Sihirin 1 Complete Hausa Novel

Author :  Indo Category :  Love

Chapter   4 / 16

9K to 12K   out of 47.8K words

ta rakata har ta nemi guri ta zauna sannan Ummin tace, "oo Lafiyarki ?alau kuwa? kin shigo da gudu haka ko sallama babu? farin cikin kuma na meye?"

Dariya tayi kafin tace, "wallahi Ummi lafiya lau, kawai dai nishaWi nakeji"

Ummi tace, "to ya jikin ?awar taku"

Sai a lokacin ta tuna ?aryar da suka zundumawa Ummmi cewar zasuje dubo ?awarsu bata da lafiya, Wan ?asa tayi da kai tana zare ido, kafin tace, "da sau?i sosai, wallahi me adai-daitar da ya kawoni yana da mutunci sosai ko kuWin be karSa ba"

Ummi tace, "Allah ya saka da alkairi, Allah sarki dama ana samun irin haka sai taka tazo Waya da mutum, amma yadda naji ana faWe masu adai-daitar nan wasu ba mutunci ke kam kinyi sa'a"

TaSe baki tayi Tace, "wallahi Ummi yanada mutunci sosai kuma shine ma wanda muka yiwa Sarna jiya sai gashi yau mun haWu"

Ummi tace, "to Allah ya tsare gaba shi kuma da ya kyautata miki Allah yayi masa albarka Allah ya haskaka hanyoyin nemansa"

Ta amsa da "amin"
sannan Ummi ta?ara cewa, "ki shirya gobe kije gidan Antin ku Madina tana nemanki zaki taya ta aiyuka"

A take annurin fuskar ta ya Wauke duk wani farin ciki da take ya gushe, kamar zatayi kuka tace, "haba haba nidai bazani ba, haka kawai ina zaune a gidan ubana sai ace wani na tafi gidan wasu"

Ummi tace, "to dalilin me yasa baza kije ba??"

?asa ?asa tayi da ido a shagwaSe tace, "Allah Ummi kunyarsu nakeji, gaskiya ni bazani ba"

Ummi tace, "to Allah ya kyauta nidai zan gaya mata kince baza kije ba, kar ta zuba ido tajiki shiru"

MurguWe baki tayi tace, "gaya mata wallahi yafi ma"

Waya Ummi ta cira ta kira Anty Madina bayan ta Wauka ta sanar mata sa?on Minoji Mi?a mata wayar tayi tareda cewa, to karSi tace na baki"

KarSa tayi ba dan ranta yaso ba tace, "ina wuni"

Anti Madina ta amsa da Lafiya lau ?anwata akan meyesa baza ki zo ba?? ko saboda Annur ne?? indai saboda shi ne bazaki zo ba to ki kwantar da hankalin ki bama ya ?asar nan, kuma koda bansani ba amma ba lallai ya dawo yanzu ba"

Sosai Anti Madina tayi mata kwarjini duk zan?alewar da take sai tayi la?was tace, "shikenan zanzo"

Da haka sukai sallama ta mi?awa Ummi wayar tana cewa, "to gaskia kwana biyu zanyi kafin wannan uban takurar ya dawo"

Ummi tace, "Allah ya kaimu kwana biyun"

Bata ?ara magana ba ta wuce Wakinta tana ?ara sauke ido ?asa.

Yaaye Anyi nasara wajen gyaran adai-daita sahun amma an samu tsaiko daga me gidansa, sai da ya bashi kyakkyawan kashedi sannan ya sakar masa ita bayan sunyi yarjejeniya akan indai wani abu ya?ara faruwa ko lafucinta aka ?arayi ze ?wace ta, Bashi da zaSin da ya wuce ya amince da hakan dan kuwa yanzun ma sai da yayi da gaske sannan ya samu ya dawo masa da ita sakamakon da da yace yadakatar dashi a aikin.

suna zaune, Ayiya ta kalleshi tace, "Amma Yaaye tsautsayi ne yafaru haka amma baka sanar mana ba?? ko addu'a ai da munyi ko ba gaskiya ba??"

