Haihuwa Da Hanji Complete Hausa Novel

Author :  Halima K Mashi Category :  Adventure

Chapter   6 / 53

15K to 18K   out of 158.4K words

mai tafe da gunjin kuka mai taSa zuciyar mai saurare don kowa ya ji kukan ya san ba na wasa bane
"Ku barni na mutu! Don Allah ku bar ni na mutu ba zan iya rayuwa ba! Ku sakeni....! Ku sake ni na ce!"
Duk ta haukace kuma yawan su bai sa sun iya natsar da ita ba..

"Will you shut up and stay still?? Giyar wake kika sha ne?? Hauka kike yi ne??"
Kalaman suka fito cikin wani irin amo da ya amsa duka Wakin...




=???Gureenjoh=???

HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

*FREE BOOK*

*008*

"Karen hauka ne ya cije ki? Ko stupid lunatic brain naki hauka yake karanto miki?? Are you stupid?? Ki kashe kan naki oya take this..."

Muryarshi mai cike da fushi haWe da zafi ya cigaba da sau?a wane aradu bisa kan su ba ita kaWai ba hatta nurses da suka san shi sai da suka sha jinin jikinsu a take, wani irin shiru ne ya ratsa Wakin kan takun sawayenshi suka amsa ya isa ganganta ri?e da scapel (aska irin ta likitoci) ya dam?a mata a hannu ya fusgo Wayan da karfi har canular Winta na fita daidai jijiyar Wrist Winta ya sa yatsarshi babba.

"Nan! Nan kawai za ki katse ki mutu idan sha'awar wutan Jahannama ne yake Wibarki, ba mutuwa kike ?aunar yi kafura ki tabbata cikin azabar Allah ba? Oya yanke mana!!!"
A zaune take amma sai da tayi wani tsallen tsoro saboda tsawar da ya daka mata sai da ya kaWa 'yar hanjin ta.

"Haba Rayyan, yarinya ce don Allah ka bita a hankali mana ka ga yadda duk ka firgitata?"

A zafafe yace
"Za ta ci kashi ne salim? Muddin ba za ta ci kashi ba to tabbas babu zancen yaranta a lamarin ta sai tsagwaron iskanci da ?arancin ilimin addini... Tana tunanin da kashe kai shi ne hukunci mafi sau?i ga bawa a duk sadda ?addara ta ruro wutarta za ta samu miliyoyin mutane a raye ne?"

Ita dai bata san a wace duniyar take ba don tsabar yadda take kaWuwa bata sani ba a farke take ko a sume ya juyo da figitattun idanunsa da basu yi mata kala da na mutane ba ya zura mata
"To bari ki ji, idan ma ba ki sani ba ki sani idan ma kin sani danne sanin kika yi to gidahumar kwakwalwarki ta tuna kuma ta yi hadda wutar Allah ya fi gaban wasa, kar ki zaci wannan wuta da kuke girki da shi duk zafi da raWaWin na wannan duniyar, duk irin hatsarinshi da in ya Wan taSa ki za ki ihu sai da aka wanke shi sau dubu saba'in kan aka jefo mana"

Kanshi ya dafa yana wani jan tsaki mai tsawo saboda rabon da yayi magana haka ya manta, amma dole ya ?arasa don zuciyarshi a tunzure take ji yake kaman ya faffalla mata maruka wa ta fi shiga cikin damuwa da zata kashe kanta?
"Tabbas duk wanda yana musulmi ya kashe kanshi da gangan ya fita daga musulunci kuma zai mutu ya kuma tashi ranar gobe a kafiri... ?arbar kaddara mai kyau ko marar kyau na Waya daga biyar Win cikacikan musulunci. Ki yi gaggawar tuba domin a yanzu haka kin nunawa ubangiji ba ki da cikakkiyar imani ki kuma gode Allah we were there on time Nonsense& !

Wani irin rawa da jikinta yake ya sa tuni askar ya zame ya faWi ?asa yana ba da sautin kwankwataraaaan, yadda kalamanshi suke fita a hautsine cike da zafi da Waci mai tarin zallar gaskiya haka su ke hautsina mata 'yar hanji suna kaWa hantarta kuma suna shiganta ba da wasa ba.

