
“Yaya yanzu idan da gaske Hamad ya dawo gidan yari za a kai Hajiya Kenan?”
Ya cije baki ya saka cewa komai sai hawaye ke sauko masa. Tashi yayi ya fice daga falon ya nufo bangaren mahaifinsa ya zauna a gurin yana jin wani bala'in gabas da na yamma yana hade masa, da ma ace wata ce daga cikin kannensa zai ji sauki amman uwarsa? Abun yayi masa muni gaba daya ma sai ya rasa abun da zai yi, tun farko be ga dalilin Hajiya na aikata hakan ba, domin bata rasa komai a gidan Appansa ba idan ma ta tasa me yasa ba zata barwa Allah ba. Yanzu wa gari ya waya? Karshenta jifan akan wa ya dawo? Waye yayi mummunan karshe? A yanzu ya kara jin kaunar Amma a ransa domin ita da ta wakkala ga Allah gashi yayi mata mafita kuma yana kan mata, Hurriya ma haka, Amman Khairy gashi ta girbi abun da ta shuka tun abun be yi nisa ba, Hajiyarsa ga abun na kokarin taba hankalinta ko ma ya taba.
Allah kawai yake ambato ya rasa me zai yi, wa zai tunkara da maganar ya rasa ina zai bullowa lamarin. Yana zaune a gurin har la'asar, sallamar ma yana yi ya sake dawowa gurin ya zauna tunani yake amman tunanin ya ki tsaya masa ya tasa wanda zai ba shi shawarar abun da ya dace ya aikata. Asibiti zai dauki Hajiya ya kaita? Ko kuma dai ya sanar da Iyayenta da kanenta domin babu iyaye a yanzu, ko kuma dai ya samu mahaifinsa da maganar. Daga balcony din da yake zaune ta bangaren Appa ya hango shigowar motar Maama, hakan ya saka shi tashi ya nufi bangaren mahaifiyarsa, a dakin ya sameta tare da sauran yan'uwanta Khairy da Ruma suna kuka har lokacin Hajiya Kaltume bata daina tonawa kanta asiri ba.
“Ku kira su Hajiya Fanna da Mama Zainab ku fada musu halin da ake ciki, idan asibiti za a kai ta sai mu tafi...”
Maama ta juya ta kalleshi tana hawaye