Sihirin 1 Complete Hausa Novel

Author :  Indo Category :  Love

Chapter   8 / 16

21K to 24K   out of 47.8K words

ya sameshi kema ze shafeki"

Bata jira Abunda Minoji zata faWa ba ta tashi tafice.
Minoji kam taSe baki tayi tace, "ga ni ga ki ai duk abunda zaki iya sai kiyi banson ?aramta dama ai bance ina sonshi ba bare kuce yaudarar sa nayi"

Ita kaWai tai ta mita har lokacin da ?awayen nata suka dawo sannan suka cigaba da ?ar hirar su.

Da daddare jirgin amarya ya tashi zuwa gidanta.
Ayiya da YaaYa duk suna Waki sun ?ule sai Yayyi da Yarinya da wata ?awar Yayyi da ma?ociyar su ne kawai a tsakar gida sune suka tari ?an kai amarya cikin mutuntawa, ko Wakinta ba'a kaita ba Hajiya Umma tace sai an kaita ta gaida Ayiya tukunna.

Yayyi ce tayi musu jagora kanta tsaye dan duk abunda ze zamo na fitina bata son shi kamar yadda YaaYa da Ayiyan suke nemansa ido rufe. sai da sukai ta ?wala sallama sannan ta amsa cike da rashin kulawa.

Yayyi tace, "ku shigo kawai ga shimfiWa"

?arasawa sukai aka zaunar da amarya sannan suma suka zauna, Hajiya Umma tace, "ina wunin mu?"

Ayiya ta amsa a ciki ciki ba tareda ta kallesu ba.
Hajiya Umma da Mami sukai kallon kallo kafin Mami tace, "to mudai amana muka kawo yarinya ce ?arama wadda nasan kin kusa yin jika da ita dan haka idan tayi kuskure fisabilillahi kiyi mata gyara ki gyara mata kuskurenta"

Sai lokacin Hajiya Umma ta samu bakin magana ta Wora da cewa, "yauwa wannan haka yake Allah ya bada ikon ri?ewa, amin, zamu ?arasa da ita cikin Wakinta, dan Allah aita ha?uri kunsan lamarin yaro sai da ha?uri"


Ayiya ta jinjina kai gami da cewa, "Amin Allah ya sanya alkairi ya bada sa'a"

Suka amsa sannan suka tashi har sauri saurin fita suke, suna kaita Wakinta suka gama abunda zasuyi suka koma gida dan kuwa sun lura Ayiya neman nayi take kuma su bazasu so ayita dasu ba shiyasa sukai komai cikin hanzari.

ko ?an matan amarya babu wadda aka bari gidan ya rage sai su kaWai.

Minoji kam jin babu danshi danshi danginta a kusa da ita yasa zuciyarta ta?ara karaya nanfa ta sake Salle sogar kuka.


Yarinya ce ta shigo ta zauna kan sofa tana kallon Minoji cikin tausayawa saboda jin tana kuka cikin sanyi tace, "Aunty ki dena kuka kinji?"

jin muryar Yarinya ne ya katse mata tunanin da take a cikin kukan ta Wan saurara tana nazarin maganar.
Yarinya kuwa da yake irin yaran nan ne masu wayo sosai cikin sigar rarrashi tace, "yanzu Yaaye ze dawo ba nisa yayi ba kuma ze siyo miki alewa kiyi shiru kinji? dani da Yayyi muna sonki zamu dinga tayaki surutu"

sassanyan murmushi Minoji ta saki lokaci Waya taji Yarinya ta shiga ranta har ?ololuwa share ?wallar tayi ta murje idanunta sannan ta kalleta fuskarta Wauke da murmushi tace, "na dena to amma indai bakwa tayani hira kullum zanyi kuka"


Da sauri tace, "aa zamu dinga baki labari"

Minoji tace, "to yanzu ma bani labarin"

Dariya tayi tareda cewa, "kai? to ai yanzu Yayyi bata nan bari naje na kirawo ta"

ta ?arasa maganar tana ?o?arin tashi.
Da sauri Minoji ta dakatar da ita da cewa, "aa barta karki wahalar da ita"