Tun da idanunta suka sau?a cikin nashi a karon farko ta yi saurin sadda nata ?asa don ba za ta iya ko da gangancin jurar ganin cikinsu ba, ganin tana shirin zubewa a sume ya sa salim damke hannun Rayyan da har kaman zai rufeta da duka at any moment ya ce
"Calm down please dude"
Ya maimaita kusan sau uku don ya san haya?in kan rayyan ba kowa ne ke iyawa dashi ba, hatta shi karan kanshi wani lokacin shakkar shi yake saboda wani irin kwarjini da Allah ya zuba masa na ban mamaki, bare wannan yarinya da rubdugun rayuwa yayi mata ?atutu.

"Sister ku taimaka mata ko da allurar bacci ne samu ta huta ta kuma samu natsuwa please"
Salim Win yayi directing kalaman to nurses Win, da sauri suka shiga ?o?arin aiwatarwa don babu wadda bai san Zafin kan Surgeon General Ryan Moh'd Khamis ba, a lokacin da suka ro?i ta kwanta ko uhmm bata yi ba ta mi?e flat zuciyarta har a lokacin tana jin shi a tsaye kyamm tsabar tsoro.

Jan Rayyan da ke tsaye ya zubawa gini idanu yayi suka fice, haWadWen office ne mai cike da ?awa tamkar ba asibiti ba suka shiga, fasalta kyau da tsaruwar office Win bata lokaci ne sai wani masifaffen ?amshi yake fitarwa tare da sanyin Ac mai ratsa jiki. A doguwar kujera Brown mai cin mutum uku salim ya mishi masauki, ya nufi chan dungu wurin wani tsararren frigde ya buWe ya Wauko mishi ruwa masu sanyi ya taho ya mi?a mishi bayan ya Salle murfin ba tare da yayi magana ba ya karSa kaman faWa ya kafa kai, sai da ya shanye tasss kan yayi wurgi da goran

"I need some space Salim"
Maganan ya fito daga chan ?asan ma?ogoronshi in ba ma salim Win hankalinshi na kanshi ba ba zai taSa cewa shine yayi maganan ba, dama kuma ya san za'a yi hakan dole ya fice ya barshi nan yana zamewa kwance cikin kujerar Dukda tsawon shi ya zartawa kujeran nesa ba kusa ba.

Salim na fita Wakin ya koma ya janyo kujera ya zauna tare da tsura mata idanu, duk da ba zai ?ira ta kyakyawa ajin farko ba sai dai tana da nata qualities Win na daban da ba kowa ke da shi ba kuma da matu?ar wuya a same su wurin wata macen, ba?a ce amma ba?in mai haske tana da doguwar tsiririn fuska da dogon hanci duk da idanunta ya musu kallo ne na tausayi don a rine suke a kuma firgice zai iya ?iransu manya kuma farare, girarta kaman ita ta zana yanayin tsawon gashin idanunta da ma masu she?i irin na ba?aken Fulani dake kwance lublub bisa goshinta za su tabbatar maka da cewa tana da tarin suman kai, bakinta kalar peach da ya ?ara haskaka kalar skin Winta ya amshi fuskartata.

Ta yi mishi yarinya kwarai da tunanin kisan kai, kuma ya tabbatar duk abin da zai saka mutum tunanin kashe kan shi ba ?arami ba, ba zai ce ga iya adadin lokutan da ya Wauka yana gwamutsa biyar da goma ba a kan matsalar yarinyar sai motsin ta ya ji, da Wan hanzari ya mayar da hankalinshi kanta don dama tuntuni kallonshi na a gareta.

"Sannu 'yanmata kin farka?"
Tsura mishi idanu ta yi tana tariyo abin da ya faru a Wazu da sauri ta shiga dube dube tana jin gudun zuciyarta na wani irin ?aruwa ganin firgici a idanunta ya sa ya mi?e ya isa gangarta yana furta
"Natsu 'yanmata dodon Wazu ba ya nan, da ma matu?ar wuya ki sake ganinshi a gangarki."

