Sihirin 1 Complete Hausa Novel

Author :  Indo Category :  Love

Chapter   10 / 16

27K to 30K   out of 47.8K words

saki jikinta sosai. sukan zauna suyi hira da Minoji Yarinya da Yayyi, tsakanin Minoji da Ayiya kuwa gaisuwa ce kawai take haWa su, tsakanin ta da YaaYa kuwa sai dai kowa ya kalli kowa sai jefi jefi suke Wan gaisawa, ita YaaYa zafin kishi ke damunta ita kuwa Minoji jinkai ne yake sa ta?i yimata magana.
Kullum tana Waki idan sun ganta a waje to rana ta Sace ko da safe ko da yamma shine zata fito girkinta ma a Waki takeyi sai ta gama zata zuba a kaiwa Ayiya.
Hakan kuwa ba ?aramin ?una yake musu ba musamman YaaYa wadda take Waukarta tamkar kishiya.

Yau tana Waki a kwance tana danne dannen waya Yarinya ta shigo tace, "wai kizo inji Ayiya"

Badan batason gardama mata ba amatsayinta na tamkar uwa a gurinta da babu dalilin da ze sa ta fita yadda rana ta buWe fau Winnan, a hankali take takawa tanayi tana cije baki saboda wani irin zafi da ranar ke yi mata duk da ba wata tafiya bace daga Wakin nata zuwa Wakin Ayiyan amma ko gilmawa batasonyi ta cikin rana gashi kaf tsakar gidan ba inuwa.

Daga baki baki ta dur?usa tace, "gani Yarinya ta kirani"

YaaYa ta kalleta ta watsar sannan tace, "Ayiya take nemanki"

Kai tsaye Minoji tace, "dama bance kece ba ai ko?"

Shiru YaaYa tayi badan taji daWin maganar ba.

Ayiya tace, "dama cewa nayi ya kamata ki dinga fitowa kina kamawa YaaYa aiki kinga yau ta tashi jikinta ba daWi kuma ko sharar tsakar gidan ba'ayi ba Yayyin ma tinda kika shigo gidannan shikenan lafiyarta ta?are koda yaushe cikin laulayi take"

Yayyi zatayi magana YaaYa ta dakatar da ita da cewa, "ke kuma kiyi shiru mana tinda ba dake ake ba"

Ayiya tace, "ina kika ajiye tsintsiya YaaYa?"

da sauri Minoji tace, "kuyi ha?uri dan Allah zan dinga yin sharar da safe amma bada rana ba ban iya shiga rana ba wallahi illata ni take yamma tanayi zan share"


Ayiya tace, "aa baze yuwu ba yanzu yakamata a share ba sai yamma ba, idan yin ne bazakiyi ba shikenan"

Cikin sanyin jiki ta tashi ta Wakko tsintsiyar tafara sharar, ko rabi batai ba jikinta yafara kakkarwa, Yayyi tace, "yaya Minoji ki kawo na share sai ki huta"


Murmushin ?arfin hali tayi tace, "zan iya"

YaaYa tace, "ni dai inaga Mayya Yaaye yaje ya auro mana"

Kamar saukar aradu haka Minoji taji maganar sam bataji daWinta ba amma sai ta danne kawai ta cigaba.

Ayiya ta taSe baki kafin tace, "nima dai ina tantama Yayyi bata taSa abubuwa makamantan wannan ba sai yanzu a wannan lokacin, Allah dai yai mana tsari amma abun akwai ban al'ajabi"

YaaYa tace, "ai ni kaina banajin daWin jikina"

Yayyi tace, "haba dan Allah meyesa kuke irin maganganun nan ba daWi wallahi"

Ayiya tace, "wuce kije gidan Adama kice ina gaisheta"

a zafafe tayi wurgi da tsintsiyar gami da fashewa da kuka ta nufi Wakinta.
Yarinya da Yayyi ne suka mara mata baya suna ?o?arin rarrashinta amma tayi banza tana shiga Wakin ma ta kulle ?ofa.

