HURIYYA 1&2 COMPLT BY KHADEEJA CANDY

Author :  KHADEEJA CANDY Category :  Romance

Chapter   19 / 86

54K to 57K   out of 257.5K words

Hajiya Allah ya amsa”

“Ameen”

Hajiya Kaltume ta aje wayar tana murmushi kamar wadda aka yi ma bushara.

“Hmmmm Iyami.... Lallai kin zama labari a gidan nan, yaranki ma da yardar Allah sai sun zama su da babu duk daya a gidan nan”

Ta nufi bakin gadonta ta zauna tana kokarin sake yin wani kiran Khairi ta shigo dakin ta zauna kusa da ita ta kwanta jikinta.

“Hajiya yaushe Ruma zata dawo ne?”

Hajiya ta yi saurin saka wayar key tare da gefenta.

“Babu jimawa Khairi, mahaifinki ne yace a bashi lokaci zai nemi ragi, kuma kin ga ai ana neman ragi a komai”

“Toh Hajiya da zai yarda da sai ya bada kudin ya karbo Ruma, albashi Hamad din a barsa sai an shirya daman ya fitini kowa a gidan nan”

“Ai kin san ba zai yarda ba, kuma mutane ma sai su saka mana ido, ace saboda uwarsa bata gidan ne, kara dai a karbo su tare gaba daya”

“Allah sarki Ruma, Allah dai ya tsare ta”

“Ya ma tsare In Shaa Allah ba za su mata komai ba, ai yarinya ce kuma kin ga ba ita kadai suka dauka ba ko dan ganin idon Hamad za su raga mata tun da dan'uwanta ne”

“Allah yasa”

“Ameen tashi kuje ku karya, ni wanka zan yi yanzu”

“Na karya ai”

“Yayi kyau Maama da Salma duk sun karya? Yayanki fa?”

“Ban sani ba gaskiya”

“Je ki fada masa ya fito ya karya”

Khairi ta tashi ta fice daga dakin, sai da Hajiya Kaltume ta tabbatar ta rufe kofar dakin sannan ta fiddo wayarta ta fara danne danne. Misalin sha daya na safe Bappa da Gwaggo suka dira a gidan, Bappa ya faka a harabar da ya saba fakawa duk lokacin da wani abu mai muhimmanci ya kawo shi gidan, duk kuwa da kasancewar Iyami bata gidan. Shi ya fara fita sannan Gwaggo ta fito tana sanye fa farin hijabinta.

“Ki fara shiga ki yi magana da Hajiya Kaltume a sallamo mana Alhaji mu yi magana da shi”

“Ko kuma dai ayi mana iso ba”

Gwaggo ta gyara masa domin a ganinta ba bara ko roko suka zo gurinsa ba da za ace a sallamo musu shi. Bappa dai be sake cewa komai ba domin be shirya musu da Gwaggo a yanzu ba, ya san duk gyaran da zai mata ba zata fahimta ba. Gwaggo ta daga kai ta kalli apartment din Amma da kyau sai ta ji ranta ya bace, domin a yanzu yarta bata cikin gidan ba kamar da ba. Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta fito ta nufi bangaren Hajiya Kaltume, ba dan zuwan ya zame musu na dole ba ba za su zo a gidan ba, musamman ma ita da Hajiya Kaltume har Hajiya Nafisa basa girmamawa, Hajiya Nafisa na yi musu kallon matalauta masu kwadayi Hajiya Kaltume kuma na yi musu kallon maciya amana wadanda suka hanata zaman lafiya da kwanciyar hankali, Appa ne mai girmamata idan yaje mata ko kuma ita ta zo gidan ya rasa ina zai dauke ta ya dora tsabar farinciki da girmamawa. Ta murda kofar falon ta shiga da sallama fuskarta dauke da damuwar data kasa boyuwa.

Salma da Maama suka amsa mata ba dan sun ga fuskarta ba, domin su ma ba girma suke bata ba. Yasir ya aje cup din hannunsa da sauri ya baro dinning din ya nufota yana mata sannu da zuwa har da dan risinawa.

“Sannu Yasir ya hakurin lamarin nan?”

