Haihuwa Da Hanji Complete Hausa Novel

Author :  Halima K Mashi Category :  Adventure

Chapter   23 / 53

66K to 69K   out of 158.4K words

da kuruciyarta don ganin ta gina rayuwarka ba... Ta gina ka ne don ka girma ka tallafi kannenka, yau idan baka biyawa su Samha kudin makaranta ba wa kake tunani zai biya musu? Me ya hau kanka haka saleem?"
A tausashe yake maganan, saleem bai ce komai ba ya zauna shiru duk yadda Rayyan ya buga ya kaWa akan ya faWa mishi menene matsalar bai ce komai ba, daga karshe Rayyan ya ce

"Saleem ka ba Samha kudin makaranta yadda ka saba bata"
?ago ido yayi ya kalleshi shima shi yake kallo zuciyarshi na rawa, tabbas akwai ayar tambaya akan dabiun saleem sai dai ba zai yi saurin yanke hukunci ba, yana zaune nan sai da saleem ya dauki tsawon mintuna biyar kan ya zaro wayanshi yayiwa Samha transfer Win kudin yadda ya saba bata, mommy ta du?ar da kai tana kuka mai ciwo. Da zafi abin da zafi kana gani a sauyawa danka rayuwa daga yadda yake zuwa wani abu daban.

"Je ka shirya mu tafi masallaci"
Bai ce komai ba ya mi?e ya haura sama, Rayyan ya runtse ido a hankali sama da seconds goma ya buWe sun dan sauya, Mi?ewa yayi ya fice bai kula godiyar da mommyn ke mishi ba, a gaban motar shi ya tsaya yana kallon Sabrina da ke tsaye ana sau?e wasu kwalaye cikin store nazarin ta sossai yake yi chan ya Wauke idanu ya sau?e kan saleem da ya fito, yana kallo sai da yaje wurinta suka yi magana ta Waga ta kalleshi kan ta gyaWa kai saleem ya wuce ya zo ya shiga motar suka fice daga gidan.

"Saleem idan ka ga Afeefah a yanzu za ka iya aurenta?"

Shi karan kanshi bai san ya jefawa saleem Win tambayar ba don ya jima yana mishi yawo a rai kuma yana son tabbatar da zarginshi kan Sabrina. Sunan Afeefah ya sake maimaitawa a ranshi don dai bai taSa ambatar sunan a fili ba ma sai yau.

"Aure? Ai ina da aure"
Ya amsa shi muryarshi babu wannan karsashin idan yana maganar da ya shafi Afeefah, kaman ma wata ce chan daban da bai wani sani ba.

Bai ja maganan ba ya yi shiru, dole su tashi tsaye akan Saleem da alama zautar da shi ake shirin yi, amma yayi matukar mamaki irin mamakin nan da bai taba zaton hakan zai iya faruwa da saleem daga aure ba, auren ma na dangi ba bare ba.

****

Zaune take gaban Mammi don sai da ta tabbatar ya fice kan ta dawo, abincin ta tsurawa idanu yadda ya tsara shi kaman wani chef tana mamakin yadda ya iya girki haka, Mammi bata ce komai ba ta shiga cin abincin sai da ta gama tsaf ta dubi Afeefah tace

"Afeefah akwai maganar da nake so mu yi da ke ko kuma in ce akwai alfarmar da nake so na ro?e ki ban san ko za ki iya yi min ba, ba abu bane da ya saSawa shari'ar musulunci abu ne da muddin kika amince min Afeefah zan yi matu?ar farin ciki fiye da zaton ki"

Afeefah ta gyara zama jin maganar serious ne, kuma a yadda Mammi ta Wauke shi da muhimmanci ya sa itama ta ji ta bashi muhimmanci itama
"Tashi ki dawo nan Afeefah"

Mi?ewa tayi ta koma kusa da ita yadda ta ro?a hannayenta duk biyu ta ri?e

"Afeefah na dauke ki ne tamkar Abeeha, ba zan taSa yin wani abu da zai cutar da rayuwarki ba amma ban san yadda za ki Wauki maganar ba.."

