RAINA KAMA Tagwaye Cikin Gidan Fitina by Bilyn Abdull

Author :  Bilyn Abdull Category :  Romance

Chapter   2 / 36

3K to 6K   out of 107K words

idonsa abinda ke faruwa).
Dady ya k'araso da sauri yana fad'in “Inna miya farune haka da kuka? Keda waye??.
“wannan shed'aniyar yarinyar mana? tayi maganar tana nunani “waini yarinyar nan zataima d'ibar albarka saboda uwarsu kullum tana aibantani a gurinsu, shiyyasa duk sun rainani....?
Baki bud'e nake kallon innaro da sherinta. wlhy wannan tsohuwar bazataga Annabi ba........
Maganar Dady ta dawo dani daga mamakin innaro. Yace, “Munaya ce ko Munubiya? miya farune keda inna??.
Dady yanada sauk'i, ba kamar Abbanmu da baba k'arami ba sun fishi zafi.
Nace, “dady Munaya ce. wlhy babu abinda namata, kawaifa daga shigowarta duk muka gaidata, shine kawai ta hau zagina wai ban gaidata da k'yauba.......?
“amma ai gaisuwar rashin tarbiya kikai mata?. ‘cewar Aunty khaleesa?.
Dady zaiyi magana Aunty Ramlah tace, “wlhy Dady ba haka bane, duk abinda yafaru akan idona yafaru, dan nafito zan d'iba ruwa a fanfo?.
Dakuwa Innaro ta mata, “kinci uwarki hadiza, kema ashe munafukace ban saniba, to ko hadizar ta haifama Ai'sha ne ke??.
Fakar idon Dady aunty Ramlah tayi ta dallama innaro harara, sannan tace, “yo daga fad'ar gaskiya, nidai wlhy Dady abinda nagani nakuma ji kenan?.
Girgiza kai Dady yayi, sannan yace, “kiyi hak'uri Inna, Munaya tayi kuskure amma bazata sakeba. Munaya zoki bata hak'uri?.
Ban musaba nazo har gabanta nace tayi hak'uri, bata amsamin ba, saima hararata datayi kawai. nima saina bar wajen nakoma kan wankina.
Dady Yakama hannun innaro suka shiga falonsa, matan gidanmu duk suka bar wajen, basuso wasan yak'are a nanba, sunso ace cin mutuncin innaro yasauka har kan innarmu.
Innarmu dake tsaye daga k'ofar falonta tanajiyo abinda ke faruwa dukda katanga ta shiga tsakiya, ta girgiza kai kawai tana komawa ciki da fad'in ALLAH ya k'yauta.

Ina wanki ina zubda hawaye, sosai raina ya sosu yau akan abinda Innaro tamin, dukda bawai yaune karon farko da hakan ya faruba, sai dai na yau yamin zafi ainun, har inaji natsani zaman gidanmu, a fili na furta ALLAH kabamu miji muyi aurenmu mubar gidannan?.
Munubiya dabansan tazo wajenba naji ta amsa da Amin sweetheart, wlhy koni yanzu addu'ar danake mana kenan, sai dai banason mutafi mubar innarmu a wannan halin dasu Aryaan?.
“hakane Munu..., karki damu, insha ALLAH munayin aure d'auke innarmu zamuyi ko Abbah ya yarda kobai yardaba wlhy!!?. ‘ta k'arashe maganar a harzuk'e?.
Murmushi Munubiya tayi, dan tasan ran 'yar uwar tata yakai k'ololuwar 6aci.
Har muka gama wankin innaro na gidan bata tafiba, bamusan uwarmi takeyiba. dayake girkin gwaggon Haleema nema ranar. ina tsaye a bayan flowers d'in d'akinmu ina goge glass d'in windows naga Abdul yafito d'aukeda tire an jera sabbin kuloli akai, nasan Abbanmu baya gari, dan haka nace, “Abdul wazaka kaima abinci haka??.
Yace, “Aunty zan kaima innaro tana falon dady?.
Kai na jinjina masa kawai nace jeka, cigaba nayi da aikina ina fad'in “shidai munafurci ai dodone, maishi yakeci?.
Koda na koma ciki sai nake bama Munubiya labari, innarmu dake bayanmu bamu saniba tace, “to ina ruwankine wai Munaya?, nifa banason gutsiri tsoma wlhy, wai sai yaushene zaku daina jamin fitina a gidanan ne??.
A sanyaye mukace kiyi hak'uri innarmu?.
Batace komaiba tashige d'akinta, muduka da kallon tausayi muka bita, dukda tasan ita ake tauyema hak'i amma bata ta6a nuna itace mara laifi, kullum ta amince itace a k'asan kamar yanda kowa ke kallonta agidan.


