HURIYYA 1&2 COMPLT BY KHADEEJA CANDY

Author :  KHADEEJA CANDY Category :  Romance

Chapter   40 / 86

117K to 120K   out of 257.5K words

cikin hayyacin Tsoho?''

Ya kada kansa kasa.

“Hajiya ba umarninki nake kokarin karyawa ba, bana son zaman Hurriya a ko'ina sai a gida, sanin kanki ne tun kamin yau kin ce na baki ita ban baki ba, saboda bana son kowa ya rika min da”

Hajiya Binta ta masa wani kallo na tsanaki, shi kuma ya ki yarda ya daga kansa ya kalleta sai yawo yake da idon a kasa. Tun tashinsa har girmansa bata ba shi umarni ya tsaba sai a yanzu, ba kuma yanzu ta yau ba, yanzu da girma ya cin masa ita kuma take gangarawa. Ko a lokacin da ya saki Iyami babu yadda bata so ya dawo da ita ba yaki, yanzu kuma saboda Hajiya Kaltume ta sako shi a gaba ya zo a maida Hurriya yake wannan bubutan.

“Kai ma haihuwarka aka yi, kamar yadda ka haifi Hurriya idan baka yi hankali ba, kai ma sai na baka umarnin da idan ka saba ba zaka ga da kyau ba”

Hajiya Kaltume ta kama gafen mayafinta tana share hawaye tare da mikewa tsaye domin ta lura ran Appa ya bace kamar yadda na Hajiya Binta ma ya bace har ta fusata.

“Ba za'ayi haka ba, ba ta kai ga haka ba, Alhaji mu tafi, tun da Hajiya na zon zaman Hurriya a nan ka barta ta zauna Allah ya bada hakurin zama”

Appa ya kalli Hurriya sai da hantar cikinta ta kada ta fara kokarin zare hannun Hajiya Binta a hannunta, ba kuma dan komai ba sai dan saboda Hajiya Kaltume, sannan ya dan risina ya ce.

“A tashi lafiya Hajiya”

Hajiya bata amsa masa ba bata ce masa komai ba har ya fice, kana ita ma Kaltume ta yi ma Hajiya sai da safe ka roki gafararta sannan ta fice. Sai a lokacin Hajiya Binta ta zauna ranta a jagule.

“Hajiya dan Allah ki yi hakuri ki bar na tafi, kar na kawo rudani tsakaninki da Appa, ko kuma Appa yayi fushi da ni kamar yadda ya fada”

Hajiya bata kula hawayen Hurriya dake saukowa ba ta daka mata tsawa.

“Ke rufe min baki nemi guri ki zauna babu inda zaki je, gaba daya sun canja masa kwakwalwarsa, idan yace ya yafe ke ni ma sai na yafe ki, idan takamar yana da kudi yana kula da ni, ai ai ba haka ya tashi yana ciyar da ni ba, Allah ke min komai”

Hurriya ta duka tana kallon Hajiya bi ta data koma ta zauna.

“Idan kika samu tsabani da Appa saboda ni, zai kara wutar kiyayyata a zuciyarsa ne, kuma zai tsine min domin baya a cikin hayyacinsa a yanzu, da ba ke ma ba zai tsaba umarninki ba, idan kika yi fushi da shi ba zai ga da kyau ba, idan kuma hakan ta faru da shi, ke da mu abun zai shafa, domin ke uwarsa ce babu yadda zaki da danki sai hakuri, mu kuma yayansa har kasa ta hade bamu da wanda ya fi shi, amman matansa za su iya gina kansu har su manta da shi, wuya bata kisa Hajiya, kuma duk yadda suke nufina da sheri Allah zai kareni, ina jin tsoron fushin iyayena akaina, yardar Allah tana tare da yardar iyaye, mahaifiyata bata da lafiya kuma bana kusa da ita, ki fahimta Hajiya su suke su raba ni da Appa, dan Allah karki bari haka ta faru, ki yafe mishi ki sauko daga fushin ki yi hakuri na koma...”