Yaa-ya tace, "hakane wallahi nima banji daWin Soye mana da kayi ba, ai ba abun kayi shiru bane"

?an murmushi yayi sannan yace, "ai banaso ku tashi hankalin ku ne bare ga Yayyi ga Yarinya be kamata ace suna fuskantar ?unci irin haka ba shiyasa nayi shiru amma komai ya wuce ai da sau?i dan Allah ku dena tayar da zancen ma"

Ayiya tace, "to Allah ya ?ara kiyayewa"

Suka amsa da "Amin"


Minoji sai bayan kwana biyu da ta gama rigima sannan ta shirya zuwa gidan Anti Madina, tafiya take kanta a ?asa sai haWe rai take, Yaaye kuwa ya mayarda sabgoginsa yankin su Minoji saboda sa ran gamuwa da ita bayason zuwa gidan su dan idan yaje bashi da abinda ze ce musu shiyasa ya ma?ale anan ko zasu haWu, cikin sa'a kuwa ya ganta tana faman ?asa da ido Winnan da sauri ya tsaya tareda cewa, "Madam tafiya zakiyi?"

?an murmushin ?asan baki tayi murya ?asa ?asa tace, "yau naji ikon Allah idan ba tafiya zanyi ba zama zanyi?, sai da taji ya?ara cewa, "ina zakije?" sannan ta Wago kai ba tareda ta kalleshi ba ta gaya masa, kai tsaye yace, "to"

Shiga tayi ta lafe a inuwa sannan ta sauke ajiyar zuciya tareda lumshe idanunta sai da ta Wan Webi lokaci sannan ta buWe su a lokacin ne ta lura basu fara tafiya ba, da Wan mamaki tace, "Lafiya kuwa?"

Da sauri yayi ?asa da idonsa tareda rintse su, sannan yace, "kiyi ha?uri fa madam gani nayi kamar baki gama shiryawa ba"

Murmusawa tayi tace, "muje kawai ba shiryawa ne banyi ba gajiya nayi shiyasa ga rana"

Da mamaki yace, "rana kuma Madam yanzu taran safiya zuwa goma ne, har wata rana ake yanzu?""

Sai a lokacin ta kalleshi karaf sukayi ido huWu, ko gama ganin ?wayar idonta beyi ba tayi saurin kawar da kai sannan tace, "ooh sannu kaine na jiyan nan ko?"

Yace, "eh Madam hakane, ya kikaje gida?"

Ta amsa da lafiya lau sannan tace, "gashi yau ma mun ?ara haWuwa"

Murmushi yayi yace, "gaskiya ni me sa'a ne da nake haWuwa da Madam me alkairi Madam duk inda zakije kawai zan dinga zuwa na kaiki"

Da sauri tace, "wayyo Wan Aljannah, kamar kasan wallahi bana son rana kaga kawai sai ka Wakko ni daga ?ofar gidanmu, amma fa dole ka karSi kuWinka wallahi"

Cike da farin ciki yace, "na yarda Madam ina godiya sosai"

Murmusawa tayi gami da gyaWa kai.

Bayan sun isa tace, "to ka bani lambarka yadda zan dinga nemanka idan zan fita ko?"

Ba musu ya saka mata sukayi sallama, tayi gaba sai a lokacin ta tuna inda ta dosa nan takaici ya dawo mata saboda ta?arasa ta gunguni har ta shige gidan, sai a lokacin ya sauke ajiyar zuciya sannan yabar wajen, saboda farin ciki ji yake kamar ya taka rawa"

Da sallama ta shiga Anti Madina tana murna ta amsa tana cewa, "sannu da zuwan ?anwata"

Murmushi kawai Minoji takeyi bayan sun gaggaisa suka fara hira sai kuma ta saki jikinta.

kwananta biyu bata ga Annur sai yanzu ta yarda baya ?asar dan haka ta sake sosai har ta manta dashi a duniya.

Yaaye kullum sa ran ganin kiranta yake amma shiru kuma kullum sai yazo unguwar sai dai bashida ?ancin da ze tinkari inda take dan haka sai dai ya gama shataletale ya koma gida.

Kallon Anti Madina tayi tace, "Anti Madina zan shiga kicin"

Murmushi tayi tace, "me za'a haWa mana?"

gefe tayi da idonta tana murmushi tace, "nima ban sani ba kawai sai abunda kika gani duk abunda zeyi min sau?i shi zanyi"

Anty Madina tace, "ko nazo na taya ki?"

Da sauri tace, "aa ba sai kin tayani ba kiyi zamanki"

kafin Anti Madina tayi magana har taje ?ofa, kicin Win ta shiga bayan ta gama kalle kalle tafara kici kici,
Tsalle takeyi tana ?o?arin Wakko wata roba a sama wadda kori yake ciki, kasancewar ba irin mugun tsawon nan ne da ita ba yasa takasa Wakkoshi.

Kamar daga sama taji muryarsa yana cewa, "zan iya temaka miki?"

