Haihuwa Da Hanji Complete Hausa Novel

Author :  Halima K Mashi Category :  Adventure

Chapter   16 / 53

45K to 48K   out of 158.4K words

iya rudewa a karamin abu"
"Mammi wannan yarinya da kuka dawo tare Afeefah kin ji jikinta? Kaman wuta sai kuka take yi tana bukatar a duba ta ko mu tafi hospital?"

"Subhallah! Tashi mu je in ga jikin"
Har sun mi?e Mammi tace
"Taho min da wayata"
Taje ta Wauka a bedside suka fita, a ta babban parlorn nan suka yi sashen da take Win wanda na 'yan matan biyu ne Jannah da tayi aure bai jima sossai ba sai Abeeha su suke rayuwa anan.

Suna shiga Mammi ta hau gadon da taimakon Abeeha suka Waga Afeefar Mammi ta jinginata da kafaWarta tana yi mata sannu cikin kulawa, wannan dumi na jikinta da kulawar sai ya sake karya zuciyar Afeefah tana tsoro! Tana tsananin tsoron su san tarihin ta suma su guje ta, tana son wannan dumi da kauna a tare da ita in ba haka ba kila mutuwa zata yi kawai sai ta fi hutawa, ta gaji haka zuciyarta ya fi glass tarwatsewa a yanzu haka.

"Kira min Yayanku"
Layin shi ta nemo a wayan mammin ta ?ira ringing na farko ya Waga da sallama.
"Mammi jikin ne?"
"No Saraki! Na ma ji ?arfin jikin ka san abin kaman tashin aljannu yanzu sau?i anjima babu sau?i sai na Allah, ya jikin saleem Win?"
Ya amsa cikin muryarshin nan
"Ya ji sau?i though he's still on admission, amma komai zai daidaita in shaa Allah"
"Toh Allah ya bashi lafiya, ina so ka zo ka duba Afeefah fa ashe itama bata jin daaWi jikin nan rau sai kuka take"
Shiru yayi for seconds kan yace
"Mammi bai wuci yunwa ba and stress she should just eat nd get enough sleep"

"Ta ya mutum zai iya bacci with this temperature? Idan ba zaka zo ba in Wauki mayafi in kaita asibiti"
Zaune ya mi?e daga kishingiden da yake a office nashi yana wara ido, yaushe Mammi ta san yarinyar nan da har take mishi irin maganan nan a kanta? Yamutsa fuska yayi ko dai da gaske asirin take yiwa mutane da har ta asirce mishi Mamminshi?

"Ina zuwa"
Abin da ya fada kenan da kyar, Mammi ta kashe wayan Abeeha tace
"Lallai Mammi kina so Ya Rayyan ya tsani yarinyar nan, tabbb he sound upset fa da yadda kika mishi maganarta yo ko mune bamu da lafiya ba sai ya gama shan kamshin shi yake duba mu ba, wani sa'in ba sai dai mu ha?ura mu tafi asibiti ba ma"

"Abeeha yarinyar nan haka kawai nake jin she gets special place in my heart, kin san taimakon da tayi min?"
Nan Mammi ta shiga bata labarin abin da Afeefah tayi mata
"Mammi wlh har Naji ina sonta sossai nima, to ina 'yan gidansu ina parents Winta?"
"Ina ga sun yi magana da Saraki while i was unconcious don shi ya ce min bata da kowa"
Afeefah dai na jinsu, tunda Mammi ta kira Rayyan tsoro ya rufeta, gashi ya ji haushin yadda mamanshi ta mishi magana a kanta kar ya zo ma yayi mata allurar da ba?ar mugunta ita dai da an barta kawai.

Suna Wakin suna ta hira kadan kadan don Abeeha bata son zama baki shiru har Afeefah na mamaki kaman ba ?anwar Rayyan da magana ke mishi wahala ba, ita ma dai bata ga kamanninsu ba sai dai Abeehar kyakyawa ce kuma ta fi Mimmi haske amma ba ta kai ko farcen Rayyan ba, bata gama nazarin ba ya shigo Wakin hannunshi rike da karamar Red briefcase.