★★★★?

Washe gari Abbah yadawo da yamma, duk munyi murnar ganinsa, shima kuma hakan take a garesa.
Sai da daddare suka tara iyayenmu mata meeting shida Dady da baba k'arami.
Abbanmu yay gyaran murya sannan yace, “dama wani abune yasaka muka taraku, maganace akan yaranmu mata, Ramlah da khaleesa da Rahaima da Hauwa'u kowa yasan sun fida mazajen aure harma an tsaida bikinsu nanda bayan salla?.
Duk suka amsa da eh.
“yauwa to Alhmdllh, yanzu munada sauran yara 'yan mata agidanan ak'alla su 8, kuma duk kusan Kansu d'ayane, dukda su Ramlah sun girmemusu, to wani uzirine yataso na tilas zamu had'awa auren wasunsu danasu khaleesa. shin ko akwai wad'anda a cikinsu sukeda tsayayye? domin a fiddasu??.
Da sauri maman safara'u tace, “Safara'u nadashi, dan harma yanason turo iyayensa, amma nace ta dakatar dashi sai angama na yayyensu?.
“to Alhmdllhi, sai kuma wa??.
Umma Ruk'ayya ma tace, “Fiddausi tanada tsayayye itama?.
“masha ALLAH, to bayansu fa??.
“mamansu yaa hameed tace, “ai inaga sukenan kam Abban Hameed?.
“yanzu su 6 kenan suka rage? to dama Alhaji halliru d'an majalissar datta6ai, nasan duk kunsan abokinane shak'ik'i? to shine yanemi alfarmar nemama 'ya'yansa maza biyu auren biyu daga cikin 'ya'yana, d'aya d'ansane na cikinsa, d'aya kuma d'an yayarsane tarasu tabari yacigaba da rik'onsa. to harga ALLAH nasan yaransa sunada tarbiyya dan haka na amince, amma dukda haka saida nasake dogon bincike akan yaran saboda yaron yanzu ka haifeshine baka haifi halinsa ba, to Alhmdllh suma basuda wata matsala, dan haka mun yanke magana dashi akan suzo saisu za6a acikinsu, wannan shine dalilin dayasa muka taraku kenan?.

Hummm yaufa anzo da Sabon al'amari a gidan namu, nanafa iyayenmu mata suka hau tsugunne-tsugunne, kowa burinta ace d'iyarta aka za6a, harma da iyayensu safara'u dakeda mijin a hannu, ganin sunji gidan maik'one kowacce tafara k'ok'arin gani da fatan 'yarta ta kasance acikin gidan, aiko sai shirye-shirye kowa keyi a asirce, aka fara gyara 'ya'ya.
Mudai a 6angarenmu babu abinda innarmu kemana, hasalima inda taji maganar anan ta barta, komu bata sanarma ba, sai abakin Fauziyya mukejin komai.
Yanda ake shirye-shiryen bak'i takowanne 6angare saika d'auka 'ya'ya. Shugaban k'asane zasuzo, ni abinma mamaki yabani dan kowanne d'aki da nasu shirin, dayake kowane d'aki akwai budurwa d'aya, mu 8ne, su shida kowanne d'aki 1 kenan, saimu mu biyu a d'akinmu, 'ya'yan abbanmu mu 4 kenan, na baba k'arami 2 na Dady 2, gashi biyu za'a za6a acikinmu amma saika d'auka mu duka za'a za6a saboda shirye-shiryen da iyayenmu keyi.

Ranar Asabar (Saturday) kenan takama zasuzo, dan haka muduka 'yan Matan 8 baba k'arami yace muhad'u muyi girkin tarbarsu.
Ni Munaya, Munubiya, Safara'u, Fauziyya, Haleematu, Fiddausi, Zarah, Siyama.
A kitchen d'in 6angarenmu muke girkin, dukda dai iyayenmu sun d'an saka mana hannu wajen tsara kalolin abincin daya dace a tanada. Ni abunma haushi yabani, yanda naga 'yan uwana NATA rawar kai, sai wani k'alk'ale-k'alk'ale akema abinci da drinks na gargajiya damuka had'a.
A raina nace Kodai sune iyayen cin tsiya, ai bazasuci ko quarter d'in abincinnan ba, wannanma ai almabazzaranci ne wlhy, mutun biyu kawai amma anmusu abinci wajen kala 6, banda kuma kayan ciye-ciye irinsu snakes da nau'in nama da aka sarrafa zuwa daban-daban. haka dai muka gama aka kai falon baba k'arami aka shirya, sannan kowa takoma 6angarensu danta kimtsa........✍?