Ido ta zazzaro cike da mamakin zuwansa a lokacin aranta tana cewa, "ai fa da be zo ba da an canja masa suna"

gyara tsayuwarta tayi tareda dai-daita nutsuwar ta a take ta koma kamar ba ita ba fuskarta babu walwala babu alamun wasa sannan ta juyo, cikin son kauda zancen tace, "sallama yakamata kafara yimin ba temako ba"

?asa yayi da kai cikin sanyi yace, "kiyi ha?uri Assalamu'alaiki"

Murmushi ne ya suSuce mata ta kawar da kai kafin ta amsa sallamar sannan tace, "zaka iya Wakko min kuwa?"

Da sauri yace, "zan iya"

Zamewa tayi zuwa baya har ya Wakko ya mi?o mata ko kallonsa bata ?arayi ba sai da ya yabata sannan tayi masa godiya.

Shikuwa Annur murmushi kawai yake saki yana binta da ido, yace, "yaushe kikazo ne?"

ba tareda ta kalleshi ba tace, "tin ranar nan nama manta ko yaushe ne"

Ya Wan murmusa sannan yace, "na takura miki ko?, bari naje wajen Anti dan Allah ko meye kikayi ki kawo min nawa"

murmushin gefen baki tayi sannan tace, "shikenan wai dama kana nan ko?"

Girgiza kai yayi yace, "aa bana nan, na tambayi yayan mu kina ina ne shine yace min kina wajen Anti kuma na daWe ban ganki ba duk nakasa nutsuwa shiyasa nayi saurin zuwa dan na sami ganinki"






*INDO CE..*
[8/1, 5:27 PM] Maryam Muhammad: *=???=???=???SIHIRIN K'AUNA=???=???=???*


=???Shafi Na 10=???



Na INDO CE..


*('ELEGANT ONLINE WRITER'S('*



(Kyauta ne=??)




Bismillahirrahmanirrahim
(3E 'DDG 'D1 -EF 'D1 -JE




dariya tayi kafin tace, "sai kace ganin annabi?, to ya hanya?"

Ya murmusa har cikin ransa yana farin cikin samun kanta da yayi cikin sau?i yau, a tsanake yace, "Alhamdulillah, yau naga kina cikin farin ciki sosai, nima ina jindaWin haka"

Gefe tayi da idonta tace, "ko?"

Yace, " eh mana"

" Yayi kyau" kawai tace bata ?ara kallonsa ba ta cigaba da abunda take ko murmushin da take ma ta dena, ya lura tafara burkicewa sai dai baya iya yiwa kansa shamaki akanta indai idonsa ya gani to tabbas bakinsa ze furta, indai tunaminsa ya kai to dole zuciyarsa zata wassafa, sai dai abunda ya kasa bayyanar mata, tsananin sonta da yake har yanajin idan be aureta ba rayuwarsa zata samu tangarWa,
Cikin sanyi yace, "kiyi ha?uri fa Minoji bakina ne bashida linzami, na takura miki, kar kiyi fushi dani dan Allah"

Ajiyar zuciya ta sauke dan kuwa har zuciyarta tafara hargitsawa ?iris take jira ta?arasa fusata, murmusawa tayi tace, "ahh ba komai"

hanyar fita ya nufa yanayi yana wai-wayenta sam bayason Wauke idonsa daga kanta, ita kuwa ya lura bata damu da ko kallonsa ba hakanne yake sawa yaji zuciyarsa tana tsinkewa.

jiki ba ?wari ya koma wajen Anti Madina, tinda ya zauna ko ?ala be ce mata ba, kallonsa tayi ta Wanyi dariya kafin tace, "iyayen Miskilanci ya dai?? nifa ban taSa zaton akwai macen da zata dinga sa ?anina surutu haka ba, wai har ka dawo daga gurin nata kenan ? ah yau kayi ?o?ari, lallai Annur ka ajiye mana Wanyen aiki"

Kamar zeyi kuka yace, "Anti bata son saurara ta, ko dai muryata tanayi mata ba daWi ne?? bata so ta kula ni ko kaWan, ina jin tsoro fa"

murmushi Anti Madina tayi kafin tace, "daa nayi tunanin Minoji ba komai bace a wajen mu, muna da kuWi da duk wani abu na more rayuwa, Annur kana da kyau irin wanda ake cewa azo a gani, duk wani abun burgewa na Wa namiji ka tara, amma naga tsaurin yarinyar ya wuce duk inda nake tunani, batayin duba da arzikin mu bata kallon matsayinta da namu bata hangen duk wani abu me jan hankalin ?an mata kanka, shin ita wata ta dabance a cikin su??"

