Sihirin 1 Complete Hausa Novel

Author :  Indo Category :  Love

Chapter   15 / 16

42K to 45K   out of 47.8K words

haiyacinsa ze gazgata miki zan gaya masa inda ?an uwansa suke idan yana bu?ata"

Kafin Ziyada tace wani abu Usman yace, "ina mahaifiyata take?? na tafi nabarsu bansan halin da suke ciki ba, wane irin hali nafaWa haka??, Baiwar Allah ki temaka min ki kaini wajen su zan nemi yafiyarsu ba'a son raina na tafi ba wallahi kuma bazan ?ara tafiya ba zan kasance tareda su"

Minoji tace, "yanzu kadawo nutsuwarka kenan? shikenan to sai ka haWa da matarka waccan da wannan su zama biyu dan Sumayya ta Wauka ka mutu har tafara ha?on mijin wata"

cikin sanyi yace, "wallahi ban mutu ba kawai na tsinci kaina acikin wata rayuwa ne"

sai da tayi masa kwatancen da ze gane sannan ta maida hankalinta kan Ziyada cikin haWe fuska tace, "bani hijab zan tafi"

Ziyada da kanta yagama kullewa tace, "ina zakije?? keda baki da lafiya? nifa har yanzu kallon mahaukaciya nake miki"

Mugun kallonda Minoji tai mata ne yasa ta haWiye surutan nata ta Wakko mata hijab Win, tana zura hijab Win ta fice daga gidan.

Usman yace, "Ziyada maza ki shirya mutafi"

Tace, "zuwa ina?"

Yace, "idan Sata min lokaci zakiyi to ki gayamin zan Wauki ?a?ana mu tafi"

Badan taso ba ta tarkato yaran suka shiga mota shi dama tini ya gama komai sai tafiya.

Yaaye sai da yayi kuka me isar shi sannan yatashi ya fice daga gidan ba shi ya dawo ba sai ?arfe 12:23am sai da yayi mamakin ganin basu rufe gidan ba batareda ya damu da hakan ba ya shiga sai da ya kulle ?ofar sannan ya?arasa ciki yana mamakin surutan da yakeji.

Ayiya tana ganinshi ta mi?e tana murna tace, "Umar? Alhamdulillah yau gashi Usman yadawo gida abun Al'ajabi mun Wauka ma shikenan mun rasa shi amma gashi yau harda iyali"

Kallon su kawai Yaaye yayi ya wuce batareda yayi magana ba.
Lototo Ayiya tayi da baki tana kallonsa cike da mamaki.

Yayyi ce tace, "Yaaye kafi kowa son ganin Yayan mu amma yau muna farin cikin dawowarsa naga kai baka damu ba"

Ayiya tace, "haba Wannan farin ciki yakamata kayi fa kamar ba kaine Yaaye na ba?"

Cikin zubda ?walla yace, "Ayiya ku kun samu naku farin cikin ni kuma kun rabani da nawa, inayin kowane ?o?ari dan naga na faranta muku amma kullum shirin ku shine ku tarwatsa ni kun rabani da ita yanzu kunji daWi kukan da kuke so kuga nayi yanzu kun gani YaaYa ku cigaba da farin ciki nima na tayaku murna"

Kallon kallo Ayiya da YaaYa suka shiga yiwa juna,
Usman yace, "akan me kake magana ne ?ani na?? kodai laifina ne da na tafi na barku, dan Allah ka yafe min Umar nima ba'a son raina nai hakan ba"

Girgiza kai yayi alamar aa sannan yace, "ina magana ne akan Minoji matata, dama sun tsane ta kuma sai da suka rabani da ita batareda tai musu laifin komai ba"

Caraf Ziyada tayi tace, "laa ai itace ta gaya mana inda kuke shine muka zo Wazun ma tana gidan mu Usman ya tsinceta atiti ne batada lafiya ashe ma aljanu ne da ita"

YaaYa tai karaf tace, "kaji kwanan zancen to ba aljanu ne ma da ita ba itace aljanar da kanta"

Zaro ido Sumayya tayi a firgice tace, "kenan Aljana kaje ka Wakko mana Abban Amira???"

Abban Amira kuwa kasa magana yayi saboda abun ya gama kulle masa kai, bazeyi jayayya ba dan kuwa yaga alamu duba da yadda take magana ita kaWai tana bawa kanta amsa ita kaWai dole zata kasance Waya acikin biyu ko aljanar ko me aljanu, amma idan hakane tayaya ze bar Wan uwansa tareda Aljana hakan kuwa yayi???"







