Author : KHADEEJA CANDY Category : Romance
cewa mahaifinta baya a gidan sai idan wani abu ya dawo da shi ko kuma ya hana shi fita, dan haka Hajiya Kaltume uwargida, nan ma sai da ya ki bacin ranta da take ganin za a cusa mata, ta bawa zuciyarta hakuri ta danne duk wani abu da zata ji tun gabanin su fada mata, sannan ta tura kofar ta shiga. Sukan na su falon a cike yake suna ta murnar dawowar Salma, sai dai ganin Hurriya ya saka sun tsaya cak suna kallonta kamar irin wanda aka jefo daga sama daga gabansu.
“Hurriya”
Hajiya Kaltume ta fada da mamakinta karara a fuskarta.
“Na'am Hajiya ina wuni, Yaya Khairy Yayana, ina wuni yaya Salma sannu da zuwa”
Salma ta amsa tana kokarin boye munafurcinta a cikinta.
“Lfy kalau”
Yasir kuma ya ce.
“Lafiya Kalau kanwata, na jidadin da kika dawo, Hajiya kin yi abun da ya dace”
Hajiya Kaltume ta yi murmushi, wani abun da ya bawa kowa dake falon mamaki ciki har da Hajiya Kaltume da ita kanta Hurriya shi ne tashin da Khairy ta yi ta koma kusa da ita ta rumgumeta tana far'a.
“Alhamdulillah, Allah ya kawar da bacin rana na jidadin da kika dawo, I'm so happy”
Hurriya ta kalleta har tana rasa abun furtawa, mamaki ya lake mata a zuciya.
“Ina taje ne ake ta murnar dawowarta?”
“Abubuwa da yawa suka faru Salma sai kin zauna zaki sha labari”
Khairy ta amsa bayan ta saki Hurriya.
“Ni ma fa ina da labarin da zan baku, kuma dukansu sai mamaki ya kama ku”
“Mamaki zai wuce ki ce kin samu wanda kike so zaku yi aure soon bla bla bla ni ma aurar da ni Hajiya take kokarin yi fa, ga Fadeel kin san shi ai dan Hajiya Fatee”
A yanzu ma Khairy ce ke amsawa Salma tana dorawa da zancen auren dake ci mata rai. Da mamaki Salma ta kalli Hajiya ta ce.
“Da gaske Hajiya? Fadeel ba yana da mata ba?”
Hajiya ta daga mata kai.
“Yana da mata amman kirkinsa ne ya saka nake son ba shi auren saboda ya nuna yana son Khairy”
Yasir ya mike tsaye daman shi ba gwani ne na sauraren irin wadannan maganganun na mata ba, dan haka ya kalli Hurriya.
“Muje waje Hurriya ina son magana dake”
Hurriya ta juya ta nufi kofa, tana gaba daya bayanta, sai da suka fice sannan Salma ta kalli Hajiya Kaltume ta ce.
“Har yanzu yaya ganin mutuncin yarinyar yake yi?”
Khairy ta tabe baki.
“Hmmm me za'a fasa kwanan baya saboda yarinyar nan ya lalata min birthday”
“Amman hugging dinta kika yi yanzu fa, kina murna dawowarta”
“Toh ai Salma idan baka iya kama barawo ba sai barawo ya kama ka, kara ina haka idan ba haka ba wani abun na samunta nan gaba za a iya cewa ni ce”
“Nikam i can't fake love, shiyasa wannan kawar tawa ma na ja mata kunne”
“Wace kawa wai?”
Salma ta gyara zama tana kara fitar da sauti saboda labarta musu abun da ta kumso.
“Hmmm Appa be fada muku zai kara aure ba?”
Sai a nan Hajiya Kaltume ta yi murmushi mai sauti ta ce.
