Haihuwa Da Hanji Complete Hausa Novel

Author :  Halima K Mashi Category :  Adventure

Chapter   18 / 53

51K to 54K   out of 158.4K words

you are sick already kukan nan bashi da amfani, dole ne sai mutum ya rayu da dangi? Dole ne sai sune kaWai za su baka farin ciki da kulawa? Na Allah na nan dayawa Mammi..."

Yankewa maganan yayi ya Wago garin kaucewa idanun Mammi sai nashi suka sar?e cikin nata, sama da seconds huWu yana kallonta kan kawai ya juya ya bar Wakin.
"Saraki.! Saraki....!!"
Bai juyo ba ya fice, ta du?ar da kanta tana ambatar sunan Allah... Chan ta sau?e numfashi ta waigo ga Afeefah da tunda taji sau?ar muryarshi da yadda yake magana da amo kukanta ya tsaya chakk, haWa idanun da suka yi ya matu?ar Dakar zuciyarta idanunshi abin tsoro ne a gareta amma a yanzu sai taga ya zama wani iri duk yadda zata fassara ma'anar kallon nashi ta kasa, maganan Mammi ne ya dawo da ita tunaninta.

"Lallai Afeefah kin ga rayuwa, ha?i?a na kaWu da labarinki abin mamaki kika iya daurewa kika cije kika tsallake wannan jarabawa duk da kananun shekarun ki, Afeefah rayuwar nan duk jarabawa ce kuma ko wani lokaci yana da karshen sa, za mu yi ta shan wahala a duniya amma sakamakon yana hannun Allah kuma ya fi jarabtar wanda ya fi kauna daga cikin bayinsa, Afeefah ina so ki san idan dai har ni, Abeeha, jidda ko Saraki muna raye a wannan duniya kin gama kuka, zan cigaba da rikeki har karshen numfashi na haka zan yi musu umarnin cigaba da kula da ke da baki kariya har nasu karshen numfashin, in shaa Allahu kin gama zubar da hawayen ba?in ciki Afeefah... Sannu! Sannu da juriya"

Sabon hawaye ne suka cigaba da silalo mata ta sake rungume Mammi tana fashewa da kuka, Abeeha ta taho ta Wago ta tana ri?e hannunta
"In shaa Allahu ba za mu taSa kyamatarki ba Afeefah ai duniya ce idan wani ya ?i ka dole wani ya so ka haka Allah yayi rayuwar, ni na yarda ki ?irani Addah don ko kowa zai guje ki in shaa Allahu ni ba zan taSa gudar ki ba"

Sossai take kuka, a ranta Adu'a take tana tuna irin kaunar da Aunty zee ta nuna mata a ?arshe ta tafi ta barta, anya ta zama mai adalci? Anya zamanta a gidan zai haifar da Wa mai ido? Karshen wahalar kenan ko kuma akwai saura? Duk ta bar wa Allah.

Sossai suka rarrasheta ta natsu kan Mammi ta mi?e tayi sashen Rayyan don duk yana cikin ranta tun Wazu, a kwance ta same shi hallau dai idanunshi a lumshe, kai tsaye ta je ta sa hannu a goshinshi ganin jijiyoyin kanshi raWa-raWa a waje, jin hannunta ya sa ya buWe idanun da suka sake sauyawa ya zuba mata

"Saraki ciwon kai ne? Ko za ka je asibiti?"
Girgiza kan yayi kaWan yana yamutsa fuska
"Ba sai na je ba Mammi"
"Saraki in na barka haka dare ba zaka iya bacci ba, ka taimakeni ka je ka ga psychiatrist din ka"
Shiru yayi bai ce komai ba. Ta sau?e numfashi ta fara duba wayanta cikin mintuna kaWan sai ya ji muryarta tana magana da likitarshi, buWe ido yayi ya kalleta bata damu ba har suka gama wayan.

"Za ta zo, don Allah ka tashi ka saka wani abu a jikinka mu je parlor"
Ta faWa cikin kulawa kaman yadda yake damuwa da ciwo da damuwarta, shi ma bai san yadda zai yi bane, bai san ya zai yi ya hana kwakwalwarshi tsayar da tunanin baya ba, bai san ya zai yi ya cire tsananin nauyi da damuwar da ke kwance a ?asan ranshi ba, a duk lokacin da ya samu sassauci to fa a tsakanin da yake ganin farin ciki da walwala a fuskar Mamminshin ne saboda baya so yake sakata cikin damuwa amma yaya zai yi?

