Sihirin 1 Complete Hausa Novel

Author :  Indo Category :  Love

Chapter   13 / 16

36K to 39K   out of 47.8K words

bayyana a tareda ita amma a wani lokacin tana dawowa dai-dai, da mahaifiyarka zata gane da ta bar mu mun cigaba da gudanar da rayuwarmu inason Minoji ita kuma tana sonka zefi sau?i ta zuba mana ido kawai, ni ba Aljana ce me cutarwa ba idan da zan cutar dasu da abunda sukayi wa Gimbiyata ma kaWai ya isa na tsaurara mataki akansu amma bazan iya hakan ba, amma zan barka da ita indai kana sonta da gaske kuma tsakani ga Allah ka cigaba da kulawa da ita kamar da ko fiye da haka idan kuma naga kuskure zaka neme ta ka rasa kuma bazaka ganta ba"

cikin sanyi ya jinjina kai ya kasa magana sai dai ido kawai tunane tunane barkatai suke masa yawo.

Zama tayi a kusa dashi kafin tace, "kayi tunani ka yanke hukunci wa rayuwarka da matarka bazance komai a kai ba har sai abunda ka zaSawa kanka"

tinda tayi shiru bata ?ara cewa uffan ba shima haka dan kuwa ya rasa bakin magana"

Washegari Yayyi ta tashi cikin lafiya da kwanciyar hankali kamar batayi ba.
YaaYa ce ta kalli Ayiya tace, "nifa nakasa gane komai yanzu ana nufin kenan haka zamu zuba ido??? nifa gaskiya nagaji da ganin ta a gidan nan"

Ayiya tace, "haba YaaYa kema kinsan ai komai yazo ?arshe tinda gashi ta bayyana kanta ya gane ba mutum Win bace ai kinga tinda yana da hankali baze zauma da Aljana ba, wai ni zata yiwa barazana to nafi ?arfinta Allah ya fita azzaluma, Bari ma Yaayen yazo kiji ai dole ma yace ya ha?ura"

da Yamma kuwa yana dawowa suna gaisawa YaaYa tace, "ya maganar da kukai da Ayiya Yaaye ya kamata fa yanzu ace an wuce wannan matsayar gaskiya aita mai-maita abu Waya?"

Duk da ya fahimci me take nufi amma sai yayi kamar be gane ba yace, "kamar ya kenan wace magana?"

Ayiya tace, "Allah sarku ruWanin da ya shiga ma yasa ya manta, magana take akan batun sakin Minoji da nace kayi, yanzu ma ka gani da idonka abunda muke nusar da kai ka kasa fahimta yanzu ai rabuwa da ita wajibi ne gareka dan mutum baya taraiya da Aljan"

Girgiza kai yayi kafin yace, "Ayiya kimin kyakkyawar fahimta dan Allah, a ganina tinda har Minoji ta yarda dani kuma ta zauna dani a irin wannan halin bayan beyi dai-dai da rayuwarta ba to gaskiya da gaske take, ni kuwa butulun ina ne da zan sake ta kawai saboda tata ?addarar? ni itace tawa ?addarar ita kuma Mariama itace ta-ta itama Mariaman tana da tata ?addarar dan haka kawai na zaSi kasancewa tareda ita har ?arshen rayuwata , kamar yadda nayi wa danginta kyakkyawan al?awari to insha Allahu sai na cika shi, kuyi ha?uri da jin hakan daga gareni amma ko yanzu kuka korar min mata to nima bazaku ganni ba zan bita duk inda tayi koda bazan ganta ba zanyi neman ta har lokacin da rayuwata zata ?are"

Ayiya da YaaYa har haWa baki suke wajen cewa, "Innalillahi'wa'inna'ilaihirrajiun"

Ayiya tace, "Yaaye??? haka ka zama???, kodan bazanyi mamaki ba dan kuwa aljani ba wasa bane, Allahumma ajirni Allah gani gareka yau an wayi gari Wana yayi gamo da aljana Allah ka shiga tsakanin nagari da mugu, Yaaye yanzu har ka manta suwaye mu a gareka?? yanzu aljanar tafiye maka mu kenan??"

