Haihuwa Da Hanji Complete Hausa Novel

Author :  Halima K Mashi Category :  Adventure

Chapter   7 / 53

18K to 21K   out of 158.4K words

da suka dan sake hira kan ya mi?awa salim takardar sallamar ta

"My patient is good to go, kawai dai ta kiyaye sa damuwa a ranta and gaskiya ku kula da ita sossai da sossai Dukda SG Ryan yayi mugun ?o?ari a kanta babu wani traces na guba a jikinta amma don Allah ku sake kula, ke kuma Afeefah ki saka a ranki komai yayi zafi maganinshi Allah. Manzon Allah S.A.W ya ce; "Wanda ya gangaro daga kan dutse ya kashe kansa, to yana nan madawwami a cikin Wutar Jahannama yana ta gangarawa har abada. Wanda kuma ya sha guba ya kashe kansa, to gubarsa tana nan a hannunsa yana ta kwankwadar ta a cikin Wutar Jahannama, yana madawwami a cikinta har abada. Haka wanda ya kashe kansa da wani karfe, to karfensa na nan a hannunsa yana ta soka wa cikinsa a cikin Wutar Jahannama, yana madawwami a cikin ta hakan har abada. (Sahih Al-Bukhaariy: 5778; Sahih Muslim: 109)".

"Allahu akbarr" Baaba jummai ta zabga kabbara Afeefah dai kanta ?asa zuciyarta na sake shiga cikin tsantsar nadamar wannan yunkuri da tayi da ta mutu ta shiga ukunta.
Godiya sossai ta musu haka salim yayi wa Sulaiman da Baba godiya murmushi kawai Sulaiman yayi yana shaida wa Baaba akwai driver waje zai mayar da ita gida sai ga Baaba na hawayen rabuwa da Afeefah Dukda zaman nasu na kwana biyu ne amma sanin ranar sake haWuwa sai Allah, Afeefar ma sai ta kama hawaye, a duk sadda ta ga wani ya kaunace ta Saboda Allah ta kan ji son shi fiye da yadda shi ya kaunace ta don masu hakan a gareta basu da yawa, bata yi shiru ba ko da Baabar ta tafi sai ma zuciyarta da ya tsinke, tsoro da fargaba suka lallaSo suka rufe ta.

Daram! Haka zuciyarta ya buga a sadda Salim ya Wauki 'yan kayanta yana furta
"Mu je ko Afeefah?"

Jiki a saSule ta sanya kafafunta ?asa ta shiga takawa har ta wuce shi yana ri?e mata da ?ofa bayan ta fita ya ja kofan a bayanta ya rufe suka jera a tare har motar shi, ya buWe mata gidan gaba ta shiga ya buWe baya ya ajiye kayanta kan ya zagaya ya shiga ya ta da motar suka fice daga cikin asibitin, cikin natsuwa yake tukin kan ya Wan kalleta

"Anchau muka nufa ko?"
Kamar mai karyayyen wuya haka ta gyaWa kai gabanta na dukan tara-tara, bata fata Uncle ya raba ta da su suhail bata fata su tashi a hannun kishiyar uwa, daga shi har yaran wani irin tausayinsu take ji har Sargonta bata ga laifin uncle ba don ta tabbatar dole mutuwar Aunty zee ta jijjiga shi fiye da ?ima tana fata da adu'ar Allah ya sa ya sassauto ya karSeta kar ya kore ta.

Salim ya gyaWa kai shima, motar ya Wauki shiru na seconds kan yace
"Afeefah!"
A hankali ta amsa
"Na'am"
"Na san kowa abinda yake faWa miki jarrabawa, kaddara ha?uri. nima ba zan chanza ba don akan hakan Allah ya hal??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????icce mu ha?uri kuma da kaddara ibada ne kaman yadda ya halicce mu don mu bauta masa, idan kika ga na wani Afeefah sai kin yi hamdala wani jarabawar shi 'ya'yanshi, wani za ki samu jarabawarshi Mata ne, wani talauci, wani dukiya hatta Mahaifiya ta kan iya zama mummunar jarabawar Wa, kaman yadda rayyan ya faWa kuma Sulaiman ya ba ki har hadisi, da kashe kai shine mataki mafi sau?i a yayin da duniya ta yi wa bawa tsanani da ba za mu tarar da miliyoyin mutane ba a raye, akwai wani hadisi da Manzon Allah S.A.W ya tashi tsoratar da masu yunkurin kashe kansu da ko tunanin aikata hakan ka yi to ka yi gaggawar tuba ka tsarkake zuciyarka daga shaidan. Ban san irin naki ?alubalen ba amma ina sake jan hankalinki da ki kiyaye dokokin Allah ki du?ufa da Adu'a In shaa Allahu komai yayi farko yana da ?arshe kinji ?anwata?"

