Author : KHADEEJA CANDY Category : Romance
ta yi da dakin Momy sai ta isa bakin kofar dakin ta yi sallama ta kwankwasa.
“Shigo”
Ta murda kofar ta shiga idonta na bayyana tsoronta a fili domin bata san dalilin kiran ba, gashi ance mata magana ce mao muhimmanci kuma har ba a son kowa ya ji. Kusa da kofar ta tsaya ta rigina tana zuba gaisuwa.
“Hajiya ina wuni”
“Rufe kofar ki matso nan”
Ta juya ta kalli kofar sannan ta saka hannu biyu ta rufe ta, ta matsa kusa da Hajiya ta zauna a kasa.
“In ce dai ba wani laifin na yi ba”
Hajiya Kaltume ta kalleta tana murmushi.
“Aa ba ki yi laifi ba for now, na ma kiraki ne na yaba miki, sai dai nan gaba ban sani ba ko zaki yi laifin idan kika biyewa sherin zuciya”
“Hajiya kin saka ni a hudu me ya faru?”
Hajiya Kaltume ta gyara ta kalleta da kyau irin duban nan dake nuna babu alamar wasa a zancenta.
“Ke kika dauki kudin da yake uwar dakinki Nafisa, da sarkokinta da kuma sarkar Namra ko ba haka ba?”
Hausawa suka ce marar gaskiya ko a ruwa gumi yake. A take gumi ya karyowa Kulu ta fara hadeye yawu tare da dora hannu akai tana zaro ido.
“Ni Kuma? Innalillahi Wa'inna Ilaihiraji'un Allah Wallahi Hajiya... ”
Hajiya ta daga mata hannu.
“Ban ce ki rantse min ba, abun da na sani ne nake fada miki, kuma bana bukatar ki jadadamin, idan kuma kin yi musu zan mu iya zuwa ni da ke da Nafisa da kowa ma na gidan na nuna gurin da kika boye kudin, bayan dakunanku cikin itacen fulawa”
Jikin Kulu ya fara rawa irin rawar nan dake kara bayyana rashin gasjiyarta.
“Kin ga daga nan sai Alhaji ya koreki, daman kuma ita Nafisa na san ba zata kyaleki ba sai ta hadaki da Police, baki ga aikinki ba ki ga kudin da kika sata, kuma ga zubewar mutumci da zuwa gurin yan sanda”
“Hajiya ki rufa min asiri dan girman Allah ki yafe min, ki dubi girman Allah ki rufa min asiri, Wallahi zan maida duk abun da na dauka, dole ce ta saka na sata, shekarata nawa a gidan nan amman ban tana daukar ko akaifa ba balle kudi”
Ta karasa da kuka sosai ko'ina na jikinta yana rawa, ta dayan bangaren kuma tana mamakin ta ina Hajiya ta san da wannan bayan bata fadawa kowa ba, kuma babu wanda ya san gurin da ta binne kudin.
“Ban ce ki maida kudi ba, da ki maida kudi da karki maida kudi duk daya ne a gurina, ni ina ma jinjina miki da kika aikata hakan, domin Nafisa ban da bakar rowa da wulakanci bata aje komai ba, na kira ki a nan saboda na fada miki cewar na sani, kuma na jidadi da baki wahalar da kanki gurin bayyana gaskiya ba, ni nan da kika ganina har duniya ta nade ba zan taba fadawa kowa cewar ke kika saci kudin Nafisa ba ko sarkarta”
“Hajiya ina kika ji wannan magana?”
“Da wa kika yi maganar?”
Ta daga hannayenta sama.
“Wallahi ban yi da kowa ba.. ”
“Karki damu da inda naji, ba wani ya fada min ba, abun da nake son ki damu da shi ne, abun da zan fada miki yanzu”
Ta kara gyara zama tana hade yawu da karfi.
