Sihirin 1 Complete Hausa Novel

Author :  Indo Category :  Love

Chapter   3 / 16

6K to 9K   out of 47.8K words

sai yaji ba?in ciki idan yaga tana kama hannun Boss haka kawai ba tareda dalili ba.

Sai a lokacin ya samu ?afar tafiya gida da karsashin sa.

ganinsa salo salo yasa Ya-ya saurin jefo masa tambayar "lafiya kuwa??"

cikin yanayinsa na sanyi sanyi yace, "lafiya lau, su Yarinya sunyi bacci ne?"

Ya-ya tace, "sunyi bacci harma Yayyi, nima kai nake jira na kwanta dan yau a gajiye nake, kuma bazan iya baccin ba idan banga ka dawo ba"

?an murmusawa yayi sannan yace, "yayi kyau yanzu ai sai aje a kwanta ko??, Ayiya ma naga gyangyaWi take abunta, ku kwantar da hankalin ku Lafiya ?alau nake"

ajiyar zuciya Yaa-ya ta sauke, Ayiya da yanzu ta motsa daga gyagyaWin nata tayi saurin cewa, "To Wannan, Allah yayi maka albarka bari muje mu kwanta tinda ka dawo lafiya ai fita tayi riba, Alhamdulillahi Allah ya dafa maka"

Ya amsa da "amin" sannan yatashi, har yaje ?ofa Yaa-ya tace, " dan Allah ka dinga yin bacci sosai Yaa-ye kar ka tsaya tunane tunane kaga da wuri kake fita"

Da kyar yayi ta maza ya gyaWa mata kai maganin kar yayi gaba bece mata uffan ba,
Kasancewar gidan nasu babu wuta yasa Wakin nasa yayi duhu dan haka ya lalubo kwaruSar wayarsa keypad ya kunna fitilarta sannan ya shiga Wakin, sai da ya Wan gyaggyara Wakin ya karkaWe shimfiWarsa sannan ya kwanta nan fa abokin nasa Tunani yace, "salamu'alaikum"

tunani barkatai daban daban ne suke kunno masa kai, gefe guda tunanin irin mazantakar Minoji yake da har take iya bugar ?irjin namijin da da an ?yaleshi da shi kansa dukansa zeyi bare ita wai har tanayi masa tsawa lallai kai tsaye za'a iya kiranta jarumar mata, gefe kuwa tunanin shine WACECE?? har yanzu bashi da tabbacin cewa mutumce kamar kowa dan shi da kansa yaga banbanci harda banbance banbance, wani gefen kuwa begenta ne yake masa sukuwa, ji yake idan da ze samu dama da ya kasance tareda ita har zuwa lokacin da ze dena numfashi da kowane motsawar lokaci jinta yake tana ?ara shiga cikin ransa ta gama mamaye jininsa, Zuciyarsa kuwa ba wani fili gaba Waya tagama mamayeta,
gefe guda kuma Yana mamakin yadda akai suka bashi kuWi har suka bashi ha?uri.

a wani gefen kuwa tunanin yadda ze kwasota shida me gidansa wanda yabashi adai-daitar yakeyi dan yasan bashida sau?i baya son wasa baya Waukar raini.

Haka Yaaye ya kwana da tunani kala kala tareda sa ran fitar wuri dan neman me gyara gami da yiwa kansa fatan alkairi da samun nasara.


koda ya samu ganawa da me gyara ya gaya masa bazata samu yau ba dan sai anyi mata babban gyara dan haka ya koma dandalinsu yayi zaune da yake yawancin abokan nasa anan ne suke sana'arsu wasu kuma masu adai-daita ne idan sukaje suka dawo hutawa da cin abinci sai su tare a wajen.

da misalin ?arfe 4:20pm suna nan zaune suna hira suka ga ?an mata akansu tsaibe tsaibe sunkai su biyar ko wacce tana jin kanta, basuyi wani mamaki ba domin kuwa Isah sana'ar sa a wajen caji da siyarda igiyar caji da covern waya da sauransu harda turi yakewa mutane hakan yasa mata da mazan ma duk suna zuwa shiyasa abun beyi masa Sautata ba cikin sakin fuska yace, "me za'a baku?"