Dammm haka gabanta ya buga, ya kalli Mammi da har lokacin Afeefah ke kan kafaWarta ya wara kyawawan idanunshin nan kan ya ce
"Me wannan? Mammi yaushe kika yi lafiyar daukar wata? Watan ma stranger?"
Da sauri Afeefah ta mi?e zaune jiri ya kwashe ta ta koma jikin gadon ta jingina idanunta a lumshe zuciyarta na harbawa da tsoro.

"Haba Saraki ji yadda ka tsoratata?"
Ganin sossai ranshi bai mishi daaWi ba yasa bata sake cewa komai ba, ya dubi Abeeha
"Wawuyar banza come on raka Mammi Wakinta she should be resting ba stressing kanta ba"
Tura baki tayi ya nufeta ta mi?e da gudu ta koma kusa da Mammi sai Harare Harare yake.
Mammi tayi dariya
"Zan je in huta Saraki don Allah ka yi mata a hankali, she's suffering"
Ta dubi Abeeha
"kin ga kama ni mu tafi tunda overprotective Yayan naki ya kore mu"
In ta shi ne fa tafiya ma zai iya yi mata, itama kuma son da take mishi bata hada da kowa ba, kuma babu wanda ya kaita saninshi don ko kallon abu yayi ta san ma'anar kallon, Dukda fuskarnan ya fi zama a haWe amma ita tana gane idan yana cikin farin ciki, damuwa ko bakin ciki, yanzu haka ta karanci akwai 'yar damuwa a ranshi sannan har da rigima irin tashi don baya so yaga tana fifita wani a kanshi, su Jannah kan ce Ya Rayyan idan ya samu wacce yake so kamar rai za'a ga kishi kamar hauka.

Bayan fitan su Wakin ya zama shiru sai su biyu kawai hakan ya kara tsinka Afeefah.

"Kwanta"
Ta ji muryarshi ya daki dodon kunnenta duk da ba da ?arfi ko tsawa yayi maganan ba.

Da sauri ta kwantan tana kara jan bargo, hannunta dake kan cikinta kawai taji sassanyar tafin hannunshi mai taushi ya kama babu shiri ta buWe idanunta sai suka faWa cikin nashi da shima a lokacin ya kalleta...

****

Ta Sangaren Sulaiman yana ta gwada Layin Afeefah don ya ji ya jikinta har yamman ya kasa samunta, ya ajiye kila network ne don haka ya cigaba da huldar gabanshi har Magrib baya samunta, yana gama shirin asibiti ya nufi gidan don ya ji ko lafiya baya samunta haka bayan ya isa suka gaisa da su mudi.

"Don Allah ko za ku dubo min Afeefah?"
Iliya ya ce
"Ai Afeefah bata gidan nan, ina zato ma ta barshi gabaWaya don da akwati ta fita tun safe"
Gabanshi ne ya faWi
"wani irin tafiya ba dawowa? An taSa tafiya haka babu shiri? Gida ta koma ne?"

Mudi yace
"Wallahi bamu sani ba amma dai kaman gidan dai ba lafiya dai, don Oga saleem ma yanzu haka yana kwance Hajiyar na a hasale, 'yan matan kuma sai kuka Toh ita ma Afeefar da ta fito a chan ta tsuguna ta ci kukanta isashe kan ta tashi ta tafi"

Sossai damuwa ya nuna a fuskanshi, idan tunanin shi ya bashi daidai Saleem ya faWawa Afeefah yana sonta mamanshi ta ji shine suka kore ta, godiya yayiwa su Mudi ya juya ya nufi gida, kila ta koma kauyensu yana ji a ranshi da sau?i ma tunda har ta faWa mishi sunan kauyen kan su rabu da bai san inda zai sa kanshi ba, dole ya je ya neme ta.

Gida ya dawo Umma na ganinshi tace
"Ah Sulaiman ina asibitin? Me ya faru na ga kaman kana cikin damuwa?"
"Umma su saleem sun kori Afeefah a gidansu, mamanshi ta kore ta ta koma kauyensu dole gobe in nemi leave in je in sameta ban san ya take ba kuma wayanta baya shiga"

"Wacece haka?"
Suka ji Muryar Abba!