“Toh Hajiya”
“Daga yanzu ina son ki zama karkashin ikona ba ikon Nafisa ba, ita kike yi ma aiki amman ni nake da iko dake, ina son ki saka min ido sosai akan uwar dakinki, kuma nan gaba duk abun da na ce ki aikata zaki aikata shi”
“An gama Hajiya Wallahi an gama.. Komai kike so shi za'ayi”
“Yayi kyau, ke kuma asirinki zai yi ta rufuwa har ki mutu, kuma zan cigaba da biyanki bayan biyan da Nafisa take miki”
“Hajiya ni ba sai kin ba ni komai ba, kawai dai ki rufa min asiri idan kika min haka kin biya ni”
Hajiya Kaltume ta yi murmushi ta dauke fuskarta ta dauki wayarta tana latsawa, haka ta kyale Kulu a gurin tana ta share gumi har na kusan minti biyar sannan ta kalleta ta ce.
“Wake share dakin Hurriya?”
“Ni ce Hajiya ni nake sharewa na yi mopping ko'ina na saka turare”
“Yayi kyau da ba ke ba ce zan ce ki karba ki share saboda, aikin da nake son ki fara min a yanzu shi ne, ki shiga dakin Hurriya ki bincike min komai na dakinki idan kika ga wata laya ko wani kullin magani ko wani abun na dabam ki dauko min shi”
“Toh Hajiya amman sai gobe, saboda dare ne yanzu, kuma Momy bata son kowa ya shiga bangarenta idan tana nan”
“Ni ma ban ce ki yi yanzu ba, amman dai ki tabbatar kin samo wani abu karki zo min hannu sake, domin ni na san akwai abu a dakin shiyasa na ce miki ki dauko, kamar yadda na san ke kika yi sata kuma na san gurin da kika boye kudin”
“Toh Hajiya, Wallahi zan yi”
“Shi ke nan tashi ki tafi”
“To na gode Hajiya na gode Allah ya saka da alheri Allah ya rufa mana asiri, Allah ya kareki daga duk shari”
Hajiya Kaltume bata ji zata iya amsa addu'ar ba dan haka bata amsa ba, sai kawai ta daga mata hannu. Kulu ta tashi ta fice rike da zanen da ya kwance kuma ta kasa daurawa sai rike shi da ta yi a jikinta ta sauka haka. Hajiya Kaltume bata sake fitowa dakin ba sai da ta auna lokacin da ya kamata ace Khairy ta dawo cikin gidan sannan ta fito dakinta ta nufi dakin Khairy, sai ta same ta kwance ruf da ciki bandir din 1k a gafenta wayarta ma a gafenta aje. Sai da Hajiya ta gama kallon komai sannan ta zauna kusa da ita ta kai hannu ta taba ta
“Ke Lafiya kike?”
Khairy ta bude ido.
“Lafiya kalau”
“Waye ya zo gurinki?”
“Waya fada miki wani ya zo gurina?”
“Na ga Hurriya na tambaye ta ina ta fito tace min ke ta raka gurin saurayinki, waye wannan?”
Khairy bata son jin magana dan haka ta ce.
“Baki san shi ba”
“Hakan yayi, danan bana son saninsa, domin bana son ganin kowa a tare da ke sai Fadeel”
Da far'a Hajiya Kaltume ta fadi haka tana kai hannu ta shafa bayan yarta irin na uwa mai alfahari. Sai a lokacin Khairy ta zabura ta tashi zaune ta kalli Hajiya Kaltume.
“Wane Fadeel kuma Hajiya?”
“Fadeel dai, dan wajen Hahiya Fatee yayanki”
Khairy ta lumshe ido ta bude alamar gajiyawa.
“Hajiya ina tunanin na nuna miki tun ranar da kika min maganar nan cewar Fadeel baya a cikin tsarina, namiji mai mata da yara uku me zan yi da shi?”
*I know littafin nan zai fito, i know zai yi yawo har ya iso gareki. Na fada kuma zan saki repeating Wallahi duk wanda ya karanta min littafi ba tare da ya biya ba, na barshi da mai mafaɗar rana da fitowarta. Daga masu sharing har masu karantawa ba tare da biya ba na barku da Allah...!*
Hajiya Kaltume ta juyo da kyau ta fuskance ta tana kokarin lurar da ita duniya.