girgiza kai yayi sannan yace, "bata fi min ku ba amma dai kowa matsayinsa daban ke mahaifiyata ce kowa yasani YaaYa kuma matar Yaya na ce ita kuma Minoji matata, da idan kukace mata aljana banajindaWi amma yanzu banida damuwa tinda na tabbatar dan kun kirata da haka bazanji komai ba, YaaYa ki nema min sau?i kema ki nemawa kanki ki nemi wani ki aura amma ba ni ba"

Yana rife baki tace, "wallahi bazan auri kowa ba kai nake so indai ba kai ba sai dai mijina kuma kasani be zama lallai idan yana raye ba dan haka ka shirya wallahi ko da tsiya sai na aureka sai dai aljanar ta kasheni idan zata iya"

tayi maganar tana kuka kasidin.

Zeyi magana yaji muryar Minoji tana kiransa
"Farook!!!"
Tashi yayi ya nufi Wakin cikin sauri sauri da sallama ya shiga ta amsa kafin tace, " surutu kake ta yi ka barni ni kaWai"

Murmushi yayi gami da cewa, "ai gani na dawo meke faruwa Aljanata?"

Dariya tayi sosai kafin tace, "Wannan ba takan bace ta Yarima Yusuf ce"

Da Wan mamaki yace, "bayan Yarima me suna na akwai wani kenan?? kenan kema kinada aure??"

Girgiza kai tayi alamar "aa" a ?asaice tace, "banida aure amma zanyi Yarima Yusuf shi nake so shima Yaya na ne kamar yadda nake da Yarima shima hakan ne bambancin kawai baya nuna min izza kamar Yarima na rasa menene ta?amar sa akaina kuma ba wanda yake iya dakatar dashi"

Gyara zama Yaaye yayi sannan yace, "uhum?? ina jinki nima yau abani labarin masarauta a matsayina na talaka hakan zeyi min daWi sosai"

Murmushi tayi tareda cewa, "banida surutu fa kamar matarka"

Yace, "kamar ya kenan??"

kamar bazatayi magana ba sai kuma tace, "ina nufin matarka ta fini surutu ni bana iya doguwar magana kamar bazan iya baka labarin ba"

Yace, "ohh kenan kece kike sawa ina magana tayi min shiru ko?? sai naita magana tayi banza kuma tanaji sai dai tayi murmishi koda maganar ma ta kuka ce"

Dariya Sarauniya Mariama tayi kafin tace, "kana da abun dariya sosai, ni yanzu na kusa komawa zanje naga wane aikin Yarima yake min nasan ba'a rabashi da shiga shirgina"

Yaaye yace, "ikon Allah abun mamaki to amma gaskiya zaki bani labarin"

jinjina kai tayi tace, "be zama lallai ba zefi ka maida hankali kan neman Wan uwanka dan yanzu yana kusa da kai ba kamar da ba"

Da sauri yace, "da Win ina ya tafi?"

Tace, "tafiyar ba ta???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?shi bace, Sihiri akai masa kuma saboda dukiyar mahaifin ku"

gyaWa kai yayi cikin sanyi yace, "Allah ya baiyana min shi ko dan jarabar matarsa"

Dariya kawai tayi ba tareda tayi magana ba ta kwantar da kanta akan kafaWar sa sannan tace, "zan koma masaurauta nafi so na dam?a maka ita a hannun ka shiyasa na kira ka"


Daga haka taja dogon numfashi ta sauke gami da lumshe ido, hannu tasa ta rungumeshi sosai cikin sanyi tace, "Yaaye? kana tareda ni har yanzu??"

Ido ya zubawa fuskarta cike da tausayawa yace, "Minoji idan ban kasance tareda ke ba gurin wa zan fake? ki kwantar da hankalin ki komai ya wuce"
...

Murmushi tayi tareda cewa, "ina sonka abun alfahari na"

Sassanyan murmushi ne ya baiyana akan fuskarsa ya sauke ajiyar zuciya, yanzu ya tabbatar Minojin sa ce ta dawo.


Haka rayuwa ta cigaba da tafiya kowa yana aiwatar da abunda yake gabansa.