Komawa tayi ta zauna, daidai lokacin Yaaye yayi sallama a tsakar gidan tsalle ta doka ta falle da gudu tayi hanyar fita tana cewa, "ga Yaaye ga Yaaye"

Minoji ta rakata da ido har ta Sacewa ganinta sannan ta murmusa gami da cewa, "sai kace wadda aka zabura"

Sai da yaje ya gaida Ayiya sannan ya nufi Wakin sallama yayi ta amsa cikin fara'a. ajiye ledar hannunsa yayi cike da farin ciki ya ?arasa kusada ita ya zauna cikin tattausar murya yace, "Amarya kinsha ?amshi sannu da hutawa rangida"

Lallausan murmushi ta sakar masa gami da cewa, "sannu da dawowa ina fatan dai kana lafiya"

yace, "ina lafiya lau Matata kinsha hira a gurin Yarinya ko? naga daga nan ta fita, kimin afuwa fa na makara banzo da wuri ba"

?asa tayi da kai tana wasa da ?an yatsunta murya ?asa ?asa tace, "Yarinya nikam na samu ?a dama inason yara sosai"


Yace, "nako sani tinda dasu nafara ganin ki sune ma suka gayamin sunan ki"

?ar dariya tayi ba tareda tayi magana ba.
Daga haka kuma tayi gim da bakinta ko uffan ta?i cewa duk da irin ?o?arin da yake wajen ganin ya sata magana.

Da yaga ta shiga halwar miskilancin nata sai ya tashi ya cire babbar rigarsa ya ajiye ya kalle ta cike da zallar ?auna da kulawa yace, "Mino kizo muyi alwala mu gabatar da sallah muyi godiya ga Allah"

Kyakkyawan murmushi ta saki gami da mi?o masa hannunta, tafin hannunsa ya saka cikin nata sannan ta tashi yana gaba tana biye dashi.

Bayan sun Wauro alwala suka gabatar da sallah raka'a biyu da addu'o'i kamar yadda addinin muslinci ya tanada.
Ledar da ya shigo da ita ya janyo yafara buWewa tayi saurin dakatar dashi ta hanyar tashi tana tangaWi ta haye kan gado tana cewa, "kayi ha?uri bazan iya cin komai ba yanzu, bacci nakeji sosai jikina duk ya mutu"


Bayason takura mata dan haka ya mayar ya ajiye shima ya tashi yana cewa, "baccin tin yanzu?"


Tace, "eh wallahi amma dan Allah karka ?ara magana ko me ka ga nayi kayi shiru abunka"


Da mamaki yace "to? izzar jalla karnayi magana? amma dai zan iya kwanciya akan gadon ko?"

Dariya tayi wadda bata fita sosai sai dai alamunta kawai cikin sanyin murya tace, "ka kwanta mana"


yace, "to nagode"

har ta kwanta kamar Tayi baccin sai kace gaske bayan ?an mintina kuma sai tafara malelekuwa tana mutsu mutsu sai kace tsutsa, yana son yin magana amma yana gudun karya sharaWin da tayi dan haka ya ja bakinsa yayi masa mukulli.






*INDO CE..*
[8/1, 5:27 PM] Maryam Muhammad: *=???=???=???SIHIRIN K'AUNA=???=???=???*


=???Shafi Na 16=???



Na INDO CE..


*('ELEGANT ONLINE WRITER'S('*



(Kyauta ne=??)




Bismillahirrahmanirrahim
(3E 'DDG 'D1 -EF 'D1 -JE




(Fatan Alkairi gareku mabiyan littafina, kuyi ha?uri yau na makara=?? typing Win DOGON YARO ne ya tsareni wallahi=?? nafiso na fitar dasu a tare=??>?#?>?#?)




har na Wan wani lokaci sannan yace, "kuma da kin kawo shawara me kyau ai kuwa gobe sammako zanyi in Allah ya yarda"

Ta amsa da "Allah ya yarda"

Washe gari yana fita be zame ko ina ba sai gidan Yayan mahaifinsa, sai da ya gabatar da kansa wa me gadin sannan yace ze sanar musu, bayan Wa lokaci ya dawo yace ka shigo daga ciki"

Sai da ya sauke ajiyar zuciya kafin ya sa ?afa a cikin gidan cike da fargaba da zullumi gefe guda kuwa yana fatan samun karSuwa a gurinsa.

