Haihuwa Da Hanji Complete Hausa Novel

Author :  Halima K Mashi Category :  Adventure

Chapter   39 / 53

114K to 117K   out of 158.4K words

ce aka yi kidnapping suka je suka samu sa'ar tseratar dasu, gobe duk su Afeefah za su tafi chan nima yanzu zan sayi ticket"

"ikon Allah ikon gaske, wato a wannan duniya ka kalli mutum ne kawai baka san waye shi ba, No wonder yake da Wabi'ar sarautar... Ikon Allah wannan abin mamaki dayawa yake"
Sadiqa tace
"Oh wa zai tuna Afeefah za ta iya sa'ar zama matar irin wannan mutumi? Yanzu mu fa ko kallonshi sai da hanya...waye bai san irin tarin dukiyarsu, karfin mulkinsu da izzarsu ba!"
Samha tace
"Gaskiya tayi dace kam tsuntsu daga sama... Mun mata murna Allah ya cigaba da basu zaman lafiya haWe da zuri'a dayyaba"
Duk suka amsa da Ameen amma mamaki da tsoron Allah na sake rufe su rufff.
Saleem ya mi?e ya fice daga gidan.

****

Kitchen ya shiga kai tsaye bayan shigarshi sashen ya dafa indomie don babu abinda babu na girki cikin babban kitchen Win komai na zamani komai kuma fess kaman ka lashe don walwali, a plate ya juyo ya dawo parlor hannunshi Waya rike da ruwa yana gama ci ya mayar da kwanonin ya wuce Waki bai samu ya Kira Abeeha da ya ga missed call nata ba saboda lokacin masallaci dake kokarin ?urewa ya sauya kaya zuwa wasu Fararen jumpha hadadden Winki 'yar ciki da babbar riga ya fita yayi kyau ainun daga ka ganshi zaka san yaro da kuWi ne abokin tafiyar manyan, ga sarautar amma ya tafi da tsantsar wayewa, ilimi da sanin kan tsarin shiga.

Hula da takalmin da ya saka duka farare fatarshi sai shining yake Dukda ma ya Wan yi duhu kaWan saboda zaman da suka yi daji amma fess yake ba ma zaka gane ba idan ba ka san shi ba, turare ya feshe jikinshi da su kala daban daban kan ya zari wayanshi ya fito tuni duk suka mi?e dogaran suka fara zabga mishi kirari ya Waga musu hannu don bai cika so ba yayi gaba suka rufa mishi baya har mota, Dukda masallacin ma a cikin masarautar yake sai dai akwai 'yar nisa don haka dole mota ya shiga suka yi har motoci uku da dogaran suka nufi masallaci.

Mai martaba na shiga shima ya iso ya shiga nan aka fara huduba bayan an gama tsaf aka gabatar da sallah kaman yadda addini ya tanada aka yi adu'o'i kan aka shiga watsewa a hankali, daga nan fada suka nufa don sarki na son ganinshi yana isa gaban manya jagoran addini da al'ada na fulani wato LaamiWo ya gabatar dashi a matsayin Ciroman Fombina kuma Yarima Fuunange na ?asar Fombina (Yariman Matasa) a take aka mishi rawani fari ?al mai kamshi wow ya fita kaman ka sace shi ciki, kasancewar wurin akwai yan jarida kala kala tuni ya fara zagaya duniya.

Turaki ne ya karSi abin magana ya gabatar da kanshi kan ya ce
"Ciroma alhakina ne da in sanar maka aikin matsayinka, na san ka riga ka san Ciroma shine wanda aka Wauka matsayin Wan gado ko mai jiran gado. Yarima Fuunange wato Yariman Matasa kuwa mun bar maka goben matasan mu ne a hannunka, kai ne shugabansu wurin ganin sun cimma al'adar mu na fulani bisa kan daidai wato:
" Koyon Pulaaku (hakuri, ladabi, kunya, jarumta).
" Koyon sana'a ko aikin iyaye (kiwo, noma, ko fatauci).
" Haskawa a cikin al'umma ta hanyar waka, rawa, da wasan al'adu da gargajiya.
Muna yi maka Fatan alkhairi da Fatan Allah ya baka ikon sauke wannan nauyi da aka Wora maka"

