HURIYYA 1&2 COMPLT BY KHADEEJA CANDY

Author :  KHADEEJA CANDY Category :  Romance

Chapter   45 / 86

132K to 135K   out of 257.5K words

shi ya ba ni”

Khairy ta kama hannunta suka zauna bakin gado.

“Ba ni labari shi ma sonki yake?”

“Aa ni aa”

“To ai kin san ke din mai kyau ce ga farinjini, tsaraba ce?”

“Haka nan dai ya ba mu”

Hurriya ta amsa tana jin kanta guilty saboda ta yi karya, abun da ba halinta ba.

“Dan'uwan Momy ne ko, ina yawan ganinshi ai ance dan yayanta ne”

“Eh”

Ta amsa tana daukar dayan chocolate din ta mika mata, a nan Khairy ta juya ta kalli bayanta, Chocolate ta gani ba daya ba ba biyu ba uku ba zai kai 12 kala dabam dabam kuma duk masu tsada.

“Kin ce ba sonki yake ba, amman ya kawo miki chocolate haka, maybe dai baki son na sani ne ko? Haba Hurriya ki dauke ni kamar kawarki mana, ko da yake dai be kamata na takuraki ba”

Ta mike tsaye.

“Daman Hajiya ce ta ce na kiraki”

“Ni kuma? Me na yi to?”

“Sai kin yi laifi za a kiraki? Haba Hurriya karki ma Hajiya wannan kallon mana”

Hurriya ta hade yawu tare da sauran chocolate din dake makoshinta, gabanta ya shiga faduwa ita dai ta san alheri baya sakawa Hajiya Kaltume ta kirata, sai da ta wuce gaba sannan Hurriya ta bi bayanta gaba daya ta saka mata tunani cewar Hajiya Kaltume tana nemanta sai ta fara tunanin ko fitar da suka yi ne a dazun, ko dai wani abun aka shirya mata? Ko Hajiya Binta ta sake yi ma Hajiya Kaltume wata maganar ne? Da tambayoyi kala kala ta sauko stairs din, a daidai lokacin da Captain yake hada takardunsa Namra na saka masa laptop din a jakarta. Sai da ta fara kallon Khairy kamin ya kalli Hurriya dake biye da ita a baya, a shi da alaka ta Hurriya dan haka ba shi da hurumin tambayar ta ina zata je ko kuma da waye take tare. Sai da suka fice sannan ya kalli Namra ya ce.

“Amman wannan yarinyar tana shaye shaye ko?”

“Me ka gani?”

“Fada min kika yi?”

Ya jefa mata bakar magana kamar yadda ya saba.

“Allah ya baka hakuri, tambaya ce kawai”

“Ni m amsa na bayar, ke ma idan kika fara yi zan gane”

Namra ta yi murmushi tana mamakin yadda yayi saurin ganewa bayan kuma bata fada masa ba.

“Amman ba a tabbatar ba, haka dai ake zargi saboda friends dinta wasu daga ciki suna yi”

Be ce mata komai ba ya daga kansa ya kalli Momy ya kalli agogonta.

“Tun dazun ake ta kirana Momy sai gobe idan na dawo”

“Zaka dawo”

Ta tambaya daga inda ta tsaya ganin kamar yana sauri, ya daga mata kai.

“Kullum zaku rika ganina har na gama watannin da zan yi In Shaa Allah”

“Haka nake so, Allah ya taimaka ya maka albarka Jameel”

“Ameen”

Ya amsa suna hada baki da Namra, sannan ya karbi Laptop dinsa.

“Dauko min wasu kayan da suke dakin Musib”

“Okay”

Ya fita Momy na binsa da kallo, Namra kuma ta nufi stairs domin dauko masa sauran kayansa. Dan lokaci da ta bata kamin ta kawo masa jakarsa da ipod da agogon daya cire a dazun, har ya fusace ransa gaba daya bace, tana bude kofar falon ya ja motarsa ya barta nan tsaye rike da kayan tana kallonsa.

“Kuma har ka yi fushi?”

Ta juya ta koma cikin falon.

“Be karba ba?”

Momy ta tambaya tana operating remote ganinta da rike da jakar ga kuma fuska na bayyana labarin zuciya.