“Irinsu ai sun fi rikon aure, balle kuma shi da muka san halinsa ciki da waje? Baki ga yadda yake zaune da matarsa ba? Sannan yayansa ai ba ke zaki rika su ba ko da ya rabu da matar, sannan yaron nan yana da kyau ga kudi, irin sa mata suke rubibi fa amman ke Allah ya kawo miki shi a arha”
“Ko duniya yake da ita, ni baya cikin tsarina bana sonsa, ina da wanda nake so... Saurayi matashi be taba aure ba kuma shi ma mai kudi ne dan masu kudi da baya jin zafin kashe naira”
Hajiya Kaltume ta yi murmushi.
“Yaro yaro ne, ke Khairy ban da yarinta irin naki, har akwai saurayin da zai fi Fadeel a garin nan? Ke dai ki bude idonki kuma ki ba zuciyarki hadin kai nan da nan zaki ji kina sonsa, kuma ki duba ko amincin dake tsakanina da mahaifiyarsa”
A karo na biyu Khairy ta runtse ido ta bude da karfi, cikin ihu ta ce.
“Hajiya bana son Fadeel kuma ba zan so shi ba, baya cikin mazanjen da nake so, ni ina da wanda nake so”
“Khairy lafiyarki kuwa? Ni kike yi ma magana da daga murya haka?”
“Toh Hajiya kina son cilasta ni auren wanda bana so, na fada miki bana ra'ayin Fadeel, ba a auren dole yanzu”
Rai a bace Hajiya Kaltume ta mike tsaye tana nuna Khairy da wayarta a hannu
“Baki isa ba, shi da yake namiji be bijirewa mahaifiyarsa ba balle ke da kike mace, kuma duk samarinki nan naki na banza ba, domin babu wanda ya nuna alamar da gaske yake har kika gama karatunki, kowa na ganki da shi sai ki ce abokinki ne, sai yanzu da na gabatar miki da wanda nake son ki aura mutumen kwarai wanda zai rike ki da gaske sai ki gabatar min da wata maganar banza, to baki isa ba dole ne ki bi zabina, ni na haife ki ba ke kika haife ni ba”
Fuuu Hajiya Kaltume ta fice daga dakin kamar walkiya rai a matukar bace. Khairy ta fashe da kuka gaba daya Hajiya tana son rikita mata lissafi bayan wanda Adam yayi mata. Kuka ta yi sosai sannan ta shiga bathroom dinta ta yi alwala ta fito ta gabatar da sallah Isha'i tana gamawa ta nufi jakarta ta bude ta dauko kwayar magani ta balla ta jefa a baki, sai da ta fara taunawa sannan ta kora da ruwan bandaki ta hade ta hau gado ta kwanta.
Some weeks Later....
Hurriya tana zaune rike da kofin ruwa tana kallon MBC 4 Namra ta fito zauna kusa da ita tana murmushi.
“Hurriya dan gidanki kullum sai yace na gaisheki, kuma ya ce yau zai shigo mu gaisa saboda an ki gayyatarsa gurin gatsar tsire”
Hurriya ta dago ta kalleta da alamar tunani domin bata gane wa take nufi ba.
“Dan gidana kuma?”
“Yeah Ethiopian...”
“Oh... Hmmmm Yaya Namra ashe yau akwai daukar wanka?”
Namra ta harareta hana dariya.
“What do you mean?”
“Yaya Namra na ga taku ta zo daya fa, all my life a yanzu babu wanda nake son ganin aurensa ko partner dinsa kamar ke da Yayana”
“Shi ke nan sai kuma aka ce miki wani abu ne tsakanina da shi?”
“Hmmmm ai yau idan ya zo fita zan yi na tsareku da ido har na gane komai”
“Okay ai tare zamu tafi, daman yace yau sai ya ga kanwata da nake ta masa rowa, but bari na fada miki Gaskiya babu komai tsakaninmu fa, gaisawa kawai muke shikenan”
“Hmmm Yaya Namra i can read your eyes fa, shi ma alamunsa suna nuna akwai abu a zuciyarsa fa”
Namra ta watsa ido da mamaki.
“Ke Hurriya yaushe kika zama haka? Wato ko kunyata baki ji kai tsaye kike fadar haka”
Hurriya ta saka dariya sosai, sannan ta matsa kusa da Namra.
“Yaya Namra maganar Allah mutumen be miki ba?”