Tuni sarkin busa ya fara busa algaita mai daaWin sauraro dogarai suka shiga jefo kirari daban daban, ya mi?e tsaye ya isa gaban mahaifinshi yayi godiya ya juya aka yi mishi rakiya da wannan busa da sarewa
"Taaakawarka lafiya Wan sarki jikan sarki kuma uban sarkin gobe, kaaaareka Ciroman duk duniya Yariman Matasa gaba saalaamun baya salaaamun, ma?iyanka fadawarka Waawisu sarkin ado... Kyaun Wa shi ne ya gaji mahaifi kaareka Ciroma"
Abin da ake ta nanatawa kenan busa da sarewa na tashi har parlorn ba?in shi na sashenshi inda anan zai gana da 'yan jaridar da suke jiran shi kan aikinsu.

Zama yayi ya Wora kafa Waya kan Waya yana dan lumshe ido ya buWe saboda gajiyar da yayi ga chan ?asan ranshi wani abu na mintsininshi na kewar abin da zuciyarshi ke mararin ko da sauraron muryarta ne bai samu dama ba.

"Ranka ya daWe Dukda abin da ya ajiye mu anan daban sai dai za mu fara ne da taya ka murnan shigowa cikin ahalinka lafiya, shin me za ka iya cewa akan farin cikin da kake ciki a yanzu? Menene kuma ya zama babban mukamin bayyanarka a wannan lokaci?"

Murya ya Wan gyara bayan yayi sallama da Fatan alkhairi kan ya furta
"Komai lokaci ne na yarda da wannan, sannan bafulatani yace Munyal deefan hayre, ko va'i fu jippan"(mai ha?uri kan dafa dutse kuma duk nisan jifa ?asa zai dawo)"

Amsar kenan da ya bayar, dan jaridar ya zaci zai kara wani abu amma sai ya ji shiru sai yace
"Masha Allah, Toh bari mu koma abin da ya ajiye mu anan shin menene ya faru? Ta ya aka yi taron al'umma suna jiran ganin waennan miyagu sun kasance Fulani kaman yadda aka jima ana yi wa Fulani kuWin goro sai kuma aka haihu a ragaya?"

"Dama chan kulba ta jima tana Sarna ana cewa jaSa ce, bana manta ina da wani shugaba a baya da sanadiyar kudin goro da ya mana ban taSa furta mishi ni bafulatani bane amma ya kafa min karar zuka ban ci mishi ba ban sha mishi ba, hakika wannan irin zato na duk bafulatani Wan ta'adda ne ya jima yana ciwa dayawa tuwo a ?warya.
Ba a tuna baya in ji masu iya magana wai gyartai ya ci sarauta, a lokacin da duniya ke kwance kabilu mabanbanta kan shiga rugagen Fulani ayi wasa tare, a ci abinci tare a sha kindirmo a dalilin haka har zumunci ya ?ullu sai auratayya ta shiga tsakani. Da tafiya tayi tafiya a sannu sannu aka fara kwacewa Fulani shanu da matayensu a rugage kafin komai ya ta'azzara da abin ya fara zuwa gidan gona da kauyuka sai aka yi musu kuWin goro aka far musu da kisa na kan me uwa da wabi wanda kan iya Warsa Waukar fansa, dayawa daga cikin Fulanin da suke rayuwa a daji babu ilimin addini ba na zamani, malamai babu ruwansu da kai da'awa, gomanti babu ruwan ta da samar da ingantacciyar ruwa ko makarantun zamani, aka kwace sandunansu na kiwo aka dam?a musu makamai saboda wani ?udiri kawai na samun duniya a ji daaWin cin ta da tsinken sakace.
A hankali ringingimu suka fara yawa ta yadda zaman lafiya yayi mana ?aura hakan ya shafi har waenda basu ji ba basu gani ba, shi fa Wan ta'adda bashi da ?abila, yare, addini ko jinsi in dai mutum bai da imani ko wanene shi bahaushe, Fulani, kanuri, yoruba ko igbo zai iya kasancewa Wan ta'adda hasali ma ku sani ba Fulani bane suka aikata mana wannan ta'asar idan ma su ne suka aikata wa wasu daga cikin mu a wannan karon ba su bane don ma turanci ne tsantsa a bakin waennan, makamai da abincin da suke ci be yi yanayi da na bafulatanin ruga ba sai na wayayyen mutum Wan zamani amma kuma idan zasu yi hausa su kan yi da sigar harshen Fulani Lallai an jima ana ruwa ?asa na shanyewa."