“Wata kila cewa zai yi na bata lokaci, wai har yayi fushi”

“Ya kamata ki saba, ki lura da duk wasu abubuwan da baya so ki rika kiyayewa, kin ga yanzu hankalinsa ya dawo gidan nan wata kila ma saboda ke ne, kuma kin san halin Captain ba sai an fada miki ba shi da fushi da zuciya da saurin kai hannu ba su da maraba”

“Amman Momy wani lokacin abun sa ya kan yi yawa, dauko kaya kawai sai ya zama laifi?”

“Toh haka Allah yayi dan'uwanki ya zaki yi? Je ki aje kayan amman make sure kin kira shi a waya kin bashi hakuri”

Ta lumshe ido ta bude alamar damuwa.

“Shiyasa ya kasa zama da budurwa, komai aka yi masa bacin rai ne”

Momy bata bi ta kanta ba ta cigaba da kallon tv ba. Namra ta yi wuce da kayan ta fara taka stairs.




HURRIYA POV.

Da tsoro ta shiga bangaren na Hajiya Kaltume, da farko ta ji tsoro ganin Yayanta da Salma a falon sai ta yi zaton za ace ta yi wani abun ne, cikin karfin hali ta gaishe shi ta gaishe da Salma, yanayin yadda ya amsa mata ya fahimtar da ita bata da laifi a gurinsa. Khairy ta zauna kusa da shi.

“Wai yau na gaji da yawa, ina yin Sallah Ishan'i zan sha magani na kwanata”

Yasir ya dubeta

“Maganin me? Aikin me kika yi kika gaji?”

“Pain killer nake son cewa, zan shafa a kafa driving na yi yau mun yi yawa sosai”

“Good shiyasa na yi ta shigowa ina ganin kowa ban da ke, ke kawai kin fi son rayuwar waje, ki je yi ta abubuwan da kike so babu mai ce miki uffan, kawaye ma idan an rabaki da wannan gobe da wata za'a ganki? Khairy abun da kike yi fa ba shi da kyau, kuma ina miki fada ne ki gyara ba dan ni kadai ba sai dan ke kanki da future dinki, idan kika dauko wani abun magana ko, mutane za su zageki kuma kimar gidan nan zata zube, amman ke da Hajiya kun kasa gane haka”

Salma ta ce.

“An kusa aurar da ita Yaya ka kusa hutawa”

“Mtscheeeeee”

Tsaki Khairy ta yi ta mike tsaye, ita dai har yanzu ba wani son auren take ba, ganin take gana cikin cin lokacin ta ne za a yanke mata, ko da wani ne balle Fadeel da ke da mata kuma da dukan alamu ba zai dauki irin rayuwar nan ta barin mace ta yi wasu abubuwan da suka tsabawa dokar Musulimci da al'adar Malam Bahaushe ba.

“Hurriya shiga ciki Hajiya na kiranki”

“Toh”

Hurriya ta nufi stairs din tana jin cewar idan dai ba mahaifinta zata tarar a dakin ba irin wacan karon da aka koreta, to komai mai sauki ne domin zagi da wulakanci na Hajiya Kaltume ta saba da shi dan haka be daga mata hankali. Sai da Hurriya ta haye sama sannan Khairy ta kalli Yayanta cikin sifar magiya da lalama ta ce.

“Yaya dan Allah ka daina irin fadan nan a gaban Hurriya”

“Hurriyar bakuwarki ce? Ko kuma ita wata bare ce da ba zan miki fada a gabanta ba? Kuma da kin zama yadda nake so zan miki magana ne? And Salma was right idan an miki aure dole ai ki tsanu, and wannan ya zama na karshe da zaki fita ba tare da kowa ya san gun da zaki tafi ba! Dazun na tambayi Hajiya tace min baki fada mata gurin waye zaki je ba, ki daina wannan dabi'ar tun a yanzu”

“Zan daina Yaya ba zan sake fita ba tare da na fada”

“Ya fi miki, ai saboda kun samu Appa yana musu sauki ne yanzu, ace kamar baya ne da yake daukar zafi baku isa duk ku yi wannan ba, kuma ko. Yanzu idan kika sake irin haka sai na fasa miki jiki”

Ya mike tsaye.

