Haihuwa Da Hanji Complete Hausa Novel

Author :  Halima K Mashi Category :  Adventure

Chapter   11 / 53

30K to 33K   out of 158.4K words

sa ta shiga mishi sannu da zuwa a dole, gaisheta ya shiga yi cikin girmamawa bayan sun gama Sameerah ta shiga gaishe shi, ya amsa da murmushi saman fuskanshi dole Samha itama ta gaishe shi itama ya amsa mata kan ya dubi mommy
"Da ma akan patient Wi ta Afeefah na nemi ganin ki Hajiya, na zo duba jikinta don ganin lokacin komawarta checkup ya yi ban ganta ba sai na samu ashe tana kwance rip da zazzabi mura da kuma low BP da ya addabe ta"

Mommyn ta yi kaman bata san bata da lafiya ba tace
"Asshaa ka ga aikin rashin wayaun Afeefar ko? Babu fa wanda ta sanar wa bata da lafiya, mutum kullum a ma?ale a Waki ya ba za'a yi zazzabi ya dame shi ba? Allah dai ya kyauta"
Sulaiman ya Wan murmusa don wannan ba hujja bace a gareshi idan kai ka kula da mutum ba lafiya ba sai ka jira ya gaya maka ba, haka kuma idan baka ji mutum ba ana dai zaune tare kai ke da alhakin le?a wa ka ji shin yana lafiya?

"Ai duk alamun rashin lafiyar ne Hajiya, a likitance duk wadda ba ya son interracting da kowa ya fi gane kaWaici da rashin magana yana shiga ?uncin ko damuwa duk akwai alamar tambaya kanshi, Don Allah a taya mu kula da ita idan tana samun kulawa in No time za ta ji sau?i ta komawa aikinta in Shaa Allah"
Sameera ta riga mommy magana
"In shaa Allahu Dr. Za mu yi duk yadda ka ce Allah ya bata lafiya"
Yayi mata murmushi kan ya amsa da Ameen itama dai fuskar nan cike da fara'a take ta kallonshi.
Mommy ta ce
"Ba na son ka faWawa Salim, ka ga yana wurin aiki kar ya zaci ba ma saka ido ne a kanta duk hankalinshi ya tashi, bills Win ka dinga turomin zan ke covering"
Ya gyaWa kai kawai yana kokarin Mi?ewa Sameera tace
"Ko ruwa baka tsaya ka sha ba?"
Ya ce
"No na gode, ai daga gida na fito"
Daga an suka fice suka bar su.
Wayanshi ya zare bayan ya yiwa motar tashi key ya Wan zubawa Layin salim ido yana nazarin abin da ke faruwa, Salim ya ce kar mamanshi ta san shi ya turo su, mamansu ta ce kar salim ya san Afeefah bata da lafiya to me kenan? ?an shrugging Kafada yayi kan ya danna ?iran salim yana ficewa daga harabar gidan, kaman jira ko ringing na farko bai yi ba salim ya Waga
"Ya ya jikin nata Dr.? Is it worst? Sai an tafi hoapital ko?"
"Calm down Captain jikin da sau?i"
Nan ya shiga koro mishi bayanin yadda suka yi da mommyn. Numfashi ya sau?e bai wani ji damuwarshi ya ragu ba don ya san da matu?ar wuya su bi ta kanta, ro?on Sulaiman yayi da akan ya dinga zuwa yana duba masa ita kaman yadda yayi alkawari.
Yana dan murmushi yace
"ba ka da matsala in shaa Allahu"
"Thank you so very much Doctor"
"?o not mention"
Daga nan suka ajiye wayar.

"Oh ashe wannan baiwar Allahn aiki take gidan su salim Win?"
Baaba tayi maganan da alama dai har yanzu tana jimamin yadda suka tafi suka bar Afeefah Win.
"Ni ma sai yau nake fahimtar hakan Baaba, kaman kuma mutanen gidan ba su Wauki ma'aikatan su da muhimmanci ba"
Ta Wan juya kai cikin manyanta tace
"ko kuma ita Afeefar ce ba su Wauke ta mutum ba ba"
Ajiyar zuciya ya sau?e daga nan bai sake magana ba itama haka har suka isa gida, ta sauka kenan yana shirin ?arasar da motan parking space ta juyo ta kira shi
"Alhj ?arami Don Allah idan za ka koma da dare ko ban bi ka ba zan baka kunun gyaWa ka kai mata kila ta iya shan shi"
Ya amsa da
"Toh Baaba Allah ya kaimu dare Win"
Ya ?arasa da motan yayi parking kan ya nufi cikin gidan shi ma don bashi da aiki da safen sai dare za shi asibitin ya kwana, Salim ne ya fitar dashi dole.