"Mammi yanzu fa kika ce ni tamkar Abeeha ce a gareki nima kuma ba ni da uwar da ta wuce ki, wlh duk abin da kike so matu?ar zai faranta miki kuma bai saSawa shari'a ba ni mai amincewa ne Mammi, faWa kawai za ki yi in cika shi na san ba za ki taSa cutar da ni ba."
Afeefah ta katse ta ganin kaman contemplating take na gaya mata abin da take so, ita kuma tana da yakinin koma menene Mammin za ta ro?a ba sharri bane.

"Afeefah za ki iya auren Saraki??"

Afeefah ji tayi kaman kunnenta bai ji mata daidai ba, bata motsa ba don bata gama fahimta ba jin Mammi ta yi shiru tana kallonta yasa tace
"Mammi ina sauraranki in shaa Allahu zan yi duk abin da kike so"

"Afeefah abin da nake so shine kafin na mutu in ga na haWa aurenku ke da Saraki...! Shin za ki iya auren shi? Za ki iya yi min wannan alfarmar?"

Wani irin shock ne ya ratsa Afeefah daga kanta har cikin tafukan sawayenta, a matu?ar razane ta zare hannunta daga na Mammi ta mi?e tsaye zuciyarta na wani irin bugawa kaman zai ratso kirjinta ya fito

"a..ure? Ni Mammi? Ni... Ni Afeefah da Wanchan mutumin...??"
Don ji tayi ba zata iya ?iran sunanshi ba ma ko Rayyan Win ko Saraki idan tayi hakan kaman wani zunubi ne da muddin ya ji ta sai ya sauya mata kammani, kallon kanta take yi daga sama zuwa kasa ta Wago ta kalli Mammi kaman wacce ta zauce...




=???Gureenjoh=???

https://chat.whatsapp.com/BuI7cmoy3ed3C3IimZKZA0

HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

*FREE BOOK*

*29*

Hasaso Rayyan Win ta shiga yi a majigin kwakwalwarta, kallo Waya tak za ka yi mishi ka san cewa shi Win soja ne a sojojin ma na daban, yana da lafiyayyar jiki murWaWWe kuma a tsaye yake fatarshi babu Wigon ba?i ko guda Waya, Dukda ba zata ce ga yadda yake cikin khaki ba amma ko daga maganar shi zai tabbatar maka jajirtacce ne kuma gwarzon namiji wanda ko daga kallonshi za ka sha jinin jikinka.
Zaman shi, tafiyar shi da yanayin dabi'unshi kuwa za ka zaci wani babban sarkin ne na wani yanki na daban, yana da wasu irin idanu kyawawa da ko tuna yanayinsu tayi sai ta ji tsikar jikinta ya zuba kaman ba namiji ba, fasalta kyaun fuskarshi da sauran halittar da Allah yayi mishi ma wani tulin bayani ne na daban, don Allah ina ita ina irin gawurtaccen nan? Ta ina ma Mammi ta fara wannan tunanin?

Tazarar da ke tsakaninta da Rayyan kaman tazara ne da ke tsakanin sama da ?asa ko ta amincewa aurenshi ita ce zata wahala daga karshe saboda ba zai taSa son irin ta ba, ba zai taSa kaunar mace kamar ta ba wacce ta fito daga kauye cikin tsantsar jahilai, wacce take da tambarin Maita kuma annoba, wacce ko wucewa ta zo yi gidajen mutane sai an zuba tafarnuwa, ?ashin kifi da garin kukan miya a wuta don haya?in Mayu.... Ai ko da gami wane ita da Rayyan.

"Mammi kaman ban ji abin da kika faWa ba"
Ta sake maimaitawa har yanzu a kidime.