“Yaya, ka yi hakuri dan Allah ba zan sake ba, ko dazun ma fa ba ni kadai na fita ba, tare muka fita da Hurriya ita tace gidan so boring shiyasa muka dan fita ta samu ta sake ita ma”

“Ki dai koya mata fitar kike so, shekara nawa tana zaune a gida bata gidan so boring sai a yanzu, ita ma ta fara raina wayon mutane, wata fadawa da zata fita?”

“Ita ai bangaren Momy take laifin ba na Hajiya ba ne”

“Shiyasa kullum Rukayya ke fadar na kula mata da Hurriya, wani lokacin sai a rasa ta ina ma za'a fara controlling dinku Mtscheeeeee”

Ya karasa yana jan saki, Khairy da Salma suka kalli juna a gurin da Yasir yake ambatar sunan Rukayya. Sai dai babu wanda ta isa tace wani abu domin sun san halin yayan na su. Sai da ya fice sannan ya Khairy ta koma kusa da yar'uwarta suka tasa gulmarsa da na Rukkayya.


HURRIYA POV.

Ta shiga dakin na Hajiya da Sallama ta zauna a kasa tana gaisheta, Hajiya Kaltume ta amsa irin amsawar nan kamar ta dole fuska babu yabo ba fallasa, idan ta kalli Hurriya wani kololin bakinciki ke taso mata saboda tuna Iyami da take yi.

“Lafiya Kalau, ya jikin Iyami? ”

“Ta ji sauki”

“Eh”

Ta daure ta kirkiro murmushin yaƙe.

“Maa Shaa Allah, haka ake so ai, Allah ya kara rikawa yanzu tana tafiya ko?”

“Aa bata tafiya”

“Ah ah kuma kika ce ta ji sauki?”

Hurriya ta yi shiru idonta da kanta a kasa kana ganinta ka ga natsantsiyar yarinya.

“Tana iya tashi zaune da kanta?”

Huriyya ta yi shiru na dakiku kamin ta girgiza kai.

“Ashha dai, Allah yasa jinya ta zama kaffara, ni fa ina son naje na dubata amman ina gudun ka ce na ce, idan kin je dai ki gaisheta”

“Toh Hajiya”

Hajiya Kaltume ta dauko wayarta ta bude Gallary ta kama hoton wani farin lace ta mikawa Hurriya wayar.

“Duba ki gani, daman wani Lace ne nake son na siya muku”

Bata yarda ta karbi wayar ba, a madadin haka ma sai ta bi Hajiya da wani kalami.

“Aa Hajiya na gode”

“Toh har da kyautar Iyami ta hanaki karba?”

“Aa Hajiya ai Amma bata iya magana, bata ce min kar na ki karbar kyautar kowa ba, ni ce dai ban karba a karan kaina”

“Toh tashi ki kara gaba, daman duk yadda aka muku mutuncin sai kun ce ba ayi ba, an riga an gado bakin hali, daman ni ai ba so na zaku yi har abada”

Hajiya Kaltume kamar wanda ta zare haka ta rika fadawa Hurriya kalamai marar dadi, Hurriya dai bata dauki ko daya a nan gurin da ta fada mata su a nan ta bar su, ta fice daga dakin. Fitar Hurriya da kamar minti goma Kulu ta shigo dakin ta zube kasa tana dagawa Hajiya hannu kamar wata sarauniya ko matar sarki.

“Ranki ya dade gani, Khairiya ta fada mjn ina nema ma na fito har na kusa sai na hango ta doso nan tare da Hurriya shiyasa na koma”

Hajiya Kaltume ta yi kamar bata ji ba ta shiga wani bangaren na wayarta, kamin ta kara wayar a kunnenta.

“Yasir kana kusa?”

Yasir ya amsa a dayan bangaren.

“Eh ina nan waje, muna tare da Kamal ne”

“Asibiti nake son mu tafi idan ka gama”

“Waye ba lafiya”

“Ni ce, amman dai da sauki, ka bari sai ka gama ni ma akwai abun da zan yi yanzu”

“Toh”

Ta sauke wayar ta kalli Kulu, sai a lokacin take amsa mata maganar da ta yi.