*INDO CE*
*=???=???=???SIHIRIN K'AUNA=???=???=???*


=???Shafi Na 30=???



Na INDO CE..


*('ELEGANT ONLINE WRITER'S('*



(Kyauta ne=??)




Bismillahirrahmanirrahim
(3E 'DDG 'D1 -EF 'D1 -JE





=??? Ina mata yan kwalisa , mata masu aji ,KASAITATTUN mata masu malakan zuciyan me gida kuzo ga Ummu Abdullah tazo muku da mayikan gyara jiki, kala kala, da sabulai na gyaran jiki, da turarrekan wuta da na jiki Dana kaya da na tsuguno,da humra kala kala da shi'umar humra, da kayan chemical,irin su liquid soap, perfume,air freshener,, Hair cream,Shampoo etc tana kuyawa tana hada kaya ,domin Neman Karin bayani Sai ku tuntibi wannan lambar 07046858716





Shiru Yaaye yai musu ya wuce Wakinsu.

Washegari tin da sukayi sallar asbah basu kuma bacci ba suka sake dasa hirar yaushe gamo, Ayiya sam ta manta ma da Minoji a duniya bare ta tuna halin da Yaaye yake ciki dan kuwa farin cikin ganin Usman ya rife mata ido.

Yaaye kuwa da yakasa jurar hayaniyarsu sai ya fita waje ya zauna.
yana cikin sa?a da warwara Usman ya iso ya zauna kusa dashi cikin sigar rarrashi yace, "haba Zakin Zakuna Umar Wina me yai zafi haka ne?? na kwana da tunaninka narasa ina ke min ciwo laifina ne ko??"

Kauda kai yayi kafin yace, "aa"
Usman yace, "bakayi farin ciki da zuwana ba ?anina?"
Girgiza kai yayi alamar "aa"
Usman yace, "bakayi farin ciki da zuwana ba??"
hawaye ne suka fara tseren sauka daga idanunsa ya girgiza kai gami da kwanciya ajikin Wan uwan nasa cikin shashshekar kuka yace, "Yaya na idan kana kusa dani jina nake tamkar jariri amma ?addara tasa ka tafi ka barni, silar hakan ne na faWa cikin gararin rayuwa da kana nan da Ayiya da YaaYa basu rabani da matata ba, tunaninta ne yasa nakasa gane kaina amma nafi kowa farin cikin dawowarka Yaya"

Jiki a sanyaye Usman yace, "bana son kukanka kasani Umar ka dena kaji ko? ba dai Allah ya dawo dani ba? to da yardarsa zan dawo maka da matarka ka kwantar da hankalin ka ?anina, amma ina son sanin dalilin su na yin hakan kuma da gaske aljana ce ko kuwa?"

Yaaye yace, "ni ko mecece ina sonta dan nasan bazata cutar dani ba kuma zamu rayu cikin farin ciki bare ma nasan ba aljana bace nidai abunda nasani kawai ita ba mutum ce kamar kowa ba"

jinjina kai Usman yayi sannan yace, "ba komai Umar yanzu ka gaya min ina zanje na sameta?"

Umar yace, "bansani ba nima dawowa nayi na tarar bata nan Yarinya ce ma kawai ta gaya min gaskiya"

Usman yace, "to shikenan da anjima idan hantsi yayi zamuje gidan iyayenta ko? sai muji ko tana can, yanzu katashi muje cikin gida karkayi fushi damu kaji? insha Allah komai yazo ?arshe"

Tashi yayi suka shiga cikin gida YaaYa ta kallesu sama da ?asa sannan tace, "Yaaye? me kakewa kuka ne?"

Kafin yayi magana Abban Amira yace, "bana son jin komai daga gareki Sumayya, Ayiya ku shirya yau zamu koma can gidan dukan mu"

Cikin fara'a Ayiya tace, "Alhamdulillahi m??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ungodewa Allah, nayi farin ciki sosai Allah ya saka da alkairi"

Da amin kawai ya amsa. Anti Ziyada kuwa banda zumSurar baki ba abunda takeyi.