?aya daga cikinsu tace, "au tambaya ma kake?? mu ba abu zamu siya ba karya ?ashi mukazo yi"

a matsayin wasa Isah ya Wauki abun dan haka yace, "to shikenan marabanku ko a kawo muku ruwan sanyi kwafi jin daWin aikin ku"

Waya tace, "ba bu?ata ka ri?e abunka"

Sagiru da tin Wazu yake binsu da ido yakasa magana sai yanzu yace, "nifa nakasa fahimta meke faruwa ne?"

buWa tsakiyarsu sukayi sai ga wata budurwar ta bayyana sai taunar cingam take tana wani ?yall-?yall da ido sai a lokacin Isah ya firgita dan kuwa ya gane Mabruka sarai itace budurwar da yake so kuma yake ta bibiyarta sai dai ta?i saurarar sa ?irjinsa ne yafara dukan Wari da sittin.

Cikin kwarkwasa ta ?araso ta tsaya tana kallonsa, cike da ruWani yace, "Mabruka lafiya kuwa??"

kai tsaye ta bashi amsa da cewa, "shugaba ce take son ganin ka"

Duk da besan ko wacece ba sai da ya?ara jin buguwar zuciyarsa ya ?aru, cikin inda inda yace, "wa,, wacece?"

Mabrukha ta zame tayi gefe a take shugabar tasu ta bayyana a tsakiyar su, tasha wata shegiyar duguwar riga ta shadda tasha dutsina tin daga sama har ?asa, babu wata kwalliya a fuskarta da alamu ma ko hoda bata shafa ba sai tsabar halittar ta,,, ?an ?ananun idanun nan nata a ?asa fuskarta babu alamun wasa, cikin wani taku irin na wahainiya ta ?arasa wajen da Isah yake tsaye yana zazzare ido, sai da tayi masa Lallausan shu'umin murmushin nata kafin tace, "kaine Isah ko??"

kai kawai ya iya gyaWa mata dan kuwa tayi masa bala'in kwarjini duk da bata bari sun haWa ido ba sai dai ta kalleshi harr harr kuma cikin sauri zatayi gefe da idon amma hakan be hanata cika masa ido ba.

yanzu ma saida ta murmusa duk da murmushin nata iya kan bakinta ne zuwa gefensa amma hakan be hanashi bala'in yimata kyau da kuma Waukar hankalin mutum ba, kallon Mabruka tayi tace, "wannan ne?"

Mabruka tace, "shine, dan Allah ?AR MAI kiyi masa rashin mutumci gaba Waya ya takurawa rayuwa ta"

lumshe ido tayi ta buWe su kafin tace, "me kike so ayi masa"

Mabrukha tace, "kyakkyawan kashedi kar na?ara ganinsa a cikin sabgata kuma rashin mutunci nakeso ayi masa, a nuna masa nayi masa nisa"

?an nisawa tayi kafin ta kalli gefen Isah, cikin kiWima ya buWi baki zeyi magana ta Waga masa hannu.

Cikin wani irin manyance da nuna isa tace, "kaji abunda Mabruka tace tanaso ayi maka rashin mutunci sai dai ni kuma bata tsaya taji hukuncin da na yanke ba, yanzu zaku iya nutsuwa ku saurara.

?an gyara tsayuwarta tayi kafin tace,,,,




(Daga taku Marubuciyar SIRRIN ?ETA.
A JINI ?AYA.
TAJMAHAAL Paid book
IB ?AN WANKA.
tareda SIHIRIN ?AUNA....)




*INDO CE..*
[18/05, 11:20 a.m.]
[8/1, 5:27 PM] Maryam Muhammad: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/C8LQPha96zwJHwEWXkZ9aG


*=???=???=???SIHIRIN K'AUNA=???=???=???*


=???Shafi Na 8=???



Na INDO CE..


*('ELEGANT ONLINE WRITER'S('*



(Kyauta ne=??)




Bismillahirrahmanirrahim
(3E 'DDG 'D1 -EF 'D1 -JE





Tace, "Isah kake kowa?? Meyesa kake son ?awata?? sannan ka takura mata, Lokacin da ka tashi son nata baka tambayi kanka ko batason takura ba??"

?asa yayi da kai yace, "nima bansan ya akai na kamu da sonta ba"

tace, "kana nufin dai dare Waya, To shikenan yanzu me zaka iya yi game da soyayyarta??"

sai da ya Wanyi nazari sannan yace,, "zanyi ?o?ari sosai dan ganin na sata farin ciki zanyi iya ?arfina dan kare mutuncin ta sannan duk abunda bataso zanyi ?o?arin ?aurace masa"

Tace, "da kyau da kyau, ni nan da kake gani na shugabar kare mutuncin masoya ce, banason duk wani abunda ze kawo matsala, kuma duk yadda zanyi na kare mutuncin so inayi a ?a'ida kaci zarafin So tinda ka takurawa masoyiyar ka, kasan meye hukuncin da ya dace da kai???"