?an jaridar cike da gamsuwa yace
"Barka da Yariman Matasa Ciroman Fombina, hakika gwalagwalan kalamanka sun fi yanayi da na hikima Allah ya sa mu gane. Toh wace hanya kake gani za'a bi wurin dakile wannan al'amari da ya ta'azzari al'umma yake kuma lalata musu Matasa?"

"Hanyoyin masu sau?i ne ga al'umma amma masu wuya ga gomnati don zai kawo musu cikas amma idan al'umma suka tashi suka yi aiki a tare za'a iya maganceta cikin sau?i, hanyoyin za su iya haWa wa da
" Karfafa tsaro da sa ido a kan dazuka da
hanyoyi.
" ?ara horo da kayan aiki ga jami'an tsaro.
" Bincike da hukunta masu laifi cikin hanzari.
" ?arfafa al'umma da aikin yi ga matasa.
" ?arfafa haWin kai tsakanin al'umma da hukumomi - wato tsaro na gari.
" ?in biyan kudin fansa - domin rage ribar garkuwa"
Yana maganan ne yana ?irgasu da yatsun shi cikin aji da iya magana.

Kanshi duk ya ishe shi da ciwo da kyar ya gama sallama da mutane yayi la'asar ya shiga ya kwanta yana lumshe idanunshi da suke mishi nauyi ainun duk yadda ya washi baccin yamma bai san ya Wauke shi ba don ya sha magani ga gajiya da ya tarar mishi.

***

Idanu kawai Afeefah ke Binshi dashi tun sanar da dawowanshi hasko shi da aka yi ana mishi sarautar Yariman Matasa da ma hirar da aka yin don live ne a manyan jaridu har international, Fatan alkhairi da ake Binshi da shi da yabon da yake sha duk suna kallo a ipad Win Abeehar, ita dai ta rasa me ke damunta ma hawaye kawai ta fara tsabar feelings Win sun zo mata daban daban, ya mata kyau ba ?arami ba yadda kuma ya mata ta san yayiwa yanmata dayawa, kishi na taso mata sai kuma ta shiga damuwar anya ma a mace ya dau?eta? Don ko ta wani Sangare tana ganin ita Win ba tsararshi ba ce, tun daga tsatso, asali, ilimi, dukiya da kuma mulki ba ta inda tayi matching da shi kenan 'yan uwanshi za su iya ware ta yadda take jin labarin gidan sarauta?

Meyasa be neme ta ba? Sukuku haka su Abeeha suka taya ta haWa kayanta akwati biyu suna ta surutu bata ce musu komai don faWuwar gaban da take fama dashi kaWai ya ishe ta, ko da suka bar Wakin kifewa kawai tayi ta saki kukan da bata san na menene ba, ko abinci bata ci ba tayi kuka ta koshi har bacci ya Wauketa a haka wuraren bakwai na dare.

****

Shafa fuskar ipad Win take da ake nuno hiran tana kuka, tana ganin yadda yaronta ya girma ya zama mutum, tana ganin tarin baiwa da nasaba da Allah yayi mishi tana jin guilt na tauye mishi wannan hakki tun daga yaranta, tana tuna yadda ta zame kafafunta daga cikin hannunshi tana tafiya ta barshi a bakon wurin da bai san kowa ba.... Bata ga laifinshi ba don bai zo inda take ba itama kunyar fuskantar shi take ji kaman ta nitse.

Turo kofan aka yi aka shigo, ta Waga kai ta kalli Aisha, Matashiyar kyakyawar yarinyar da ke tsananin kama da Rayyan Win ta iso gangarta
"Ammi Meyasa kike son sakawa kanki damuwa har haka? Baya nan kullum kuka da tunani ba ki samu cikakken farin ciki ba ya dawo ma baki huta ba? Gashi shi ko ya damu dake tunda bai tako kafarsa ya zo inda kike ba?"

