Haihuwa Da Hanji Complete Hausa Novel

Author :  Halima K Mashi Category :  Adventure

Chapter   5 / 53

12K to 15K   out of 158.4K words

shafa mata powder sai tayi kaman ka sace ta ka gudu, masu hidima da kitchen ita suke kira tana mi?awa mutane abinci daidai ta zo mi?awa wasu mata kenan da yake ta bayansu ta zo ta ji Wayar tana cewa

"Ni kam dai ina tausayawa Zainabu saboda fa da gaske yarinyar da take ri?o rikakkiyar Mayya ce kuma fa an ce Mayu sun fi zaluntar wanda ya ji tausayin su"
?ayar ta ce
"Ni fa ban san yarinyar ba amma kuma ina da labarin tun tana ciki take cin maita, uban ta ma bai tsira ba haka uwar da ta haife ta, aiko Allah raba mu da irin wannan iri. Haihuwa bata yi rana ba"
Wani irin abu mai nauyi ne ya taso ya tsayawa Afeefah a kirji tana ji na ukunsu na furta
"za ki gane ta mana wata ba?a marar kiba ta saka leshi maroon, ai daga kallon idanunta da suke manya kaman kwai kin san za'a ga kurwa da kyau... Allah dai ya hana farin ciki komawa ba?in ciki"
Gabansu ta zagayo suka Wan sha jinin jikinsu ganin fuskarta babu Wigon walwala idanunta da suka surke zuwa ja ta Wan zuba musu kan ta ajiye abincin ta juya ta bar wurin.

A karshe dai ba'a tashi suna lafiya ba don wata wai aljannunta sun tashi ai sai ta kashe Afeefah Mayya ce! nan fa gidan suna ya kachame dayawa suka shiga kururuwa su ma, da ?yar aka fita da ita a gidan zuwa ma?ota ban da kuka babu abin da take, bata san wani irin tunani zata y???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?i ba duk ta ji kaman ta sallamarwa duniya farin ciki da rayuwarta sai ta tuna Aunty zee da ta yarda da ita take kuma bata kariya don yanzu ma ita ce ta nuna jan ido ta sallami kowa da abin da za'a yi sai ya fi haka, chan kuryar ma?ociyarsu ta takure tana kuka sossai bata ji Shigowar Aunty zee ba amma ta ji hannu ya taSa ta firgita ta yi ta mi?e tsaye tana girgiza kai

"Wallahi ni ba Mayya ba ce! Ban san ya ake yi ba don Allah ku yi ha?uri ban taSa cin naman mutum ba wallahi..!"
A rikice take maimaitawa da sauri Aunty zee ta rungumeta tana hawayen tausayinta
"Ya isa Afeefah! Ni ce! Auntynki ce, na sani wallahi na sani ke ba Mayya ba ce na yarda da ke"
Kuka kawai ta saki mai tsuma zuciya tana yin luff a jikin Aunty zee Win.

Jiki a sanyaye duk suka dawo gidan, yayinda abin da ya faru a sunan ya tsayawa Afeefar ta yadda ko kuzarin taSa yaran bata da shi, tsoro take ji kar ta taSa su abu ya faru haka Aunty zee ta sa uncle usman a gaba tana kuka sossai
"Duk laifin matar ka ne usman da bata fara ba da hakan bai faru ba, yaran nan fa kannen Afeefah ne amma ka ga yadda take baya baya da su ko taSa su sai na yi da gaske take yi! Haba mana ko bata duba komai ba ta duba maraicinta mana wallahi ta Wauki alhakinta dayawa kuma ni kam ta daina burgeni sam"
Shiru yayi chan ya ce
"Ki yi ha?uri zan yi mata magana, amma ki dinga dubawa itama hamdiyyar ba don tsanar Afeefah bane ya sa take hakan saboda kare yaran nan ne ganin tsawon lokacin da muka Wauka kafin Allah ya ba mu"
"Wallahi na fi ?aunarta a kan su, ta cigaba da rayuwa da wannan tsangwamar rayuwarta na cikin haWari don Allah zan ro?e ka Alfarma don girman Allah kar ka chanza mata kaman yadda ka fara mata, ka dubi maraicinta ka ri?e ta kamar yadda za ka ri?e suhail da suhaila".