Umma ce ta mishi bayani yana murmushi yace
"Toh ai Alhamdulillah! Dama da niyyar aura maka mata na dawo a yau na gama maka uzuri goben da su Yaya Zubairu za ku tafi a yi maka tambaya gabaWaya tunda Allah ya sa ka samu wacce kake so kuma mahaifiyarka ta gamsu da tarbiyar ta"

Murmushi ya saki yana jin sanyi a ranshi Dukda ta wani Sangaren yana tunanin kar Afeefah taji ba daaWi tunda bata sani ba kuma ba wai soyayyarsu yayi zurfi bane ita ke ture shi yana sa kai amma dai ya ji daaWi don da farin ciki ya koma asibitin da bai yi niyyan zuwan ba ya tafi saboda ya samu leave a gobe Win don su tafi Dutsen-wai.

A waya Abba ya sanarwa yayyenshi biyu akan za'a je wa Sulaiman tambayar Na gani ina so a kauyen Dutsen-wai, basu wani damu ba don duk su burin su ba su hada zuri'a da masu kuWi ba sai su hada da gidan mutunci gidan tarbiya da sanin ya kamata shi ne abin da suke dubawa.



=???Gureenjoh=???

HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

*FREE BOOK*

*Gobe in muna raye sai dare za ku ji ni da yardar Allah*

*020*

Harara ya sakar mata da sauri ta mayar da idanun ta rufe ruff tsaki ya ja a fili, ya fara ?o?arin neman vain Winta... 'Asshh' ta faWa a hankali jin ya soka allurar sai ta fara kokarin janye hannun.

"Kina janye hannun nan sai na wanka miki mari akwai wanda yace ki yi ta tuna samarin ki kina kuka har ciwo ya kama ki?"

Tsit tayi bata kuma motsan ba, kila Rayyan shine ajalinta wa ya sani don tunda ya daka mata tsawar nan ko numfashi mai kyau ba ta iya ja har ya gama Waura mata drip Win, bata ji fitan shi ba ita kam tun tana pretending har baccin gaske ya Wauke ta a haka, don dama jiya ba baccin ta samu ba na kirki gashi yau ta yini a kan hanya tana galantoyi.

Sashenshi kawai ya mi?a daga nan don ya matu?ar gajiya hutu kawai yake bu?ata, wanka yayi ya fito da alwala ya zo ya shirya cikin wani morrocon jallabiya ba?i sidik mai sheki wanda ya fito da ainihin kyaunshi fatarshi ya haska jallabiyar, masallaci kawai ya wuce bai dawo cikin gidan ba sai da yayi isha, time ya kalla ya Wauke ido ya nufi cikin main parlorn kai tsaye Wakin da take ya wuce, ta mi?e zaune bayanta jingine da jikin gadon kafafunta na cikin bargo, idanunta sun kara girma sun dan sauya saboda kukan da ta yini yi ga kuma bacci da tayi tayi, hulan kanta ya zame sosai ya bayyana rabin gashinta mai sulbi, tunani take ya zata yi in ruwan ya ?are sai taji an yi knocking seconds uku zuwa huWu ya turo kofan ya sanyo kai da sallama wadda iya shi kaWai ya san yayi kayanshi.

Kanta tayi saurin mayarwa kasa Alamu sun nuna bashi da niyyar magana don har ya zo ya cire ruwan da ya ?are ya bare wani allura ya fasa yayi mata a canular bai ce takk ba itama bata ce ba, kamshinshi duk ya cika Wakin har ya gama ya juya zai fita ta furta

"Na gode"

Bai ce komai ba ya fice daga Wakin, kai tsaye wurin Mammi yayi, tana daga parlor a zaune cikin kujera abinci ne a gabanta wanda ta gama ci yanzu cikin kula sossai da cimar tata Win don professional cooker ya samo mata wacce take kulawa da zallar abincinta kuma take da karatu na musamman akan cimar da ake ba wa masu ciwon ?oda da kan tafi da diabetes, ba'a so ta ci late kuma da ta gama ta sha magani tana so ya Wan saketa sai taje ta duba Afeefah.