"Zan zo!"
Ya faWa a hankali.
Ta juya ta fice da damuwa a fuskarta, bai yi bacci ba a daren jiya dama ya saba da rashin isashen baccin dare, tun tana kwana dashi har taga yayi girman da bai kamata su cigaba da kwana ba amma ko bacci take tana tunanin yadda yake tafiyar da nashi daren, ba'a yi mishi adalci ba amma kuma to ya suka iya ne?

Da kyar ya mi?e ya saka armless vest mai fadi da three quater da ya kai mishi gwiwa, a bakin gadon ya zauna yana dafe kai har lokacin fuskarshi jazir babu Wigon fara'a a kan fuskar tashi, ba'a jima sossai ba sai ga Mammin ta dawo ta kama hannunshi suka fito, a zaune kan kujera ya ga Dr. ?in tashi macece babba da a haife zata haife shi, ganin sun haWa idanu ya sa tayi mishi murmushi ya Wauke idanu, ajiyar zuciya ta sauke har ya zauna ya kishingida ya Waura kafa daya kan daya Mammi ta fita bata ce komai ba.

"Malam Rayyan! Barka da warhaka"
Ido ya Wan buWe ya kalleta kan ya amsa.
"Whats happening? Na zaci mun wuce wurin nan duka..! Mafarkin ne?"
Shiru yayi chan dai ya gyaWa kai
"Am having a sleepless night for almost a month now"
"Me ya faru? Are you taking your pills?"
Gira kawai ya Waga don kan ya mishi nauyin da ba zai iya dagawa ba.
Ba don ma ya san darajar likitar ba ba zai kula ta ba, tayi ta janshi da magana dai har ya Wan sake ta bashi magani cikin kulawa da kwarewa a aiki.

"Mammi wants me to get married, tana tsoron ta mutu...." Ya Wan yi shiru zuciyarshi babu daaWi sam kan ya cigaba
"ba ta so ta bar ni ni kaWai ba tare da mata ba and i hate the idea... Me yasa take yawan zancen mutuwa? Yana damun zuciyata da kwakwalwata kina tunanin zan rayu bayan bata nan?"
Idanu ta zura mishi, Rayyan a cikin patients Winta da take gani sama da shekaru talatin yana daga cikin na daban da take jin damuwarshi tamkar Wan cikinta, tana tsananin tausayinshi gashi kuma Allah sai ya sake aiko mishi wata jarabawar akan wata na rashin lafiyar Mammi da fargabar mutuwar a kowani lokaci, sam bata so Mammin tashi take kawo mishi zancen tunda a ranshi ya riga ya san kowa zai mutu idan ajalin shi ya zo amma kuma ta taya ta duba raunin da yake danne wa a cikin zuciyarshi he was already traumatized, yana fama da insomia for so long ciwon Mammi kuma ya haifar mishi da anxiety tsoro da fargabar barin shi da zata iya yi.

LallaSa shi tayi tayi har ya Wan sake, maganin da ta bashi kuma ya taimaka mishi don kafin ta tafi ma yayi bacci a kan kujerar, Mammi ta samu
"Don Allah Maman Rayyan ki taimakeni a kan Rayyan, ki daina mishi maganganun da zai ji a ranshi kaman wasiyya ne, kin san matsalar shi kin san da ya ya girma in ba Allah ba babu mai iya kawo Rayyan matakin da yake kai yanzu"

"Dr. Ya zan yi ne? Ina faWa mishi hakan ne saboda ya shirya, ya kamata ya shiryawa hakan dole zata kasance amma bana Fatan hakan ya kasance bashi da wani kafaWar, bana Fatan hakan ya kasance ba shi da inda zai iya bayyana damuwarshi shiyasa nake so yayi auren"
"Amma kin san matsalar da niyyar auren nan ya jawo a baya, a maimakon ya gyara sai tabargaza da yayi mana har ya zama for months Rayyan baya aiki baya kuma fita ko ina, bakya tsoron abin da ya faru ya sake faruwa?"
Shiru Mammi tayi itama duk damuwa a kan fuskanta kan ta ce a hankali
"Zan san yadda zan yi likita, na gode sossai da taimakon ki ina fata zai Wore ko da bana nan"
Murmushi kawai tayi ta taso ta dafa kafadar Mammin ta Wan bubbuga kan ta fice bata iya ta ce komai ba.

