Sihirin 1 Complete Hausa Novel

Author :  Indo Category :  Love

Chapter   14 / 16

39K to 42K   out of 47.8K words

tattaunawa.

Kwance take saman gado sai malelekuwa take tana juyi sai cije gefin bakinta takeyi, Yaaye ne ya katse mata tunani da cewa, "Minoji meke faruwa ne?"

Kamar zatayi kuka tace, "Mariama ta"

Da Wan mamaki yace, "meyefaru da ita? lafiya dai ko?"

Tace, "sai neman ta nake ko amsa kirana batayi ba bare tazo idan ba sa'a ba Yarima ne ya Waure ta ko kuma ya kaita Daular Larabawa"

Yaaye yace, "to fa?? ikon Allah, shi wai Yariman nan baya rabo da neman fitina ne? kiyi ha?uri ki ?yaleshi zata dawo duk inda ya kai ta ma ze dawo da ita kuma kinsan ba lallai ya cutar da ita ba tinda ?anwarsa ce kodan mahaifiyarta ma ze raga mata"

TattaSe baki ta?arayi tana shirin rushewa da kuka tace, "ni dai ban yarda ba gara ma naje na gano ta da kaina"

Zaro ido yayi akanta tareda cewa, "me?? kije da kanki to ta ina zaki bi kenan??"

Tace, "ina ruwanka? kabarni kawai na tafi ko kazo ka rakani"

Yace, "aa dai Mino ki jira na Wan wani lokaci zata dawo babu abunda ze faru da ita da yardar Allah, idan kika tafi ni kuma ya zanyi da rashin ki? banason nesanta dake ko da sunan wasa dan Allah ki kasance tareda ni"

Jinjina kai tayi tace, "to na yarda amma zan nemi Gimbiya Malika ta gaya min"

Yace, "kinsan zaki iya yin hakan da kika tashi hankali na?"

Murmushi tayi gami da cewa, "ina ruwanka?"
Tana rufe baki yace, "na shanye idan kuma akwai ?ari to?"

Tace, "bazaka sha Win ba"

Yayi dariya tareda cewa, "ran Aljana ta ya daWe"

Murmushi kawai tayi batareda tayi magana ba.

Washegari tin wuri YaaYa ta kammala abunda zatayi suka saSe ita da Babar Fiddau sai gidan me maganin Aljanu kamar yadda Babar Fiddau ta gaya mata.

Kallo Waya za ai mata a gane kawai zallar shirka take ba wani abu ba.
Ido matar ta zazzaro a yayin da YaaYa ta kora mata jawabi.
YaaYa da tayi mamakin ganin alamar tsoro akan fuskarta tace, " meke faruwa ko baki fahimce ni bane?

hhhhhhhhh matar tayi dariya sannan tafara cewa, "?ar mulki jikar mulki ?ar gado ba haye ba da yaro yaja dake gara yaja da tsohon sa ?ar babban gida ?ar manya jikar manya gaba da baya duk kune kune sarauta kune mulki agurinku muka gani muka koya ?ar Sarki jikar sarki Wiyar zinare hasken masarauta dake ake ado fitilar gida ran gida hhhhhh"

cikin mamaki YaaYa tace, "meye kuma hakan? nakasa ganewa"

Matar ?asa da kai aranta tace, "tinda nake aiki ba'a taSa ganin gajiyawa ta ba dan haka sai na jarraba duk da irin ?arfin mulkin su ai yanzu gimbiyar bata kuda tayi nisan kiwo har nayi abunda nayi"

?agowa tayi tana wasu ?an surutai kafin ta tashi zumbur tace, "yanzu yanzu yanzu zamuyi abunda zamuyi dole ne tabar miki gida gida naki ne ke da ?arki kune kuke da iko dashi "

Lokaci Waya murmushin farin ciki ya buwayi fuskar YaaYa.

haka suka tarkato suka dawo tareda matar ko sallama batayi ba tafara wasu ?an tofe tofe tin daga soro sai da ta shigo sannan tace, "kina inaa munafuka ?ar munafukai fito yau kwanan ki a cikin mutane ya?are, wuta balbalin balai tsakanin mu dake hhhhh"

Yarrrrrrrrrrrrrrrr taji tsigar jikinta ta yarfa tareda mimmi?ewa lokaci Waya jikinta yafara tsuma, kwata kwata muryar matar batai mata daWi ba dalili na farko kenan da yasa jikinta ya rikice lokaci Waya.