Girgiza kai yayi alamar a'a ta lumshe ido sannan tace, "hukuncin ka shine ka tsugunna ka bata ha?uri sannan ka lallaSata har sai ta dena fushi,
To amma anyi maka afuwa rashin sani ne yasa kayi hakan da alamu bakasan sai an nemi izinin ?awaye na sannan ake faWawa son su ba, to yanzu abunda za'ayi shine daga yau Sai yau karka kuma takura mata, bayan haka kuma a ?a'idar kare mutuncin soyayya yana da kyau inyi maka wata tambaya idan ka shirya"

Yace, "a shirye nake" tace, "kai madallah da wannan ?warin zuciya naka da alamu kana sonta sosai, yauwa tambayar itace meyesa kake sonta? yanzu idan nace ka turo manyanka zaka turo su dan ayi maganar aurenku?? domin kuwa babu amfanin soyayyar da bazakuyi aure ba kunga ta tashi a shiririta kenan, dan haka a matsayina na me kare ha??in soyayya yana da kyau ka bani amsa"

farin ciki ne ya lulluSe Isah dan kuwa yanzu ya lura ba rashin mutuncin zatayi masa ba hasalima goyon bayansa take, har rawar jiki yake wajen buWe baki zeyi magana amma Mabruka ta katse shi da cewa, "Wannan wane irin wula?anci ne?? munyi dake zakiyi masa kashedi akan karya ?ara shiga sabga ta ya dena sona ma shine zaki dinga yimasa zancem turo magabatansa? kinga har wani farin ciki yakeyi"

Minoji tace, "kwantar da wu?ar ki mana aikinta be zo ba tukunna, wannan abu fa ba na ya?i bane, meye abun tashin hankali?? ya gani yana so ba shikenan ba, ni ?o?arina shine na gane son gaskiya ne ko na mugunta, idan da gaske yake sai mu haWa mu ai bamaso a rabu"

Ta?arasa maganar tana dariya. suma sauran ?awayen nata suka sa dariya yayin da ba?in ciki yake neman she?e Mabruka.

Minoji ta?ara da cewa, "idan na gane cewa soyayyar ?arya kake mata to sai nayi maganinka, sai nasa an kakkarya min ?asusuwan ka"

Tinda Tazo wajen idon Yaaye yake kanta, anan zaune inda yake yayi suman gan-gan, ko idonsa da kyar yake ?iftasu saboda tsabar mamaki, da sannu sannu yake saurarar kalamanta abun nasu dariya ma ya bashi ganin yadda abokinsa ya burkice da kuma yadda tazo ta goyi bayansa sai abun ya kai masa, ta gefe guda kuwa tunanin damar da yasamu yake sai dai besan ta ina ze fara ba, da wane yaren ze fara yimata magana? me ze furta mata?? irin wannan tunanin sune sukafi caja masa kai .

sai da sukazo kan wannan gaSar sannan yayi ?ar ta maza yace, "YAMINOJI?"

Tsalle tayi a tsorace ta koma bayan Mabruka tana cewa, "A'uzubillahi minashshaiWanin mutum, wannan Aljanin fa daga ina??, bawan Allah ya akai kasan sunana???""

Sai da Mabruka taga irin firgitar da Shugabar tasu tayi sannan tafara dariya, shima Yaaye abun ya bashi dariya sosai saidai mamakin kasa ganeshin da tayi yafi yawa,
Isah kuwa cikin mamaki yake kallonta yana kallon Yaaye, idan ya fahimta dai-dai itace wadda idan abokin nasa ya zauna bashida wata hira sai ta-ta.

murmushi Yaaye yayi yace, "a'a ni mutum ne mana Madam har kin manta ni??"

Girgiza kai tayi tace, "a'a rufamin asiri mana malam wane,
ni ban taSa ganinka ba ma, ni har yanzu ma ban yarda kai ba aljani bane dan kuwa nayi mamakin jin sunana a bakin ka raWau haka"

Cikin ?arfin hali Yaaye yace, "ai sunan ki ba Soyayyen suna bane akwaishi da sau?i musamman a bakin mutum irina, wata rana da yamma na taSa kaiku Gadon ?aya tareda yaranki har kikai min kyautar dubu Waya, kuma kin tuna abunda yafaru jiya?? har mukayi hatsaniya nida Yayanki??"