Da misalin ?arfe bakwai na dare ya fito a shirye tsaf cikin kananun kaya da suka amshi kalarshi na ba?i, skin Win shi da yake kalkalewa tamkar mace sai shining yake don shi mutum ne mai tsananin tsafta, hannun shi rike da ninkakken labcoat Win shi, mahaifiyarshi Hajiya Amina da ke zaune cikin kujera ta Waga kai ta kalleshi
"An fito kenan bokan Turai?"
Yayi murmushi yana furta
"Eh umma zan fara bi gidan su saleem akwai patient da zan duba kan na wuce asibitin"
"A'ah ko dai wacce Baaba jummai ke ta jajenta tun safe?"
"Ita fa Umma da safe mun fita kina bacci, ko da na dawo ban le?o ba ashe Baaba kam tayi ta baki labarin Afeefah"
Tana murmushi tace
"Ai ina ga zuwa yanzu kowa ya san labarinta a gidan nan, Allah ubangiji ya bata lafiya. Sai ka le?a kitchen ta yi mata kunu da ferfesu ka karSa ka tafi mata dashi"
Yayi murmushi kan ya amsa yana nufan kitchen Win baabar tana side Win su bai neme ta bane saboda ba gida zai dawo ba daga chan asibiti zai wuce shiyasa ma bai ba kanshi wahalar neman ta ba don sai yayi mata dogon bayani da kyar ta fahimce shi, kwando ne mai kyau da tsari ta shirya mata komai ciki, ya dauka kawai ya fito yana yi wa Ummarshi sallama take sanar mishi Abban su yace ta sanar mishi lallai lallai yana son ganinshi da safe saboda kullum a saSani suke.

Ko da ya isa gidan su saleem a mota ya cigaba da zama yana tunanin yadda zai nemi iso don bai ga gilmawan kowa ba, sai time yake dubawa ganin zai iya makara ya sa ya sauka ya nufi mudi dake zaune bakin gate da iliya.

"Assalamu Alaikum warahmatullah"
Yayi musu sallamar yana sake mi?a mishi hannu duk da sun gaisa Shigowar shi
"Don Allah ku dan yi ha?uri zan shiga lokacin aikin ku, Afeefah nake son gani ko za ka min iso?"
Shiru suka yi cikin tunanin wacece ma Afeefah a gidan, a tare suka tuna ta sai suka kalli juna suna zazzaro ido, mudi ya ce
"A'a malam sai dai ko in nema maka Talatuwa ta maka iso amma mu kam magana ma da wacce ka ambata ya haramta tsakanin mu har Abada"
Ya ?arasa c??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ikin yanayin jimami da tabbatarwa iliya ma na gyaWa kai tabbacin hakan ne.

"Magana ya taSa haramtuwa tsakanin musulmi da musulmi kuwa Malam mai gadi?"
Yayi maganan yana Wan dariyar yadda suke reacting.
"Kai dai in ana sallah ba'a magana"
Iliya ya faWa, tuni mudi ya nufi ciki ta baya ya bi ya tsaya daga kofan mashigan kitchen Win
"Talatuwa akwai wadda ke neman iso wurin yarinyar nan mai wanke-wanke zo ki ji da shi"

Sameera da ke shigowa kitchen Win ta Wan yi jimmm kan tace
"Talatuwa ci gaba da aikin bari na je"
Da kallo Talatuwa ta bi ta har ta Sace, sai da ta koma Waki ta dubi kanta ta kuma ?ara turare kan ta fito ta nufi waje, Sulaiman na ta bugar cikinsu don ya ji dalilin rashin mata magana kuma wai na har abada dole ya sa suka shiga bashi labarin abin da saleem yayi musu, Sossai Sulaiman ke dariya... Tahowar Sameera ta wani zuba mishi idanu tana tsintar kanta da murmushi.