“Ya ma isa Salma? Duk bayan wahalar da muka sha, ga tarin tashin hankali da munafurci da ba mu gama fuskantarsa ba saboda Nafisa da Iyami? A yanzu kuma da ya kamata ace ina da ikon gida ya tunkare da zancen aure? Haba wa..... Ba dai shi ba sai idan wani kuma ko kuma idan na mutu”
“Hajiya wannan fa ba wasa ba ne, abu ne da na gani da idona, and she's my friend muna daf da kare karatun nan take suka hadu, tana da va ni labarinsa but ban dauka Appa ba ne sai yau da muka sauka airport”
Hajiya Kaltume ta karkata da kyau tana kallon Salma dake magana with full confidence.
“Motar da ta dauke ta ma daga Airport ta kaita gida, Appa ya kawo, ban kara yarsa shi din ba ne har sai yau da ta fada min cewar shi ne mamallakin Yadi's Motors”
“Ho... How... How... Comes....”
Cewar Khairy tana kallon yar'uwarta.
“Boye min ta yi, amman ta fada min cewar yana da mata biyu ya saki 3rd wife dinsa yana da yaya maza hudu dayan ya rasu, yana da yan mata bakwai, amman na zama wata sakarai da ban gane ba har sai a yau da ta fada min wai sunan wanda take son ta aura Alhaji Haruna Mai Yadi, and she was telling me shi ya aiko da motar nan a dauke ta”
“Amman baki mareta ba? Ta fa san mahaifinki ne?”
“Ban mareta ba, amman na fada mata zata jefa kanta a matsala ne kawai dan haka ta rabu da mahaifina tun wuri, ni babu abun da ya fi bata min rai ma kamar yadda na zama sha sha ban fahimci mahaifina ba ne har sai da ta fada min, bayan kuma ita din ta sam cewa mahaifina ne domin sunana Salma Haruna Mai Yadi, and the most annoying part is yarinya ce kamar ni sai barikin tsiya”
Hajiya Kaltume ta girgiza kai.
“Aa ni dai ban yarda da wannan ba, ko dai akasi aka samu ko kuma wani abun ya hada su take zaton sonta yake, amman ni na san dalilin da ya saka mahaifinku ba zai kara aure ba, kuma idan har zai kara din zan riga kowa sani”
Salma ta yi dariya.
“Okay idan baki yarda ba, zan baki duka nunbers dinta ki saka a wayar Appa, ko kuma ki kawo ni na saka ko Khairy ko kuma ki yi wata dabara mu duba Instagram chat dinsa dan na fi kyautata zaton nan suka hadu”
Khairy taja tsaki.
“Ni Wallahi wannan auren auren na Appa yana damuna, daman tun da na ga gidan nan da part hudu na san yana da burin karo wata, kuma yanzu Fisabilillahi ace sa'ar yarsa kawarta ma? Haba...!”
“Wannan burin ada ne ba, ba yanzu ba duk wacan rayuwar ta kau, ku kwantar da hankalinku babu wani aure da zai kara, ni ban ma yarda zancen aure ne tsakaninsu ba ko soyayya”
Cewar Hajiya Kaltume tana murmushi, sannan ta mike tsaye yana fadar.
“Yanzu dai an huta yar'uwar shawara ta dawo, sai ku shirya duk abun da kuke ganin ya dace, zan sanarwa Appanku kamin Iyayen Fadeel din su zo”
“Hajiya Fadeel dai? Yana da mata fa? Kuma kin san yadda sherin kishiyoyi suke tun da muna cikinki”
Taku kadan Hajiya Kaltume ta yi ta dafa kafardar Salma fuskarta da murmushi.
“Kyakkyawar makoma ake buri, bana fatar kowa ya sake yin irin auren da Maama ta yi, tana can yana gana mata azaba, matarsa ba matsala ba ce domin Hajiya Fatee bata sonta, kuma saboda matarsa take son ya auri Khairiya saboda Khairiyyah ta share mata hawayenta, fata muke kamin ma ta shiga cikin gidan matarsa ta fice”
“Idan ta fita kina ganin Khairy zata iya rainon yayanta? Kuma yadda Hajiya Fatee ta tsani matarsa zata iya juyowa ta tsani Khairy fa...”
Khairy ta kada kai kamar kadangaruwa domin an taba mota gurin da yake mata kaikaiyi.