Matar ta?ara da cewa, "zaki fito ne ko sai na shigo??"

"Umarrr!!!" sunan Yaaye tafara ambata cikin sigar neman Wauki sai dai akwai tazara me yawan gaske a tsakanin su dan kuwa ya tafi nema musu abunda zasu ci suyi amfani.

Da sauri ta haura kan gado taja bargo ta lulluSa.

YaaYa ce tace, " taurin kai gareta bazata fito ba gara ki shiga da kanki"

Matar tace, "yimin jagora a matsayin ki na ?ar gidan.
Kai tsaye YaaYa ta kutsa kai cikin Wakin Minoji itama matar tareda babar Fiddau suka bi bayanta,
tsayawa sukai curko curko suna kallon yadda jikin Minoji yake karkarea daga cikin bargon"

Matar tace, "Ni ?ar mutum ba aljan ba ?ar me ganye jikar jaraba nagi ?arfin aljan ba mutum ba, ki buWe kafin na buWe ki da kaina"

Ko motsi Minoji batayi da sunan zata buWe ba hakan yasa YaaYa tasa iya ?arfinta ta fizge bargon.
Cikin hanzari matar ta guntsi wani ruwa ta fesa wa Minoji.


Wani azababben numfashi taja tareda firgita a rikice tafara ?o?arin gogewa .
?ara fesa mata tayi hakan yasa ta ?walla ?ara tareda yankewa ta faWo daga kan gadon zuwa ?asa.

Cikin hargagi matar tace, "muguwa kibar musu gida, ki barwa masu gida gidan su ko na jefa ki cikin bala'in da bazaki iya dashi ba"


Girgiza kai kawai Minoji takeyi a wahalce tana wani irin kuka.
Lokaci Waya ta?ara rikicewa suffar ta ma tafara canjawa daga mutum zuwa wata halittar duk inda maganin ya taSa ta ya tashi yayi saSa sai juye juye take.

Matar tace, "wannan iska ce me haWari wato rikiWaWWiyar iska ta ta'alla?a da macijai da aljanu da kuma bil'adama har ma da wasu halittun da ta?i bayyana su "

Idon Ayiya da YaaYa kamar su fito saboda tsoro da firgici.
Babar Fiddau ce tayi ?o?arin cewa, "yanzu ya za'ayi?"

Matar tace, "ku kawo tsintsiyar laushi da garwashi.

Da gudu gudu sukaje suka kawo, ta karSa sannan ta kwance wata jaka ta ciro wani ba?in abu a farar leda sannan ta zumbuWa shi a cikin garwashi ta Wakko wani turare mara daWin ?amshi ta yayyafa a wutar da jikin tsintsiyar, a take Wakin ya gauraye da haya?i wanda su kansu su YaaYa sai da suka toshe hanci.

Matar ta cigaba da tsoma tsintsiyar a ruwan ta tana yarfawa Minoji tana cewa, "zaki bar gidan ko bazaki bari ba???, idan baki tafi ba bazan dena azabtar dake ba"


Duk kukan da Minoji takeyi tana kiran Umar ta dena saboda ta kai ma?urar galabaita yanzu temakon Allah kawai take nema dan yafi kowa sanin halin d take ciki.

Sunan tsaye suna kallomta yayin d matar take ta bata ruwan azabu iri d kala, kamar wal?iya suka ga giftawar wani abu wand basu bambance ko menene ba yayi kan Minoji kafin su farga suka ga ya Waga sama ya fita ta ?ofa suna maid kallonsu inda take kwance suka ga bata nan.

Ihu YaaYa ta tsillima saboda razanar da tayi sai da suka rirri?e ta.

matar ta bushe da dariya cike da son koWa kanta tace, "wannan itace ake kira zarra!!! Zarrar mu masu magani, daga yau matsalar ku ta kau babu ku babu wannan shaiWaniya a gidan nan Wanku ma mantawa zeyi da ita baze sake tunanin ta ba ke kuma ya zaba wajibi burin ki ya cika hahahahaha"

Ayiya tace, "mungodewa Allah mun gode miki kin temake mu yanzu gidan mu ze dawo dai-dai"

Matar tace, "ni nagama aikina zan tafi"

Sukace "ki gaida gida"

Haka suka zauna sukai ta maid yadda akai tsakanin su ukun, Yayyi kuwa da abun ya isheta sii ta tafi ta kwanta Yarinya ma ta koma gurinta ta ma?ale sai kuka take.