Hawaye ya zubo a idon Hajiya Binta, kalaman Hurriya na hankali sun ratsa kwakwalwarta, sai ta saka hannunta biyu da tsufa ya canja musu halittar fata ta rike fuskar Hurriya.

“Ke yata ce ta gari Hurriya, kuma kamar kore kamar kumbonsa, barewabata gudu danta yayi rarrafe, kin fi duka Yaya da Tsoho ya haifa hankali da hangen nesa, karamar yarinya mai kwakwalwar manya, Allah ya miki albarka, na barki na barki ki koma gidan ki zauna, zalinci baya dorewa kuma da yardar Allah sai kin fi su albarka, sai sun koma karkashinki sai rayuwarki ta dawo tana burgesu, ki shirya gobe zan saka direba ya kai ki, kuma zan biki da addu'a, zan rika zuwa ina dubaki”

Hurriya ta lumshe ido tana kwantar da kanta a hannun Hajiya binta hawayenta na sauka a tafin hannun kakarta. Ita kanta bata son komawarma amman ta lura kamar wani abu suke shirya mata kuma suke son hada mata ita da mahaifinta shiyasa suka har Hajiya Kaltume ta nace sai an koma da ita.

“Kin fadi gaskiya, Tsoho be taba musa ba sai a yanzu ta aka cire masa kowa a zuciyarsa, yau a gaban matarsa nake cewa ba za'ayi ba yace za'ayi Allah mai girma”

Hajiya Binta ta sake fada tana hawaye. Hurriya ta bude ido ta kalleta

“Daman na yi tunanin haka Hajiya, saboda kin fadawa Yaya Namra sakon da zata  fada musu, suna ganin kamar kin zafafa sona ne akan na kowa, ita kanta Yaya Namra ta fada min bakar magana, gaba daya a munafuka suke kallona ganin suke kamar zan iya hada ki da Appa ne, Allah kadai ya san fushi da Appa zai yi da ni akan wannan, ni kaina ina tunanin zafafan da Appa yayi ne a kaina ya saka suka raba ni da shi, hawayen nan kuma Hajiya dan Allah ki share su kar wani abu ya sami Appana”

“kin yi tunani kuma na yaba da hankalinki, daman ina masa addu'a kuma zan kara, zan dage, ke ma kuma zan cigaba da yi min kuma ba zan zauna haka nan sai na nemi maganin tsari kala kala na baki, daga kuma karki sake wasa da addu'a Allah ya miki albarka”

Hajiya Binta ta share hawayenta, tare da bawa zuciyarta.


***   ***   ***

A mota babu kalar wutar da Hajiya Kaltume bata hurawa Appa a zuciyata akan Hurriya, har tana fadar Hurriya ta hada shi da Hajiya gashi nan har ta yi fushi gashi kuma ta hana Hurriyar komawa.

“Ni daman abun da nake ta ji ma tsoro kenan, nan gaba kuma ba san me zata kulla ba, yarinya karama ta zama munafuka. Ko yanzu karka yarda ka barta a can idan ba haka ba, Hajiya sai ta tsine maka nan gaba, amman karka sake waiwayar gidan sai idan ta huce”

Kwafa kawai Appa yayi be ce komai ba har suka isa gida.

WASHE GARI.

I know littafin nan zai fito, i know zai yi yawo har ya iso gareki. Na fada kuma zan saki repeating Wallahi duk wanda ya karanta min littafi ba tare da ya biya ba, na barshi da mai mafaɗar rana da fitowarta. Daga masu sharing har masu karantawa ba tare da biya ba na barku da Allah...!