Kallonta yayi cikin sanyi yace, "mun kammala aikin ginin fa amma yau naje kasuwar tiles kuma naga ana samun aiki sosai idan na koma gobe zanyi ?o?ari na nema aikin ko zasu yarda su temaka min"

Murmushi ta sakar masa tareda faWih, "Allah ya baka nasara Hubby kayi da gaskiya kuma da ya?ini, kai amintaccen mutum ne Allah ze nuna maka wanda ze temake ka, inajin daWi gami da yabawa da irin ?o?arin ka ina fatan Allah ya bani jajirtattun ?a?a kamar kai"

Yana murmushi yace, "amin ina alfahari dake matata maman ?a?a na"

Murmushi kawai tayi sai kallonsa da take sanin ba lallai ta?ara magana ba yasa yayi shiru daga baya ma sai ya tashi ya Wauro Alwala ya shimfiWa sallaya ya zauna ya fara karanta Al?ur'ani me girma"

















*INDO CE..*
[8/1, 5:27 PM] Maryam Muhammad: *=???=???=???SIHIRIN K'AUNA=???=???=???*


=???Shafi Na 27=???



Na INDO CE..


*('ELEGANT ONLINE WRITER'S('*



(Kyauta ne=??)




Bismillahirrahmanirrahim
(3E 'DDG 'D1 -EF 'D1 -JE





=??? Ina mata yan kwalisa , mata masu aji ,KASAITATTUN mata masu malakan zuciyan me gida kuzo ga Ummu Abdullah tazo muku da mayikan gyara jiki, kala kala, da sabulai na gyaran jiki, da turarrekan wuta da na jiki Dana kaya da na tsuguno,da humra kala kala da shi'umar humra, da kayan chemical,irin su liquid soap, perfume,air freshener,, Hair cream,Shampoo etc tana kuyawa tana hada kaya ,domin Neman Karin bayani Sai ku tuntibi wannan lambar 07046858716




har ya kammala yayi addu'a tana zaune sai lumshe ido take tana murmushi da alamu karatun yanayi mata daWi sosai.

da murmushi akan fuskarsa yace, "Mino? ?ar uwarki tace min Yayana yana nan nayi zaton fa ya mutu"

Murmusawa tayi ba tareda ta kalleshi ba tace, "haka ne be mutu ba amma banso ta gaya maka ba dan zaka iya tashin hankalin ka akan sai ka nemeshi na?i gaya maka ne tin farko saboda wannan dalilin"

Yayi ?ar dariya kafin yace, "amma kinsani kika barni cikin ruWani? nayi farin ciki sosai da ta sanar min kuma na gode mata godiya ta musamman gareta amma banda ke"

MurguWe baki tayi tace, "ba komi dan ka gode mata Win, idan zakayi aure na biyu ma sai ka aureta, duk ranar ma da na?ara ganin ka zauna ta baka wani labari sai na yanke maka harshe"

Dariya sosai yayi ba tareda ya dena ba yace, "ashe ana kishi na nikam Wan baiwa ne haihuwar sa'a, amma banda abunki ya zanyi da sarauniya guda ai sai manya ke Win ma kawai Allah ne yabani badan na isa ba, amma shikenan idan kika yanke min harshe sai na dena magana shikenan fa an wuce gurin"

Tace, "baze yuwu ba fa kenan na dena jin muryar ka? aa gara na cire maka ha?ora biyun nan na gaba"

Ya?ara tintsirewa da dariya yace, "na daWe fa banyi dariya irin yau ba, kin bani dariya sosai, to na yarda ita bazata bani labarin ba amma ke zaki bani"

Dariya tayi kafin tayi ?wafa alamar yaro besan wuta ba sai ya taka, cikin salonta na ko in kula tace, "zaka iya?"

Yace, "me fa?"