"Aisha bashi da laifi don bai zo ba, baki san me na aikata mishi bane"
"ko me kika aikata mishi uwa fa uwa ce Ammi don Allah tunda ya bayyana cikin koshin lafiya yana ci yana sha kuma babu abinda ke damunshi ki bar wannan kuka haka ki nemi natsuwar ki"
Da lallami tayi maganan, Ammie tayi murmushi mai ciwo sati uku kenan ko kallonta mai martaba bai sake yi ba bare har yayi magana da ita, ta san tayi kuskure amma su saurare ta kan su yanke kowani irin hukunci, tana kuma ganin Aishan bata san zafin dake cikin Abandoning bane ta tashi gaban iyayenta da gatanta shiyasa take wannan magana amma ita ta san dole sai an dauki lokaci Sameer zai sau?o.

Karfe shidda ya tashi ya watsa ruwa yayi sallah kan ya kira Abeeha ta Wauka suka gaisa kan yace
"Me kaman Muryar jannah nake ji?"

"Eh Yaya ta zo ne da shirin tafiya akan gobe kawai sai mu wuce airport daga nan"
"Me zai faru idan goben kuka haWu airport da ita? Mijin yarinyar nan na sakacin barin matarshi sakaka tana yadda take so fa... Ina Afeefahh?"
Mi?ewa tayi
"Bari na kai mata tana Sangarenku"
"Wayanta fa me ya same shi?"
"Ruwa ne ya shiga sai ya Wauke Yaya"
Bai ce komai ba chan kuma ya fara ja mata kunne akan su tabbatar basu bar komai da zai iya lalacewa a gidan ba tana amsawa har ta tura Wakin Afeefah da sallama.

"Yaya ta yi bacci fa in tashe ta?"
Ya Wan yi shiru yana jin ba daaWi kaman ya ce eh sai kuma yace
"Kyaleta..amma sallah fa?"
Sai tayi shiru ya fahimta don haka yace
"Shikenan! Da safe za mu yi magana"
Ta mishi sallama ya katse wayan ita kuma ta fice daga dakin.




=???Gureenjoh=???

HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

ADABI WRITERS ASSOCIATION

*FREE BOOK*

*48*

Washegari saboda tarin gajiyar da ke jikinshi bai iya ya farka ba tun bayan Sallar asuba sai wuraren karfe sha Waya, ko da ya kalli time ya san any moment from then sun kusa isa already Mai martaba ya tanadar da duk motocin da za su Wauko su daga airport da ma masauki har da abin da zasu ci kan ya zauna da su gabaWaya yadda ya shirya.

Wannan dalili ya sa kawai ya shiga wanka a natse yake komai cikin sarauta da ya bi jiki, ya fito ya shirya cikin manyan kaya mint green ne yadin mai Wan duhu ya mishi kyau ainun ya feshe jikinshi da turaruka kan ya fito parlor sai karab idanunshi suka sau?a akan kuyangi har biyar da suke zaune daga chan kusurwan parlorn bai tanka su ba ya shiga kitchen ya haWa tea ya fito ya zauna tare da crossing legs nan suka fara kwasar gaisuwa kai ya gyaWa kan ya yi kiran GaabWo yana cigaba da sipping tea din yana karkaWa ?afafu.

"Wa ya aiko su?"

"Uwargida Fulani Adama ce ranka ya dade ya baka yawan rai"
Ya amsa
Bai Wago ba idanunshi na kan waya yace
"Duk su bani wuri ba na son ganinsu ka kuma tabbatar basu sake shigowa sashen nan ba"
Da sauri ya amsa ya juya ya kallesu tuni suka mi?e suka tafi Win.