Kamar yadda Usman yace haka suka shirya sukaje gidansu Minoji sai dai suka iske bata can Win haka suka dawo cikin damuwa.

da daddare da Alhaji Usman yazo gidan cikin damuwa Ummi tace, "Usman ba'a san inda Minoji tayi ba, yaron nan Umar yashiga mugun hali ta dalilin wannan al'amari dan Allah ka nema min maslaha da Sarauniyar nan ta rabu da yarinyar nan ta samawa mijinta lafiya, danginsa duk sun tsan-gwame-shi akanta yana cikin damuwa sosai idan nice ma mahaifiyarsa bazan damu da komai ba wanda ya wuce damuwa da halin da yake ciki, muyi masa adalci dan Allah"

Alhaji Usman yayi dariya kafin yace, "shiririta kenan ai dukansu suna gidana, su can dangin mijin Minojin sunce aljana ce sun koreta shi kuma Yarima Noor ya Wauketa ya jefar acan wani guri daban har Allah ya dawo da Sarauniya Mariaman ta Wakko ta daga gidan yayan mijin suka tare a gidana, kinsan ma abunda ze baki dariya? wai itama sarauniyar gurin fakewa tasamu sakamakon suna son aurar da ita kuma sun samu saSani da Baban Yariman gobe wato Yarima Umar shine fa ake ta fushi aka baro can akazo nan aka tare"

Ummi ta rausayar da kai sannan tace, "Allah sarki gwara itama tayi auren nidai tabar Minoji tarayu da mijinta lafiya, dan Allah ka san yadda zakai ka sama min maslaha daga garesu"

yace, "amma fa Mariama tana da gardama akan abunda ba ita tasa kanta ba, dan haka zefi sau?i a nemi mahaifinta"

Ummi tace, "duk ma yadda za'ai ayi"

Minoji tana zaune tareda Umman Sultana suna ?ar hira Alhaji Usman ya shigo da sallama, bayan ya zauna yace, "Minojin ce ko Mero??"

Dariya tayi sannan tace, "kazo mana da tsaraba ne? Mariama ta koma masarautar Gabas gurin Yarima Ubaid"

ya jinjina kai kafin yace, "yaushe zata dawo?"

Minoji tace, "bata gaya min ba amma bazata dawo da wuri ba kuma tace kar na faWawa kowa dan dai kaine kawai na gaya maka"

Yace, "to shikenan"

A Sangaren su Ayiya kuwa cikin Woki suka shirya komai na tafiya tareda sa ran sun rabu da ala?a?ai.

YaaYa ce ta kalleshi tace, "ya baka shiryawa Yaaye?"
Yace, "nan shine gidan mahaifina anan zan cigaba da zama da matata idan ta dawo"

YaaYa ta saki murmushin gaiya dan kuwa gani take kamar Minoji ta tafi kenan acewarta aljani idan yaga guri ya gagare shi baya iya dawowa bare yadda taga ba da ?afarta ta fita faga gidan ba.
Sai da tazo daf dashi yadda shi kaWai ne ze ji abunda tace sannan tafara magana, "uhm Allah sarki Yaaye gaskiya tsarin naka ya burgeni amma tinda yayanka yanada kuWi kuma yana sonka nasan ba abunda bazeyi maka ba ka biyo mu kafin ya gyara mana gidan namu mana?, lokacin mun ?ara fuskantar juna sai aure kawai, karfa ka zata dan yadawo zan fasa sonka ne, a'a na riga nayi nisa banajin kira ka manta da Minoji kawai muyi sabuwar rayuwa"

murmushin takaici yayi sannan yace, "ni ba irin ragon namijin nan me dogara da abun wani bane, koda dukiyar mahaifi na ce bazan damu da ita ba zanyi ?o?arin kafa kaina ne zan gyara gidan da kaina kuma zan zage nayi aiki tu?uru na nemi halak Wina, dama can haka nake kuma zan Wora saboda matata Minoji, ya rage naki ko ki ha?ura ko karki ha?ura hukunci na ya yanku"

Daga haka yatashi yabata guri.
Babu yadda basuyi dashi akan ya bi su ba ya?i.
Yamma tanayi suka tarkata suka bar gidan yarage saura shi kaWai.

misalin ?arfe 09:24 yaji ana ?wan?wasa ?ofa kamar baze tashi ba sai kuma ya tashi tareda tunanin waye?,
sallama Alhaji Usman yayi masa bayan sun gaisa yace, "ka gane ni kuwa? nine Usman yayan Minoji, tana gidana kuma gata nan na dawo da ita duk da cewar naji abunda yafaru da ita, to amma kasancewar nasan kai tsakaninka da Allah kake sonta baze yuwu nayi muku shamaki ba amma banda haka da na rabaka da ita tinda danginka basa ?aunarta, mu anamu Sangaren hakan ba damuwa bace tinda bata cuta bata cutarwa amma ta dalilinka dole musan abunyi, karka damu komai yakusa zuwa ?arshe da yardar Allah zata dawo daidai insha Allah"