Misalin karfe goma sha biyu na rana 12:00pm Captain ya shigo gidan, ya bude tsadadiyar motarsa ya fito ipod a kunnesa yana magana cike da gadata, shi alaka dole ga soja, kuma jinin sarauta ga kuma naira, shigar kananan kaya ce a jikinsa kamar yadda ya saba, domin abu ne mai wahala ka ga Captain Da Shadda sai idan wani abun ya taso. With little strong ya hau entrance din ya murda kofar falon Momy ya shiga, hakan nan dai ya ji yau baya ra'ayin yin sallama even though ba fushi yake ko bacin rai ba, haka kuma ba cikin farinciki yake ba, not happy not sad. Kulu na ganinsa ta mike tsaye ta sauri tana kallonsa bakinta da jikinta suna rawa saboda kwarjinsa, abu mai wahala ka yi arba da shi baka ji tsoro da fargaba ba, musamnan idan haduwar farko ce, ba kuma tsoro na wanda zai maka wani abu, kwarjini da yake da shi da murufa ta tsananin mazantaka da zakantaka ya wuce ka lalleshi baka ji kwarjinsa ba, balle kuma ace ka san yadda yake da saurin fushi da tsananin fada kamar gawurtaccen zaki.

“Sannu da zuwa Sannu da zuwa...”

“Yauwa sannu ya gida ya aiki?”

“Lafiya Kalau Yallabai”

Ya dan juyarta da kai yana kokarin yin murmushi

“No ki kira ni da Captain ko Jameel that's my name, amman wani Yallabai Yaya ko ranka da ya dade old fashion ne, bana so. Ina Momy?”

“Toh toh na tuba, carpet bari a kirata tana sama”

Ya runtse ido saboda yadda ta sauya masa suna saboda rashin iya pronouncing din. Ta haura sama da sauri, sanin kanta ne ba a shiga dakin Momy kai tsaye idan ba ita ta kira mutum ba, musamman masu aiki, dan haka ta fara ya da zango a dakin Namra ta sanar mata domin ita kuma ta sanar da Momy. Sannan ta sauko da saurinta kamar zata fadi.

“Na fadawa Namra zata fada mata yanzu”

“Na gode”

Ta fice da sauri tana amsawa da babu komai, ai aikinta ne. Namra ce ta fara sauko da far'a jin cewar dan'uwanta ya dawo kamin Momy ta biyo bayansa tana masa lale marhabun.

“Yau kuma an sake ziyararmu, sannu da zuwa dana”

Sai a lokacin ya zauna yana murmushi da murna arba da yar'uwar mahaifinsa kuma mace mai tsakanin kaunarsa fiye da kowa a familynsu.

“Momy ya gida”

“Lafiya kalau, yanzu ka dauki wata bakar dabi'a da ba zaka fada min yaushe zaka zo ba sai dai na gane ka kawai ko? Balle na shirya maka wani abu”

“Ni kaina bana sanin zan biyo ta nan sai dai na biyo kawai, kuma idan ina ra'ayin wani abu ai zan iya kira na fada miki”

“Captain sannu da zuwa”

Namra ta fada sannan ta nufi kitchen.

“Ya aikin? Yanzu ka dawo nan kenan? Yaushe ka dawo kasar wai?”

“Just two days ba, shi ne suka sake kawo ni nan na yi wata biyu zuwa uku sannan na koma gida”

“Kaduna za a maida kai kenan?”

“Yeah na dade ina yawo, so yanzu fitar da na yi waje da kuma sa hannun Daddy, za a bar ni Kaduna na zauna a nan, amman idan aikin ya taso na wasu garuruwa zan tafi mu yi, akwai aikin da ban karasa ba nan Gusau kuma kin san tana ta kokarin a magance matsalar tsaron nan shiyasa aka dage sai na dawo”

“Maa Shaa Allah, Allah ya taimaka gashi nan ka yi Fresh ka kara samun lafiya”

Yayi murmushi tare da kallon Namra data aje masa abun tabawa a mini center table dake gefen kujerar daya zauna.