Tace, "ganin abunda zan nuna maka, labari da baki abu ne me wahala a gurin mu dagani har itan amma idan kana so zata buWe maka ido zaka ga har Yariman ta da kuma Yarima Yusuf harma da Sarauniya Bilkisu da Sarki Sulaiman, idan kanaso ma har su kuyanga Kilbi da Yarima Umar ya turo suka takurawa Yayyi su ma zaka gansu"

Da sauri ya katseta da cewa, "salamun alaiki, ina zaune ?alau bazaki nuna min aljanu ba na kasa bacci haka siddan aa na yafe iya ke kaWai ma kin isheni rayuwa"

Ta kwashe da dariya harda tafa hannuwa, lokaci Waya kuma ta dena ta haWe rai sannan tace, "ba kana so ba? ai kuwa dole zaka ga masarauta, kasa idonka cikin nawa ko kuma nasa akaika"

marai-raicewa yayi yana cewa, "kiyi ha?uri na dena Allah Waya ina jin tsoro"

Tace, "kenan baka yarda dani ba?? kai fa mijina ne bazan iya cutar da kai ba kuma a suffar mutane zaka gansu kamar ni ba'a wata halitta ta daban ba"

Yace, "na yarda amma kawai ki faWamin da bakin ki"

Ta saki murmushi gami da cewa, "to naji bari na baka labarin Wabi'un wasu a ciki"

Gyara zama yayi tareda cewa, "ina sauraron ki"

Tace, "ooh ikon Allah baya ?arewa ga kai ga son labari ga kuma tsoro"

Ya murmusa yace, "idan fa bazaki gayamin ba zanyi fushi"

Tace, "ka tsaya mana to, yanzu ka zaSi takan waye zamu fara?"

Da sauri yace, "me suna na Yarima Umar"

Tace, "izza jinkai ta?ama wannan manyan abubuwa ne daga cikin halayensa, ya kasance soja kuma shugaban su, be fiye magana ba sai tayi tsauri ko mahaifiyarsa baya Waga harshe yayi mata magana da sunan fira ko yana bu?atar wani abun, da yace ayi masa da bakinsa gara yayi da kansa, zafin jini yana daga cikin halittar sa indai ya kusanci inda Sarauniya Mariama take sai ta faWi a sume, manyan mu sun san meye nasabar abun amma har yanzu dani dashi da ita da duk sauran yara bamusan menene fa'idar hakan ba, yakan Waga harshensa akanta yayi magana saboda yasan babu wani alamu da ze nuna mata tayi abunda yaso har sai ya magantu batajin maganarsa kuma batayi masa biyayya saboda tanajin izzar karagarta Waukarsa take tamkar bawan ta hakan yasa shi kuma yake karya dokar masarautar ta a duk lokacin da yaso gashi ya gagare ta, mahaifiyarta bata son laifinsa musamman akanta duk abunda zeyi mata dai-dai ne a gurin Sarauniya Bilkisu, Debi sunan da muke kiran mahaifiyarsa kenan, abunda ze baka takaici ko mamaki ita Win baiwa ce a masarautar su Sarauniya Bilkisu amma Yarima yake da wannan zarrar, ?anin Sarki Sulaiman shi ya aureta ta zama babbar giwa a masarauta ta sanadin Yarima Umar sai ta ?ara zama cikakkiyar sarauniya a cikin gidan sai dai fa ko da yatsa bata isa ta Wagawa Wanta da sunan ita ta haifeshi ba sai Sarauniya Bilkisu tayi hukunci akai, Mahaifiyar Yarima Yusuf da Debi sai Sarakan gidan Sarki Sulaiman da Yayyen sa da ?annensa sune wanda Suke marawa Sarauniya Mariama baya, sai dai izzar Sarauniya Bilkisu ta wuce gaban kwatance, shiyasa zaka ga tsantsan izza da jin mulki a tattare da Sarauniya Mariama abunne ya haWe mata biyu ga mahaifinta ga mahaifiyarta kowa yanaji da tashi, uhm ba ma wannan ne abun mamakin ba ta yadda akai Yerima yakeda wannan muguwar izzar duk da cewar ta Sangare Waya ne yake da sarauta"


Yaaye yace, "abun ya tsuma ni sosai fa, to ya akai hakan naso naji fa"

Tace, "ai bance ka katse ni ba ko? ko nace maka nazo ?arshe ne?"