Hannayenta duk biyu ya ri?e
"Ban tsani Afeefah ba Zainabu, in shaa Allahu kuma zan cigaba da iya ?o?arina a kanta"
"na gode sossai Baban 'yan biyu"
Ya saki murmushi ita ma ta mayar masa.

Duk su biyun sun mayar da hankali kanta ta yadda hatta shi uncle Win kan ja Afeefar jiki ko ma ya bata babies Win da take matukar so ta ri?e, yau satinsu na biyu kenan a duniya.

Tsaki Aunty zee ta Wan ja kaWan karo na ba adadi hakan ya saka Afeefah dake jijjiga suhaila yayinda Auntyn ke ba Suhail Mama ta kalleta ganin tana ta yamutsa fuska ya saka Afeefar katse shirun nasu
"Aunty lafiya kuwa?"
Ta sake jan wani tsakin karo na barkatai kan ta furta
"Wlh Afeefah ciwon ciki ne ke Wan matsa min tun haihuwar nan kullum sai na yi shi kaman ?a'ida"
"Sannu Allah ya ba ki lafiya, babu maganin da suka ba ki a asibiti?"
"Akwai fa ina sha amma kaman bana sha"
"Sannu"
Haka tayi ta jera mata duk ta saka kanta a damuwa domin sam bata so taji wani na ciwo a gidan sai gabanta yayi ta faWuwa fargaba ya bi ya rufeta har sai an furta mata yayi sau?i.

Shigowar Uncle da karbar babyn da yayi daga hannunta ya sa ta yi musu sai da safe ta shige ta bar su nan parlor.
Chan cikin dare sai ta ji kaman ana motsi da ?arfi, sai kuma ta ji bugun kofar Wakinta a razane ta farka tana salati jin Muryar uncle ya sa ta dirko da hanzari ta zo ta buWe kofar
"Afeefah ki zauna da yaran nan idan sun yi kuka ki ba su madara zan kai Auntynki asibiti ciwon ciki ya tasar mata sossai"
Tuni ta rikice hawaye har sun fara zarya a idanunta.
"Toh uncle"
Ta faWa tana bin bayanshi, shi ya ri?o Aunty zee da ke tafiya da kyar Afeefah na ta bin su tana share hawaye har zuwa kan babur ya hau ta kwanta jikinshi suka fice tana ta jera mata sannu da Allah ya bata lafiya. sai da taje ta rufe kofa kan ta dawo kan yaran ta zabga tagumi cike da damuwar ciwon Auntyn.

Yaran sam ba su da rikici daman, tun tana tagumi har bacci ya sure ta a kansu ?iran Sallar farko da kukan suhaila su ne suka farkar da ita, ta tashi ta haWa musu NAN1 Win su da ake basu saboda abinci ya ishe su, ba zallar nono Auntyn ke ba su ba, sai da ta saisaita ya zama da dumi cikin tsafta ta fara ba su don suhailar na koshi sai suhail ma ya tashi bayan ta gama ta fice taje tayi alwala ta zo ta fara sallah sai da ta idar tayi Adu'a ciki har da ro?on Allah ya ba Auntynta lafiya kan ta mi?e ta bar sallayar zuwa tsakar gida.

?o?arin Wora musu breakfast ta fara a natse take aikin Dukda hankalinta rabi na ga su Uncle da suke asibiti rabi na ga 'yan biyu kar su farka bata ji kukansu ba har ta gama haWa abinda zata bu?ata ta Wora kan ta shiga sharar tsakar gidan.

Ta gama haWawa tana ?o?arin kwashewa kenan ta ji ana bubbuga kofa ba irin bugun hankali ba, jikin kofar ta isa sai ta ji kaman surutai dai ba na mutum Waya ba, bata buWe ba ta shiga tambayar waye ne?
"Ki buWe mana ai za ki gani!"
Muryar hamdiyya da ta ji ya sa ta buWe kofar sai dai me za ta gani...!




=???Gureenjoh=???

HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

*FREE BOOK*

*Jama'a kuna manta cewa na rubuta True life story a jikin labarin nan, Meyasa na yi kyauta ne kam? Saboda ina so mu ?aru da ilimin dake ciki, na tabbatar daga page 1 zuwa yanzu kun za?ulo darusa masu dumbin yawa kuma ko ban kawo gyara ciki ba kun san amsar hakan. Wallahil azeem ban ?ara komai a labarin Afeefah ba, ban ce babu ?ari ba akwai amma sai a gaba yanzu duk abinda kuka gani a gaske ne ban chanza komai ba, please bear with me=?O?*

*007*

Wasu gungun matasa ne Wauke da makamai suna ?o?arin HankaWa hamdiyya su rufta mata ai da wani irin hanzari ta mayar da kofar ta rufe jikinta na wani irin Waukar tsuma, hankalinta sai ta ji yayi wani irin tashi tsoro da fargaba suka rufe ta, ko kafafunta ta kasa motsa su daga inda take tsaye... ?uuuuu haka cikinta yayi wani irin ?ara a sadda ta ji kukan uncle haWi da maganarshi daga bakin kofan

"Ki buWe ki ba ni yarana...! Kin riga kin cuce ni kin raba ni da uwarsu rabuwa ta har Abada a yanzu ba zan iya sake Waukar raba ni da su ba, in kuma su ma kin cinye kurwarsu ne kaman uwarsu nima duk ki haWa da ni ki cinye Afeefah..."
Sossai yake gunji daga jin muryarshi zaka san baya cikin hayyacinshi ne.
Tsurewa ta yi tana jin kaman ta zauce ko kunnuwanta ba sa ji da kyau. Tamkar sau?ar aradu ta ji wani da kaman yanzu ya iso a gigice yana furta
"Da gaske ne Usman Zainabu ta rasu?"

'Zainabu ta rasu!'
Ko kan kalaman su gama shiga kwakwalwanta sai ji tayi uncle na amsawa
"Zainabu ta tafi ta bar ni. Sai da aka gargaWe ni amma na ?i saurara saboda ta ba ni ya?ini a kan yarinyar, ashe ba haka ba ne kai duniya...! Ashe wanda ya maka rana za ka iya masa dare? Afeefah ta yi mana shigo shigo ba zurfi, lafiya ?alau muka kwanta da zainabu daga ciwon ciki farar Waya muna zuwa asibiti sai ga kiran hamdiyya take sanar min ta yi mummunar mafarki a kan zainabu, sai na sanar mata muna asibiti bata da lafiya ta tsorata tace gata nan zuwa Dukda dare ne haka ta bi gidan wani malami ta taho da shi akan mafarkinta mai muni ne Afeefah ta gama cinye kayan cikin zainabu ashe da gaske ne! Duk irin taimakon da malamin nan ya so bata ya gaza haka likitoci suna gani ta ce ga garin ku..."

Hamdiyya ta chafe cikin kuka
"in ba aikin maita ba menene wannan? an riga an cinye mata kurwa, sai da na faWa wlh sai da na gargadi Aunty akan mayyar yarinyar nan.."
Gayyar mutane bayan waenda hamdiyyar ta zo da su suka sake cigaba da taruwa suna hayaniya akan tabbas ita ce mayyar ai dama daga Dutsen-wai ma gudu wa ta yi saboda yunkurin kashe ta da ?an uwan wadda ta kashe last suke kawai a kasheta.