Yayyi ma tinda ta dawo baya ta zauna sai ta fashe da kuka.


Kallon kallo Ayiya da Yayyi sukayi kafin Ayiya tace, "tabWi jam wannan babban aiki haka kiga wata yarinya sangargar? lallai sai mun tashi tsaye kinga dan tayi kuka Yayyi ma kukan take wannan wace irin masifa ce narasa meye ala?ar Yayyi da ita da batason ganin Sacin ranta, hasalima sai ta bata umarni sannan take wani abun meye hakan ke nufi ne? anya kuwa yarinyar nan mutumce?"

YaaYa tace, "gaskiya yakamata mu binciko gaskiya dan baze yuwu mu zauna da al?a?ai a gida ba Yaaye yazo ayi ta ta?are ko mu ko ita sai dai ya saketa ma wallahi dan banajin yarinyar nan mutumce idan ma mutum ce to mayya ce kuma idan ta haifa mana Wa a gida kinga an samu irinta kenan, gwara mu yiwa tufkar hanci"








*INDO CE..*
[8/1, 5:27 PM] Maryam Muhammad: *=???=???=???SIHIRIN K'AUNA=???=???=???*


=???Shafi Na 20=???



Na INDO CE..


*('ELEGANT ONLINE WRITER'S('*



(Kyauta ne=??)




Bismillahirrahmanirrahim
(3E 'DDG 'D1 -EF 'D1 -JE







yace, "amma dai ban kai ki ba ai"

Shiru tayi masa ganin hakan yasa ya canja labarin bayan ya ?ara sassauta muryar sa yace, "meyesa bakyaso na ganki a madubi?"

Batareda ta kalleshi ba tabashi amsa da cewa, "tsorata zakayi idan ka ganni"

Da Wan mamaki yace, "kai tsorata fa? nifa namiji ne kinsan mu jarumai ne to wai ma tayaya zan tsorata kamar ban taSa ganinki ba?"

Kai tsaye tace, "baka yarda ba? wani jarumai duk a baki ne fa kunfi kowa tsoro"

Yayi dariya gami da cewa, "faWi gaskiya dai ku da har mage ma tsoronta kukeji"

Tace, "eh munji amma a hakan mun fiku jarumta kuma idan zaka iya mu gwada zanga iyakar jarumtar taka"

Gyara zama yayi yana cewa, "na yarda amma fa banda abunda bazan iya ba gaskiya"

Tayi dariya me isarta kafin tace, "har kafara karaya ne tin yanzu?, bafa wani babban aiki bane kawai ina so kasa idonka cikin nawa har na tsawon da?i?a Waya (minti Waya) ba tareda ka kawar ba indai ka iya kaiwa to na yarda kunfi mu jarumta idan kuma ka kasa kaga ya tabbata tsoron mu kukeji tinda idan mun faWa sai kuce aa"

Shiru yayi yana nazari kafin yace, "anya kuwa zan iya batai min tsauri da yawa ba? ke fa ba'a iya haWa ido dake"

Murmushi tayi ta Wan kalleshi ta basar sannan tace, "cikin sauri haka? gaskiya ka yar da maza"

Da sauri yace, "ban yarda a taSa mu ba gaskiya bamu faWi ba sai na jarraba"

Ta wani rausayar da kai tana murmushi tace, "ina jiranka"

Yace, "na shirya ke nake jira har minti goma ma zan iya"

Tace, "kamar gaske"
A hankali ta Wago idonta ta jefa cikin nasa.
Sai da yaji tsikar jikinsa ta yarfa har sai da ya Wan zabura amma ya danne ya cigaba da kallon ?wayar idonta, cikin ?an sakanni yafara ganin idanun nata sun fara canja launi wanda yasa yake jin idonsa yafara zafi daga baya ma yaji kansa yafara juyawa yana neman fita daga hayyacinsa zuwa yanzu yafara dena gani sai dishi dishi da wani irin juyayi da tunaninsa ke yi.
Cikin sauri yayi ?asa da kai tareda rintse idon da ?arfin gaske jikinsa yafara wata irin tsuma.