Bai yi magana ba kawai ya zo ya zauna gefenta, ta kalleshi tayi murmushi
"Gajiya ne a jikinka sossai Saraki, ka ci abinci sai ka je ka huta"
Kai ya gyaWa kawai don bashi da niyyar magana, da intercom tayi amfani ta kira su a kitchen a kan a kawo abincin Saraki, simple abinci ne marar nauyi yake ci da dare suka kawo suka jere a gabanshi, har lokacin yana kishindige kusa da ita idanunshi a lumshe.

"Tashi ka ci kar yayi sanyi babana ko in baka?"
Ya buWe ido a hankali ya Wan yi murmushi kaWan sai wani sirrin kyaunshi ya bayyana Dukda murmushin bai jima ba sai dai tabbas duk wanda yayi wa irin murmushin zai jima bai manta ba.

Itama murmushi tayi don ita kam akwai fara'a masha Allah, abincin ya Wan ci kaWan ya kalleta jin tana cewa
"Ina zuwa zan duba Afeefah"
Da Kai ya amsa ta fice, ta samu Afeefar ta idar da sallolinta tana kokarin cin abincin da aka shigo mata dashi Abeeha na zaune cikin kujera daya daga cikin huWu dake gefen Wakin tana danna waya ganin Mammi ya sa ta taso

"Afeefah Wiyata ya jikin?"
Murmushi ta saki a kunyace tace
"Alhamdulillah da sau?i sossai Aunty na gode"
"Bana son sake ji kin ce Auntyn nan baki ji Abin da su Saraki ke faWa bane?"
Murmushi tayi.
"Abeeha ki kula da ita har tayi bacci zan je Saraki na jirana in na sha sauran magungunan kuma kin san bana iya taSuka komai sai da safenku"

"Toh Mammi sai da safe Allah ya kara sau?i"
"Allah ya baki lafiya sai da safe Mammi"
Afeefah ta faWa ta amsa da murmushi kan ta fice.

"Na ga dai baki da niyyar sa abincin nan bari na zuba miki"
Abeeha ta faWa tana zuba mata Afeefar ke cewa yayi amma sai da taji ya mata a ranta kan ta bari kuma tace sai Afeefar ta cinye, sossai moment Winta a gidan na yan awannin nan yayi mata daaWi in ka cire arangamarsu da Rayyan amma Mammi da Abeeha mutanen kirki ne da suka yi ?arancin samu a wannan zamani.

Mammi na komawa ta samu ya gama, Waki ta shige ta fara shirin kwanciya cike da dauriya take komai fuskarta dai baya nuna wa amma ita ta san me take ji, sai da ya bata mintunan da yake da tabbacin ta gama yayi knocking ya shiga Wakin tana zaune bakin gado sanye da doguwar rigan bacci har ?asa mai kauri, frigde yaje ya Wauko mata ruwa tulin magungunanta da suke cikin wani basket guda mai kyau ya Wauko ya zaSi na daren ya bare ya sanya mata a tafin hannunta, babu musu ta sha yadda ya bu?ata kan ta kwanta, ya ja mata bargo ya zauna daga gefenta tare da ri?e hannunta Waya.

Adu'a yayi ta mata tun tana kallonshi tana danne hawayen da suke ta yunkurin zubo mata har tayi bacci, idanunshi da suka rine ya Wan rintse yana jin azaban da zuciyarshi ke yi, da yana da yadda zai yi ya mayar da ciwon Mammi jikinshi da bata shekara takwas tana fama da kidney failure ba, da kuWi za su yi mishi maganin ciwon Mammi da ko zai yi yawo tsirara sai ya samar mata lafiya, sai dai yana ro?on Allah a koyaushe yadda aka bata wa'adin watanni uku za ta mutu amma yanzu shekara har bakwai da abin ya san ba yin su bane ba kuma dabararsu bace Allah ne mai yadda ya so, sai dai a tsananin tsorace yake hakan ya sa sadaqa da duk adu'ar shi yake kan Mamminshi itama saboda rage mishi damuwa take danne wani abin.

Sai da ya tabbatar komai intact kan ya fice daga Wakin yayi Sashenshi, Saleem ya ?ira da har lokacin yana asibiti yana samun kulawa

"Har yanzu babu labarin Afeefah ko Rayyan?"