Mi?ewa tsaye Mammi tayi ta ri?o hannunta suka koma zaune.
"Ki natsu Afeefah kin ji? Ki ba ni hankalinki kar ki yi wani tunanin fin ?arfi, namiji bai taSa fin karfin mace ba in har ta amsa sunanta mace, ke kyakyawace kar kyaun Rayyan ya ruWe ki, ke yarinya ce mai hankali, ladabi, natsuwa da kuma biyayya kina da zuciya mai kyau, you are the purest soul i've ever met... Afeefah ba zan hada ki da Rayyan bane saboda wani ra'ayi nawa ko buri eh ina da buri a kan ku duk biyu, sai dai burin ba na komai bane sai na son ganin rayuwarku duk ya inganta kun tabbata cikin farin ciki"

"Mammi shi ya ce miki yana so na?"
Ta tambaya a sanyaye don ba fahimtar kalaman Mammin take ba don abu ne da take ji ba zai taSa yiwuwa ba.

"Ba shi ya ce ba, ni ce na ga cancantar kasancewarku inuwa Waya kar ki damu da halinshi ko yanayinshi na fushi da dacin rai Saraki na da wani tabo ne da ya mayar da shi hakan wanda dole zan faWa miki Afeefah... Ina so in fada miki ba don tonon asiri ba, sai don ya zama dole ki sani kan ki yanke shawarar za ki aure shi ko ba za ki aure shi ba? Ba zan miki dole ba wlh kuma ba na so ki dube ni a yayin yanke hukunci ki yanke duk abinda ke ranki ni me karSa ce don sai da na nemi zaSin Allah kan na tunkareki"

Shiru Mammi tayi idanunta sun rine sossai har suka tara hawayen da ya fara bin ?uncinta, Wacin maganan da zata faWa take ji har kan harshen ta maganan da bata taSa faWa da Bakinta ba bata taSa ambata ba sai a yau da ya zame mata dole, idanunta na kallon gefe ta furta

"Rayyan ba Wa na bane!!!"

Wani irin bugawa zuciyar Afeefah yayi da har sautin shi na fitowa fili ta zaro idanu gabaWaya tana kallon Mammi dake ta zubar hawaye

"Eh Afeefah ba ni na haife shi ba, hasali ma babu abin da ya haWa ni da shi na jini ko na kusa ko na nesa... Ni sunana Khadija ni haifafffiyar wannan gari ce ta Kaduna, mahaifina Alhj Isma'il mai rasuwa mutum ne mai tarin dukiya mai yawa a gaske kuma su biyu Allah ya ba wa iyayensu Wan uwanshi ma na da nashi arzikin don gada suka yi, mahaifina mutum ne da dukiyar shi bai taSa rufe mai ido ba, yana da kyauta tsantsa haka yana da taimako don haka ko da na zama ni kaWai 'yar shi yana da ?a?a dayawa da suke karkashin shi don lakabinshi ma shine Uban marayu da masu uba... Yaran da ya biyawa suka karatu basu kirguwa sai dai in baki zo wurinshi da kuka ba sai ya share miki hawaye, wannan dalili ya sa nima na taso da irin zuciyarshi Dukda rashin lafiyarmu don shi ma ciwon sugar ne ya kashe shi kaman yadda ya kashe baban shi, ?annunshi ma Uncle Musa haka yake don suna da nasaba mai kyau suna da ilimi boko da arabi.

Akan irin rayuwar da na tashi kenan har na kamallah jami'a ta ina da shekaru ashirin da Waya a duniya, wata rana ina driving na zo daidai wurin ba da hannu sai na hangi wani kyakyawan yaro da ba zai wuci shekaru shida ba yana da irin kyaun da in ka kalleshi sai ka sake da sauri ya zo ya shiga gaban motana ya fara wanke mini glass don kaman sana'ar da yake yi kenan a wurin ake bashi goma biyar na cin abinci, Dukda fuskarshi a matu?ar haWe ko alamun dariya babu kayan jikinshi kuma basu ji jiki chan chan ba amma sun dan yi duhu kaman ana yawan tsoma su ruwa, bayan ya gama ya dawo gefena ya tsaya tsantsar tausayinshi ne ya rufar mini, wannan yaro ?arami da ke bukatar ingantacciyar rayuwa yaron da bai wuce a ce yana gaban mamanshi a kwance ba shine ke wannan walagigi yana neman abin da zai sanyawa cikinshi, sau?e glass din nayi muka haWa ido na sakar mishi murmushi
"Yaya sunanka?"
Na jefa mishi tambayar ga mamaki na ko ci kanki bai ce ba banda idanu da ya tsura min yana kallo, ganin an ba da hannu sai na zari dubu biyu na mi?a mishi kaman ba zai karSa ba sai ya karSa ya juya ya bar wurin bai ce min komai ba.