Namra ta yi shiru tana murmushi.
“Yaya, amman ba abun da kike tunani ne ba”
“Zai zama abun da nake tunani soon Yaya Namra, daga ganinshi mutumen kirki ne dan Allah idan ya ce yana sonki karki ce aa”
Namra ta girgiza kai tana dariya ganin Hurriya ba zata barta da zancen ba, ta dauki filo ta rumgume.
“Kyaji da shi ke dai”
Hurriya ta yi murmushi. Haka Hurriya ta saka mata ido har yamma tana lure da yadda ta shirya turaren ma na musamman ta saka ta feshe jikinta ta ko'ina kamshi take. Ana gama Sallah Magariba before Isha'i Namra ta sauko tana sanye da wata Egyptian Abaya ko ina kyalli take gashi ta sha kamshi kamar wata amarya. Kusan wannan ne karon farko da wani ya ziyarci gidansu da sunan ganinta kuma shi ba dan makarantarsu ba kuma ba dan'uwanta ba. Har ta fita sai kuma ta dawo ta shiga dakin Hurriya dake kwance tana karatun Qur'ane.
“Hurriya ta so mu je”
Hurriya ta juyo ta kalleta.
“Ya zo”
Namra ta daga mata kai tana murmushi fuskarta har annuri take. Hurriya ta aje kur'anen ta dauko ta nufi Hijab dinta ta dauka ta saka.
“Amman Yaya Namra ki fadawa Momy? Kar ta fito nemanki ko nemana ba mu kusa”
“Ban fada mata ba, dadina dake akwai zurfin tunani, bari na fada mata sai na sameki kasa”
“Okay”
Ta juya ta fita daga dakin ta nufi dakin Momy, daga bakin kofar dakin ta tsaya ta fada mata tana da bako a waje zata je su gaisa, a take Momy ta yanke wayar da take fuskarta ta cika da annuri.
“Maa Shaa Allah, haka nake son ji a gaishe shi”
Ta yi murmushi ta yi baya ta ja mata kofar, kasa ta sauko ta samu Hurriya tsaye tana jiranta. Hannunta ta kama suka fita tare. Sai da Namra ta yi ta rabon ido kamin ta hango shi tsaye can gurin gate din gidan.
“Laa har can ya faka?”
Hurriya ta fada tana ganin kamar ya tsananta ma kansa fakawa a nesa da apartment din Momy. Tun kamin su karaso ya bude motar ya fito, farar shadda ce a jikinsa da hula shi ma sai kamshi yake zubawa irin na manyan samarin nan dake gasar nuna ado a gurin yan matansu. Haka nan Namra ta samu kanta da kunyar kallonsa har suka karasa gurin.
“Salam”
“Salam...”
Ya amsa musu yana kallon Hurriya da murmushi a fuskarsa.
“finally yau dai an fito min da kanwar nan da ake ta min rowa”
Namra da Hurriya suka yi dariya kusan lokaci daya.
“Ba rowarta nake maka ba, kai ne baka bukaci gaisawa da ita ba”
“To ai tsoro nake ji, kar ki ce min na karya doka kuma kin san mai nema taka tsantsan yake”
“Haka ne”
Hurriya ta kalleshi ta ce.
“Barka da dare”
“Hey Young Lady”
“Lafiya Kalau”
“Maa Shaa Allah, yau dai na ce zan zo na dubaki, even though dai aiki yana min yawa amman Yayanki tana min rowarki kullum idan ina cewa ina gaisheki bata ce min kina amsawa sai dai tace min zaki ji kina ji kuwa”
Hurriya ta yi dariya tana kallon Namra dake girgiza kai tana murmushi kawai yadda yake da son ban dariya abun yana burgeta.
“Tana fada min, kuma ina amsawa”
“Good”
Ya fada still yana kallonta. Namra ta kalleshi kadan ta ce
“Ka shigo ciki”
“No nan ma ya isa, kawai dai ki kawo min kujera na zauna”
Hurriya ta wara hannunta
“Bari naje na dauko...”
“No bari na dauko”
Kamin Hurriya ta sake cewa komai ta juya ta nufi cikin gidan. Hurriya ta juya zata bi bayanta sai ya kirata.