Kallonsa tayi sosai suna haWa ido tayi saurin kauda kai tana murmushi sannan tace, "na tuna kayi ha?uri dan Allah ta yuwu da ido kawai na kalle ka ba da idon zuci ba shiyasa nakasa ganeka, amma daga yau zan iya ganeka sai dai bama lallai mu?ara haWuwa ba"

Rasss zuciyarsa ta buga, atake yanayinsa ya canja duk da ba tabbaci tabashi akan bazasu ?ara haWuwa ba sai yaji maganar tayi masa nauyi tazo masa a bazata.

Ganin yanayinsa ya canja yasa jikinta yayi sanyi, ita a tunaninta ganeshin da batayi ba ne yasa yaga kamar wula?anci ne shiyasa taji ba daWi har cikin ranta, a sanyaye tace, "kayi ha?uri fa, Yanayin halitta ta ne a haka ba komai nake iya sakawa a raina lokaci Waya ba, ba wula?anci bane wallahi da gaske ban ganeka ba, ni yanzu zan tafi gida Allah yabaka ha?uri"

Murmushi ya ?a?alo sannan yace, "banji komai ba nasan bazaki wula?anta ni ba dan nasan ba halinki bane, nagode sosai"

Wan Murmushin tayi masa tareda juyawa tace, "na ha?ura da sulhun masoyan nan gaskiya ni yanzu gida zan gudu duk nayi sanyi"

......

Isah ne yayi masa alamar yace ze kaisu dan haka ya shiga sosa kai sai da ?yar yace, "Madam idan ba da mota kikazo ba inzo in kaiku tinda ba abunda nakeyi"

Shiru ta Wanyi kafin tace, "kuma fa ka kawo aidiya me kyau, yanzu kafin nasamu ta yankin mu ma aiki ne, yaran nan duk kuje ku nemi wata ku wuce gidan ku nima na wuce gidan mu sai mun ?ara haWuwa yau bamuyi sa'ar haWa kan masoyan nan ba amma ba komai watarana zamu haWu"

Sosai Yaaye yaji daWin samun karSuwar da yayi kai tsaye,
adai-daitar abokinsa ya ara ya janyo ta ya tsaya, shigewa tayi tayi lakurr sannan ta Wagowa ?awayen nata hannu sukayi Sallama, tsakanin ita da Mabruka kuwa sai ?ar harare harare Da murguWa baki.


bayan tafiyar tayi nisa har lokacin babu wanda ya?ara buWar baki da sunan magana, ita ba ma tashi take ba kalle kallenta kawai take yayinda shikuma duk wata nutsuwarsa take gareta, ganin batada girman kai ko Wagawa yasa ya?ara yin ?arfin hali wajen cewa, "Dabar Mata daga ina kuke ne haka, naji ana cewa za'a karya ?ashin abokina"

Tuntsirewa tayi da dariya kafin tace, "a gidan mu sukaje suka Wakko ni, ?awaye na ne na makaranta fa shikenan dan yace yana sonta take ta zuba tijara iri iri, ni kuma naji abun yayi yawa nace muje muyi masa kashedi ni kuma dama kowa yasan ni ?ar kare martabar soyayya ce, Kaga Mabruka sai harara ta take kamar ta cinye ni ta Wauka zanyiwa bawan Allah rashin Albarka"

ta?arasa maganar tana dariya.

Shima dariyar yayi dan kuwa iya yadda take dariyar ma kawai abun dariya ne, sai da ta Wan ?ara nutsuwa sannan yace, "kuma naji suna ce miki shugabar su, na zata kece shugabar Dabar"

yanzu murmushi tayi tareda lumshe ido, kafin tace, "wannan kuma Sirri ne wanda ya zauna dani ne kawai yake iya fahimtar dalilin amma nima bazan iya furtashi da baki ba, haka kawai na wayi gari naji suna kirana Sarauniyar su ko kuma ?ar Mai bansan meyesa ba"

Shiru yayi aransa yana addu'ar Allah yasa yana Waya daga cikin wanda zasu gane wannan sirrin nata.