Kai ta gyaWa mishi a hankali cikin sassanyar Murya tace
"Yaya Salim hakika ba ni da bakin gode muku, kun ceceni daga azabar Allah da baku zo ba a lokacin da ban san a yanzu wani hali nake ciki ba. Na gode Na gode Allah ya yaye maka naka matsalolin ya saka maka da gidan Aljanna"
Ya amsa da Ameen yana Wan murmushi.

Kaman yadda ta zata isar su Anchau kai tsaye gidan uncle suka yi, ko da ya tura yaro yayi mishi sallama da uncle ba'a jima ba sai gashi ya fito idanunshi na sau?a kanta yayi mugu-mugun Waure fuska bai tsaya ma salim ya gama bashi ha?uri da koro mishi jawabin da ya sa bai dawo da ita kan lokaci ba ranar ya shiga karta musu rashin mutunci yana kwashe mata albarka duk yayi wani irin susucewa, sai jefanta yake da munanan kalamai da suka zama tamkar rurin garwashi a zuciyarta, ya shiga tuna mata Alkhairin Aunty zee a rayuwarta da mugun sakayyarta, ya kuma yi alkawarin muddin bata bar mishi kofan gida ba wallahi shi zai kawo karshenta yayi ajalinta.

Kokarin bashi hakuri salim ya shiga yi ganin tana wani irin kuka amma ina tuni ya soma tara musu jama'a babu arziki suka koma mota, ta haWa kai da gwiwa tana ?ara fashewa da wani kukan mai taSa zuciyar duk mai saurare.
A hankali salim ya ja motar sai da suka yi nisa sossai yayi parking tare da jingina bayan sa da jikin kujerar ya lumshe idanu yana sauraren kukan nata da idan har ka ji ka san duniya bata yiwa mai yinsa daaWi. Sai da tayi ma'ishi bai ce mata komai ba da kanta ta Wago ya mi?a mata ruwa ta fita ta wanke fuskanta ta dawo ta sha kaWan kan ta mi?a mishi ba tare da ta kalleshi ba ya sa hannu ya karSa.

"Ki yi ha?uri Afeefah!"
Ta gyaWa kai
"Yanzu ina kuma kike da shi da zan kai ki?"
Hawaye ne ya sake cike idanunta a sadda take furta
"Akwai kawuna a Dutsen-wai"
Cikin dasasshiyar muryarta da ya dishe saboda kuka.
Motar ya ja tare da mi?a hannu ya kunna musu ?ira'a domin zuciyarta yayi sanyi.

Awanni kaWan ya sada su da kauyen, ita tayi ta nuna mishi hanya har gidan kawu Labaran. Yana zaune rumfar kofar gida yana cinikin Nono da wata bororuwa ganin tsayuwar mota ya sa ya shiga shafa rantalin kanshi da babu gashi ko guda sai mai?o yake a rana, a tunanin shi Waya daga samarin yaranshi ganWa-ganWa da suke zaune ba aure ne domin sun rantse sai mai mai?o iyayensu mata kuma sun ba su goyon baya alhali gidanshi ko keken hawa mai kafa biyu babu.
Idanu ya ?ura mata bayan sau?owarta yana tunanin inda ya santa kan ya zabura ya runtuma a guje sai cikin gida, ganinshi da gudu ya sa mata da 'ya'yanshi kowa ya fara yin ta kanshi don tsallake su kawai yake bai tsaya ba sai da ya dangana da Wakinshi ya zaro sandar goran shi tare da wasu manyan layu ya zura a wuya, wasu ya saka a hannu kan ya fito ya nufi waje da saurinshi har yana kifawa....