Annur yace, "Anti dan Allah ki ma dena maganar dukiya banaso ta soni dan kuWi ko wani abu nafi so ta Soni da zuciya Waya kuma tsakani ga Allah, ban damu ba koda bazata dinga yimin magana ba"

Jinjina kai Anti tayi tace, "na fahimce ka Annur amma gaskiya shawo kan Minoji a gurinka abu ne mawuyaci, har yanzu baka gaya mata abunda ke zuciyar ka ba, kuma ina ganin sai ka dage ka fahimci yadda take domin Minoji abai-baice ba dai-dai take ba, bansan meyesa komai nata yake banbanta ba wani zubin nakanji mutane suna cewa ANYA MUTUM CE?? da ina Waukar abun kamar wasa amma nima yanzu na dasa wannan alamar, Annur kayi ?o?arin samun kan Minoji dan kalarka ce da kai tafi dacewa ba da kowa ba"

GyaWa kai kawai yayi ba tareda yayi magana ba.

Anty tace, "bari kaji yanzu zatazo tace gida zata"

Murmusawa yayi yace, "bata son gani na ko?"

Anti tace, "sai dai ka tambayeta kaji"

Yana shirin fita daga falon tayi sallama hakan yasa ya koma ya zauna, sai ?asa ?asa take da ido ta zauna a kusada Anti sannan tace, "Anti inata daWewa a Gidan nan fa, yakamata na tafi, kicewa Boss yazo ya Waukeni dan Allah idan nice na gaya masa da kaina baze zo ba sai yaga dama"

Murmusawa Anti tayi tace, "har kin gaji damu?"

Girgiza kai tace, "aa gaskiya ni ban gaji daku ba kawai dai gida nakeson komawa"

tayi magana Cikin wata irin murya me kama da ta shagwaSa sai dai ita dai-dai tayi maganarta a nata tunanin, wanda yaji kuwa kai tsaye cewa zeyi tana sane takeyi.

Annur yace, "bakya son ganina ko Minoji?"

?an ?ananun idanunta ta waro masa tayi ?asa dasu kafin tace, "wallahi ni ban gaji da ganin kowa ba, ni ban taSa ?in son ganinka ba"

?an murmushi yayi kafin yace, "shikenan ki shirya sai na kaiki ko"

Da sauri tace, "aa Boss ze zo ya tafi dani, au inama da me adai-daita sahu wanda yake kaini unguwa shine zan kira yazo ya Waukeni"

Anti tace, "be kamata ki hau adai-daita ba Minori"

Dariya tayi tace, "ni wacece a ?asar nan Anti?? ban wuce wannan matsayin ba ko da wasa, dan Allah ku barni na hau kawai na tafi gida"

Annur kasancewar bayason fushinta yasa yayi saurin cewa, "shikenan amma dan Allah kiyi ha?uri zuwa gobe lokacin kin gama shiryawa sosai"

Badan taso ba tace masa "to"

Washegari Annur tin wuri ya fita domin yimata siyayyar abunda zata tafi dashi kafin ya dawo tini ta kira Yaaye shi kuwa me jiran kaWan yazo ya tsikara parking yana jiran fitowarta,
Bayan wani Wan lokaci ta fito, tin daga nesa yana iya hango yanda take rintse ido tana cije baki sai gyatsine gyatsine take.

Da ido ya rakata har ta ?araso ta shiga ta zauna ta jingina a jikin kujerar sannan tace, "muje ko?"

Tayarwa yayi suka fara tafiya shiru shiru har suka Wan tafi sosai sannan tace, "barkan ka da safiya ya aiki??"

Murmushin da be shiryawa zuwansa ne ba ya ziyarce shi, cikin sauri ya amsa da lafiya lau Dabar Mata ya ?o?ari?"


Dariya tayi tace, "sunan abun dariya to mungode Allah dai"

Jim kaWan ya?ara cewa, "naga kamar baki da lafiya Madam"

tana dariya tace, "ooh Alatsinanajo inji fulani, kaima nan har ka lura da bana jin daWi? to wallahi ?alau nake Matar yaya na ce ta Sata min rai ita a dole sai na ?ara kwana ko kuma na jira azo a kaini a mota, ni kuma duk ban damu da wannan ba abunda tayi min shi nafi tsana, banaso a tilastani akan abunda ba nice nayi niyya ko kuma nake da ra'ayinsa ba, amma su basa ganewa"

Ta ?arasa maganar tareda jawo tsaki ta ajiye a wajen.