Minoji kuwa dariya tafara ?yal?yalawa harda tafa hannuwa.
Sai da ya gama murtsike idon bayan wani Wan lokaci ya dawo hayyacinsa sannan yace, "shikenan nafaWi wai? anya kuwa zan yarda? abun kamar a mafarki ni narasa ma me nagani na tsorata haka"

?are masa kallo tayi sama da ?asa aranta tace, "wayece maka idon mutum da aljan haka kawai yana gaurayuwa guri Waya?"
Azahiri kuwa cewa tayi, "cikin sau?i ka tabbatar min da cewar tsoron mata kukeji, gardama ta?are amma fa kabani dariya wallahi"


Rausayar da kai yayi yace, "ya zanyi tinda anfi ?arfina amma fa ba dan mun gaza bane kima dena murna"

Cigaba tayi da dariyarta har sai da ta gaji sannan ta dena, tinda tayi shiru bata ?ara ce masa cikanka ba sai shi kaWai yake surutunsa yayi kiWan sa yayi rawarsa.

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya kowa da abunda ya dameshi, a Sangaren YaaYa kullum abun ba sau?i har ta kai ga tanajin inama zata samu hanyar da zata raba Yaaye da Minoji koda baze aureta ba.

Ita kuwa Ayiya irin halaccin da YaaYa ta nuna musu ne yasa takejin takaicin gazawar da tayi wajen cika mata muradinta gashi kullum cikin ?orafi da kushe Minoji take a gurinta hakan yasa Ayiya har tafara jin ta tsane ta kuma dama can tasu batazo Waya ba.

Yayyi ma kullum ta ta dambarwa daban ita bata yarda su muzgunawa Minoji ba haka bazatayi wani motsin kirki ba idan Minoji bata bata izini ba.

Yarinya kuwa koda yaushe tana wajen Minoji suna hira indai Yaaye baya nan ganin kullum sha?uwa suke ?arayi yasa YaaYa tafara ?o?arin shiga tsakanin su a cewarta baza'a cinye mata kurwar ?a ba.

Aunty Madina
Har gobe ba?in cikin halin da Wan uwanta ya faWa a dalilin Minoji yakasa barinta kuma ta ?udure wa kanta sai ta muzguna mata kamar yadda Annur ya azabtu itama zata WanWana mata, da ta tsinkayi labarin abunda yake faruwa tsakanin Minoji da YaaYa sai tayi ?undumbala a cikin maganar ta nemi hanyar da zata samu YaaYa kuma ta sameta ta?ara tunzura ta gami da nuna mata wasu hanyoyin da zata ?untata mata cikin sau?i.

A Sangaren Yaaye da Minoji kuwa hankalin su kwance dan suna samun kulawar juna ga so da ?auna da suke Wawainiya dasu hakan yasa basa iya ganin laifin juna, ko me Ayiya da YaaYa zasu faWa akanta baya taSa yarda, haka itama duk abunda sukai mata bata buWar baki ta sanar masa bare ransa ya Saci haka take jure duk wani wula?anci nasu, zuwa yanzu har ta kai ga yara da matan unguwar suna shigowa kallonta ko ina ya Wauka da yake sanannu ne a unguwar, wasu suce mayya Wan Ayiya ya auro wasu suce ba mutum bace wasu suce aljana ce wasu suce wata halittar ce haka dai kowa da irin abunda yake cewa.
haka take zaune waccan ta le?o ta fita tana Worar da ?arya da gaskiya waccan ma ta le?o ita kuwa duk abunda zasuyi hakanan take jurewa dan bata so tayi ?wa??waran motsin da za'a rabata dashi.


Ayiya da YaaYa ne zaune suna tattaunawa Ma?ociyar su, Babar Fiddau ta shigo, cikin salon gulma da tsugudidi ta tsugunna gami da cewa, "hmm Ayiya??"