Kallon farko da ta mishi ya tafi da imaninta, ya shiga ranta fiye da yadda tarin samarin da suke bibiyar ta, a yanzu da ta ci karo da shi yana dariyar nan kuma sai taji tana narkewa, zuciyarta na wani irin macewa a kanshi, ganinta ya sa ya tsagaita dariyar shi, ta shiga gaishe shi ya amsa yana murmushi

"Whats so funny haka Dr.?"

"Ki bari kawai ni da su mudi ne, zan iya shiga?"
Ta Wan yi farrr
"Sauri kake haka?"
Ya Wan duba time a agogon dake Waure bisa tsintsiyar hannun shi
"Kusan hakan don kaman na shiga lokacin aikina"
Ya ?arasa yana nufar mota, ta bishi suka jera.
"Ai ma kuna ?o?ari SLT nake karantawa amma ji nake kaman na gudu bare likitance da aikinshi"
Ya Wan yi dariya bai ce komai ba, ta tsaya tana kallonshi har ya buWe booth ya Wauki kyakyawar basjet da Baaba jummai ta shirya mata kunu da ferfesu Win kayan ciki da suka nuna suka yi tuSus cike da kayan kamshi, ganin basket Win sai da ya ba Sameera haushi amma ta danne, ta sake ganin ?atuwar leda sai zuciyarta ya shiga tambayarta Anya ala?ar nan na likita da marar lafiya ne ko akwai abin da bata sani ba?

Amma me Afeefah take dashi da guy irin Sulaiman zai so ta? Dukda haka zuciyarta bai huta da bugun tara-tara ba, kar dai ta faWa soyayyar abin da ba za ta samu ba, ji tayi bata da ?warin gwiwar bin shi don tabbas matukar ta bishi ta fahimci akwai alaqa tsakaninsu zuciyarta zai iya bugawa ko ta sha?e yarinyar har lahira, ba za ta iya bin shi ba sam bata da ?warin gwiwar. Ta manta cewa kwata-kwata ma yau ne ta fara ganinshi har da za?ewa haka, wayar ?arya ta ?ir?ira ya Wan kalleta

"Ka je Dr zan sameka"
Tana kai nan ta juya tana cigaba da magana a ?arya, shi kam bai damu ba ya nufi Wakin Afeefah Win a kan varender ya tsaya yayi knocking, a jiran da ya Wan yi ya fahimci maza ne cikin ainihin Boys quaters Win don ga wani murya na waya, kuma shine aka ajiye mace tare da su? Sam tsarin bai mishi ba... Anan ne kuma ya shiga tuna hirar su iliya sai ya fahimci saleem yayi hakan ne don ya bata kariya Dukda haka shi abin bai burge shi ba, ya juya ya kalli main building na gidan, yanzu duk girman gidan nan a ce babu inda za'a ajiye Afeefah sai cikin maza?

Kimtatar lokaci yayi daga knocking da sallamar shi zuwa yanzu kan ya tura kofan ya shiga da wani sallama again, ta lallaSa ta tashi zaune ta sanya hijabi tana jingine da gini ?afafunta na cikin bargo
"Sannu da zuwa Dr"
Ta faWa cikin sassanyar muryarta da ya ?ara ?asa sossai.
"Sannu Afeefah ya jikin dai?"
Ya faWa yana ajiye abubuwan hannunshi
"Da sau?i"
Plate na safen nan ya ?ara gani a yadda aka ajiye da safe, wani tunani ne ya darsu a ranshi hakan ya sa ya mi?a hannu ya buWe ga mamakin shi abincin nan na safe ne still zaune cikin plate Win, bata ci ba don ko da Talatuwa ta shigo ta duba ta ta Wauka ta tafi da shi don ta kawo mata wani mommy ta koro ta akan ba za su yi almubazzaranci ba sai dai ta cinye shi kan a saka mata wani.