Ya daWe yana jira sannan Alhaji ?ahiru ya fito cikin shirinsa na fita, be nemi inda Yaaye yake ba kai tsaye gun motarsa ya nufa, har direba ya buWe masa murfin motar ze shiga Yaaye yayi saurin ?arasawa wajen ya Dur?usa har ?asa ya gaisheshi.


Amsawa yayi a yatsine kafin yace, "amma meyesa kazo a irin wannan lokacin? yanzu fita zanyi kuma"

Da sauri Yaaye yace, "dan Allah Abba kayi ha?uri yanzu abun ya taso min ne nakasa ha?uri shiyasa nazo"

Sai da ya ja lokaci sannan yace, "shikenan inajinka meke tafe da kai??"

Cikin nutsuwa yafara kora masa bayani daki daki har ya kammala zayyana masa abunda yafaru.

Alhaji ?ahiru ya nisa sannan yace, "lallai ka taro aiki babba babanka be ajiye ba be bawa wani ajiya ba amma ka tattagi aure ga nauyi akanka, toh shikenan ni banida damuwa akan matsalarka abunda ya shafeka ne koda batai maka daWi ba abunda zance anan kawai shine idan na riga na shige maka gaba har Allah yasa sukai na'am suka baka ?arnan to fa daga lokacin hannu na ya kau daga kan ku, walau kuyi zaman lafiy walau ba na lafiya ba kar a sake azo nema na kaji ko??"

Yaaye ya gyaWa kai yace, "insha Allahu Abba baza'a samu matsala ba na amince da duk sharuWan"

Alhaji ya murmusa sannan yace, "yaro me ?wazo me zuciyar zinare, tamkar mahaifinka haka kake, eh!! karkayi mamaki ?anina haka yake tamkar kai Winnan sai dai duk da ya gama wannan ?wazon nashi ga kyakkyawar zuciya ga zuciyar tamkar dutse hakan ba abunda amfana har ya amfana muku haka dai ya koma, to shikenan Allah ya ji?ansa da rahma ni yanzu zan wuce zan kuma nemi abokina zamuje mu nema maka auren wannan Wiya, Allah ya sanya alkairi"

cikin farin ciki Yaaye ya amsa da "amin Abba nagode nagode Allah ya ?ara girma Allah ya saka da alkairi"

Alhaji ?ahiru yayi dariya gami da cewa , "amin amin amin Allah ya temaka"

Yaaye yace, "Allah ya tsare"

Hannu kawai ya Wago masa lokacin har ya shiga mota.

Yau cikin farin ciki da nishaWi Yaaye ya nufi gidan su Minoji, yana zuwa ?ofar gidan yayi parking yana fitowa yafara jin saukar ruwa a jikinsa kuma gashi ba lokaci damuna ba.

Sai daga baya sannan ya lura da inda ruwan yake.

a harabar gidan, Sanye take cikin doguwar riga ta atamfa ta Waure Wan-kwalinta a ?ugu sai juyi take tana hajijiya hannun ta ri?e da tiyo Tana feshin ruwa ita da yara wanda daka gani kasan duk inda taje tazo jininta ne tushen su Waya tana yi tana dariya dogon gashin ta yayi linkif a gadon bayanta Saboda ji?ewar da yayi da alama hakan yana yi mata daWi sosai.

tsayawa yayi tsam ya zura hannayensa cikin aljihunsa ya zuba mata narkakkun idanunsa lallausan murmushi ya buwayi fuskarsa har cikin rai.

ya daWe a tsaye har ya Wauki dogon lokaci be ga alamun zata gaji ko kuma ta dena ba dan ta gajin ba dan haka ya taka zuwa ciki.