“Alhamdulillah Gwaggo Bismillahi zauna”

Ya nufi kujerar da sauri ya dauke pillows din da suke kai ya mata mazauni.

“Ya gida ina Rukayya?”

“Gida Lafiya kalau, Rukayya ta tafi makaranta tun safe”

“Ya Hurriya da Amma?”

“Toh Alhamdulillah Hajiya Kaltume na ciki? Tare muke da Malam ai”

“Oh... Ya tsaya a waje?”

“Eh ai ba jimawa za mu yi ba, magana kawai za mu yi da Mahaifinku”

“Okay Salma shiga ki kira Hajiya bari na tafi gurin Bappa”

Salma ta motsa hanci ta mike tsaye ba tare da ta gaishe da Gwaggo ba ta nufi upstairs, Maama tun da ta kalli Gwaggo sau daya bata sake juyowa ba balle har ta gaishe ta. Ba abun mamaki ba ne a gurin Gwaggo domin sun saba yi mata haka kishi suke taya uwarsu. Daga kiran Hajiya Salma bata sauko ba balle Gwaggo ta san halin da ake ciki haka ta zauna a gurin har kusan minti ashiri sannan Hajiya Kaltume ta sauko tana sanye da wata gizna mai fari da baki irin ta mutanen nijar ta irin aikinsu a gaban rigar da ta sauko mata har guiwa.

“Gwaggo ce yau a gidan na mu”

“Ni ce, halan Salma bata fada miki na zo ba Hajiya Kaltume”

“Ta fada min ba shi na sauko ba? Ina dan abu ne shiyasa Allah yasa dai lafiya”

Gwaggo ta tabe baki ta girgiza kai.

“Ba lafiya ba kan, tun da kowa ya san abun da ya faru, tare muke da Malam muna son magana da Alhaji ne”

Hajiya Kaltume ta zauna tana yamutsa fuska irin an takura musu din nan, kamin ta fara magana da izza.

“Oh Allah sarki, dazun ma ai na ga Bappa ya kira Iyamin ma ta kira, Alhaji sai fada yake Gwaggo ba a haka, ku baku san shirinsa ba, kuna son daga masa hankalin ne kawai shi ma fa ya damu da yaran nan kuna neman ku daga masa hankali”

Gwaggo ta nuna Hajiya Kaltume da yatsa.

“Ke Kaltume ke kin sani ko ban haife ki ba, na yi kanwa da ke, dan haka na cancanci girmamawa a gareki ko dan Iyami”

Hajiya Kaltume ta yi murmushi da ya fi kama da yar siririyar dariya.

“Wannan kuma ai da ne Gwaggo, yanzu babu wannan alakar, kuma da kuke neman daga mana hankali ni ma fa tawa yar tana can tare da Hamad aka sace su, ko kuma ita ba mutum ba ce?”

Gwaggo ta mike tsaye.

“Kwarai kuwa mutum ce, shiyasa ai na ganki kin sha wanka kina ta far'a da jindadi an sace miki auta, gashi nan ai ya nuna a fuskarki”

“Gwaggo karki gayan magana, to faduwa zan yi na yi birgima? Ko kuma an fada miki ni din kamar yarki ce Iyami da bata yarda da kaddara ba? Ai ma dai da kunya Wallahi ku tako gidan nan da sunan ganin Alhaji shi be nemu ba ku za su neme sa, abu dai kamar ba Fulani ba”

“Ba rokonsa muka zo akan ya ba mu wani abu ba, kuma ba zuwa muka yi akan ya maida Iyami ba, shi ne abun kunya, mun zo ne saboda Hamad, ai kin san ko an rabu idan akwai yaya kamar ba a rabu ba ne, sai hakuri Hajiya Kaltume Iyami dai ta zama murucin kan dutse, ta zama kadangaren bakin tulu, kuma ta zama ƙashin wuya bata haɗuwa bata amayuwa”

Maama ta juyo tare da tasowa daga dinning din zata fadawa Gwaggo magana Hajiya Kaltume ta yi saurin daga mata hannu.