Hawaye ne ya silalowa Mammin, ita kadai ta san me take ji, ita kaWai ta san tsoro da fargabar da bawa kan shiga a duk sadda aka ce maka ga wa'adin mutuwarka Dukda bata yarda ba amma hakan ya tsaya mata a rai tun shekaru bakwai baya, Dukda ta wani gefen hakan ya matu?ar bata kusanci da ubangijinta sai dai tsoronta yadda zata tafi ta bar Rayyan, bata jin yaranta matan saboda basu da matsalar komai amma Rayyan fa? Raunin shi sabo zai dawo bata son hakan bata Fatan hakan don haka dole ne a gareshi ya nemi abinda zai tallafeshi a bayanta.

****

Ta Sangaren Dr. Sulaiman neman duniya ya saka an yi wa Afeefah sai dai babu ita babu alamunta, police station har uku daban daban ya kai report sai dai babu ko duriyarta.

Tun yana ciwon kai a tsatsaye har sai da ya kwanta don da gaske ya matu?ar damuwa, a ?arshe ha?uri umma tayi ta bashi akan ya fawwalawa Allah ya karSi auren da aka bashi don Abba ya nuna mishi babu gudu babu ja da baya.

A dole daga ita har ?annenshi suka fara shirye shiryen auren tunda sati biyu kachal ya saura a yanzu.

****

A Sangaren saleem ma duk ya ?are a tsaye saboda damuwa da tunani, a kullum adu'ar shi a kan Afeefah ne Allah ya tallafeta ya hanata faWawa halaka Allah yayi ri?o da hannayenta ya bata uwar Waki na ?warai, har yanzu iya gaisuwar ?annenshi kawai yake amsawa wanda abin ya dame su sossai ya zura musu ido kawai musamman mommy da ke ta shirye-shiryen aure ka'in da na'in ita uwar amarya kuma uwar ango.

Sameera na zaune a kan plastic chair a wurin parking lots saleem ya shigo da motar shi ya zo yayi parking ya sau?a, bai mata magana ba don ta gaisheshi da safe kuma ya amsa har zai wuce tace
"Yaya!"

Ya juyo ya kalleta duk tayi wani iri da ita
"Yaya don Allah kayi hakuri da abubuwan da muka yi maka, wallahi na gane kuskurena tun da jimawa na tuba don Allah"
"Me kuka yi min Sameera? Ai ni dan uwanku ne ba zaku iya min komai ba ko? Sai bare ne zaku iya yi wa... Babu komai Allah yana gani"

Kuka sossai take yi.
"Allah ya riga ya nuna min iyaka ta ko a haka na gane kuskurena, Yaya in na tuna abin da muka yi wa Afeefah sai Naji tamkar jayayya muka yi da ubangiji... Za ka yi mamaki yaya idan na ce maka na san abin da kake ji a ranka, na san zafi da raWaWin rashin masoyi domin Allahnta ya saka mata, a sadda take nan ina samun sau?i ne kawai da kallonshi amma a yanzu ko arzikin kallon babu tunda Afeefah bata nan haka kawai ba sakayya bane?"

Idanu ya zura mata duk ta zama wani iri ta rame,
"Sameera wa kike so? Rayyan?"
Ta girgiza kai
"Sulaiman?"
Tayi shiru ya Wan yi jimmm, kan ya matso ta.
"a haka kawai Allah ya barki ya rama mata, ba yafiyata za ki nema ba ita za ki nema ta yafe miki"
Yana kai nan ya juya ya fice.
Ta saukar da kai tana hawaye, tana bibiyar Sulaiman sossai Dukda bai sani ba a haka ta san auren shi wadda hakan ya sake daga mata hankali amma ya zata yi? Jarrabawarta kenan, ashe Afeefar ma ba laifi tayiwa ubangiji ba ya zaSi jarabtar ta ta hanyar da ya so, ba zata taSa cewa Sulaiman tana son shi ba amma zata yi Adu'a Allah ya sassauta mata ya kawo karshen shi.