Ba'a jima da tafiyan su ba sai ga kira daga mai martaba dole ya mi?e ya nufi sashenshi, a zaune ya same shi shima ya samu wuri ya zauna ya kwashi gaisuwa
"Mamanka ta kawo min ?ararka, Meyasa ka kori kuyangin da aka tura sashenku? Ka dai san ko kai baka bu?ata matarka tana bu?atarsu saboda hidima"

"Basu yi min bane ranka ya daWe"
Murmushi mai martaba yayi
"Toh shikenan zan yi magana da jakadiya sai ta kawo maka wasu"
Shi dai idan ba don mai martaban ba da ba wata da za'a tura mishi shashe amma bai ce komai ba.
"Ba?inmu za su iya sauka cikin kowani lokaci motoci na nan suna jiransu a Airport da Wambai da shi na wakilta ya tarbe su saboda muhimmancinsu"
Ko kan yayi magana aka fara sanarwar Shigowar Mahaifiyarshi Dukda yadda gabanshi ya faWi zuciyarshi ya chanza bugu hakan bai sa ya Wago kai ba kanshi na kasa har ta samu wuri ta zauna ta mayar da kanta ?asa a hankali hawayenta ke diga bisa kan kyakyawar shimfidar parlorn.

Shiru wurin ya Wauka kan a hankali Rayyan yace
"Barka da safiya ranki ya dade"
Bai jira amsarta ba ya mi?e zai fice tayi saurin Wago kai tace
"Sameer...!"
Chak ya tsaya yana jin sunan har cikin ranshi sai dai yana tuna ranar da ta mishi umarnin cewa ya manta da ya taSa amsa wannan sunan, ya manta ya taSa sanin su a rayuwarshi.

"Kaico na! Kaicon uwar da Wan ta ba zai iya Waga idanu ya kalleta ba saboda wani tabo da ta samar masa mai wuyar warkewa, Don girman Allah ka dawo ka zauna ka saurare ni, Mai martaba ka yi min alfarmar tsayuwa ka ji uzuri na idan kai kana fushi shi yana fushi wani hali kuke so in shiga? Wani hali kuke so ku riske ni a ciki kan tausayina ya darsu a ranku ku ji cewa za ku iya min uzuri? Ni fa uwa ce ni kaWai na san irin zafin Waukar ciki, rainonsa zuwa haihuwarsa da gayya ba zan salwantar da rayuwarka ba Sameer, da gayya ba zan ?untaci kaina tsawon shekarun nan ina kuka da hana kaina bacci wurin ro?on ubangiji ya baka ingantacciyar rayuwa da farin ciki ba... Don Allah ku saurareni ko da sau Waya ne"

Tausayinta ne ya rufe mai martaba Dukda haushin ta da har yanzu yake cike a cikin zuciyarshi, wlh in bai ce har tunanin sakinta yayi ba yayi ?arya kasancewarta macen da ya fara so kuma har abada yake jin sonta daban cikin matanshi bai sa yaji cewa zai iya yafe mata abinda tayi mishi ba amma a yanzu tausayinta ne ya fara rinjagayar fushin, kallon Rayyan da bai motsa ba bai kuma ya dawo ya zauna ba yayi yace

"Ciroma samu wuri ka zauna"

A dole ya zauna ko sau daya bai kalleta ba don idan ya kalleta zai iya jin zafi da raWaWin shi ya ?aru kaman yanzu yake tuna yadda ta jefar dashi aka ce zuciyar yaro babu mantuwa a daidai lokacin da yake jin daaWin rayuwarshi yake kuma da gatan shi ta zabi mayar dashi marar galihu har ma ana kallon idanunshi ana mishi zancen kila shi Win shege ne marar uba! Idanu ya runtse kukanta har ranshi yake ji amma baya jin kukan a matsayin uzuri.

"Ban san ta ina zan fara ba amma na san duk kun san cewa a wannan gida na sarauta aka haife ni amma ban tashi nan ba kasancewar mahaifiyata ta rasu ina da kananun shekaru, na koma wurin dangin mahaifiyata da zama ta yadda duk wani tuggu, makirci ko fuska biyu na gidan sarauta ban sanshi ba, i was a care free person with a pure soul ina rayuwa kaman kowacce mace ba tare da na san akwai alkawarin auren sarkin gobe a kaina ba kasancewar mahaifina Galadima kuma har yanzu gidanmu ke sarautar Galadima, ina da shekaru goma sha huWu Yaya Maudo ya turo kuyangi na musamman don su fara horar dani zaman cikin masarauta da ma abin da ya kunsa Dukda a lokacin kana da uwargida wacce itama duk jini Waya ne tunda daga Makama har Madaki sarautar gidansu ne kuma

39 / 53