Ayiya tace, "babar Fiddau? Allah yasa dai lafiya"

Ta gyara zama sannan tace, "Allah dai ya sittira ai daga gidan gargajiya nake yanzu muka gama maganar sirikar ki da Habi wallahi tace ta taSa ganin irin haka kinsan ya akai aka tona asirinta? wai ashe yarinya aljana ce? ai wani magani aka barbaWa mata a kofar Waki wanda idan mutum maye ne ko aljani za'a gane indai mayyace zakiji tana ta ihu tana tonawa kanta asiri idan kuma ba mutum bace to bazata iya fitowa ma daga Wakin ba zakiga duk ta ?one"

Cikin sauri YaaYa tace, "ke dan Allah?? wallahi Allah muna so ina ake samun sa?"

Ayiya tace, "Babar Fiddau kin tabbatar?"

Tace, "haba Ayiya wallahi kinji na miki rantsuwa irin ta musulmi yanzun nan Habin gidan Gargajiya tagama bani labari tin yaushe nake gaya miki wannan ?a akwai ayar tambaya akanta?? kinsan suk duniya babu halittar da ta kai Maciji ?in rana?? sune basa son rana ko ta gamin gafara ina ganin dai wannan ?a Iska ce ba mutum ba idan zaki tashi tsaye ki raba Wanki da ita ki tashi idan bazaki iya ba ke kika jiyo"

Ayiya tace, "dan?ari ma?ari aikuwa bazata yuwu ba wallahi na haifi Wana na gama rainonsa ?arshe ya zama ba rabona ba aljana fa? aa wallahi ba dani ba, Babar Fiddau yanzu ina ake samun maganin nan?"


Babar Fiddau tace, "yauwa ko kefa? ai wallahi zamanin nan ba'a zama aljanu yanzu sun san siga iri iri ta cutar da mutane, ai kibari gobe goben nan sai muje Habi ta raka mu"

YaaYaa tace, "dani za'aje Babar Fiddau dan ko me yasamu Yaaye ni aka yiwa wallahi"

Ayiya tace, "aa idan kika fita yazo yatarar bakya nan masifar duniya akanki ze juye ta kinga kuwa idan nice naje da kaina babu yadda zeyi dani sai dai ya gaji da mita yabari baze min faWan ba"


Babar Fiddau tace, "wallahi hakane gara kije ma da kanki sai ya fi"















*INDO CE..*

[8/1, 5:27 PM] Maryam Muhammad: *=???=???=???SIHIRIN K'AUNA=???=???=???*


=???Shafi Na 24=???



Na INDO CE..


*('ELEGANT ONLINE WRITER'S('*



(Kyauta ne=??)




Bismillahirrahmanirrahim
(3E 'DDG 'D1 -EF 'D1 -JE






YaaYa tace, "?aryar banza ai mun saba jin irin tatsuniyar nan bare ko a shirga mu munafuka kawai"

?arasawa Yaaye yayi inda take ya zuba mata idanu cikin tausayawa, ba tareda yace komai ba yaja hannunta zuwa Waki, a gefen gado ya zaunar da ita sannan yace, "ba nace karki damu ba? komai zasu faWa a wasa nake Waukarshi babu ranar da zan yarda da cewar zaki cutar dani ko dangina komai wahala ina tareda dake zan kasance a tsagin ki komai tsanani, ki dena kuka akan abunda be kai matsayin ki zubar masa da hawaye ba ni zaki tausayawa ni nasan zafin zubar hawayenki ni nasan ciwon su kiji tausayin mijinki dan Allah"

Cikin nutsuwa tafara share ?wallar tareda jinjina kai alamar ta gamsu da abunda ya faWa"

Rungume ta yayi tsam cikin tausassar murya yace, "Minoji duk suna kan kuskure ne akwai abunda yake yawo a tunanin su ne shiyasa suke miki kallon wata daban dan Allah kiyi ha?uri "

bata barshi ya ?arasa maganar da ya Wakko ba tace, "bana so ka dinga bani ha?uri nima nasani ana kan hakane kuma karka manta gaskiya tana sama da duk wani ?alu bale wata rana zata baiyana sai dai be zama lallai tai mana daWi ba kasan dama ta gaji haka"

Yace, "shikenan na dena amma gaskiya tana da daWi idan an jure, yau baki tambayeni game da aikina ba"

Ta ?ara gyara kwanciya a jikinsa sannan tace, "kasan ai dole zan tambaya shine yau ka rigani magana?? to ni na canja salon tambayar tawa, yau ka wuni lafiya? sannan kuma ka ci abinci? ka kula da kanka kamar yadda kake kula dani??"