?aya daga ciki yaran ne tace, "Yami kinga wani ya shigo"

Dakatawa tayi da hajijiyar da takeyi dan ganin kowaye amma jirin hajijiyar ya hanata damar ganinsa sai duhu take gani, tafara tangal tangal tana shirin faWuwa.

Cikin zaro ido ya furta sunanta "Minoji!!!!"

Cakkk!! ta tsaya tareda rintse idonta lokaci Waya tsigar jikinta ta yarfa duk ta mimmi?e, ?an?ame jikinta tayi tareda tayi wani shan yaji "shishshshsh!!"

Mus'ab da Yaaye sukai saurin yin kanta cikin tashi hankali, da sauri ta Waga musu hannu dukansu suka dakata suna kallonta.
A daddafe ta koma jikin bango ta lafe tana ?ara rintse ido gami da cije leSenta.

Cikin sanyi da tsarguwa Yaaye yace, "kiyi ha?uri Minoji na Sata miki rai ko?"

Cikin wannan yanayin da take ta girgiza masa kai.

Mus'ab yace, "kaine Yaaye ko??"

Yace, "eh nine"

Yace, "to kayi mata shiru kawai karka ?ara magana har sai ta nemi hakan idan ba haka ba kuma zaka jika a sijin"

Da mamaki gami da firgita Yaaye yace, "Sijin ba kurkuku ba?? to meyesa??"

kafin Mus'ab yayi magana tace, "Mus'ab!!!!!"

ta kira sunansa a kausashe sai da ya Wan firgita ya zaro mata ido, har lokaci idonta a kulle yake, a hankali ta motsa kyawawan laSSanta tace, " ka bani ruwa insha"

"To" yace sannan ya koma cikin gida da gudu ya dakko mata ruwan a gora ya bata, kurSa Waya tayi ta sauke ajiyar zuciya sannan ta jefi Yaaye da Gorar.
taja numfashi ta sauke sannan ta buWe idonta a hankali shima ?asa ?asa bata Wagashi ba, bare ma iska ta shiga.
Yalwataccen murmushi ta saki sannan tace, "Yaaye! Sannu da zuwa"

sai da ya ida cewa "Alhamdulillah" sannan ya amsa da "yauwa gimbiyar mata sannu da wasa da nishaWi"

Ta murmusa gami da yimasa nuni da wata kujera tace, "zauna mana"

Zaman yayi sannan itama taja ta zauna, ya buWi baki zeyi magana ta katseshi da cewa, "naji daWin ganinka sosai, kwana biyu da banganka ba na Wanji ba daWi gashi kuma kazo dai-dai lokacin da na faWa cikin wani yanayi, sai dai fa kayi ha?uri dani Yaaye domin rayuwa tareda ni akwai ?alu bale sosai, uhm sai ka jurewa ?ilinbona dan kuwa ko wanda suka zama dole na ma, ina nufin iyaye na da ?an uwana har cewa suke ni ba mutum bace, to ya zanyi kuwa tinda da siffar mutane akayi ni kuma aka jefoni cikin mutane kaga kuwa ai nima mutum ce"

yadda take maganar cikin sanyi sai da ta bashi tausayi sosai, ya Jinjina kai sannan yace, "gaskiya ne kema Waya daga cikin mu ce ina nufin kema mutum ce kamar mu, ina fatan dai lafiya kike"

Da kai ta amsa tayi masa alamar "e"

Shiru ce ta biyo baya na wani lokaci kafin Mus'ab ya katse shirun da cewa, "Yami ko ruwa fa baki bashi ba haka ake tarbar ba?in??"

Murmushi tayi tareda yin ?asa da kai sannan tace, "na manta ne kawo masa "


Yaaye yace, "ai bana ma jin ?ishi"

Tace, "ai kuwa sai ka sha indai ya kawo"

ya murmusa tareda cewa, "shikenan zan sha, dama nazo ne na sanar miki na nemi yayan baba na kuma yace zasu zo shine farin ciki yasa nakasa ha?ura sai da na gaya miki"

Murmushi tayi gami da lumshe ido ta jinjina kai tace, "masha Allah hakan yayi min sosai kaga yanzu na samu ?warin guiwar nunawa duniya cewa kaine gwani na, to yanzu meye ya rage kana ta shirye shirye dai ko??"