Har na dawo gida tunanin wannan yaro ne a raina bayan kwana biyu na kasa mantawa da shi haka na Wauki mota na koma inda na fara haWuwa da shi na ajiye mota na shiga yawon neman shi da ?afa, na yi nema sossai kan na same shi zaune gefen wani juji ya haWa kai da gwiwa Dukda uban ranar da ke dukanshi ko motsi bai yi ba, daga farin Fatan shi da yanayin sumanshi na gane shi don ya fi yanayi da Fulanin usuli, gangar shi na je na du?a na taSa shi ya Wago ya kalleni da idanunshi da suke a matu?ar rine fuskarshi yayi jazir, dabiun yaron sai bai min yanayi da na sauran yara ba don idanunshi na nuna wasu al'amari da na kasa fahimta, maganan duniya na mishi bai ba ni amsa ba sai ido na mi?e na je wurin wani mai wankin mota a kusa da wurin na nuna mishi yaron

"Malam Don Allah wanchan yaron baya magana ne?"
"Hajiya yadda kika ganshin nan haka mu ma muka ganshi kuma in za ka mishi maganar duniya ba zai amsa ba amma kin ganshin nan idan ya kwana da kayan jikinshin nan da safe zai zo ya ba ni goma in bashi ruwa da bokiti ya kwaba omo ya wanke zai zauna daga shi sai karamin wando idan ya bushe zai saka ya cire wandon ma ya wanke ya mayar da kayan, kin ga inda yake zaunen nan idan ba zai fita neman kudin abinda zai ci bane bai taSa barin wurin ba sai wanka ko wanki da ya kan zo nan"

Wani iri na ji har cikin raina, na mishi godiya na bar wurin na koma wurin mota na tafi na je na sayo duk wani abin makulashe da na san yaro zai bu?ata na dawo na bashi ya ?i karSa a ?arshe ajiye mishi nayi na tafi, Washegari na sake komawa don tausayi da kaunar shi ya riga ya samu gurbi a zuciyata, a ranar takalmina na cire na yi irin zaman da yayi nima Dukda ina jin zafin ranar minti minti sai ya Wan waigo ya kalleni ban ce komai ba shima kuma bai ce komai ba, har dare ina tare dashi sallah kawai nake zuwa wani masallaci a wurin dake da Sangaren mata abin da ya bani mamaki kuma shima haka zai je Sallar ya dawo ban tafi ba ranar ma sai da na sake cika mishi gaba da abubuwan cima kala kala, a takaice na jera kwana uku ina zuwa wurinshi a na huWu ne ina zaune kawai sai na kama kuka, yayi shiru sai ya juyo ya kalleni kaman zai share chan dai na tsinci muryarshi kaman daga sama yana cewa

"Me ya same ki?"
Numfashi mai nauyi na sau?e ashe ba kurma bane
"Ba ni da lafiya ne kuma bana son zaman rana"
Ga mamakina sai ya mi?e ya kama hannuna muka koma inuwa duk muka zauna bayan nan duk yadda zan yi yayi magana ya ?i na sake yin kwana biyu muna zama a inuwa kan ranar kawai ya kalleni ya ce