Anan ne za'ayi kece rainin👌🏻😄🏃🏻‍♀



Guys kumuje zuwa😉👎🏻





One luv🥰🥰






*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*👏🏻😭
[4/22, 2:13 PM] Zuraiyah Zuzu💖: *_Typing📲_*



*_HASKE WRITERS ASSO...💡_*





*_♦RAINA KAMA......!!♦_*
_{Kaga gayya}_




*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*



_Ban yarda wani yaymin amfani da labarin nanba tako wace irin hanya, idan hakan tafaru ban yafeba gsky, ALLAH yabani ikon fad'ar abinda zai amfanar dani da Ku, ya tsare harshena daga fad'ar abinda zai cutar damu baki d'aya._

*_ALLAH ka gafartama mahaifina da dukkan sauran musulmai dasuka kwanta dama, kabama marasa lafiyarmu lafiya👏🏻._*




👉🏻2?


...........Zan iya ce muku fitinar gidanmu ta farone daga tushe, dan kuwa ginannen abune tun zamanin k'uruciyar iyayenmu...

Malam Faruku shine kakanmu, matarsa d'aya Marwa'natu (Innaro), 'ya'ya hud'u suka Haifa a duniya, maza uku mace 1. Auwal, Hameesu, Saffiya, Jafaru.
ALLAH yayi Innaro mace mai mugun son abin duniya, arayuwarta tanason ace komai daga gareta aka fara ganinsa, kokuma wajen 'ya'yanta, sun tsayama 'ya'yansu duk sunyi karatun addini dana boko, sai dai Safiya iyakarta primary aka mata aure. Sukuma mazan duk sunkai matakin babar makaranta (jami'a). wannan yasaka Innaro d'aukar burin duniya ta d'ora akan 'ya'yan, harma matan dazasu aura.
Auwal shine yafara kammala karatunsa, dan haka Malam faruku mahaifinsu yace ya fiddo matar Aure.
Bai wani tsaya Jan rai ba ya gabatar da Ai'sha amatsayin wadda yakeso.
Kai tsaye innaro tace sam bata aminceba, d'anta bazai auri d'iyar buzayeba kuma 'Yar iska, Auwal yayi lallashin yayi rok'on akan fahimtar da ita sonda sukema juna shi da Ai'sha, amma Sam tak'i saurarensa balle ta fahimcesa.
Da farko Malam faruku yasaka musu ido, azatonsa innaro zata sakko cikin sauk'i, amma ganin yanda ta kafe akan bakanta saiya sanya baki da tambayarta dalilin k'in amincewar.
Kai tsaye tace batason su Ai'shar ne, Dan ba'asan asalin suba, sannan kuma 'Yar iskace, shima kuma yasani ai. cikin hikima Malam yaso fahimtar da ita halin k'addara kowa da irin tasa, itama Aishar bayin kanta bane ba, amma tak'i saurarensa shima. ganin abin zai tasamma rashin mutumci yace to aure tsakanin Auwalu da Ai'sha kamar anyi an gama. A wannan lokacin ba k'aramin birkicewa innaro tayi musuba, amma Malam faruku yace tayi tagama, dan hujjarta batada muhimmancin dazai haramta auren Auwal da Ai'sha. babu 6ata lokaci kuma aka fara shirin bikin.