Numfashi mai nauyi ta sau?e duk da tarin tsoron da take ciki hakan bai hana kalamanshi na Wazu na sake bijiro mata ba, wani irin sanyin jiki da tsoron Allah na lulluSeta a take ta fara tuba hawayenta na Sallewa take furta
"Allah na tuba ya Allah! Wallahi na yi nadama Allah na san kana sane dani da kuma halin da nake ciki ya Allah ka sassauta min, Allah ka ba ni ikon ?arbar kaddara ta a yadda ta zo min Allah ka yafe min..."
Sossai take kuka har tana shiWewa, bai hana ta ba ya barta tayi kukan sossai har tana ajiyar zuciya kan ya Wauki ruwa ya mi?a mata, sai da ta jima tana kallon hannun nashi kan ta sanya hannu ta karSa ta sha sossai kan ta sau?ar tare da gintsewa cikin hannunta tana sau?e numfashi ta sake ?ura wa bango idanu.

"Ya Sunanki?"
Ta ji tambayar ya zo mata, kallonshi ta yi yana da tausayi haka yana da sanyin hali duk da khakin sojojin da ta ganshi da shi ba irin wanchan Wayan ba da ko a mafarki bata fata ta sake ganinshi don kila sai ta sume.

"Afeefah"
Ta furta a hankali
"kina da suna mai daaWi Afeefah".
Shiru ta yi.
"Ko za ki kwanta ki huta? Ko in samo miki abin da za ki ci?"
Nan ma shiru tayi, a hankali kuma ko me ta tuna tace
"Eh"
"Eh wa wanne kenan? Kwanciya ko abinci?"
Da wasa yayi maganan hakan ya sa ta sake kallonshi kan tace
"kwanciya"
"duk biyu dai Afeefah, yanzu kwanta ki na hutawa ni kuma zan je in samo miki abincin kin ga ina dawowa ke kuma kin gama hutawa sai cin abinci ko?"
Ta gyaWa kai
"yauwa Afeefah"
Kwanciya tayi shi kuma ya fice.

Ya fi awa Waya da fita kan ya dawo, ya samu wani baccin ya Wauke ta yadda kuma fuskanta da idanunta suka sake suntuma suka tabbatar mishi da ta sake wani kukan fiye ma da na Wazu.
Sossai ta bashi tausayi adu'ar samun sau?i a ko ma menene dake damunta ya yi mata kan ya ajiye babbar ledan da ke hannunshi ya fice, office na Ryan ya koma sai dai ya samu a rufe girgiza kai yayi kan ya juya ya koma nurses station inda ya roki a duba mishi Drn da Ryan yayi referring Winta to don ya san ko mutuwa za tayi ba zai sake duba ta ba. Ganin Dr Sulaiman ya sa ya nufi office Win nashi.

Dukda Captain Saleem zallar soja ne na ?asa wato land army sai dai tarensu da Ryan ya sa kusan duk wadda ya san Surgeon General Ryan Moh'd Khamis ya san Salim, Salim shi ne ?wallin abokin Ryan don shi kaWai ke iya tolerating murWaWWiyar halinshi da zafin Ranshi sam Ryan ba shi da hayaniya kuma ba ya shiri da mai hayaniya, ba ya dogon magana kuma ko da ido yana so idan yayi magana ka fahimce shi bare kuma in ya buWe baki ya furta ko za ka mutu ba zai maimaita ba, yana da saurin fushi kullum a hasale yake ga ko in kula a koma menene matukar ba shi ya so yin abu ba babu mai mishi dole, sarauta da ?asaitarshi wane sarki don har wasu kan tambayi ko shi Win jinin sarauta ne?

A kofan office Win yayi knocking aka bashi izinin shiga ya sanya kai, Dr Sulaiman ya mi?e ya bashi hannu suka gaisa kan ya zauna yana dubanshi yace
"Dr. Ka san yanayin aikin namu tafiya ce ta kama ni babu zato, zan tafi Kano kuma zan kwana biyu ban san ko za ka iya sallamar ta a yau ba samu in mayar da ita kar in tafi kuma aiki ya ri?eni in kasa dawowa da wuri".