"Me kike so?"
Ina mamakin yadda yake magana wane babba
"Kai nake so in taimaka kai nake so in Wauke daga wannan jujin in kaika gidan mu kayi rayuwa mai kyau, za ka bi ni?"
Kallona kawai yake, ni kuwa ina hakan ne da zuciya Waya ba zan so rayuwar shi ya ?are a kan titi ba ba zan so ya tashi a haka ba zai iya shiga ko wani hali.
Kai ya gyaWa min na yi farin ciki kwarai na kira bab??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ana ina mishi albishir don ya san labarin yaron har ya yarda duk ranar da yaron ya tanka ni kuma ya amince ya biyo ni ina da kyautar kujerar umura na yi farin ciki sossai da amincewarshi Dukda ba don kujerar ba saboda ko a lokacin na je Makka so ba adadi, na dauke shi daga nan muka dawo gidan mu.

Ban barshi cikin ma'aikata ba na kaishi Waki na musamman na fita na yi mishi sayayya kan na dawo yayi wanka ya ci abinci na bashi kayan a hankali ya ce min
"Na gode"
Murmushi nayi a raina ina raya wannan yaro idan ya girma ba karamin mutum za'a yi ba don bashi da rawar kai irin na yara masu shekarun shi.
"Ya sunanka?"
"Ban sani ba"
Abin da yace kenan na yi mamaki ?warai kuma kaman akwai abinda ya Soye min amma ban bincika ba nace
"Zan saka maka suna amma sai na yi tunani sunana Khadija, mahaifiyata ta rasu ni kaWai ce sai babana a gidan nan ka Waukeni tamkar mahaifiyar ka duk wani abin da kake so ni kuma zan cika maka shi ka ji?"
Ya kalleni nayi murmushi
"ban kai in haifeka bane? Shekarunka nawa?"
Ya Waga min yatsu shida nace
"To ka ga, da na yi aure ina 15 da na haifeka irin auren kauyen nan da ma ba'a kai hakan"
Ya Wan yi murmushi daga nan na fahimci shi mai Wabi'ar miskilanci ne tsantsa babana na samu da shawara shi ya ba da sunan Rayyan in saka mishi ni kuma nake ce mai Saraki don ko sarki bana tunanin ya kai shi sarauta..

A lokacin gab aurena da baban su Jannah ne ko da ya zo shima farar daya son yaron ya shiga ranshi yayi alkawari zamu rike shi kaman mu muka haife shi ko da zan kaishi makaranta tare muka tafi da Mahaifin su Jannah shi yayi mishi komai aka ba da sunanshi Rayyan Mohd Khamis, bayan aurena da baban su Jannah bai fi da shekara ba Allah yayiwa mahaifina rasuwa ta hanyar ciwon sugar da ya sha fama da shi, na shiga tashin hankalin da Saraki ne kawai ke iya saka ni cin abinci kan daga baya na zo na watsakke don dama wannan dole ne, ranar da na haifi Jannah a ranar Saraki ya fara kirana da Mammi don tunda muke bai taSa kirana ba ko zai yi magana sai dai kawai yayi na ce ko Aunty ya ce min ya ?i, Rayyan bashi da lafiya don yadda yake ganin rana haka yake ganin dare idan yayi bacci kuwa haka zai yi ta wani irin juye juye yana haWa gumi daga karshe cikin wani mummunan yanayi zai farka tun yana ?arami muka fara ganin likitocin psychiatric su ma da kyar da pills ake samu yake dawowa daidai idan abin ya zo mishi especially lokacin zafi kasancewar a tsakankanin ne muka hadu.

Baya so a mishi magana akan abin da ya kawo shi wurin ko iyayenshi tunda na fahimta ban sake yi mishi ba ko da wasa, irin kiyayewa da kular da muke bashi shine sanadin da ya sa ya samu ingantacciyar rayuwa yayi karatu mai zurfi har ya zama soja, bayan nan ne aka gano ina da Ciwon ?oda Rayyan yayi fadi tashi kwarai har ?odar shi yayi offering mini Mahaifinsu Jannah ya hana aka biya makudan kudi aka yi min dashe amma ba'a dace ba, a lokacin da nake jinyar Baban su Jannah ma ya

23 / 53