Yace, "aa inajinki to"

Ta cigaba da cewa, "dalilin fa kawai ya taso ne a hannun Sarauniya Bilkisu rainonta ne, baya ga haka shima shugaba ne ga wasu sai kuma ta Sangaren mahaifinsa, Debi kuwa tana da matu?ar ha?uri ba fitina, sai kuma Yarima Yusuf, bawan Allah kenan Waukar kansa yake dashi da talakawa duk Waya yana da fara'a sai dai kuma tashi motsawa take idan tazo har sai yaso yafi Yarima izza"

Yaaye yace, "to kenan a cikin su waye magajin karagar?? kuma shi sarki Sulaiman bashida Wa namiji kenan??"

Tace, "Mariama duk itace cikamakin amsar tambayarka itace ta gaje karagar haka kuma itace babbar ?arsa duk ?annen ta kuma mata ne sai autan su Wan ?aramin shine namiji amma wanda yayi nasarar aurenta yafi kowa kusanci da mulkin shima yanada iko akai, kuma ita Yusuf take so sai dai banajin zata aureshi"

Yaaye yace, "to meyesa?"

Tace, "tambaya tambaya tambaya nagaji, mu koma labarin rayuwar mu yafi mana, mu ?yale labarin masarautar nan idan bazamu dena ba sai munfi kwanaki munayi be ?are ba"

Ya numfasa kafin yace, "to hakan ma nagode"

rintse ido tayi ta buWe sannan tace, "jikina ba daWi da kyar idan Sarauniya bata faWa hannun Yarima ba"

Yaaye yace, "ke kaWai yanzu kikace nabar zancen kuma kin cigaba idan kuma na ?ara buWe kunnuwa na to?"


Tace, "kai oo cigaba da tunanin da kakeyi nima nayi nawa karma ka ?arayin surutu naji banason hayaniya kuma"

Ya murmusa sannan yace, "na dena"


Ayiya
rausayar da kai tayi tace, "YaaYa?? kullum daga wannan sai wannan Yaaye yakasa juyuwa abun ?ara cin tira yake"

YaaYa tace, "hmm ban gajiya ba har yanzu wallahi sai naga ?arshen rainin hankali a gidan nan indai aljanu ne zanyi maganin su, duk adadin shekarun da na Sata ina ha?on Yaaye rana tsaka wata tayimin tafiyar ruwa dashi, baze yuwu ba dole ne mu sauya taku dan kawo ?arshenta"











*INDO CE..*
[8/1, 5:27 PM] Maryam Muhammad: *=???=???=???SIHIRIN K'AUNA=???=???=???*


=???Shafi Na 28=???



Na INDO CE..


*('ELEGANT ONLINE WRITER'S('*



(Kyauta ne=??)




Bismillahirrahmanirrahim
(3E 'DDG 'D1 -EF 'D1 -JE





=??? Ina mata yan kwalisa , mata masu aji ,KASAITATTUN mata masu malakan zuciyan me gida kuzo ga Ummu Abdullah tazo muku da mayikan gyara jiki, kala kala, da sabulai na gyaran jiki, da turarrekan wuta da na jiki Dana kaya da na tsuguno,da humra kala kala da shi'umar humra, da kayan chemical,irin su liquid soap, perfume,air freshener,, Hair cream,Shampoo etc tana kuyawa tana hada kaya ,domin Neman Karin bayani Sai ku tuntibi wannan lambar 07046858716



Ayiya tace, "to yanzu me kike ganin za'ayi??"

Tace, "Babar Fiddau ta gaya mana akwai wata me maganin aljanu to ita zamu Wakko "

Ayiya tace, "ai bamu da kuWin da zamu biyata tazo"

YaaYa tace, "a gurinsa zamu nema har ma sai mun tsaya jira? ko kuma mu karSi bashi dolen sa ya biya"

Ayiya tace, "yauwa gara dai mu karSi bashin ze fi, yanzu yaushe zakije ??"

YaaYa tace, "zuwa yamma zan karSi bashin kuWin washegari muje"

Da haka suka ?ar?are shawarar sannan suka cigaba da

13 / 16