*Wacece Ai'sha?*
Ai'sha d'iyace gawasu buzaye 'yan k'asar Niger wad'anda k'addarar rayuwa ta jawosu zuwa k'asar Nigeria, su biyu kacal iyayensu suka Haifa, Aisha itace babba, sai k'anwarta Rabi'atu, wurjanjan suka shigo k'asar Nigeria, sun fara rayuwane awata tashar mota, inda anan tsautsayi ya fad'ama Ai'sha wani mara imani yamata fyad'e anan cikin tasha da daddare, randa abin yafaru Malam faruku yaje tashar zai bada sak'o akaima wani d'an uwansa dake garin Maiduguri, ya taras anata cecekuce atashar, yayinda Ai'sha da iyayenta ke rungume da d'iyarsu sunata kuka da kururuwa.
Malam faruku yatambayi abinda ke faruwa daga wajen mutanen dasuka zagayesu suna kallo, babu 6ata lokaci matashin saurayi yafad'a masa komai.
Hankalin Malam faruku yayi matuk'ar tashi, danshi mutumne mai kishin al'umma, anan ya d'auki Ai'sha da iyayenta suka nufi asibiti, saboda jinin daketa zuba daga jikinta (Dan bazata wuce 15 ba sannan), duk wata kulawar da yakamata anbama Ai'sha a asibitin, har tsawon kwanaki hud'u tasamu lafiya sarai, kamarma komai bai faruba, sai dai tabo Na zuciya da aka bar mata itada iyayenta. tun suna zaman asibiti Malam faruku ya fiskanci iyayen Aisha basuda wajen zama, dan haka yak'udiri niyyar taimakonsu.
Akwai wani d'aki k'arami ciki da falo dake gidansa, saiya zagaye musu shi da Katanga yamasa gyara.
Tunda aka fara aikin innaro ta tada hankalinta, duk zatonta aure zai k'ara, ganin tana neman tara masa k'asa ya zaunar da ita yamata bayani dallah-dallah, maimakon ta kwantar da hankalinta tunda ba kishiyar bace saima takuma tadashi, tace bazata zauna da iyayen Aisha ba.
Malam faruku yace bata isaba, Dan gidansane babu mai hanashi ajiye Wanda yakeso akuma lokacin dayaso.
Dole badan innaro tasoba su maman Aisha suka zauna agidan, sai dai ko kad'an basajin dad'in zama da ita, kullum gori da cin mutunci take musu, su Aisha kam basuda sakat awajenta, saita koma sakasu aiki tamkar boyi-boyinta. Malam faruku ne ya koyama mahaifin su Aisha sana'a, har shima yasamu rufin asirin rik'e iyalensa dai-dai gwargwado, amma ko kama k'afar Malam faruku baiyiba, lokuta da fama ma shine ke taimakonsa dawasu abubuwan Na rayuwa, musamman d'inkin sitturar su Aisha da wasu matsaloli Na yau da kullum dasukan taso. tun zuwansu gidan Auwal yafara k'aunar Aisha, duk da mahaifinsu ya Sanar musu da komai akan k'addarar da ta fad'ama Aishan kuwa, shekararsu biyu suna soyayya, tun Aisha Na d'ari-d'ari dashi saboda tsoron abinda aka aikata mata har tazo tasaki jikinta dashi, sai dai babu Wanda yasan suna soyayyar sai Rabi'a k'anwarta.

Ana haka kuma Auwal yazo da zancen Aisha zai aura.

To haka dai akayi auren Auwal da Aisha badan innaro tasoba.
Wannan kuma yasakata d'aukar Karen tsana ta d'orama Aisha, kullum cikin zagi da cin mutuncin Aisha take, sosai tazamar mata Uwar miji mai kishi da sarakuwa, ga gorin datake mata akan ita 'Yar iskace, babu wani fyad'e da'aka mata, taje tayi iskancinta an fake da fyad'e an dawo an lik'ema d'anta da asiri, tujara dai iri-iri dai ta innaro.
Aisha tanada hak'uri, ko kad'an abinda innaro kemata bai hanata girmamata ba da bata matsayi irinna uwa, amma innaro bata gani.
Watan aurensu 7 kacal innaro ta samoma Auwal wata yarinya mai suna Mero, mero d'iyace ga wani matashin d'an kasuwa, tun alokacinma ana lissafashi a masu kud'in yankin balle yanzu daya zama shahararre, Auwal bayason Mairo, amma dolensa ya aura saboda innaro tace zata tsine masa.
Shigowar Mairo Yakuma k'untata Aisha a gidan, dan tunkan ta shigo innaro tagama 6ata sunan Aisha dana iyayenta awajensu mairo, shigowar mairo da wata 1 kacal kuma tasamu ciki, wannan fa yakuma k'ara ta6ar6arewar al'amura, gashi sannan ALLAH ya yalwatama Auwal d'in babu laifi, harma yasayi wasu filaye uku shida 'yan uwansa anan cikin anguwar kusada su innaro, amma ba'a ginaba, dan babu kud'in ginin lokacin.
A wannan lokacinne kuma k'addara ta afkama iyayen Aisha, ranar wata alhamis da daddare aka maka ruwa Na tashin hankali, Wanda yay sanadin fad'awar d'akin dasuke ciki suka rasu.
Aisha da Rabi'a sunshiga matuk'ar tashin hankali, hakama Malam faruku, innaro kam ko'a jikinta.
Rasuwar iyayen Aisha yasaka rabi'a k'anwarta dawowa hannunta da zama, akuma lokacinne Hameesu shima yace Rabi'a yakeso da aure. tashin farko innaro ta taka masa birki da kukarin zata tsine masa kuwa. dole yabar maganar auren Rabi'ar yasamo wata Ruk'ayya ya aura.
A lokacinne Mairo ta haihu namiji, zokaga murna wajen innaro da mairo, Malam ma yayi murna, hakama Aisha, dukda innaro tace Na munafurcine. ranar suna yaro yaci Abdulhameed, koda wasa mairo bata ta6a yarda Aisha ta d'auki hameed ba, dan innaro tahana, Auwal yayi fad'an shida Malam harsun gaji.