“Maganar aure dai shi ke nan ka watsar da ita Captain”

“Zan yi aure Momy dolena”

“To na tsorata da lamarinka fa, wacan ma ana daf da daura aure komai ya lalace kuma tun daga lokacin baka sake gabatar mana da kowa ba”

“Bata min rai ta yi da yawa, taya ana daf da daura aurena zaki yi chat da wani saurayi har ya daukeki ku fita, ni fa ina da mugun kishi da zai iya sakawa na kashe mutum, bana iya daukar irin wadannan abubuwan, idan ina son mace ko kallonta bana son ayi”

Ya aje ayar maganar tare da daukar lemun da Namra ta aje masa ta sha. Momy ta yi murmushi.

“Toh Allah ya bada ta gari, yasa kamin ka bar garin nan ka samu wanda kake so, kuma ya rage maka wannan fushi idan ba haka ba zaka yi wahalar zaman aure”

“Amin”

Ya amsa yana dauke fuskarsa da murmushi tare da shan lemun a hankali. Namra ma ta yi murmushi tana taba wayar hannunta kamin ya dago ta kalleshi.

“Yauwa Captain wai a ina ka san Salim?”

Ya juyo ya kalleta.

“Salim Sarauta, abokina ne sosai tun a jami'a muke tare, ke ina kika san shi?”

Ya daga kafada tana dan zare ido kadan kamar wanda ta rasa abun cewa.

“A hanya muka hadu, ya nuna yana so na daga baya kuma ya koma gurin Hurriya, shiyasa na kai shi gidan ma har ka ganshi, amman ban san me ka fada masa ba na ga yanayinsa ya canja kuma har yau be sake kirana ba”

Captain yayi murmushi kasaita murmushin dake kara masa kyauta da haiba

“Ban fada masa komai ba, maybe dai ita ta bata masa rai, na je karbar abu ne na gansu tare, amman karki sake kai shi gurinta, haka yake duk garin da yaje sai yayi budurwa, musamman idan ya ga mai kyau ce just like your sister....”

“Hum himm”

Ya dan kalli Momy kamin ta sake kallonsa dan amsa masa tambayarta.

“Ina yarinyar take ta dawo?”

Momy zata yi magana Namra ta yi karaf ta tari numfashinta ta ce.

“Eh tana dakinta”

Ya maida dubansa gurin Momy fukarsa shimfide da murmushi yayi mata godiya.

“Thank You Momy, ko wace mace ta fi daraja da martaba a gidan iyayenta ko mijinta, kuma a matsayinki na uwa daman haka ya kamata ki yi”

Ya dubansa gurin tsadaden agogon hannunsa sannan ya mike tsaye.

“Ya kamata na tafi kar na bata lokaci”

Momy dake mamaki yadda Namra ta yi masa karya ta ce.

“Nan da nan, baka wani dadewa”

“Yanayin aikin ne a haka, wai Musib har yanzu ba su dawo ba?”

“Suna da daf da dawowa, muna waya da su ai”

“Good”

Ya nufi kofar fita falon, Momyda Namra suka mike tsaye domin yi masa rakiya. Yana bude kofar da zimmar fita Hurriya ta dake rike da kofar tana murdawa da zimmar shigowa, dayan hannunta kuma yana rike da luggage ta sake naushin kirjinsa da kanta daidai saitin zuciyarsa, a karo na biyu by mistake. A take daga hannun sama saitin fuskarta. Kamin hannun ya kai fuskarta ta yi saurin lumshe idanuwanta dake cike da yalwatacce gashin ido ga kuma na gira da ya kara masa kyau a sama, ta dauke numfashinta tana jiran jin tafin hannunsa a fuskarta.