Sosai Yaaye yayi mamakin jin hakan zuwa yanzu ya shaida duk yadda mutum yake tunanin Minoji to ta wuce nan, idan ya fahimta bataso asata yin abunda batayi niyya ba, murmusawa yayi aransa yana cewa, "na ri?e wannan, domin kuwa matakin farko da ya kamata na taka kenan shine gane duk yanayinta da halayenta da abunda take so da wanda bata"

Azahiri kuwa cewa yayi, "jiran ne bakyaso? da kin zauna ai ko kwana biyar ki ?ara yi musu"

Kai tsaye tace, "Allah ya kyauta, kaga rufe min baki nasan ina zuwa ma haka Ummi zatace kowa ma nasan baze goyi baya na ba dan haka kayi min shiru karka ?aramin zafi"

?ar dariya yayi yace, "to Madam"

Tace, "nifa Madam Winnan taka ba ?aunarta nake ba, MINOJI Wasu Suce MINORI shine sunana kaima ka kirani da hakan, wai kai yane sunanka ma??"

Yace, "to madam,, ni sunana Yaaye"

Tace, "Yaaye??"

Yace, "eh"

Kwashewa tayi da dariya tace, "wallahi kanada abun dariya Yaaye sunanka?? To ?an gidan ku fa? nasan suma sunayen nasu irin na Aljassu ne"

Murmushi yayi yace, "mamata Ayiya muke kiranta Sai Yaa-ya sai Yayyi sai Yarinya, amma fa kowa yanada sunansa kawai dai bama faWa ne amma idan kinaso zan gaya miki"

da sauri tace, "aaaaa karka faWamin hakanma kayi ?o?ari ai kawai ka gaishe su"

Yace, "to zan faWa in Allah ya yarda"







*INDO CE..*
[8/1, 5:27 PM] Maryam Muhammad: *=???=???=???SIHIRIN K'AUNA=???=???=???*


=???Shafi Na 11=???



Na INDO CE..


*('ELEGANT ONLINE WRITER'S('*



(Kyauta ne=??)




Bismillahirrahmanirrahim
(3E 'DDG 'D1 -EF 'D1 -JE




Daga haka bata ?ara magana ba har suka iso sannan ta ciro kuWi ta bashi, ko tsayawa ta saurari godiyar da yake mata batayi ba, ta shige gida.

haka ya juya yana murmushin farin ciki, da daddare yayi sallama a gidan, da fara'a suka amsa Ya nemi guri ya zauna kafin yace, "sannun ku?"

Ayiya ce kawai ta amsa Yaa-ya kuwa sai dai binsa da ido take, Yayyi tace, "sannu da dawowa Yaaye"

amsawa yayi da "yauwa"???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? bayan sun gaisa dasu Ayiya Yayyi da Yarinya suka gaishe shi ya amsa cikin sakin fuska.

Ayiya tace, "masha Allahu, Yaaye kafara zama mutum, yafi kyau dai ka rage damuwan nan da tunane tunane gashi har kayi kyaun gani da ka dena tunanin? ai komai tsanani ha?uri shine maganin duk wani ?unci, banason yawan tunanin nan da kake"

gyaWa kai yayi tareda yin ?asa da idonsa.

Yaa-ya kam takasa magana gaba Waya sai takejin hankalinta duk ba'a kwance ba, idan taga Yaaye yadawo gida yana ta farin ciki sai taji duk ta tsargu gashi tarasa wanda zata faWawa damuwarta"

Yana shiga Waki Yayyi ta bishi bayan ta zauna tace, "Yaaye ina budurwar ka??"

Yace, "tana gidansu mana"

Tace, "a unguwar nan take?"

Ya girgiza kai tareda cewa, "aa ba nan take ba"

Yayyi ta gyara zama sannan tace, "to ya sunanta? kuma a ina take?"

Yace, "a gidansu mana, ?azu ma sai da na kaita har gidan da tadawo daga unguwa, Sunanta Minoji"

Yayyi tace, "ikon Allah wannan sunan fa kamar na bararoji??, nifa Yaaye kar kaje ka Wakko mana wadda tafi ?arfinmu ka nemo mana dai-dai mu yadda muke talakawan nan gaskiya karkaje inda za'a wula?anta mu a tozarta mu, dan yanzu a duniyar nan mutum koda kaWan ya taka matsayin da

4 / 16