Cike da farin ciki da murna Yaaye ya amsa da "to Yaya Allah yasaka da alkairi nagode nagode Allah yayi maka alfarma fiye da yadda kayimin Yayanmu"

Alhaji Usman ya murmusa gami da cewa, "muke da godiya ina fatan dai bazamu tsinci wata matsalar ba agaba? ri?eta da gaskiya da amana Wari bisa Wari akan ta daa itace babbar godiyar da zakai mana"

Umar yace, "Insha Allahu ai kunfi ?arfin komai a gurina da ikon Allah babu wata matsala Allah yasaka da alkairi"

Alhaji Usman yace, "ameen, tana cikin mota kasanta akwai son bacci tace idan an buWe gidan ta fito kabiyoni sai ku dawo tare"

da "to" ya amsa sannan suka fara tafiya.
koda suka isa wajen motar sai da Alhaji Usman yasha fama da ita akan ta fito sai da yayi da gaske sannan ya shawo kanta ya dam?a ta a hannun Yaaye"

da War War ta shiga gidan duk a tunaninta zatayi karo da su Ayiya kamar yadda ta saba sai dai taga ba hakan bane, kallonsa tayi tareda cewa, "gida shiru"
Yace, "muje Waki kiyi bacci Sar?a me rikicin gangan?"

Gaba tayi ta rigashi shiga tana cewa, "kai ai kafi sar?ar rikici"

Murmushi yayi sannan yabi bayanta yana haska mata, ?arewa Wakin kallo tayi tsaff sannan ta kalleshi tace, "Ayiya fa?"
Ya rausayar da kai tareda cewa, "da ita kaWai kika damu? kin manta bawan Allahn da kika bari yana kukan rashin ki?"

Ido ta zuba masa kafin ta faWa jikinsa ta ?an?ame shi ta fashe da kuka.
Rungume ta yayi yana dariya yace, "zaki bi Yaya Usman ne??"
da sauri ta no?e kafaWa gami da cewa, "a'a"
Yace, "to kukan fa?"
Tace, "nasha wahala sosai haka sukaita azabtar dani ranar, kuma na tafi inata tunaninka banason rabuwa dakai amma sai sun rabani dakai"

Ya murmusa tareda cewa, "bazamu rabu ba da izinin Allah shine ya haWamu kuma shi ze rabamu ki kwantar da hankalinki, Ayiya da YaaYan ma duka basa gidan sun koma gidan Yayana Usman yanzu mu kaWai ne"

Ya?arasa maganar tareda goge mata hawayen.
yasan idan tana kuka ba'a rarrashinta ko yace tayi shiru ma bazatai ba babu rarrashin da zeyi mata ta dena dan haka ya gyara mata zama ajikinsa, sai da tayi me isarta sannan ta zame daga jikinsa ta kwanta daga haka bacci yai awon gaba da ita.

bayan kwana biyar.

Tana kwance a saman gado
Umar yana zaune a gefenta suna hira yake cewa, "Nazo da kyakkyawan albishir na tarar bakya nan"
Tace, "yanzu inajinka"
Yace, "nasamu aiki a kasuwar tiles"
fuskarta Wauke da murmshi, "tace yayi kyau Mijina Allah ya taya maka ya sanya albarka acikin lamarinka, nayi farin ciki sosai"

Yace, "nagode"
Bata ce komai ba har bayan wani Wan lokaci sannan tace, "kamar tafiyar doki nakeji fa"

Yace, "doki kuma??"
Tace, "kwarai kuma ina ganin Yarima ne, gurina yazo nasan kuma kanka ze hauro ka zauna cikin shiri"

Cikin zaro ido yace, "me???? wai da gaske???"
Dariya ta shiga tuntsira masa yayin da ya shiga yimata magiya akan ta hanashi kafin ma ya farga tini aikin gama ya gama.

a ta?aice yace, "Assalamu alaiki"
Ta amsa da "wa'alaikas-salam, Sarauniya tace min baka kusa ya akai na ganka?"