Daga haka babu wanda ya?ara yin magana har suka isa, yau yayi sa'a har ?ofar gidan su tace ya kaita, kuWi ta cira ta mi?a masa tana cewa, "ga kuWin ka"


murmusawa yayi kafin yace, "bazan karSi kuWi ba, kyauta na kawo ki saboda mutunci yafi kuWi"

Murmusawa tayi ba musu tace, "nagode bazanyi maka abunda nima banaso ba dan haka bazance dole sai ka karSa ba, Allah ya tsare"


Ta faWa tareda juyawa ta nufi Wan madai-dai-cin gidan nasu. sai da ta ?wan?wasa aka buWe ta shige sannan yaja ya wuce, shi kaWai yake Murmushi wani farin ciki yakeji wanda lokaci Waya duk ya manta da wata damuwarsa ko kuma wani Wan uzurinsa, idan ya tuna yau ya samu yin magana ta nutsuwa da Minoji sai yaji kamar yafi ko wane namiji sa'a a duniyar nan, sai yamma ya koma gida, yau kam kowa yasan Yaaye yana farin ciki amma juyin duniya ya?i faWa musu abinda ya sashi farin ciki har hakan yafara jefa Yaa-ya a cikin kokonto, Ayiya kuwa itama farin cikin take dan kuwa farin cikin Wan nata yana matu?ar sata farin ciki.

Yaa-ya kuwa duk motsin da yayi idanunta suna kansa, ganin yadda ya sake yana hira da su Yayyi Yarinya da Ayiya hakan ya tabbatar mata da wani abunda ya tsinduma shi a cikin wannan yanayin, tambayarta anan shine MENENE WANNAN ABUN???.

Ko da wasa be lura da yanayinta na rashin kuzari ba dan ba ta ta-ta yake ba a zahiri da su Yayyi yake magana a zuciyarsa kuwa zancen Minoji kawai yake.

Bayan ya dawo daga masallaci ya wuce Wakinsa,
Yayyi ce ta Wauki abincin sa ta bi bayanshi da yake akwai ?ofa ta cikin gida, da sallama ta shiga amma shiru be amsa ba, ya buga tagumi hannu bibbiyu sai murmushi yake har ha?oransa suna bayyana kansu, jinjina kai Yayyi tayi ta ajiye masa abincin sannan ta Wan daga murya tace, "Yaayeee!! firgigit yayi yana zuba mata ido wuri wuri dan kuwa beyi tsammanin wani ze shigo a wannan lokacin ba.

Tayi dariya kafin tace, " Yaaye Kyakkyawa ce??"

Shiru yayi kamar baze magana ba sai kuma yace, "ajin farko ma kuwa, tanada sirrintaccen kyau, murmushinta akwai saukar da nishaWi, idan tayi dariya kuma sumar da mutum take, a yayinda take farin ciki mutum zaucewa yake"

Murmusawa Yayyi tayi tana cewa, "lallai Yaaya na ya faWa so"

Baki yasaki yana kallonta kafin yace, "wai me kikaji nace??"


Kwashewa tayi da dariya sannan tace, "kar dai zancen zuci kake ya fito sarari, naji kana cewa.."

Katse ta yayi da cewa, "yimin shiru na tuna, kuma idan kika sake naji zancen nan a bakin wani ko Ayiya ko Yaa-ya sai..."

da sauri ta Katse shi da cewa, "aa bazan faWa ba karma ka ?arasa wallahi bazan faWawa kowa ba, ni dai kace ina gaisheta"

TaSe baki yayi kafin yace, "tashi kibarmin Waki ko na harba ki waje"

Ficewa tayi tana dariya ?asa ?asa.

Sosai take murna da faruwar hakan domin kuwa daga ganin yadda yayan nata yake farin ciki tasan duk indda taje tazo yarinyar zata kasance haske a garesu, domin bazata iya tuna rabonda taga Yaaye yayi farin ciki irin na yau ba..




(To na Wan ?ara yawan page Win ?an ?orafi=??=??)



*INDO CE..*
[8/1, 5:27 PM] Maryam Muhammad: *=???=???=???SIHIRIN K'AUNA=???=???=???*


=???Shafi Na 9=???



Na INDO CE..


*('ELEGANT ONLINE WRITER'S('*



(Kyauta ne=??)




Bismillahirrahmanirrahim
(3E 'DDG 'D1 -EF 'D1 -JE




MEENOJI..
Tana shiga kewayen gidan ta arta da gudu ta shiga tana murna ... da ido Ummi

3 / 16