“Shi nake kokarin nunawa Hajiya ta gagara ganewa, ni har yanzu Fadeel din nan be kwanta min a rai ba”
“Ku yara ne ba zaku gane ba, gaba nake hango muku Hajiya Fatee kuma bata isa ta tsani Khairy ba har abada, kar ta san kar ne ni da ita, kuma ba ido zan zuba mata ba, tun kamin a tafi ake shiri ba sai an dawo ba, dan haka ki kwantar da hankalinki Khairy ki saki jiki ki saka kaunar Fadeel a ranki”
Salma da Khairy suka kalli juna kamin su kalli Hajiya su saka dariya, ita kuma ta yi murmushi ta fice ta bar musu falon, su suna dariyar ta kasa fahimtarsu kuma duk yadda take ganin abun zai zo da sauki ba zai zo, ita kuma tana murmushin abun da take hango ma Khairy wanda ta kasa ganewa.
“Hajiya ba zata gane ba”
Salma da har lokacin dariya take ta ce.
“Ina fa, kin ga ko maganar Appa musawa take yi, kuma Wallahi gaskiya ne, haka ta yi a auren Maama tana cewa tana hango mata jindadi ne saboda yana da kudi gashi nan yanzu kullum da kalar azabar da yake nuna mata, last week na muna chat take fada min yanzu har mata yake kawo mata a gida idan ta fita”
“Kullum fa iskancinsa gaba yake, ni ba zan ma iya daukar wannan iskancin da yake mata ba, ita kuma kamar an mata magani ta kasa rabuwa da shi”
“Ni kaina ba zan iya ba, kuma wai Hajiya ta kyaleta sai iskanci yake ma mutane yadda ya ga dama”
“To ya za'ayi idan ace za a masa magana ita take shiga ta tare, kar a taba mijinta wata kila sai da ya mallaketa sannan ya aureta”
Salma ta tabe baki ta sauka daga kan kujerar ta zauna a kasa.
“Ke ba ni labari ya aka yi Hurriya ta bar gidan?”
Sai da Khairy ta kalli kofar falon dan tabbatar da Yayansu ba zai shigo ba sannan ta fara bata labaran abubuwan da aka yi bata gidan.
HURRIYA POV.
Jerowa suka yi suna tafiya yana ta yi mata nasiha a matsayinsa na yayanta.
“Wallahi Yaya duk yadda kuke tunanin abun yake ba haka ba ne, ni bana munafurci ko zancen Abban su Husna ni da ita kawai na san na yi magana kuma maganar karatu kawai muka yi sai take ce min lokaci yana kurea na fada mata Appa nake jira, ban san yadda aka canja zancen ba abun har ya kai mahaifinta ya samu Appa da maganar”
“Wacan ya wuce, komai ya wuce yanzu kawai ina jan hankalinki ne akan rayuwa, duk wani abun da kika san zai janyo miki magana ko ya bata tsakaninki da mutane ki daina kuma ki gujeshi, ina yabonki Hurriya shiyasa idan aka fadi cewar kin yi wani abu nake musawa ko na yi mamaki saboda na san ba halinki ba ne, dan Allah ki natsu ki daina duk wani abu da be dace ba”
“Ba zan sake ba Yaya ba zaka sake jin an fadi wani marar dadi kaina ba na maka alkawari”
“Yayi kyau, in kin shiga ciki ki ce ina gaishe da Momy”
“Toh Yayana na gode”
Ta wuce ciki shi kuma ya juyo ya dawo bangarensu sai dai be shiga ciki ba ya shiga motarsa ya bar gidan. Sai da Hurriya ta maida kofar falon ta rufe sannan ta lura da Husna dake zaune akan sofa tana sanye da farar abaya. Da gangan Hurriya ta dauke mata kai zata wuce Husna ta yi saurin riketa tana dariya.
“Fushi kike yi da ni saboda ban zo ba kwana biyu?”
Hurriya ta cire hannunta daga jikinta fuska a daure ta ce.