****

Rayyan yayi kwana biyu yana jinya kan ya Wan sake Dukda ba sossai ba, sam ko a hanya basu sake haWuwa da Afeefah ba don bata zauna ba shima kuma ba shiga mutane yake yi ba idan bashi da lafiya, Abeeha ta Wauke ta suka yi sayayya sossai wadda Mammi ce duk tayi mata, suka je aka sama mata makaranta sun ma ?i karbar ta sai da kyar aka barta SS1 za ta yi waec kawai SS2, idan tace hankalinta ya taSa kwanciya irin na kwana biyun nan tayi ?arya, wani irin so da kulawa suke nuna mata.

Bata aikin komai don gidan ma'aikata har sun yi yawa sai ka ga daman zuwa kitchen, uniform da ake jira Winka mata bai samu da wuri ba saboda uniforms Win school din ba'a Kasar nan ake yi ba kuma tsakiyar term ne ya ?are already wanda suke dashi ba'a kawo wani ba, don haka kullum suna tare da Abeeha kusan duk wanda ya san Abeeha sai ya san Afeefah matsayin 'yar uwarta.

Gidan Jannah suka je suka sha yinin su itama bata da damuwa kaman dai Abeeha don duk sun samu nagartaccciyar tarbiya daga mahaifiyarsu.

A yau monday Afeefah ta fito sanye da uniform Winta mai dauke da bajin KIS(Kaduna international school) tayi kyau sossai a uniform din sai kuma tayi kankanta, murmushi ne sossai fuskarta tana yiwa Mammi sallama Abeeha ce zata sauketa in an tashi sai Driver ya je ya Wauko ta, har tana shirin fita Mammi tace
"Afeefah kin mance lunch box Win ko kunyar dauka kike?"

Abeeha tace
"Ana kunya da ciki ne? Oya maza yi sauri ki sameni a mota"
Da sauri ta juya bata ankara da akwai mutum ba kawai ta ji ta buga goshinta a kan kirjin shi, kamshin turarenshi ya sanar da ita waye tun bai Wago ba a razane tayi baya baya tana Wago ido sai suka sar?e cikin nashi fuskar nan tamau, uban Harara da yake zabga mata ya sa ta nemi rikecewa...

"Ba ki da hankali ne? Ko ba kya abu da natsuwa ne?"
Dakakkiyar muryarshi ya sauka a cikin kunnenta ai sai....







=???Gureenjoh=???

HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

*FREE BOOK*

*23*

"Ba ki da hankali ne nace!"
Ya sake faWa da Wan ?arfi, in za ta iya tunawa kalaman shi na farko kenan a gareta, kila to bata da hankalin ne don yanzu ma rikice wa tayi ta rasa me zata ce Bakinta ya kasa furta ko A sai baya baya da tayi da sauri idanunta da suka firfito farare tass a kanshi.

Ganin Hararar da ya watsa mata yana cewa
"Daina kallona!"
Ya sa tayi saurin Wauke idon, Mammi ce ta ceceta
"Haba Saraki! Bata san kana wurin bane za ka tasa ta gaba kana zazzare mata ido, kayi ha?uri"

Mammi yake kallo, itama Afeefah jin abinda Mammi tace ya sa tayi ?o?arin har haWa kalaman ha?uri tace
"Ka..yi ha?uri"
Tsaki ya ja ya wuce ta ya barta da fitinannen kamshin shi, kitchen ta wuce ta Wauko lunch box Win mai kyau dashi ta fito a sanyaye tacewa Mammi

"Mun tafi Mammi"
Daga haka ta fice a parlorn da sassarfa don tana fitowa ya zuba mata ido, tsaki ya ja bayan fitan ta ya dubi Mammi
"Meyasa kuka sakata makarantar da ba'a sa hijab kamar ba musulma ba?"
Mammi ta kalleshi
"Yanzu menene aibun uniform din nan?"
Sky blue shirt ne da navy blue blazer da skirt Dukda a gwiwa ne sai dai ta saka socks da ya haura mata har cinya, cover shoe Black ne kafafunta sai navy blue cap da ta rufe kanta kirip dashi, neck tie ne me layi layi sky nd navy blue sun yi mata kyau kayan kuma babu inda ke bude jikinta banda hannayenta da fuskarta.