“Yarinyar bata da hankali komai a haukace take yinsa”

Kalaman Momy da kuma jin shiru babu mari babu alamarsa a fuskarta ya saka ta bude ido a hankali pink lips dinta suna motsawa kamar zata ce wani abu. Hannu ta gani a tsaye saitin fuskarta ba tare da ya kai hannun a fuskarta ya mareta, kuma be sauke hannun ba, haka zalika be dauke idonsa daga kallonta ba, kamar yadda fuskarsa take daure saboda abun da ta yi masa. Da sauri ta duke kasa ta ratsa gefenta ta shige falon har Luggage dinsa na dukan kafarsa, abun da ya kara bata masa rai. A lokacin ne ta tuna cewar shi ne mutumen da ya taba marinta.

“Yi hakuri”

Ya ta fada tana kara matsawa baya da sauri domin jin take kamar zai iya rikota yayi mata hukunci ne, gashi babu Hamad mai rama mata. Ya sauke hannu ya juyo sai dai ba ita ya kalla ba, Namra ya kalla.

“Why do you lie?”

Ta dan yi baya kadan ta rasa yadda zata wanke kanta, Momy ta kalleta sannan ta kalli Captain ta already ya fice har yana kokarin rufe kofar. Sannan ta juyo ta watsawa Hurriya harara

“Kin dawo ko? To shiga ciki ki zauna, gida kam na ubanki ne amman ikonsa nawa ne domin bangarena ne”

Hurriya ta sauke kanta ta juya tare da taja kayanta ta haye sama. After ta shige Momy ta kalli Namra ta ce.

“Me yasa kika yi haka? Namra ki daina yin abun da zai saka Captain ya tsaneki fa”

Ta dan cize baki cikin yanayin damuwa ta ce.

“Ban dauka zata shigo yanzu”

“Ki kiyaye next, domin ni ban ki kum fahimci junanku ba har ya kai ku ga aure, ko ranar da ya bar gidan nan sai da muka yi magana da Ammy, akan ke da shi, amman saboda lura da hankalinku baya kan juna ya saka ba ma son matsawa, kuma ko da babu irin wannan be kamata kina haka ba be careful...”

“I will...”

Ta amsa tare da kallon kofar kamar mai tunani, tare da saka hannunta tana taba wuyanta. Momy kuma ta nufi upstairs cikin matukar bacin rai.



Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar  MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne  cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai  shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... 💃🏻
𝐊𝐇𝐀𝐃𝐄𝐄𝐉𝐀 𝐂𝐀𝐍𝐃𝐘

Littafin nan na kudi ne, ba free ba, idan kika karanta ba tare da biya ba kin daukarwa kanki nauyi domin hakkina ne kika rataya a wuyanki. Biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence of payment to 08036126660

𝐀𝐫𝐞𝐰𝐚𝐛𝐨𝐨𝐤𝐬 @𝐤𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚𝐜𝐚𝐧𝐝𝐲

𝐏𝐚𝐠𝐞 2⃣3⃣

Tana tsaka da cire tufafinta a luggage Momy ta turo kofar dakin ta tsaya daga wajr tana kallonta.

“Mun ga sakon da Hajiya da ta aiko mana akanki, kuma mun gode ke ma kuma zaki ga irin nawa sakon, mahaifinki yayi gaskiya gidansa ni da ke duk muna karkashin ikonsa, amman nan bangarena ne ina da nawa rules and regulations, dole kuma ki kiyaye domin ba bangaren Iyami ba ne”

Hurriya ta sauke kanta ba tare da ta cewa Momy komai ba, ganin haka ya saka Momy ta bar kofar a bude ta nufi nata dakin. Ajiyar zuciya Hurriya ta sauke ta dafa goshinta.

“Allah ka kara min hakura zama a gidan nan, kowa da kallar tsanar da yake min”

Ta sake aje numfashi mai karfi sannan ta cigaba da cire tufafin ta jera a closet ta aje luggage din gefe ta cire hijab dinta ta saka talkaminta ta fito daga dakin. Ko da ta sauko babu kowa a falon kai tsaye ta nufi kofa ta bude ta fita. By this time ta san

40 / 86