"Afeefah tun safe baki ci komai ba?"
Da Wan tausayi haWe da zafi yayi maganan ranshi na sosuwa kwarai.
Ta Yi shiru
"Ina za ki samu ?arfin jiki idan ba kya cin komai? Ai ko mai azumi zuwa yanzu dai ya sha ruwa"
Tsam ya mi?e ya nufi bayin ta, ta lumshe ido bayan ya shige chan sai gashi ya fito da bowl haWe da brush ya bata, ruwan goran da ya shigo dasu ya buWe bakin Waya ya dinga zuba mata tana wanke bakin sai da ta gama tsaf ya mayar yaje ya zubar, ya dawo ya tsuguna ya saka mata peppersoup Win da kunun ya ajiye mata a kan kafafunta Wayar hannunta na hagu ya mi?a mata kofin kunun ta karSa ta ri?e idanunta na kallon cikin bowl na psoup Win, sai turiri da kamshi yake fitarwa.

"Oya ci yanzun nan, ko in baki da kaina?"
Ta girgiza kai ta sanya hannu ta dauki spoon Win ta shiga sha, da kaWan da kaWan yana matsa mata har ta sha dayawa ta sha kunun kuwa sossai, fruits da ya sayo mata ya kara mata da shi. Ta marairaice
"Zan yi amai fa idan na ci, cikina ya cika"

"kin manta kina tare da likita? Ai aman ma tsorona yake ji Harara Waya tak zan mishi ya koma"
Ta saki murmushi karo na farko da har hakwaranta suka bayyana, ta sanya hannu ta karSi ayaban da ya bare mata.
Magungunan ta ya duba ya haWa Allura yayi mata a canular tana ta wash wash ya ce
"Wato Wazu ma saboda bakya hayyacinki ne kika manta da raki ko?"
Ta du?ar da kai, wayanta ne yayi haske ya Wauko ya duba
"Saleemullah ne yayi miki sa?o in karanta miki?"
Ta girgiza kai alamun A'a.
"Zan duba anjima"
Ya gyaWa kai ya shiga Phone ya sanya Layin shi yayi flashing kan yayi saving da
"Dr. Sulaiman"
"karSi, zan zo gobe da safe duk abin da kika ji kina so ko sha'awa just give me a call za ki samu kin ji?"
"Toh Dr na gode"
Yayi saurin cewa
"Yanzu kam na wuce wannan matsayin tunda har jinyarki kika saka ni a bati"
Tayi dariya kuma da gaskiyar shi don ta mugun samun ?warin jiki, da Allah bai turo mata shi ba haka za ta kwana don ba zata iya cin abincin safen ba.
Sallama yayi mata ya fice don ya makara yau kam ainun.

Sameera da ke tsaye jikin Window tun Wazu ta ?ura mishi ido tana jin zafi a ranta, idan ta kimtata daidai mintunanshi Arba'in da biyar a Wakin yarinyar me ya ajiye shi haka? Har zafi zafi take ji a idanunta shi kam da bai san ma tana yi ba tuni ya shiga motar shi ya bar gidan.


=???Gureenjoh=???

HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

*FREE BOOK*

*015*

Ta Sangaren Afeefah Dr. Na tafiya ta janyo wayan, number Dr. Sulaiman shi ne number na biyu da ya shiga wayanta murmushi ta Wan yi bayan ta buWe sakon Saleem. Kusan sa?on shin na ashirin da wani abu kenan a ranar.

"Ya jikin? Kin ji sau?i? Kin ci abinci? Don Allah kar ki zauna da yunwa ki ci ko kaWan ne, ko akwai abin da kike so in sa a kawo miki?"
Sa?onnin kenan masu dauke da kulawa.

A yanzu ma emphasizing yake akan ta ci wani abu cike da damuwa ?arara a kalaman nashi duk ya damu, rubutu ta fara a hankali

"Na Ci abinci kuma na ji sau?i sossai ka kwantar da hankalinka ka ji Ya Saleem?"

Numfashi mai nauyi ya sau?e a sadda sa?on ya riskeshi matsalar shi ko ya baro Maiduguri ya dawo Kaduna a yau bashi da damar bata kulawa yadda ya dace hakan na damun zuciyarshi ?warai da gaske.