“Babu ruwanki Maama je ki cigaba da cin abincinki, Allah dai baya baci zalinci da kuka min sai ya saka min macuta kawai masu abun kunya”

Hankali kwance Gwaggo ta ce.

“Ba mu da abun kunya, da muna da abun kunya mijinki ba zan lallaba ya nemi hada iri da mu ba, kuma Alhamdulillah ko yanzu kasuwa ta watse ɗan koli mai rabo ya ci riba, tun da ga ƴaƴa nan Allah ha raya su ya saka musu albarka”

Gwaggo na kaiwa nan ta kabe Hijabinta ta fice daga falon ta bar Hajiya Kaltume da ciwon rai. Ko da Gwaggo ta iso gurin Bappa na nasa masifar Yasir na bashi hakuri.

“Bappa ka yi hakuri Wata kila ransa ne a bace”

“Idan ransa ne a bace be san waye ni ba da zai fada min maganar banza?”

Gwaggo ta dubi Yasir ta dubi Bappa.

“Malam lafiya?”

“Yasir ya shiga ya kira min Alhaji Haruna, daker mutumen ya fito, kuma abun da yake fada min shi be da miliyan dari biyu da zai bada yanzu, kuma ina damunsa da kira ban san damuwarsa ba, ai ba Hamad kadai aka dauka ba har da yarsa amman mun daga masa hankali kamar Hamad ne kadai ďa, idan muna da kudin mu ba su mu karbo Hamad din har da rubuto min number mutanen ya turo min, wai shi ba zai bada kudi ba police sun ce za su karbo su”

“Hmmm Allah ya kyauta, tun da ya baka Number mu tafi Malam”

Yasir ya nufi Gwaggo cikin rashin jindadin abun da ya faru yana bata hakuri

“Gwaggo dan Allah ku yi hakuri, maybe damuwa ce ta yi ma Appa yawa, dan Allah ku yi hakuri ba halinsa ba ne Wallahi”

“Karka damu Yasir babu komai”

Gwaggo ta fada sannan ta bude motar ta shiga, Bappa yaja motar sai masifa yake ta yi domin yau Alhaji Haruna yayi masa abun da be taba masa ba.

“Har yana cewa muje mu biya kudin ganin yake kamar ba zamu iya ba ko? Har yaushe za a bata lokaci gurin jiran abun da baka san faruwarsa ba? Ko bayan haka ni bana je akan ya bada kudi ba, naje ne mu yi magana ta fahimta da shi na ji halin da ake ciki, amman mutumen ko kallona baya son yi, sai fada yake kamar shi ne uban ni ne dan, na fada masa ni ba zan dauki wannan rainin wayon ba, kuma ni da gidansa har abada, wato saboda ya saki Iyami shiyasa yanzu baya ganin kimarmu ko?”

“Allah kadai ya san abun da yake nan Malam, Allah dai ya isarwa Iyami da yaranta Allah ya saka mata da gaggawa”

Gwaggo tana addu'a tana kuka daman idan ranta ya bace bata da wuyar kuka.



_________________

Ina masu fama da ciwon dajin? Ciwon hanta? Ulcer? Hawan jini da Ciwo sashe, Ciwo sugar da ciwon mara, Ciwo sanyi kai har da ciwon HIV. Ina masu fama da Ciwon da aka kasa gane kansa, ina masu fama da matsalar Jinnu? Ina matan da sai an yi maganar aure abu yayi shiru? Ina matan dake neman mazajen aure? Ina masu neman tsarin jikinsu? To fa nesa ta zo kusa cibiyar MALAM MAITAWAKKALI ta zo musu da mafita da yardar Allah. Duk wata cuta da aka kasa gane kanta, ko kuma ciwon da yake damun mutum a jiki ko wane iri ne za ku samu warakarsa da yardar Allah. Muna bada maganin ne ta hanyar da addinin musulunci ya yarda da shi babu bokanci ko tsibbo a ciki. Kuma muna bada maganinmu ne cikin sauki da rahusa, mun saukaka kamar kyauta na goro kawai za ku bada, biya kuma sai bukata ta biya, burinmu dai shi ne samun lafiyarku da kuma biyan bukatarku.