“Ai kara da kika yi haka, saboda kaucewa ido”

“Duk wani abun da zai saka Momy ta ji ko ta gane akwai alaka a tsakaninmu ina kokarin ganin na gujewa haka”

“Kin kyauta, dabam na ce a kira min ke ne, saboda mu yi wata magana da ke, kamin nan tashi ki tura kofar dakin”

Kulu ta kike tsaye ta nufi kofa da ta bari a bude ta rufe, sannan ta dawo ta zauna ta natsu sosai tana sauraren matar da ta fi tsoronta a yanzu fiye da uwar dakinta.

“Aminci ne ya saka na nake tambayarki abu ko na saka ki yi, na san ba dan kin dauki sarka da kudi ba, wata kila ba zamu san juna ba, amman bana son kina kallon wannan a yanzu, ni daman tuni na tattara wannan abun na aje a gefe daya”

“Hajiya ai ba dan karki ce na yi karya ba, nikam da nace satar nan ta zame min alheri domin sanadinta na hadu dake”

Hajiya Kaltume ta sauke ajiyar zuciya ta marairaice fuska.

“Kulu ke da yar'uwata duk daya a yanzu, shiyasa har na kira ki nake son na fada miki damuwata, kuma neman samun mafita a gareki”

“Hajiya tafi kanki tsaye, duk wani abun da kike so zan miki shi, yadda kika rufa min ba ni da kamar ke a duniyar nan”

Dogon numfashi Hajiya Kaltume taja ta sauke sannan ta furta.

“Kulu ina cikin damuwa da matsala kala kala, amman wanda ta fi min yawa, ita ce ciwon kafar nan dake damuna, yanzu haka kiran da kika ga nayi ma Yasir ita zan kai asibiti, na dade ina ciwon nan amman har yanzu babu sauki babu alamarsa, tun ina barin ciwon a cikina abun ya fara min yawa, to yanzu kuma sai abin da biyo har da mafarkai da ba su dace ba, kuma ciwon nan sai cigaba yake, abun ya ba ni tsoro, ga maganin asibitin nan yi ake amman a banza”

Kulu ta dukufa a tunani har wani kada ido take tana jinjina kai.

“Hajiya ba zaki gwada na hausa ba? Ko Allah zai saka a dace?”

Kamar an yi ma Hajiya Kaltume albishir haka ta ji, saboda Kulu ta sosa mata gurin dake mata kaikaiyi.

“Shiyasa na kiraki ai, kin san ku ne mutanen kauye, kun fi sanin irin abubuwan nan, wata kila ba zaki rasa sanin masu irin aikin ba”

“Akwai su Hajiya kala kala, akwai wata mai aljannu tana bada taimako sosai, kuma akwai namiji ma yana yi”

“Yauwa namijin dai zai fi, ni ban cika son mata masu aljanu ba, na fi son inda zan tafi a fada min ko minene, jifa ce ko kuma ciwo ne ko iska ne”

“Aiko kina tafi gurin Malam na gangare zai fada miki ko menene, domin shi baya son ma ka fada masa abin da ya kawo ka shi zai baki labarin komai, har abun da baki sani ba, da madubi yake aikinsa yana kallo madubi ya fadi magana ta tabbata, kuma ko minene a take zai rabaki da shi, idan jifa aka yi miki ko turbuda a take ma zai ciro shi”

Hajiya Kaltume ta dauki filo ta dora a cinyarta ta kwantar da hannayenta akai tana gyada kai.

“Yauwa irin su nake so masu aiki kamar yankan wuka masu zafi”

“To idan kika kai gareshi magana ta kare, domin shi ko mutum kika ce ya kashe miki zai kashe”

“Irinsa ya dace, kin ga ko minene a take zai fada maka kuma ya karya shi, a ina hake Kulu?”

“A kauye uku yake, dake nan cikin bunguɗu”

“Babu nisa sai dai ban san yanayin hanyar ba?”