Sai bayan Magrib Yaaye ya dawo tareda kyakkyawan albishir Win da zeyiwa Minoji, suna gaisawa a gaggauce ya wuce Wakinsu ga mamakin sa sai yaga fayau.
dawowa yayi wajen su Ayiya ya tambaye su YaaYa tayi zaram tace, "Allah na tuba Aljani dan ze fita har sai mutum ya sani mu bamu san ma bata nan ba dan har abinci na shiga na kai mata naga bargo akan gado kuma kamar da mutum nayi tunanin ma itace"

Sam be yarda da maganar YaaYa ba dan haka yace, "Ayiya dan Allah ku faWamin ko ta sanar da ku zataje wani gurin"

Ayiya ta taSe baki tace, "Allah ya sittira rashin yardar dake tsakanin mu har takai haka?? ni mamakin fitar tata ma nake har na kas magana, kaje ka nemeta dan mu ba shiga shirgin mu ma take ba bare ko kace, magana ta gaskiya fa"

da sauri ya koma Wakin dan ?ara tabbatar da abunda YaaYa ta faWa cikin sa'a kuwa yayi katari da kwanon abinci kuma babu wanda ya ci a yadda aka kawo shi a haka yake, kan gado kuwa shima yayi zaton tana nan da ya shigo sai da ya duba yaga bata nan.

Zama yayi tareda furzar da zazzafar iska yana tambayar kansa "to ina tayi???"

Tunowa da yayi da cewarta zataje masarauta ta duba Mariama yasa ya mi?e zumbur yana cewa, "kenan can ta tafi duk da nace kar taje??"














*INDO CE..*

*=???=???=???SIHIRIN K'AUNA=???=???=???*


=???Shafi Na 29=???



Na INDO CE..


*('ELEGANT ONLINE WRITER'S('*



(Kyauta ne=??)




Bismillahirrahmanirrahim
(3E 'DDG 'D1 -EF 'D1 -JE





=??? Ina mata yan kwalisa , mata masu aji ,KASAITATTUN mata masu malakan zuciyan me gida kuzo ga Ummu Abdullah tazo muku da mayikan gyara jiki, kala kala, da sabulai na gyaran jiki, da turarrekan wuta da na jiki Dana kaya da na tsuguno,da humra kala kala da shi'umar humra, da kayan chemical,irin su liquid soap, perfume,air freshener,, Hair cream,Shampoo etc tana kuyawa tana hada kaya ,domin Neman Karin bayani Sai ku tuntibi wannan lambar 07046858716



Mutane na '



Tunowa da yayi cewarta zataje masarauta ta duba Mariama yasa ya mi?e zumbur yana cewa, "kenan can ta tafi duk da nace kar taje??"

nazari ya Wanyi kafin yace, "anya kuwa? banajin hakane gaskiya akwai dai abunda yafaru, amma nakasa fahimtar komai su Ayiya dai sunce basuga fitar ta ba, anya kuwa ba sune sukai mata wani abun ba?"

Tambayoyi yai ta jerowa kansa sai dai yarasa amsar su, duk ya shiga damuwa ga tarin tunane tunane.
Yarinya ce ta dafa shi tareda cewa, "Shikenan Yaaye Yaya Minoji bazata dawo ba?"

Da sauri ya Wago ya zuba mata ido tareda cewa, "bangane ba ina ta tafi?"

Tsaf Yarinya ta bashi labarin duk abunda taji da wanda tagani tanayi tana kuka.
Tsabar kaWuwar da yayi ko motsawa yakasa yi sai ido kawai yake bin Yarinya dashi har tagama ro?onsa akan yadawo da Minoji tagaji ta fita daga Wakin.
numfashi yaja tareda shafar kansa wanda yake juyawa tareda wani mugun ciwo, wasu zafafan hawaye ne suka fara shararowa kan fuskarsa duk da yana goge su amma sun?i tsayawa.