Mazauni cibiyar na nan a Kwantagora Local Government, hanyar farin ruwa kusa da dan gandu rice. Za ku iya tuntubar mu ta wannan line 08135421882 ko kuma 08061663326. Zaku iya kira ko chat, wani abun burgewa kuma shi ne za mu iya aika muku da maganinmu a duk garin da kuke ba dole sai kun zo ba. Ku dai ku kira ko kuma ku tuntube mu ta Whatsapp. Sai kun zo... 💃🏻
𝐁𝐨𝐨𝐤 𝐓𝐰𝐨

𝐀𝐫𝐞𝐰𝐚𝐛𝐨𝐨𝐤𝐬 @𝐤𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚𝐜𝐚𝐧𝐝𝐲

Littafin nan na kudi ne biya ki karanta cikin aminci pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence to 08036126660


𝐏𝐚𝐠𝐞 4️⃣

“Gaba daya an juye kan Alhaji Haruna, kuma ko rantsuwa na yi ba zan yi kaffara ba, ba zai wuce Kaltume ba, domin bata hada hanya da imani ba, kai ko gurin da ya bi ya wuce bata bi ba”

Amma ta share hawayenta bayan ta gama sauraren Gwaggo dake fada mata abun da ya faru.

“Ni yanzu ba ta Kaltume nake ba ko Alhaji, ta dana nake burina ma ga ya fito, kuma tun da har ya kai ga furta cewar ba zai bada kudin ba, ni zan bada albashi shi sai ya bada na Ruma”

“Ko daukar yaron nan da aka yi bana raba dayan biyu, Kaltume ce ta saka aka sace shi, yadda na ga ta sha ado ta sauko hankali kwance har tana neman fada min magana ya isa ya tabbatar da cewar da sa hannunta aka sace yaron nan, tasan yarta tana cikin kwanciyar hankali shiyasa hakan be daga mata hankali ba, kuma yanzu na kara tabbatar da ita ce ta aiko Maama gidan nan saboda ta rabaki da dan abun da kike da shi, ni dai da zaki yarda da shawarata da kin saurara karki kira su ki kyale su da yaron ki gani shi za a karbo Ruma ba a karbo Hamad ba?”

Amma ta daga kai ta kalli Hurriya dake zaune a waje tana cin indomie da Gwaggo ta dafa mata kamin ta fita.

“Gwaggo shin idan wani yayi garkuwa da ni yace sai an bashi kudi alhalin kina da hanyar za ki bi ku bada kudin nan zaki bada ko kuma zaki tsaya jiran sai ranar da wani ya bada ne?”

“Zan fada”

“Toh ki saka kani a matsayinki, ni ma fa uwa ce tun daga lokacin da na baro gidan uban yaran nan kullum da kalar tunanin da nake kwana a raina balle kuma yanzu da yarona yake hannun wasu mutane da ba mutanen kirki ba, marasa tsoron Allah, duk abun da nake da shi a duniyar nan be kai ran Hamad ba, Gwaggo ko rayuwata suke ce sai na basu sannan za su sako Hamad Wallahi zan ba su”

Tana maganar hawaye masu zafi na sauko mata, ita kadai take iya jin abun da ko wace uwa take iya ji idan danta ya shiga mugun hannu.

“Kana ina dana? Ka ci abinci baka ci ba? Wane kalar abinci suke baka, ina kake kwanciya? Suna azabtar da kai ko basa yi? Ka yi marmarin gida?”

Amma ta gargiza kai tana kara jin ba zata iya jure har lokacin da Appa zai ga dama ya biya kudin ba. Haka kuwa aka yi, Bappa ma ya bata goyon baya domim ransa ya bace sosai akan abun da Alhaji Haruna yayi masa, Amma da kanta ta kira number da aka bata sai suka tararda line a kashe, sai dai mai neman baya fitar da rai, jajircewa suka yi ta yi suna kiran line kullum ba dare ba rana ba safiya, har suka yi sa'a a rana ta uku kiran ya shiga da misalin karfe goma sha daya na dare. Abun da baka saba ba zuciyar Amma ta hau zillo tsoro ya kamata kamar suna gabanta, duk kokarin da Bappa yayi na ba su Hamad su yi magana da shi sai mutanen suka ki, Bappa ya tambaye ina za a kai musu kudin suka fadi gurin da za akai musu kudin a aje, wani kasurgumim daji ne dake tsakanin mafara da Gusau.