“Ba saboda haka nake fushi dake ba, ina fushi da ke ne saboda kin hada ni da iyayena, abun da kike yi sam be dace ba Husna saboda na yarda dake na saka nake fada miki sirrina ashe fitarwa kike gashi nan kin yi sanadinyar da Appa ya koreni a gidan nan yau na dawo, kuma kowa a gidan nan yanzu ya tsane ni yana min kallo da munafuka”
“Innalillahi ni kuma, dan Allah ki tsaya mu yi magana ta fahimta Wallahi ban yi miki wani sherin ba, kuma mahaifina be zo gidan nan da wata manufa ba, dan Allah mu tafi dakinki mu yi magana...”
Hurriya ta tsaya kallonta kamin ta gyara tsayuwar gilashin idonta ta nufi stairs, Husna ta rufa mata baya, dakin suka shiga suka rufe sai after sun zauna Hurriya ta fada mata abun da ya faru.
“Innalillahi, Wallahi Hurriya ba ma ni na fadawa mahaifinmu ba, Umma ce ta fada masa kuma ita ma ta yi hakan ne saboda tana tausayinki, su a nufinsu idan Appa ya amince sai su dauki nauyin karatun har ki kallama ganin kamar ba a son ki yi karatun, ni ma kuma ban san suna da wannan manufar ba sai bayan sun aikata Umma take fada min wai Abba ya samu Appanku da maganar be amince ba, sun ma yi rabuwa marar dadi, dan Allah ki yi hakuri kar ki mi dawowa fahimta baibai, ban shigo ba shiyasa ban san abubuwan da suka faru ba”
Hurriya ta sauke ajiyar zuciya, daman ta raya a zuciyarta cewar kawarta ba zata aikata mata wani abun da zai jefata a damuwa ba da ganganci.
“Amman Hurriya ke da kika samu komawa gidan Hajiya meyasa kika dawo nan?”
Nan ma sai da Hurriya ta fada mata abun da ya faru, ciki kuwa har da rumgumar da Khairy ta yi mata a yau.
“Eh gaskiya kara da kika dawo, kuma ko yanzu ki yi taka tsantsan, saboda su ya saka bana son yawaita shigowa gidan nan, yanzu kuma gashi kin fada min abun da ake kallonki da shi kuma na san ni za a kalla a matsayin mai tayaki”
“Su suka sani, ai Allah yana shaidata”
“Haka ne, kin ma san abun da ya kawo ni wai?”
Hurriya ta girgiza kai tana kallon Husna.
“Wani abokin yaya ne yace kin san shi sunansa Salim ya ce min har kun yi magana amman ya rasa ya zai shawo kanki, shi ne ya zo jiya saboda ya gan mu tare lokacin da kika je gidan kuma ya tambayi Yayana ya fada masa ni kawarki ce sosai, tare da Yaya ma suka saka ni a gaba wai yana son na lallabaki na karkarto da hankalinki ki fahimce shi, shi ba da yaudara ya zo ba...”
Hurriya ta mike tsaye ta dafe kanta tana yawuta a dakin.
“Ni kam na shiga uku, mutumen so yake ya ballo min wasu ruwan kuma? Yaushe na samu na rabu da Adam shi kuma ya kuso yana son haddasa min fitina, na yi magana da shi na fada masa cewar ni bana sonsa kuma fa ma Yaya Namra yake so daga baya ne ya dawo guna”
“Duk ya fada min, amman yace ke ce baki fahimta ba, ko kuma yayarki ce take son bata lamarin amman shi tun farko ke yake so, kuma Hurriya ni fa ina ganin idan da gaske yake kuma aka bincika yana da halin kwarai sannan aka dace kina sonsa kawai ki aure shi ki huta da wannan gidan, albashi idan zaku yi aure sai ya miki alkawarin zai barki ki yi karatu”
Hurriya ta dawo ta zauna.
“Ni be min ba, kuma na fada masa gaskiya wata kila ma saboda shi ne na ga Yaya Namra ta canja min, sai ta yi zaton ko ina kokarin kwace mata saurayi ne, kuma fa tana son shi, ni gaskiya bana sonsa ni babu ma wanda nake so yanzu”
“Shi kuma yana sonki sosai Hurriya da ace zaki ba shi dama dai zaki saurareshi, ya ce min ma zai zo gobe”
“Dan Allah kar ya zo kar ya hada ni da mutane, ki fada masa kar ya zo dan Allah, Husna kin san halin da nake ciki ki fahimtar da shi mana”
Ta karasa tana cikin son yin kuka idonta na tara ruwan hawaye.