Yace, "ba wannan ba yanzu tana ina? ina sauri ne"

Tace, "kasan dai duk nisan da zatai bazata wuce gurin Sarki Ubaid ba, amma idan kasan cutar da ita zakayi karkaje kuma karkace nice na gaya maka"

Yace, "bakisan wacece ita agareni ba shiyasa kike irin wannan tunanin, ni zan wuce sai anjima"

Kafin tace wani abu tini ya wuce ya barta da sakakken baki.
Dogon numfashi Umar ya sauke sannan yace, "Allah ya fitar dani na Wauka sai nakusa mutuwa"

Dariya tayi gami da cewa, "aa amma ka shirya ciwon jiki dan kuwa zakayi laushi saboda zafinsa, Idan da nice ma bazan iya magana kamar yadda kayi ba"

yace, "ba komai nidai tinda na tsira"
Tace, "matsoraci, aikuwa nagaya masa inda take yanzu da yaje ze dawo da ita gida nikam haka nake so"

yace, "amma dai baki kyauta ba kin kasa ri?e mata amana"
Tace, "oho ai nace kar ta tafi tabarni ta?i"







*INDO CE..*
*=???=???=???SIHIRIN K'AUNA=???=???=???*


=???Shafi Na 31=???



Na INDO CE..


*('ELEGANT ONLINE WRITER'S('*



(Kyauta ne=??)




Bismillahirrahmanirrahim
(3E 'DDG 'D1 -EF 'D1 -JE





=??? Ina mata yan kwalisa , mata masu aji ,KASAITATTUN mata masu malakan zuciyan me gida kuzo ga Ummu Abdullah tazo muku da mayikan gyara jiki, kala kala, da sabulai na gyaran jiki, da turarrekan wuta da na jiki Dana kaya da na tsuguno,da humra kala kala da shi'umar humra, da kayan chemical,irin su liquid soap, perfume,air freshener,, Hair cream,Shampoo etc tana kuyawa tana hada kaya ,domin Neman Karin bayani Sai ku tuntibi wannan lambar 07046858716





Mariama. ko kaWan batayi tsammanin ganin Yarima ba sai gashi katsidim.
Cikin kaWuwa ta shiga jera masa tambaya "daga ina kake?? meyesa kazo inda nake? waye ya gaya maka ina nan??"

Yace, "yanzu ba wannan ba, meyesa kika tawo nan?"
A Wan hasale tace, "amsa ta nake bu?ata"
Yace, "nima ai haka amma tinda baki da ita nima bani da. Tin a lokacin wanda kika sa tsarona suka so sakina saboda sun-san nine baban Yarima amma nace su barshi dan ki samu nutsuwa"

cikin shakka tace, "nakasa gane me kake nufi dani yanzu kuma mene ya kawoka gurina?"

Yace, "ina son ki bini na maidake masarauta ta lumana ba a WaWWaure ba"
Kai tsaye tace, "bazaka iya ba"
Yace, "zan jarraba kuwa"

Shugowar Yarima Ubaid ne yasa tafasa magana ta bishi da ido.
cikin salon bada umarni yace, "ki shirya zamuje Masarauta hakan umarnin Sarki Sulaiman ne"

?ara ware ido tayi akansa tareda cewa, "me?? ken..." katseta yayi da cewa, "banason jin komai ki bi umarni kawai"

Maida kallonta tayi kan Yarima tana masa kallon tuhuma. ya Wan murmusa sannan yabi bayan Yarima Ubaid.
Cike da takaici ta wuce ciki batareda ta kula kowa ba.

Koda suka koma masarauta bata saurari kowa ba ta wuce turaka ta kulle.
Washe-gari. Gimbiya Malika ce ta buga mata ?ofa tana buWewa Malika tace, "Sarki yana kira a fadarsa"

Batayi magana ba ta cigaba da abunda takeyi sai da tagama shauni sannan ta nufi fadar duk angama haWuwa ita kaWai ake jira .
Bayan wani lokaci Sarki yace, "kinada abun cewa ne sarauniya"

Tace, "aa"
Yace, "to mu muna dashi game da wannan yarinyar Minoji da kile tareda ita, munaso ki barta kwata kwata ki dawo ki rungumi karagarki"

Da sauri tace, "da kanka kake cewa na rabu da ita? to meyesa?ko na taSa cutar da ita ne?"
yace, "ba batun cutarwa bane, kema aurenki zaki zo ki runguma sannan ki maida hankali kan sarautarki"

Tace, "a'ah ina baze yuwu ba, babu ko Waya da na zaSa Minoji kawai itace zaSina"

Yace, "ban kai ga baki zaSi ba tukunna amma yanzu zan baki, ki dawo cikinmu ki barta ki cigaba da gudanar da mulki ko kuma ki bar mulkin duka ki ajiye"

Tace, "ba haka ba Sarki, idan na bar mulki wa zaku Wora? bazan amince wani daban ya hau karagata ba sannan kuma bazan bar Minoji ba ina tareda ita"

Sarauniya Blikisu ce ta shiga zancen da

15 / 16