?afafunta sai suka gaza Waukarta, ta zube yaraf a ?asa, hawayen da suke zuba tuntuni sai suka ?afe kamar rijiyar da aka yi wa yaso. Zuciyarta na raya mata cewa da gaske ita Win annoba ce, da gaske ita Win mayya ce.
Tana ji jama'a na maimaita lafiya ?alau ta kwanta ciwon ciki ya turni?e ta cikin dare daga isa asibitin su sai mutuwa. Hujjar da suka kafa kenan suna ?ara tunzura shi wasu na ta faWan abubuwan da ita karan kanta da ake yi wa ?agen bata san yaushe aka yi ba, ina ma da bata biyo Aunty zee ba? Ina ma da bata zo ba! Ina ma da bata biyo ta ba!
Da gudu ta mi?e tana komawa cikin Waki gunjin wahalallen kukan da ta fashe da shi haWe da ?ara na bala'i na cika ilahirin gidan ba wai don gudun rayuwarta da mijin antinta ke ta i?irarin ita ma sai an kasheta ta bi matarsa ba sai don rungumar mutuwar a karan kanta, tana so a yau ta kawo karshen komai tana so tayi mai gabaWaya da rayuwarta wai haihuwa da hanji... bayi ta shige kai tsaye babu wani tunani ko shawara ta zaro piya-piya da su ke ajiyewa saboda sauro ta buWe tare da kafa bakinta a kai tana kuka me tsanani da dugunzuma zuciya, ?watt! ?watt!! ?watt!!! haka ma?ogoronta ke ba da sauti a sadda ta ke haWiyewa tana jin ta yi sallama da rayuwa kaman yadda mamanta, babanta, kakar ta, innarta da ma Aunty zee suka yi.

Lallai an yi mata mummunan zato da ba za ta taSa wankuwa ba a duniya, ta gaza! Ta kasa rayuwa kaman kowa, a yanzu wa zai dauke ta kuma? Wa zai yarda wani nasa ya aure ta ko ya raSe ta? Mutuwa ita ce abu mafi sau?i a gare ta kaman yadda ta yankewa kanta.
Kururuwa da take ji a nesa bai sa ta sau?e kwalbar fiya-fiyan ba sai da ta ji an yi wani irin wurgi da kwalbar ya tafi ?asa yana tarwatsewa kwatankwacin yadda rayuwarta ta tarwatse. Dishi Dishi take gani jiri ya diSeta sai taji an tare ta sun tafi a tare suuuuu ?asa.

***

A kafa su ke takawa sanye cikin uniform kasancewar assignment da aka ba su a cikin Anchau sun gama shi kuma a lokacin ne suke shirin barin garin zuwa cikin Kaduna, Zaratan matasa ne biyu sanye da khakin Sojoji daga yanayin tafiya da tsarin zubin halittarsu zai tabbatar maka da waennan Win ko a cikin Sojoji za?a?uran ne, da wani irin ginshira suke tafiyan kowannensu na da kalar nashi kyaun, haiba da tarin kwarjini abin da ya bambamta uniform Win nasu abu Waya ne, shi wadda ya fi cin maganin fuskan nan tamau daga damtsen hannunshi akwai wani farin bandage da aka zagaye ?arshen uniform Win dashi a jiki akwai zanen plus ?' Da jan tawada wadda zai tabbatar maka da wannan Win Medical soldier ne.

"Ko wanchan taron na me?"
Na gefen da bai kai haske da wani irin ?asaitar wanchan Win ba ya faWa cikin natsuwa.
A sace ya Wan kalli wurin ya watsar kaman ba zai yi magana ba cikin halinshi na i don't care ya furta
"How would I know Saleem after all tare mu ke da kai?"
Wadda aka ?ira da Saleem ya sake kallon taron a lokacin da suka tunkaro su sossai
"Ko ma menene Rayyan ba na tunanin lafiya..."

Ko ya tanka sai ma kanshi da ya mayar ?asa yana ci gaba da takunshi cikin ?asaita da isa kaman yadda yake a halittarsa.
Ihu da ?arar da ya ratsa kunnuwansu haWe da furta kalaman
"sai mun kasheta yau za mu ga karshen maita"
Da jama'ar wurin suke ta furta wa wasu ma Wauke da makamai ya sa Saleem taka birki yana ri?o hannun Rayyan da yayi kaman bai ji ba.

"Guy akwai matsala, we cannot neglet our duty ba za mu ga ana shirin Sarna mu kama hanya mu wuce ba"
Ko ya tanka sai birkitattun idanunsa da ya kai wurin yana nazarin situation Win fuskar nan babu walwala ko na miskala zarratin.
Bai yi magana ba har Saleem ya isa ga mutanen, yana tsaye daga gefe da farko jama'ar sun so yin gardama amma jin ya kira akan a turo squad kuma ya zaro bindiga ya sa aka fara watsewa uncle da hamdiyya dai sai kuka da Allah ya isa suke yi, a mayar da maganan da ake ne ya ji abin da ke faruwa.