Minoji. da yamma li?is goshin magriba can wani sur?u?i ta tsinci kanta wanda ko a mafarki batasan gurin ba, firgigit ta farka daga dogon baccin da tayi ta shiga kalle kalle a wajen, idan ba bishuyu da tsuntsaye ba babu abunda take iya gani babu mutane a kusa bare gidajen su, da kyar ta lallaSa ta mi?e tsaye tana ?ara ?arewa wajen kallo, sai da tagama nazartar ko ina sannan tafara tafiya agalabaice tana tafe tana haWa hanya har ta iso bakin wata babbar hanya lokacin tini duhun dare ya rufa ko ganin hanyar batayi sosai kawai tafiyar take, bata lura da cewar babbar hanya bace bare tayi tunanin wani abun kawai ta afka da mufin ?etarawa ta cigaba da tafiya.

sam be ankara da ita ba har sai da ya buge ta tayi ?ar ?ara.
a Wan razane ya fito daga motar kafin ya iso inda take tini ta gangara gefe, "Subhanallah" ya furta sannan ya?arasa inda take yana haskawa da fitilar wayarsa, ?are mata kallo yayi kafin yace, " gashi dai mace ce kuma da alamun ba mahaukaciya bace sai dai babu hijab ko gyale ajikinta ita kuwa wannan lafiya ce ta fito da ita?? karfa naje na Waukarwa kaina aljana, anya kuwa ba tafiya ta zanyi ba?naga koda na buge ta bataji ciyo ba kuma ba wanda ya ganni da na Waukarwa kaina ai gwara kawai na gudu"

Ido ya zuba mata cikin ransa yanata shawarwarin yadda zeyi da ita, dur?usawa yayi yace, "baiwar Allah Baiwar Allah?? jin shiru yasa yace kodai ta suma ne? gata kyakyawa kodai rabona ce? kai sai fa na tafi da ita duk wadda za'ai ayi"

Rintso ido yayi sannan ya kinkimeta ya nufi mota da ita.
Koda ya isa kuwa yayi sa'a Ziyada bata kusa dan haka ya kaita Wakinsa ya kontar, babu aikin da yake sai kallonta duk da tayi wujiga wujiga hakan be hanashi ganin kyawunta ba, ruwa ya Webo ya yayyafa mata dan ta farfaWo.
buWe idonta da ya canja launi tayi ta Wan kalleshi sannan ta ?ara rufesu tareda sake salon konciyarta ta cigaba da baccinta cikin kwanciyar hankali.
sakin baki yayi yana kallonta kafin yace, "wai dama bacci take? to kodai ban buge ta ba ma?"

Yana zaune yana sa?a da warwara Ziyada ta shigo Wakin kanta tsaye batareda yasan ta shigo ba.
Ganin mace akan gadonsa yasa taja burki tareda cewa, "har yanzu baka dena ba kenan?? wannan wace irin rayuwa ce Usman?"

Fashewa tayi da kuka tana cewa, "ka fitar min da ita daga gidana ko in tara maka idon duniya yanzun nan wallahi nagaji da halinka Usman mayaudari macuci mazinaci Allah ya isa tsakani na dakai, wallahi ko ka koreta ko kuma nai mata shegen duka"

Usman yace, "haba Ziyada wace irin mummunar magana ce wannan ki saurare ni mana bafa yadda kike tunani bane"

Tace, "ba abunda zaka gaya min na yarda wallahi ha?uri na ya?are"

Tsaki yayi tareda cewa, "sai kiyi ai nace ki saurare ni kin ?i me kuma zan miki? sai kiyi yadda kike so"

Ruwan da ya ajiye ta Wauka ta watsawa Minoji sannan tayi kanta zata fara jibgarta, "Umar!!!!! ka temake ni kar su cutar dani wallahi banyi musu komai ba"

Minoji ta faWa lokacin da ta farka daga baccin hakan yasa duk sukai sororo Minoji kuwa tana buWe ido ta sake tabbatarwa kanta Umar Winta ne dan haka tayi saurin rungumeshi tana kuka tareda cewa, "Yaaye ka dawo?? dan Allah mu gudu daga gidan nan idan ba haka ba kashe ni zasuyi"

Kallon kallo Usman da Ziyada sukai kafin Ziyada tace, "ke dakata banason barikanci ya zaki zo kina rungumar min miji tsabar rashin kunya? ina ruwana dan an kashe ki? kije ki nemi Umar Win acan dan wannan mijina ne"