Dr Sulaiman ya buWe file Winta ya sake dubawa sossai kan ya Wago yana kallon Salim ya shiga cewa
"A gaskiya cap. Sallama ba zai yiwu yau ba yarinyar jininta yayi ?asa sossai matu?a kuma ka san hatsarin hakan, ga damuwa dake dukar zuciyarta shiyasa take ta complain ciwon kai da kirjin dole tana bu?atar kulawar likita atleast na kwana uku zuwa huWu".
Ajiyar zuciya salim ya saki.
"Dr Sulaiman ko za ka taimakeni don Allah ka kula da ita har na dawo?"
Murmushi Dr Sulaiman yayi
"Kar ka samu matsala In shaa Allah zan kula muku da ita, akwai wata tsohuwa dake mana aiki gida zan Wauko ta ta zauna muku da ita har ku dawo"
Godiya sossai salim ya mishi kan ya fice.

Ko da ya koma Wakin ya samu ta farka abinci ya sa ta ci yana Wan janta da wasa yana mata hira har ta ce mishi ya isheta bayani yayi mata a kan bayan Magrib zai bar garin akwai mai zuwa ta zauna da ita har ya dawo in shaa Allah yana fata kan ya dawo ya samu ta yi sau?i samu ya mayar da ita gida Fatan hakan ba zai haifar mata da matsala ba?
Ta amsa da "uhmm" a ranta take raya a yanzu ko Sata ta yi Sat a duniya babu mai neman ta bare ya damu da wanzuwar ta ko akasin hakan, yanzu haka aka tambayeta ina za'a kaita bata sani ba don ko giyar wake ta sha ba za ta tunkari wurin uncle ba dolenta dai shi ne kawu, Nan ma kuma bata san abin da za ta iya riska ba Shikenan ta koma Square Zero?
Wasu irin zafafan hawaye ne suka shiga zubo mata.

"Afeefah!"



=???Gureenjoh=???

HAIHUWA DA HANJI
(A True life story)

Fatima Muhammad Gurin
(Gureenjoh)

Wattpad-Gureenjo6763
Arewabooks-Gureenjoh

*FREE BOOK*

*009*

Captain Salim ya ?ira sunan nata cikin tausasawa, ta Waga ido ta kalleshi.

"Akwai wani matsala ne?"
Ta girgiza kai.
"Na gode sossai Allah ya saka maka da mafificin alkhairi"
Yayi mata murmushi, bai bar Wakin ba sai ga dattijuwar matar kuWi masu kauri ya fitar ya ba dattijuwar saboda sayan abinci ya nuna mata kaya kala biyu dogayen riguna da ya siyo da man shafawa, macline, brush, turare da soson wanka ya ro?e ta da ta kula da ita don Allah har ya dawo, kaman kar ya tafi haka ya fice a Wakin domin haka kawai ya tsinci kanshi cikin tsantsar tausayinta da har yana so ya yiwa zuciyarshi yawa.

Baaba jummai macece mai faram-faram da saurin sabo duk yadda Afeefah ta yi shiru sai ta saka ta magana har da murmushi, tana kula da ita sossai sossai, bata ma?e kuWin da salim ya bata ba ta kan sayo musu kayan daaWi ta bajo musu tana cewa
"Ke 'yannan sa hannu maza ki ga mu ci kin ga ko mutuwa muka yi yanzu za'a Wauke mu da nishi saboda nauyin mu ina amfanin kana da shi baka ci ba? Maza-maza sa hannu"

Dole Afeefah take murmushi kuma ta biye wa Baaba ta ci sossai dare idan an gama duba Afeefar kan su kwanta bacci za ta shiga ba ta labarin aurenta da ma rayuwar da tayi har ma da irin kishin su na da chan baya da kissa kala kala da kan kashe Afeefah da dariya, kan kwana biyu ya zagayo har ta fara manta tarin damuwarta, duk Sallar ta kuwa bata taSa mance iyayenta da Aunty zee ba ta kan kai wa Allah kukanta musamman cikin dare akan ya gafarta musu yayi musu rahama (Tana ro?on duk wanda ya zo across wannan littafi ya nema musu rahama domin Allah=?O?)