Rayuwa tacigaba da tafiya tsawon shekaru, zuwa sannan su Auwal sun had'a hannu sun gina filinsu, kowa da 6angarensa, gidanmu yafara yawaita da 'ya'ya, dan matar Hameesu ma ta haihu Namiji Shafi'u, hakama matan gidanmu sun k'aru, dan jafaru ma yayi aure, hakama Hameesu yak'ara aure shima, ga iyayenmu sun kuma bunk'asa, dansu wuce buk'atun yau da gobe, dai-dai gwargwado akwai rufin asiri agaresu, alokacin kuma sai Auwal yakuma auro ta uku, auren iyayenmu yakoma tamkar gasa wajen za6o 'ya'yan manya, dan kuwa Aisha ce kawai d'iyan talakawa acikinsu, tana zaunene kawai da k'arfin ALLAH dakuma Na Malam faruku, saikuma soyayyar mijinta Auwal, amma da dan ta innaro ne da tuni Auwal ya saketa.
Akwaima randa fada ya had'a mairo da Aisha akan Rabi'a ta doki hameed saboda yamata rashin kunya, dukan da mairo taima Rabi'a saiya sa Aisha kasa hak'uri a ranar ta tanka mata, nankuwa mairo tafara zuba mata gori da cin zarafi, da innaro tazo danjin ba'asin rigimar saitace dole Auwal yasaki Aisha, dukda kuma mairo ce mai laifi, Auwal yayta magiya amma innaro tace yaza6a ko ita ko Aishan, babu yanda zaiyi yasaki Aisha saki d'aya alokacin. Hankalin Aisha yatashi matuk'a, dan batasan inda zasu dosaba, tunda basuda kowa a Nigeria, ga innaro tsaye akanta tace atake saita bar mata gidan d'a.
ALLAH ya tak'aita abunne dai-dai sanda Aisha ke fitowa rik'eda hannun Rabi'a kuma saiga Malam faruku yadawo daga kasuwa, nanfa ya tambayi ba'asi, Aisha tasanar masa komai, maidata yayi gidan, yakuma saka Auwal ya maida aurensu atake awajen, sannan ya tabbatar masa ko bayan babu ransa yasake sakin Aysha bai yafeba, kuma inhar innaro tasake sakashi ya saketa itama abakin aurenta.
Wannan shine dalilin dayasa auren Aisha da Auwal bai sake rawaba. rayuwa kuma tacigaba da shurawa. Matan gidanmu 7.
Auwal matansa uku, Aisha (innarmu) Mairo (mama) Sadiya (gwaggon haleema)
Hameesu nada biyu, Ruk'ayya (umma) Hadiza (momy)
Jafaru Nada biyu shima, Suwaiba (maman safara'u) Hafsatu (maman Fauziyya).
Kowacce ta haihu acikinsu, amma banda Aisha, wadda saida sukayi shekara 20 da aure itada Auwal sannan ALLAH yabata ciki, zokiga murna wajen Auwal da ahalinsa, saidai banda matan gidanmu da innaro, dan aganinsu duk sunfi Aisha matsayi, (maman fauziyya) Ce kawai babu ruwanta, dan suna d'asawa da Aisha sosai, ita kad'aice bata raina innarmu ba, dan Yaya ma take cemata.
Babu irin wahalar da Aisha batasha agidanba acikin shekarunan, kullum cikin mata gorin haihuwa dana talauci ake, harma dana batada asali, tundaga kishiyoyinta har matan k'annen mijinta basu raga mataba, kowacce jitake ina wuta tasaka innarmu a gidan, dama ga d'aurin gidi daga innaro

2 / 36