Bayan sun gama wayar Bappa ya ce.

“Allah yasa dai yaron nan yana raye, na ga duk kokarin da muka yi sun ki yarda su ba mu shi mu yi magana”

Amma ta girgiza kai.

“Yana nan raye Bappa, yana raye In Shaa Allah”

“Yanzu waye zai shiga wannan guri ya kai kudi mai yawa haka? Ai shi ma sai su rike shi kamar yadda suka yi ma kanen Hajiya Kaltume, ni dai da zaki hakura mu ga abun da hukuma za su yi, ko kuma idan za a je kai musu kudin aje tare da police”

Bappa ya kalli Gwaggo dake maganar ya ce.

“Baki ji sun sake jaddada mana kar mu kuskura saka police a ciki ba, kai kuma kuma zan iya zuwa na kai, indai za su sako yaron nan hankalin kowa ya kwanta zan aikata haka, kawai ku yi ta mana addu'a”

Cikin yanayin damuwa Gwaggo ta sauke ajiyar zuciya.

“Kowa ke da hannu a cikin lamarin Allah ka wulakanta shi ka tona asirinsa”

“Ameen”

Bappa ya amsa. Gidan da Appa ya bata a lokacin da zai sake ta aka fara sakawa a kasuwa, domin filayen da ta mallaka guda biyu a gidan Appa ta san idan ta saka su a kasuwa ba lallai ne ayi saurin siya kamar gidan da yake gyararre ba, duk da haka kuma sai da aka siyar da shi a nakashe, gidan da zai yi miliyan 45-50 aka siyar da shi a miliyan 35 ta hada da kudin da Appa ya bata da dan abun da take da shi ciki har da sarkar gold din da Appa ya siyawa Hurriya duk ta siyar ta hada kudin ta bawa Bappa, ranar da za aje kai kudin babu yadda Gwaggo bata so a saka police a cikin lamarin ma amman Amma ta ki yarda ganin take idan aka yi haka an bata lokaci kuma za su iya kashe mata da kamar yadda suka yi ikirari, Gwaggo kuma na ta ganin rautar Bappa da Amma taya za a dauki kudi mai yawa haka a shiga daji a kaiwa barayi ba tare da sanin sami'an tsaro ba, abu dai kamar a shirin film.

Cikin karfin hali da yarda da kaddara Bappa ya shiga dajin tare da wani dan'uwansa, bayan yayi addu'o'in da be san adadinsu ba, Gwaggo da Amma, Rukayya da duk wani dan'uwa ma suka raka shi da addu'a. Dan'uwa ya tsaya daga waje shi kuma ya shiga ciki ya kai kudin ya aje a gurin da suka bukata. Har ya kai ya fito babu abun da ya same shi, a lokacin da ya fito ya kira gida ya fada musu ya fito sai kowa yayi ta hamdala ana jin sanyi. Kamin hankali ya karkata gurin ganin kiransu ko sakon inda za su ce a je a dauki Hamad amman shiru. Daga bisani suka bi sawun kiran da number da suka kira da ita last time, domin kullum canja number suke idan za su kira. Haka aka kwashe two days babu kira daga garesu kuma babu wani sako kuma idan aka kira wayar bata shiga, hankali Amma sai ya kara tashi, ta kai bata iya cin komai rashin lafiya ta taso mata har sai da aka kwantar da ita asibiti kowa yayi zaton haihuwa ce duba da tsohon cikin da take da shi, sai dai likitocin sun tabbatar musu ba haihuwa ba ce hawan jini ne, har suka so riketa saboda jinin nata ya hau sosai kuma bata iya cin komai sai dai ruwan da suke saka mata suna taimaka mata ta bangaren kuzari. Sai dai yadda ta nuna bata son zaman asibitin da kuma rokon da aka yi ta musu sannan suka yarda suka sallame ta bayan sun fada musu cewar a

19 / 86