“Zan yi magana da shi, zan fada masa yadda zai fahimta, yanzu ya maganar karatunki”
“Ni dai yanzu ki tashi ki tafi kar ace na shigo da ke a daki muna gulma”
Husna bata da wani aiki a yanzu da ya wuce ta taimaki kawarta dan haka ta mike tsaye ta yi mata sallama, cikin tsoro Hurriya ta raka falo, hankalinta be kwanta ba har sai da Husna ta fice. Sannan ta dafa zuciyarta kamin ta sauke hannun ta koma dakinta, sallah ta yi ta fito falon ta zuba abincin rana ta ci.
**** **** ****
Karamin filo ne a hannunta ta rumgume shi sosai a kirjinta, kalaman da Momy ta fada mata dazun take tunanin, suna kokarin dorata a wani tsani da bata taba hawa ba, zancen ana son su fahimci juna ita da Captain ta tsaya mata a rai. Yana da kyau da za a so shi, yana da cikar halitta da duk wani abu da ake so a jikin namiji, sai dai ganin yadda tsarin rayuwarsa yake ya saka bata taba ayyana ma kanta kaunarsa ko sau daya a zuciyarta ba. Ta dago ta kalli wayarta dake ringing ganin sunan Salim ya saka ta dan yamutsa fuska kamar ba zata daga ba, can kuma ta kai hannu ta dauka.
“Hello”
“Namra ya gida, ko da yake yayarmu ya kamata na ce”
“Haka fa, lafiya kalau ya aiki?”
“Alhamdulillah, alfarma na kira na roka kamar yadda na saba yi, kanwar nan taki dai na kasa hakura da ita, na gwada ko zan iya amman na kasa”
“Toh yanzu kuma me zan yi?”
“Lallaba min ita zaki yi, yau ma zan shigo gidan kuma tare da dan'uwanki In Sha Allah”
Har zata tambaya ta ce wani dan'uwanta sai kuma ta ji bata bukatar hakan, domin ya nuna ba ita yake ra'ayi ba, dan haka be kamata ace ta shiga hancinsa ba.
“Okay zan yi kokari, amman daga wannan ba zan sake ba gaskiya, baka fada min ya kuka kare ba a wacan karon”
“Idan na zo zamu yi maganar”
“Okay”
“Thanks”
Ta cire wayar kunnenta tana hautsina fuska, kamar zata ji haushinsa kuma sai take ganin babu dalilin haka. Aje fillon tayi ta sauko saman gadon,
‘Babu wani lalaba ta da zan yi, yarinya ta nuna vata yinka dole ne, ai maganin namiji mai shegen ruwan ido kenan da son mata’
Ta fada a ranta kamin wasu zantunka su fara zagayar kwakwalwarta, yanzu da Momy ta fada mata kudirin da suke da shi akansu ita da Captain sai take ganin wata kila canja mata ne Allah zai yi da son Salim da ta fara, ya bata wanda ya fi shi komai, dan murmushi mai kyau ne ya kawata fuskarta, ta mike tsaye ta nufi kofar dakinta ta bude sai da ta shiga dakin Momy ta duba bata ciki sannan ta sauko kasa domin ta san idan bata dakinta to tana kasa ko bangaren mahaifinsu ko kuma ta fita daga gidan. Tun kamin ta karasa saukowa stairs ta ji fadan da Momy take yi ma Hurriya har da rantse rantsen abun da zata mata idan ta sake zuwa kai tsaye ta bude mata kuloli ta zuba abinci.
“An gama abinci ban zubawa mijina ba, ni ban zuba ba sai ke ki zuba ke gaki issashiya ko? To ba zan daukar miki wannan ba, daga yau sai yau karki sake bude min kula ki zuba abinci ki jira sai na diba, ai na fada