=???Gureenjoh=???

HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

*FREE BOOK*

*010*

"Hohohooo! Da ma an gaya min za ki dawo, za ki dawo da shirin ki da ya ci uwar na da kuma sai ga ki, to idan ma junanki sammako ni a tafe na kwana yarinyaa! Namana guba a bakin ki dodanniyar Mayu!"

Yadda yake maganan a kan muryarshi ya sa tuni su inna Asabe suka yo waje, abin ka da ?aramin ?auye tuni ma?ota ma sun fara le?owa, daga Salim har Afeefah sun kasa ko da motsi ne barin ma ita da wani tsoro ya sake rufe ta.
Tuni matasa suka shiga neman makami don ma kayan sojoji ne jikin salim kuma harda ?aramar bindigar shi a gefen ?ugunshi.

Kawu ya nufa da yake zaro maganganu tamkar sabon kamu wai enchanting words Win kariya yake daga Mayu ya furta
"Haba Malam! Ba ka gane ta bane? Ya duk ka firgice kaman wanda yayi karo da zaki?"

Kawu ya gyaWa kai ya kuma girgiza yace
"Hayyyaa yaro yaro ne! Ni ko na santa farin sani, kai ma na tabbatar da ka san wacece ita babu abin da zai sa ka bari ta shiga motarka. Wannan mayyar da ta cinye min zuri'a ta je ta cinye na uwarta shine ka dawo min da ita kofar gida?"

Waigawa salim yayi ya kalleta har lokacin tana kafe kyam kaman mutum-mutumi ya waigo ga kawu hes very confused da kalaman da ake jefa mata gwara wanchan ta ce mijin yapendonta ne amma wannan dake wa ga mahaifinta? Ji abin da yake kaman sabon kamun hauka?
"Amma malam ka kuwa san yadda shari'ar maita take? Me yasa za ka jefeta da wannan kalma ta ?azafi? Ita Win fa 'ya ce a gareka kuma addini kai ya Wora wa kulawa da ita da bata kariya tunda mahaifinta baya raye amma don Allah dubi abin da kake yi na ?arancin ilimi, duk ka tara mana mutane? Me yayi zafi haka?"

"Wuta! Na ce wuta ne yayi zafi, wallahi idan baka daina haWa ni da wannan yarinyar ba kai ma sai na rotsa kan ka da wannan sandar bar ganin ka da kayan sojoji, tun muna shaida juna ka Wauke ta sawunku a likkafa ka mayar da ita inda ka Wauko ta ai Zainabun ma sai da na gargaWeta taurin kanta ya ja mata... Ni ma zaman da nayi da ita shekarun baya ban huta ba da neman kariya da yanzu babu wanda za ka tarar anan da duk ta lashe kurwowinmu"

Ya hayayya?o wa salim da ba?in ciki haWe da wani irin takaicin su ke shirin kashewa, ita dai ban da kuka babu abin da take kaman ranta zai fita hannayenta duk biyu bisa kanta jikinta na wani irin rawa.
Ya godewa Allah da ba da Rayyan ya zo ba yau da kuwa yanzu wani zancen ake ba wannan ba, duk ha?urin salim sai da su kawu suka kai shi bango, ya kaWa ya rawa a kan su karSeta sai dai cin mutunci kawai suka karta musu da kalamai masu zafi suka ma fara yunkurin far musu da sunan haushin ta dama suke ji haka ya dau?eta suka wuce suka bar garin gudun fitinar da zai iya kunno kai idan suka ci gaba da tsayuwa.

Shiru ne ya ratsa motar sama da awa guda sai tsula uban gudu yake ita kuma tana ta aikin kuka.

"Afeefah ya isa haka don girman Allah ki yi ha?uri, ki karSi wannan ma a jarabawa. Akwai inda zan kai ki kuma?"
Yayi maganan yana kallonta, Wago ido tayi ta kalleshi sai da ya ji wani yarrr a jikinshi ganin yadda idanunta suka koma tsabar kuka, Wauke kai yayi har ?asan Ranshi yana jin Wacin da bai sani ba ba?in cikin su kawu ne ko menene oho.