Ajiyar zuciya Rayyan ya sau?e
"Na ce ka daina Waga hankalinka za mu same ta, ina kan bincike dai in har tana cikin Kaduna ba zata Sace ba just focus on your health"

Kai saleem ya gyaWa sai yake ganin kaman Rayyan bai yi niyya bane, da yayi niyya ba zai kai zuwa lokacin bai same ta ba, damuwarshi ya zata kwana? A ina zata kwana? Me ta ci? Duk ya kasa kwantar da hankalinshi a gefe ga damuwar rashin ganin mommy Dukda ta mishi abin da ya zama gyambo a zuciyarshi sai dai uwa ce babu yadda ya iya kuma yana ?aunarta bata da mahadi a wannan duniya.

A Wan sanyaye yayi sallama da Rayyan, Rayyan ya bi wayan da kallo baya jin zai gaya mishi inda Afeefah take saboda yana son Saleem Win ya manta da ita once and for all yanzu in ya san tana nan zai cigaba da sa hope a kan samunta alhali mahaifiyarshi bata Waura wannan damara ba na mallaka wa yaron nata cikar burin shi hakan ya sa ya Soye mishi wanzuwar Afeefar a gidansu.

Su Samha ko da suka zo sun ?araci zamansu ko ci kanku bai ce musu ba sun gaishe shi ma bai amsa ba, wani irin zafin su yake ji a lokaci Waya yana mamaki bai taSa sanin inhumanity Winsu ya kai haka ba, suka gaji suka tafi.

****

Washegari

Da misalin karfe bakwai na safe Sulaiman ya fito shirye cikin manyan kaya, sallama yayi wa umma tana ta adu'ar dacewa Baba Jummai ma Adu'a tayi ta mishi har ya fice. Gidan Yaya Zubairu ya fara zuwa ya Wauke shi kan ya wuce gidan babban Yayansu Abban Yaya Ummaru, dattijai ne masu mutunci da kamala kuma duk suna da dukiyar su daidai gwargwadon.

Anan suka kama hanyar kauyen su Afeefah yana ta Adu'a da Fatan ya same ta chan Dukda bai yi ma tunanin rashin samunta ba don ina zata koma in ba gida ba? Tafiyan awanni kadan ya kawo su kauyen yana jin hirarsu Yaya Zubairu da suke zaune a baya, sai da suka Wan shiga cikin garin kan ya Wan tsaya jikin wani shago matasa ne zaune su wurin huWu ya sau?e glass

"Assalamu Alaikum barkanmu da warhaka"

"Barka dai Alhaji"

"Don Allah tambaya nake yi"

"To Allah ya sa mun sani"

"Gidan su Afeefah kamal"

Tsittt suka Wan yi wannan ya kalli wanchan wanchan ya kalli wanchan..

"Kai ko me zaka yi gidan su Mayyar yarinyar nan? Ai Annoba za ka ce sai mun fi gane ta"

"Annoba"
Ya maimaita sunan, abin da ta faWa mishi kenan me yasa ake ce mata annoba? Dan kallon su Yaya Zubairu yayi duk fuskar su ya Wan nuna mamaki.

"Gidansu nake nema"
Ya faWa ba tare da ya ji daaWin furucin su a kanta ba.

"Ka ga kara gaba sai ka tambaya a chan, ba mu san ko laifi ta muku ba kun zo yi wa kawunta tijara abu ya shafe mu lalala bamu shirya rigimar Labaran ba"

Babu wanda ya tanka a cikinsu har ya ja motan suka yi gaba, wasu yara 'yan daidai ya samu ya kira su su biyu
"Gidan su Afeefah kamal nake nema"

?ayan ya Wan kalli Wayan
"Mayyar nan fa suke nema ta gidan su Auwalu"
?ayan ya zaro ido
"Wacce ta cinye Amadun gidan malam yahaya ta gudu duniya?"
"Eh ita ce..."
Sai Wayan ya gyaWa kai ya juya ga Sulaiman da kanshi ya sake mugun Waurewa.

"Idan kayi gaba ka Wauki Layin hagu gida na biyu in baka gane ba ka ce gidan su Annoba kake nema ajalin duk wanda ya raSeki"
Suna kai nan suka gudu.

"Sulaimanu a wani irin gida ka nemo aure? Wace irin yarinya

16 / 53