Kaman yau Dukda safiya ce bayan sun gama karyawa da doya da miya haWe da shayi da duk a bakin asibitin Baaba ke sayo musu ta dubi Afeefar da ta Wan yi shiru tana tunani tsoron ta Waya dawowar salim ina za tace ya kaita? Ina ta nufa? Ya zata yi?

"Wai 'yannan kin kuwa san abin da ke ?ara ba ni mamaki ma a wannan zamanin?"
Afeefah ta girgiza kai tana Wan kakaro murmushi don ta san zancen baaba bai taSa wuce kan taSarSarewar tarbiya a wannan zamani ba.
"Mu a lokacin mu ina mace ta isa ta ?ira ko mai irin sunan mijinta? Kai ko bayan ya mutu ko kun rabu mu kam ba ma iya kiran sunan ko da kuwa da kuskure amma ki ji mace yanzu gatsal tana cewa Ummaruuu a gaban yara ma da iyayenshi ko nata kai ko a gyalen su"
Dariya Afeefah ke yi sossai tace
"Yanzu Baaba ko sakin ki yayi ba za ki iya ?iran suna mai irin nashi ba?"
"Eh mana! Ai da kunya 'yannan"
"Tabb baaba ba dai irin sakin wannan zamani ba, komai fa akwai silar chanzuwarshi Baaba bai wuci mazan ma na da na yanzu ba Waya ba ne shiyasa ake ganin bambanci"
"za dai ki kare su ni dai na faWa miki ki kiyaye, kin ga maza suna matu?ar son a ba su girma, idan za ki ba namiji girma toh tabbas mutuncin ki ma zai zama daban ne a idanunshi ko da kuwa ya auri wata ne"
Tana murmushi sossai tana tuna wato gidan kawu Labaran ban da rashin tarbiya har da tarin jahilci da suke dashi, daga mu'amalar iyayen har ta 'ya'yan gashinan dai gashi nan yo idan ta ciwo shi ai sai dai a ji suna dambe da mata...

Fuskanta Wauke da murmushi tana sake jinjina rayuwar da don baaba jummai na sake bata labarin yadda ma?ota sai ya hukunta Wanka baka sani ba idan ma ka sani ka je har gida ka mishi godiya amma yaran yanzu ko kanwarka ce ka mari yaronta gabanta sai ta maka Allah ya isa a gaban yaro to me yasa ba za'a lalace ba? Haka batun ?arfafa zumunci Meyasa zumunci ba zai yi ?arancin ba yara suna 'yan pendo da Wan kawu amma idan wanchan sun fi kuWi sai ka ga yana nuna bai san yayyunshi cousins ba ko ya fi karfinsu uwa kuma ta kasa kwaSa saboda tana ganin hakan ce daidai daga mutum mai kuWi ne level nashi ya fi karfin talaka ko da kuwa cikin umma Waya ne.

Turo kofan yayi bakinshi Wauke da sallama a kanta idanunshi suka soma sau?a, ajiyar zuciya ne ya kufce mishi ba tare da ya san dalili ba murmushi na yalwatuwa a fuskar tashi ganin ko da suka hada idanu murmushin bai kau daga kan fuskanta ba, fara'a na yi mata kyau ya ayyana hakan a ranshi maganan Baaba ne ya yanke mishi tunani

"Bawan Allah sannu da dawowa, lale maraba"
Ya saki murmushi ya Wan rankwafa ya shiga gaisheta ta amsa cike da kulawa tana tambayar shi aikin da sanya mishi albarka, Afeefah ya duba da ta Wan du?ar da kai tana kallon yatsun hannunta
"Na shigo kuna ta raha me yayi miki daaWi haka Afeefah?"
Ta Wago tana murmushi
"Ni da Baaba ne, barka da dawowa"
Yana zama gefen gadon tuni Wakin ya cike da sassanyar kamshin shi ya ce
"Yauwa ya jikin? Hope kin samu lafiya?"
Ta gyaWa kai tana dorawa da
"Alhamdulillah na gode"
Da Baaba suka cigaba da hira akan jikin nata ita dai sai murmushi bata magana har Dr. Sulaiman ya shigo, sai

6 / 53