"Ba Za ka tambayi wacece ni ba? Ba ka ji kana son sanin ni Win Mayyar ce da gaske ko akasin hakan ba? Ba ka ji kana tsoro da shakkar taimakona ba?"
Ta faWa cikin dasasshiyar muryarta har lokacin idanunta na a kanshi.

Ya samu wuri yayi parking kan ya waigo gabaWaya yana kallonta
"Ki gane wani abu Afeefah, Na riga na saka a raina taimakon ki ya zama min dole. Batun sanin ko ke wacece ba zan ce miki bana son ji ba amma ba na son tilasta ki ba ni labarinki, idan muna tare watarana zan sani. Ba na tsoron ki don ke Win ba Abar tsoron ba ce ba kuma na Fatan yin da na sanin taimakon ki"

Yana kallon cikin idanunta ya ?arasa maganar, zuciyarta ne ya sake karyewa hawayen da suka tsagaita sai suka fara shirin dawowa sabo, kaman da wasa ta shiga sanar mishi da tarihin rayuwarta daki-daki tun daga farko har kawo ranar da ta sha guba don ta kashe kanta. Numfashi ta ja sam bata duba yanayin shi ba ta cigaba da cewa

"Na gode kwarai da taimakon ka da kuma yarda da ni da kayi ba tare da ka san ni din wacece ba, ba na so in sake Wora maka wani nauyi ko damuwa ba kuma na son wani abu ya same ka ta dalilina. Za ka iya ajiye ni anan kawai ka bar ni ka koma gida Na gode sossai..."
Idanunshi da suka sauya sossai suka cika da tarin kwallar tsananin tausayinta da rauni ya Wauke bisa kanta yana lumshe su da ?arfi, ya rasa ma kalar tunanin da zai yi wani irin tausayinta ke bin gaSoSin jikinshi yana kassara su, ji yake kaman ya taya ta kukan ta Wauki abubuwa dayawa fiye da shekarunta, tabbas dole tayi yunkurin kashe kanta don duniyar bata dandana mata daaWi ba sai akasin hakan, hakika ya yabawa hakurin ta da tarin juriyarta da wani ne ko guba bai kashe shi ba damuwa sai yayi bindiga da zuciyarshi.

Sama da mintuna uku ta sau?e numfashi ta sa hannu ta buWe kofan tana shirin sau?a ta ji ya kira sunanta
"Afeefah!"
Waigowa tayi tana kallonshi, ya rankwafa ya janyo murfin da ta buWe ya rufe kirib kan ya kalleta
"Ba zan iya barin ki anan ba Afeefah! In na ce ma ki sau?a anan za ki yarda?"
Ta Yi shiru ya sau?e numfashi kan ya ta da motar yana mayar da idanunshi bisa titi ya shiga ja a hankali.

"Sunana Salim Mahmud ni haifaffen nan jahar ne na Kaduna, ni ne Wa na farko a wurin iyayena kuma namiji tilo ina da ?anne mata uku Sadiqa ke bi na Dukda akwai tazarar shekaru masu dama tsakanin mu sai Sameerah kan Auta Samha dukkansu suna jami'a ne presently. Tun Samha na da shekaru uku a duniya muka rasa mahaifin mu ya saura daga mu sai mommy, dangin mahaifin mu suka watsar da al'amurranmu duk da kasancewar mahaifina mai karamin ?arfi bai tara mai yawa ba, kuma duk yawan da zai tara akwai hidimomi gabanmu ya sa tun ba a je ko ina ba komai ya ?are, mahaifiyar mu ta matukar shan wahala da mu kuma ta yi Wawainiya mai yawa da ba don tayi karatu ba ma da bamu san halin da muke ciki ba a yanzu, bata huta ba sai da ta ga ta kafa ni ta yadda zan iya taimakon ?anne na. Mahaifiyar mu macece mai tausayi sai dai duniya kuma ta koya mata son nata don bata haWa soyayyar yaranta da kowa ba.
Ban sani ba ko za ki iya zama cikinmu idan kin amince zan je na ro?e ta, zan bata labarinki za ta ji tauaayinki kuma in shaa Allah za ta haWa ki da su Samha ta rungume mu cigaba da rayuwa har Allah ya kawo miki miji ki yi aure".