Baki ya taSe bai sake cewa komai ba, abin kari mammi ta kira aka kawo mishi ya fara karyawa a hankali, bayan ya gama ya dube ta
"Mammi auren salim next week friday"
"toooh aure haka kwatsam babu sanarwa babu shiri?"
"Nima jiya ne yake faWa min"
"Toh Allah ubangiji ya sanya alkhairi ya sa da mu za'a yi"
Ya amsa da Ameen.

Daga nan wani hirar ta shiga yi mishi yana bata amsa a hankali hankali har suka gama ya mi?e ya bar gidan.

?arfe biyu sai ga 'yan makaranta an shigo, bata samu Mammi a babban parlor ba kawai sai ta shige Wakinta tayi wanka ta sauya kaya zuwa doguwar riga Abaya onion colour mai kyau, hula ta saka ta fito ta nufi Wakin Mammi jinta take very fresh nd healthy, wani sa'in ta kan tuna salim da halin da yake ciki sai kuma tace kila ma ya manta da ita, Sulaiman ma kan zo mata rai ko yaya yake oho bata sani ba.

Da sallama ta tura parlorn Mammi ta shiga ta sameta zaune gabanta abinci ne, farin shinkafa ce basmati aka dafa amma dibawa aka yi kaman na jinjiri da alama ma da measurement cup aka gwada don ba zai wuce 1/2 cup ba, sai wani wake green, akwai salad Wan kaWan shi ma daga lettuce sai cucumber da lemon tsami, kaza ce gasashiya 'yar kaWan itama a gefe sai ruwa.

Murmushi Mammi ke yi tana amsa sallamar
"Barka 'yan makaranta an dawo?"
"Eh Mammi mun dawo, ya jikin?"
"Alhamdulillah, Ki karSi abinci ki ci sai ki huta ko?"
"Toh Mammi"
Abincin Mammin ta zubawa idanu sama da seconds biyu kan tace
"Mammi idan ba damuwa zan iya tambayar me yake damun ki?"
Mammi tayi murmushi tace
"Babu damuwa Afeefah, ciwo biyu ne ke damuna an haifeni da diabetes na gado don tun ina shekara biyu aka gane cewa na gaji Sangaren mahaifina ne da ciwonsu na sugar, matsalar ciwon sugar idan yayi tsanani yana iya affecting koda to wannan dalilin ne ya janyo na samu damuwa da koda shekaru tara zuwa goma baya, an ma yi min aiki an chanza duka ba'a dace ba Afeefah har ma an ba ni wa'adin wata uku shine ?arshen rayuwata sai kuma gashi da yardar ubangiji na shekara bakwai bayan nan"

Afeefah damuwa ne sossai ya nuna a fuskarta tace
"Toh Mammi shi ciwon ?odar yaya yake? Ba'a warkewa ne?"
"Allah ya halicci mutane da koda biyu, wani halitta ne kaman wake akwai wasu ma da suke da Waya jal kuma suke iya rayuwa amma kowa biyu Allah yayi mu da su, waennan kodar amfaninsu kuma su tace jininmu ne idan ruwa yayi yawa su cire ta ta hanyar fitsari, suna taimakawa wurin hana jini ya hau sannan suna kuma sake wasu kwayoyin halitta na hormones su hana ?arancin jini suna kuma haWa vitamin D dake ?ara karfin ?ashi. Akwai abubuwan da suke kashe koda ba sai ciwon sugar ba wani ma abu mai sau?i kan iya janyoshi kaman rashin shan isashen ruwa, ri?e fitsari ki ga mutum yana jin fitsari ya matse shi sai lokacin da ya maka tukuna zaka tafi da gudu, yawaitar shan pain killers baya na Wan ciwo a sha diclofenac, wani yatsa ma na

18 / 53