“Ina zaki je?”
“Zan taya ta daukowa ne”
“Hmmm baki son yayarki ta wahala kenan, ni kuwa na saba bata wahala kullum saboda sai na ce ina gaisheki”
Hurriya ta yi murmushi ta bi bayan Namra, a tare suka dauko kujerun biyu ta nufi bangaren da Motar Momy take suka aje a gurin, yana ganin haka ya san baya bukatar ace masa ya karaso ya zauna, dan haka ya cira kafarsa ya gurin ya zauna a kujerar da Hurriya ya aje. Namra kuma ta zauna a dayar, sannan Hurriya ta koma ciki ta dauko musu ruwa da cups ta aje a gabansu.
“Ke ina taki kujerar?”
Hurriya na kallon Namra sai suka yi ma juna murmushi saboda tunawa da ta yi da cewar ta fada cewar zata tsaresu da ido har sai ta gano komai.
“Tana falo tana jirana, a sha ruwa lafiya”
Ta bar shi a gurin ta wuce, sai ya bita da ido har sai da ta kauce daga ganinsa sannan ya juya ya kalli Namra.
“Kanwarki nan tana da kirki, kuma tana da kyau ba zan yi karya ba”
“Yeah haka ake yawan fada duk ta fimu kyau, kuma maganar gaskiya ta fi mu kirki, Hurriya tana da kirki sosai”
“Maa Shaa Allahu haka ake so, ina take karatu?”
“Tukuna nan dai bata fara jami'a ba”
“Why? Takardunta ba su fito ba ne?”
“Sun fito kuma sun yi kyau domin tana da kokari sosai, akwai abun da Appanmu yake jira ne shiyasa be saka ta ba”
“Ko aure za'ayi mata?”
Ta yi dariya.
“Mu ma da muka gama jami'a muke maganar zuwa NYSC ba a yi mana aure ba balle ita, ita ce karama a gidanmu yanzu”
“Oh... Na tambaya da tsoro fa, i thought answer ki would be yes”
Ta yi murmushi mai alamar tambaya.
“She's too shy bata son tsayawa ma, tana son saka glasses kuma yana mata kyau”
“That's because of her illness bata gani sai da gilashi”
“Whoo..what... Wow...”
Ya juya ya kalli part din Momy kamar zai ganta tsaye a gurin.
“Wow...”
“Wow... ”
He said for the third time.
“You make me like her more.. Gaskiya duk wanda ya samu yarinyar nan ya dace, and i think I'm the luckiest guy”
Namra ta kalleshi tana murmushi da ya zame mata kamar na dole ne.
“Hmmm”
“The true is i like your Sister so much Namra, kuma na zo nan ne saboda na yi magana da ita, amman na ga tana da kunya sosai ko tsoron mutane take ne i don't know”
Namra ta sauke idonta kasa zuciyarta ta fara bugawa da mugun karfi, but she managing to wear her light smile on her face. Ya mike tsaye ya nufi gurin motarsa sai ta bishi da kallo har ya isa ya bude ya dauko abun da zai dauko ya kamo hanyar dawowa. Sai da ya kusa isowa sannan ta share hawayenta, not because of tana sonshi but because of disappointed, all her life ta dauka ita yake so ba Hurriya ba, yawan tambayarta Hurriya da yake ba saka ta kawo a ranta son Hurriya yake ba. A gurin da ya da ya tashi ya zauna ya mika mata ledar farko kamin ya mika mata ta biyu
“This one is for you, wannan kuma na Young Lady ne, last time i asked for her contact kika ce bata da waya, so na saka mata waya a ciki, ban sani ba ko za a barta ta yi amfani da ita, idan ma ba a barta ba, ba ki iya amfani da ita, ni dai abun da kawai nake bukata ta fahimci me yake tafe da ni, kuma ta tsaya ta saurareni, ta nan zamu fahimci juna da ita kamin iyaye su shigo ciki, idan Allah yayi, amman kna son ta san cewa ba da wasa nake ba, so ina ganin ke zaki min wannan kokari ki fahimtar da ita”
Ta amsa mishi da kai sannan ta mike tsaye rike