"Wait here!"
Ya faWawa Saleem kan ya haye katangar gidan da ba shi da wani tsawo chan chan, bai buWe kofan ba sai yayi cikin gidan yana dube dube, motsi da Sheshekar da ya ji ne ya saka shi kai kyawawan idanunshi wurin sai suka sau?a kan kwalbar fiya-fiya a take warin ya shige cikin hancin shi da wani kalar hanzari ya fusgo madarar ruwa da ya gani nan cikin Wakin Auntyn kasancewar ta mai jego ya fasa guda biyu ya isa gabanta ya sanya hannu yayi wani irin wurgi da kwalbar ya haWe da gini ya tarwatse...

Sulalewa take ?o?arin yi a lokacin da ya Wago madarar yana shirin bata, bashi da zaSin da ya wuce ya sanya hannunshi Waya ya tareta suka kai ?asa ita tana ?o?arin sumewa shi kuwa ya sau?a a kan gwiwowinshi, kanta ya Wago da take ta kokawar numfashi ya kafa madarar tare da matse hancinta sai da ta kwankwadi mai yawan gaske kan ta sake yunkurowa tayi gaba wani kalar amai na kwace mata, tana gamawa ya sake dura mata Wayar ta sake kwarara wani aman ko idanunta bata iya buWewa alamu sun nuna ta jima da ficewa hayyacinta haka ya sanya hannu ya Wauko ta zuwa waje, Fitowar shi da isowar motar Sojoji lokaci guda sai ciki aka sanya ta ya shiga tare da barin Saleem wurin suka fice a guje kaman yadda suka saba.

Da gudu Uncle da hamdiyya suka shiga suka Wauko yaran da ke ta kuka suna rurrungumesu a lokaci Waya suna ta tsinewa Afeefah, Saleem dake tsaye ya iso gangar uncle Win
"A komai ya kamata ku dinga adalci da tunani, ?age ko sharri ba abu bane mai kyau shin kun taSa jin maita ko a addini? Ko kun taSa ganinta ta yi maitar?"
"Wallahi billahi na rantse da Allah idona idon Afeefah sai na sa an kasheta gwara ku gaya mata tun daga inda ta tafi ta san inda dare ya mata, sam Shigowar ta rayuwarmu bai mana rana ba"
Hamdiyya ta karSi zancen
"ba kai kaWai ba ai gwara mata mutuwar ta da dawowa unguwar nan tsinanniya"
Juyawa kawai Saleem yayi ya bar gidan suna ta zaginta da kwashe mata albarka wasu mata na shigowa ana ta kokarin mayar da magana ai dama an gargadesu.

BAYAN WASU AWANNI

A hankali ta shiga ?o?arin buWe idanunta da suka matu?ar yi mata nauyi tana jin yadda kanta yake wani sarawa, a tunanin ta za ta tsinci kanta cikin ?abari ne kaman yadda ta jima da sallamar da rayuwarta wa mutuwa sai kuma ta ga akasin hakan. Idan ma tunanin ta ya bata daidai kaman nan Win Wakin asibiti ne take ciki duba da yanayin tsarin Wakin da kuma ?arin ruwan da ke shiga jikinta ta canular dake Waure a hannunta. Tunanin dalilin mutuwar tata ne ya bijiro mata kaman ana haska mata majigin rayuwarta...

"Aunty zee ta rasu" Daram! Haka zuciyarta ya buga zuruf ta mi?e zaune kaman ba jiri ne ke walagigi da rayuwarta ba, hannayenta ta sa duk biyu ta toshe dukka kunnuwanta don ji take kaman ana maimaita mata kalaman na rasuwar Aunty zee da speakern da ya fi komai ?ara a duniya. Tamkar zautacciya haka ta saki wani irin ?ara da ya shigo da nurses har uku Wakin da gudu da ma an ba su aikin kula da ita kar ta farka ta sake yunkurin cutar da rayuwarta.
Shigowar su da fara fusge-fusgenta kusan lokaci guda rirri?eta suke kokarin yi amma kaman mai tashin aljannu sai wani irin ihu take

5 / 53