Yace, "ina ?o?artawa babu wata matsala"

Tace, "ohh da kyau jajircewar ka tana burgeni sosai kai mutum ne me zarra ya aikin ka kuma? komai yana tafiya daidai?? nasan ma a satin nan ka rasa wasu ranakun hakan baze zama matsala tsakanin ka da me gidan ka ba kuwa?"

Yace, "eh ?warai amma kuma har yanzu banji yace komai ba amma kwatsam ze iya cewar, karki fa damu dan Allah"

Ta jinjina kai sannan tace, "yayi kyau sosai, ka cigaba da dagewa sannan idan akwai wata famuwar ka sanar dani babu amfanin ka Soye mun komai dan yanzu Wauka nake dani da kai duk abu Waya ne"

Yace, "insha Allah zan kula naji daWi sosai Allah ya saka da alkairi"

ta amsa da "amin amin"

Tashi yayi yana cewa, "zan koma kar na takura miki"

Ta murmusa itama ta mi?e sannan tace, "ka gaishe da mutan gidan ku inji ni"

Yace, "to"

Har ?ofar gida ta raka shi sai da ya tafi sannan ta koma ciki sai murna take, Ummi tace, "ke kam yau dai kanki akwai motsi"

FaWawa tayi jikinta tana murna tace, "Ummi wanda zan aura ne fa yazo kinga ma ya bani kyautar alewa"

Ummi tace, "zaki aura??"

Tace, "eh Ummi iyayensa ma zasu zo wannan me adai-dai-ta sahun da nake baki labarin sa??"

Ummi tace, "eh na gane shi ooh to Allah yayi mana mafi alkairi amma fa bazance nayi murna sosai ba dan kuwa bana son rayuwar ki ta ?untata dole sai dole Minoji ri?on ki sai wanda ya shirya, zaki iya rayuwa cikin wannan ?angin kuwa??"


Ta murmusa sannan tace, "aikin sa kai ne Ummi zan iya mana tinda ina son hakan da dai wani ne ya sani to fa banajin zan iya amma ni nasa kaina kimin fatan alkairi kawai amma ni dai shi nake so"

Ummi tace, "dama bakiji addu'a na fara yimiki ba kullum dama cikin yinta nake"

Ta shige Waki tana cewa, " yauwa Ummi na ki gayawa Baba"

Ummi ta bita da ido.


Abban yana dawowa Ummi ta sanar masa beyi tantama ko jayayya ba yace zeyi bincike akai.

Cikin kwana biyu binciken ya kammala duk abunda yake bu?ata ya samu dan haka ya amince da zance, cikin kwana na ukun kuwa ana wayar gari sai ga su Alhaji ?ahiru.
a lokacin aka sanya ranar aure wata Waya kamar yadda Alhaji ?ahiru ya bu?ata shi kuma Abba ya amince.
a take Alhaji ?ahiru ya ciri dubu talatin ya bayar dukiyar aure Abba ya karSa tareda sa musu albarka.
Da haka suka rabu cikin mutunta juna.

Da Yaaye da Minoji ba'a bambance wanda yafi farin ciki dukansu babu baya.

Har gidan su Yaaye Alhaji ?ahiru yaje yayi sallama YaaYa ta amsa, yace, "Alhaji ?ahiru ne ?anin me gidan"

Cikin mamaki Ayiya tace, "Alhaji ?ahiru??? me kuma ya kawo shi gidan"

Karaf sai a kunnensa yace, "banda Wan ku ya gayyato ni me ze kawo ni gidan ?as?anci irin haka? ko yawu bazan iya haWiya ba, ki fito muyi maganar da zamuyi nai gaba dan ba zama ne ya kawo ni ba"


da sauri Ayiya ta zura mayafin ta tayi soro dan kuwa shakkarsa takeji haka kawai.

Bayan sun gaisa yace, "to Wanki ne dai ya Wakko maganar aure ni kuma nayi ruwa nayi tsaki a matsayina na yayan mahaifinsa mune da Wa kuma mun

8 / 16