Ya murmusa sannan yace, "eh ?warai naci abinci sannan na wuni lafiya kinsan abunda nakasayi? kulawa dake a wunin yau ko a waya wai ban kira ki ba dan abun takaici, na samu aikin da zan yi wasu ?an kwanaki inayi inata farin ciki ko babu komai zan samu abunda zan kawo muku"

sai da ha?oranta suka bayyana saboda murmushin farin cikin da ta saki cike da murna tace, "Allah abun godiya Alhamfulillah, wane irin aiki ne?"

Yace, "aikin gini ne amma nasan cewa zakiyi akwai wahala ko? a hakan kuma kinajin kin fini jarumta"

cikin fara'a Tace, "naji daWin samuwar aikin nan dan kuwa ba'a san namiji da zaman kawai ba, Allah ya temaka yayi maka jagora Hubby na, wani abu da yake matu?ar burgeni a tattare da kai ga ka kyakkyawa son kowa amma baka raina sana'a kasan wasu raina sana'a sukeyi sai dai rashin sani yafi dare duhu basu san ta wace hanya Allah ze azurta su ba idan yaso"

Yace, "wannan haka yake Allah yasa mu gyara"

Ta amsa da "amin"

Sai gaf da magrib YaaYa ta kammaka girki ta bayar aka kawowa Yaaye da Minoji lokacin ma duk abincin ya gama fice mata a rai hakan yasa bata ci shi ba"

Tana zaune tayi tagumi tana tunani taji sallamar Mus'ab tareda Ummi cikin farin ciki ta fito tsakar gidan tana murna ta amsa sallamar ta jasu Waki.
Ko ruwa bata basu ba ta ma?ale a wajen Ummi har wata ?ar shagwaSa takeyi,
kallonta Mus'ab yayi tareda cewa, "ganta dan Allah Ummi yadda ta koma amma haka ta zaSawa kanta"

harararsa tayi tace, "banason magana kaji ko? Wan raini kawai"

Ummi tace, "da yaya bazeyi magana ba Minoji ko da baki faWamin ba nasan ba jindaWin zaman gidan kike ba, damuwa da takura su kikafi fuskanta duk kin lalace a tsaye, ga ki da kafiya kin ?i amincewa ki raba zama da mutane kuma kinsani ba ?aunar ganin mutane koda yaushe kike ba "

?asa tayi da kai tana wasa da Yatsunta cikin sanyi tace, "Ummina kiyi ha?uri dan Allah karki damu da halin da nake ciki dan kuwa ni na jefa kaina ina son zama a hakan"

Ummi tace, "amma abun yayi yawa Minoji kullum Mariama takan kaimin ?orafi akan ki musamman saboda gardamar nan"

Tace, "idan kika biye mata fa zaki ta tunanin wani abu daban ne, tunanin ta daban nima nawa daban haka yanayin mu akwai bambanci sosai ita a tsarin ta sam namiji baya ciki bare soyayya kwata kwata bata san wannan ba Yarima ya riga yasa duk wasu maza kallo Waya take musu dalilin da yasa kenan bata fiya goyon bayana akan Yaaye ba, ki barta kawai Ummi duk zata dena komai ze warware insha Allah"

Ummi tace, "to Allah ya warware Abban ki yana gaishe ki"

Ta murmusa tareda cewa, "Ina amsawa ai duk ya fiku zuwa inda nake ma ku duk kun manta dani"

Ummi ta murmusa gami da cewa, "eh amma ai muma gashi munzo ko?"

Dariya kawai

10 / 16