Kuka take mishi mai sanyi, ashe har tana da zaSi a yadda taken nan? Har sai ta ce ta amince zata zauna da su ko da naman jikinta za su dinga yankewa da tayi bulayi a titi? Kalaman godiya tayi ta jera mishi yana hana ta don gabaWaya rauni da tausayinta sun sassara mishi gaSoSi da yake jin zai iya joining Winta su yi kuka tare.

Yamma sossai suka dawo cikin Kaduna, daga ita har shi babu mai magana idanunta zube a titi, masu hidimar komawa gida kawai take kallo Dukda zuciyarta ya jima cikin nashi duniyar, kwakwalwanta ya zurfafa a tunanin wani irin ?addara ne kuma ya dawo da ita cikin Kaduna? Shin za su amshe ta bayan sun ji labarinta ko za su kore ta? Idan suka kore ta ina ta nufa? Akwai mai sake mutuwa sanadiyar ta? Anya ta yi mishi adalci da ta biyo shi? Har suka isa cikin Unguwar rimi bata sani ba, jin ?arar horn na mota ya sa ta Wan yi firgigit ta dawo da hankalinta kan inda suke sai ta tsince su a wani layi mai jerin rukunin gidaje iri Waya.

Gidaje ne masu kala Waya kusan komai na gidajen Layin iri Waya ne bambancin kawai lambobin da ke ma?ale gefen kyauren ko wani gida, Ba?in gate Win aka zuge wani matashi ya shiga yiwa salim Win barka da dawowa hakora a washe, Salim ya tsaya suka gaisa kan ya nausa cikin tsararren madaidaicin gidan da ya tafi da imaninta, harabar shimfide da interlocks an ?awata gidan da shukoki jajaye, shudi, kore da ma wasu kalolin ma su ban sha'awa. Ginin da kaman an zana ne ba a gine yake ba saboda yadda yayi mata kyau gidan sama ne, harabar gidan shiru babu kowa har ya shigar da motar cikin ma'ajiyarta tsakanin wasu motoci madaidaita guda biyu. Hamdala yayi yana zare keyn ya dube ta

"Mu je ko?"
Babu musu ta gyaWa kai ta buWe kofan ta sau?a, shi ya buWe bayan da ya fito ya zaro ledar da 'yan kayanta ke ciki suka nufi cikin gidan yana gaba tana biye da shi a sanyaye, a gaban mashigar gidan suka dakata ya danna doorbell, babu jimawa aka buWe Brown security door Win wata kyakyawar yarinya da za ta iya girme mata ta gani tsaye, haWa idanu da suka yi da Salim ya sa ta saki ?arar murna kan ta sau?o da gudunta ta faWa mishi tana dariya sossai shima yana murmushi ya tarbeta ya Wan yi hugging Winta kaWan ya sake ta

"Welcome home bro"
"thanks Autar Hajiya mommy"
Ta saki murmushi tare da jan hannunshi suka yi ciki tana ihun sanar da isowarshi, hakan ya sa wasu 'yan mata biyu suka fito su ma a guje suna mishi maraba, yanayin kamanninsu ya sa ta tabbatar da su ne ?annenshi da ya bata labari, murmushi take saki don sun matu?ar burgeta har tana jin ina ma da ba ita kaWai aka haifa ba, ita kam ba ta da wannan gatan Allah bai ba ta ba bata gama tunanin ta da murmushi ba ta ga Fitowar wata dattijuwar mace da suke matukar kama, fuskarta cike da fara'a har hakwaranta biyu na hajji na bayyanuwa, doguwa ce kaman su salim da suke dogaye, haka ba ta da wani ?iba don idan ba a yanayin fuska da ya bayyana girma ba ba za ka ce ta haife su ba.

Ganinta ya sa salim ya ture ?annenshi

7 / 53