“Hanya lafiya kalau take, ai garin mu babu irin bata gari, su kansu suna tsoron mutanen yankin”

“Maa Sha Allahu, sai dai kuma tafiyarmu kamar ba zata yi a tare ba, saboda uwar dakinki Nafisa ba zata bari ba nake gani”

“Wannan ba matsala ba ne Hajiya, kina shiga garin Bunguďu ki dauke hanyar kauye uku, da kin isa ki ce gidan Malam Ashiru mai Yasin da Allon karfe kike nema, ko karamin yaron zai kai ki, idan kuma kina jin ba zaki iya haka ba ke nemi gidan su Kulu taroro kina shiga gidan ki ce ni na aiko ki gurin Malam Ashiru za a kai ki, zaki iya ma kira na yi magana da su”

“Allah dai ya saka miki da alheri Kulu, ina ganin ma ba zan tafi asibitin nan ba, gobe ina gama karyawa zan kama hanyar garin, zan iya tafiya da direba na ma ya kai ni garin”

“Daman Hajiya tafiya da daren ba ai ya fi sirrin da sauki”

“Haka zan yi, zan fara zuwa gidan na ku sai na kira na ba su ku gaisa idan ya so sai kun iso gurin Malamin zai fi sauki”

“Toh Hajiya, Allah ya bada lafiya”

“Amin”

Hajiya Kaltume ta mike tsaye daker tana cige baki kafar kuma kamar zata yi gurmanta da ita haka ta taka ta isa gurin kayanta ta bude wardrobe ta dauko wani lace da ba a dinka ba ta jefawa Kulu.

“Ahhhhh Kai Hajiya duk ni kadai? Alhamdulillah Hajiya na gode na gode, Allah ya kara rufa asiri ya biya bukata, Allah ya kara lafiya ya tsare ki daga duk wani sheri”

“Amin, wani abun kulu ai sai na samu lafiya ma, da yardar Allah idan bukata ta biya zan kyautata miki, ta shi ki tafi kamin Yasir ya shigo”

“Toh Hajiya, amman zan bar leshin a nan saboda idon mutane, sai idan na ga sarari zan zo na karba”

“Dadina da ke wayo Kulu kin iya sirri”

“Gidan na mu ne Hajiya sai da haka, kamin a fara fadar ana ganina bangarenki ”

Hajiya Kaltume ta yi murmushi. Ita kuma ta mike tsaye ta yi mata sallama.

“Mu kwana lafiya”

Kamin ta isa kofar dakin ta bude Yasir ya bude sai dai be shigo ba ya bata hanya ta fita yana amsa gaisuwar da take masa.

“Me ta zo yi nan?”

Hajiya ta nuna masa lace din dake kasa

“Nafisa ta aiko min da lace?”

“Ke kuma?”

Ya tambaya kamar mai shakku, Hajiya dai bata sake ce masa komai ba ta nufi gurin da ta tashi ta zauna da tafiyar nan nata kamar zata yi dingishi.

“A kafa kike jin ciwon ne?”

“Eh gurin da na taba jin ciwo kwanan baya, a nan na sake jin ciwo haka nan kawai sai na ji kamar an tureni na fadi kasa”

“Ko santsin gurinki ne ke janki”

Ya soma duba kafar da ta dan dago masa tana jin kamar ana yanka gurin sai sululi yake mata kamar an watsa ruwan zafi.

“Aa ba wani tsantsi shekara nawa ina gidan nan da can tsantsin be ja ni ba sai yanzu? Turo ni ake yi fa”

“To wa yake turoki Hajiya”

“Yo ina zan sani tun da abu ne na aljanu, amman tabbas ba faduwa ce zallar faduwa ba, turo ni aka yi”

Yasir yayi murmushi tare da kai hannu ya latsa gurin.

“Ban san me yasa ku mata kuke yarda da irin abubuwan nan ba, haka Last week Rukayya take ce min wai ance aljannu ne a jikin Amma, ku dai komai kun fi son ace aljannu ne, wani abun fa daga Allah yake kai tsaye idan ana na asibiti zaki ga an dace, ita kanta Amma da za a fitar da ita waje a dubata duba mai kyau za a gane Matsalarta”

Hajiya ta janye kafarta da sauri saboda lasa gurin da Yasir yake yi.

“Ku kuma ba ku yarda da aljannu ba ko?”

“Mun yarda da su mana, amman ba lallai komai ace su ba, kin ga kafar nan take da zaki iya daurewa mu bari sai da safe mu tafi asibitin, hoto za su miki su duba matsalar”

“Eh haka zan yi, mu hakura

45 / 86