Cikin kuka tace, "?arya ne ni kaWaice matarsa bayan ni bashida wata Yaaye ka gaya mata dan Allah"

A tsawace Ziyada tace, "mayen mata kawai ba kuma zaka saketa ba? wannan ma inaga mahaukaciya ka Wakko garin tsinannen neman mata"

Kafin ya janye ta daga jikinsa tayi zumbur ta tashi ta dire daga kan gadon tana karkaWe jikinta gami da yatsine fiska.
Da mamaki Usman yace, "oo ga wadda aka buge da mota ta tashi tangaras kamar ma ba itace take kuka ba"

Minoji ta murmusa sannan tace, "kuyi ha?uri fa ?ar uwa kiyi ha?uri a rashin sani ne ta Wafe jikin mijinki tayi tunanin mijinta ne, Usman ita Win matar ?anin ka Umar ce kuma kuna kama da juna ita Win kuma ba'a haiyacinta take ba batada lafiya"


Rasssss rassss gabansa ya shiga faWuwa kansa yafara juyawa.
Ziyada tace, "wannan wasan kwaikwayon naki yayi ma?aryaciya karuwar banza"

Baya Minoji tayi ta faWa jikin bango tareda rintse idonta har na Wan wani lokaci kafin tace, "ina kikaje? meke faruwa? naga kina cikin damuwa"

Mariama tace, "?warai kuwa abu da dama sun faru nisan da nayi ne yasa akayi miki wannan cin zarafin kuma Yarima ne silar komai"

Sai kuma tafashe da kuka,
Hankali tashe Minoji tace , "me yai miki har yasaki kuka Sarauniya?"

Kamar bazata magantu ba sai kuma tace, "Yarima ya illata rayuwata ya rabani da mutunci da darajata ya keta min haddi na"

Kamar saukar aradu haka Minoji taji maganar da sauri ta girgiza kai gami da cewa, "a'ah meyesa? meyesa zeyi miki haka?"

Tace, "Yarima yayi mugun Alwashi akaina hakan ya ?udure tin ba yau ba kuma ya aiwatar, yanada muradin rabani da mulki na kuma yana son tozarta ni a idon duniya kuma yayi nasara, ina hukunta duk wanda ya aikata hakan kuma shima dole hukunci yarataya akansa, nayi masa Waurin da be isa ya kuSuta ba na Waure shi a inda ba wanda ze iya gane inda yake koda Sarauniya Bilkisu da kanta zan cigaba da azabtar dashi har ?arshen rayuwarsa baze ?ara ganin idon rana ba acan ze mutu a ?ar?ashin u?uba ta"

A tsawace Minoji tace, " ya isa Mariama!!!! kin haukace ne???? idan ya aikata hukunci daidai da na Wan kowa zaki masa bawai hukuncin son rai ba dan kawai kin tsane shi, kije kiyi tunani Mariama agani na ba da gaiya Yarima yai miki hakan ba yanada dalili kuma kiyi bincike zaki gane"

Mariama tace, "?arya ce Minoji bashida wani dalili wanda ya wuce wannan kuma ze WanWana kuWar sa, karki ?ara fusata ni"

Minoji tace, "ya zama dole na gaya miki....."

Kasa ?arasa maganar tayi saboda dakatar da ita da Mariama tayi.

Su Anti Ziyada kuwa tini an laSe abayan Usman sai rawar jiki take ganin al'amarin yafi ?arfinta, shima Usman Win ?arfin hali yayi kawai ya zubawa sarautar Allah ido yanayi yana ?an addu'o'in sa.


Minoji ta kallesu tace, "kuyi ha?uri fa Minoji ta sa ina Waga muku murya kuma ta katse mun hanzari akan maganata, ina magana ne akan Wan uwanka da ya ya daWe yana tsumayin ka yanzu zaka iya tuna shi???, ka tuna cewar kana da mata Sumayya wadda kuke kira YaaYa da ?arka Kadija Yarinya, sunan mahaifiyarka Jamila kuna kiranta Ayiya ?anin ka Umar kuna kiransa Yaaye sai autar ku Hafsa kuna kiranta Yayyi, yanzu ka tina da hakan?"

Ziyada tace, "ban fahimta ba fa wannan wace irin magana ce? Yanada mata fa harda ?a kikace?"

Minoji tace, "idan ya dawo

14 / 16