"Alhamdulillah! Yanzu ni ma zan iya saka wani abu a baki na, na gode Afeefah. Ki kular min da kan ki sossai in akwai wani damuwa kar ki yi ?asa a gwiwa wurin sanar min"

Hawaye ne suka cika idanunta, me yasa zuciyarta ba za ta karye a kan saleem ba? Shi ne mutum na biyu da ya karSe ta a yadda take, bai damu da maganganun mutane ba, ya ba ta kariya daga cutarwa ya Wauko ta Waga kan titi ya kawo ta gidan su, yana iya ?o?arin shi wurin ganin bata zubar da hawaye ba, bata san da me za ta saka mishi ba bata ma da abin saka mishin da ya wuce Adu'a, har ranta take jin duk abin da mahaifiyarshi da ?annenshi za su yi mata in har akwai hakkinta ta yafe musu ba za ta taSa rike su ba saboda salim ya wuce wannan gaSa a rayuwarta.

"Ka ci sossai har da sauran kaso na, sai da safe"
Tana kai nan ta kife wayar tare da kwanciya don da Talatuwa ta shigo Wazu ta ro?e ta ta kawo mata ruwan dumi tayi alwala, da alwalar tayi ta sallolinta daga zauna saboda jiri da baya barin ta ta tashi.

Ta Sangaren Sameera wani tsanar Afeefar ya sake cika zuciyarta, tunanin matakin da za ta Wauka a kanta take yi, ko ta je tayiwa Afeefar gargaWi akan kula Dr ne? Wani zuciyar yace yanzu duk abin da fushi ya dibe ki kika yi mata tsautsayi ya faWa kanki a bata da lafiyan nan ai kin kaWe, gwara ta warke first a haka dai da nauyin zuciya ta kwanta tana ta juye-juye cike da haushi da tsanar Afeefah da tayi sanadiyar kasa baccinta a daren.

Kaman yadda Dr. Sulaiman ya yi al?awari bayan ya tashi aiki da safen wanka kawai yayi ko hutawa bai yi ba ya Wauki Baaba jummai don yana so ta yini wa Afeefar kila jikin ya sake ?arfi idan ta ga mutum kusa da ita, sam baya so abin da ya faru jiya ya faru yau hakan ma ya sa yayiwa Baaban umurnin shirya mata duk wani abu da ta san bakin marar lafiya zai so da basket mai girma suka nufi gidan, ba su wani nemi iso ba suka zagaya zuwa sashen Boys quaters Win ya bar Baaba ta soma shiga.

Afeefar ta ji ?arfin jikin nata sossai musamman da ta samu baccin dare mai nauyin gaske, ta samu ta lallaSa ta watsa ruwa ta Wan kimtsa Wakin tana sanye da peach abaya ta Waura gyalen a kanta, ganin Baaba ya sa farin cikinta bayyanuwa ainun, Baaba ma tana murmushi take cewa
"Ah jiki ya yi kyau Alhamdulillah"
"Sannu da zuwa Baaba"
"Sannu Afeefah, ya jikin dai? Kin ga kan gaisuwar nan bari na shigo da Alhj ?arami ya miki alluranki yana sauri zai je ya kwanta idan ba haka ba yanzu za ki ga ya kama ciwon kai da baya ?arewa ta daaWi"

Afeefah murmushi kawai tayi Baaba ta fice seconds kaWan sai ga su, Afeefar ta warware gyalen ta ta yafa bisa kanta, babu hula a kan hakan ya sa tsantsin gashinta ke ta zamar da gyalen tana gyarawa, gaishe shi ta shiga yi yana amsawa idanunshi na a kanta yana yaba yadda jikin ya fara kyau, Alluran ya haWa yayi mata yau kam ma rakin ya fi na jiya, don akwai pcm kuma babu ruwan diluting hakan ya sa yayi mata a hankali yana yi mata sannu don zafin shi.

Bai jima sossai ba ya tafi ya bar su da Baaba da ta zage ta ?arasa gyaran Wakin ya fita fess ta bata abinci tana ci suna 'yar hira bayan ta gama ma ta mi?e kwance suna cigaba da hirarsu tun tana amsawa baaban har bacci yayi awon gaba da ita.

Shi Sulaiman yana isa gida ya ga Abbanshi tsaye suna magana da mai gadi, idanunshi

11 / 53