RAINA KAMA Tagwaye Cikin Gidan Fitina by Bilyn Abdull

Author :  Bilyn Abdull Category :  Romance

Chapter   14 / 36

39K to 42K   out of 107K words

yazama kowa tausayina yakeyi acikinsu, yayunmu mazama babu laifi, suna nunamin kulawa dai-dai gwargwado.
Ahaka nafara rage wasu damuwoyin.
Satina d'aya kenan da dawowa daga asibiti, duk na k'ara ramewa Na fige, hakama Munubiya, saika d'auka tare muka kwanta ciwon.
Ahaka muka tak'ark'ara muka koma makaranta, ayanzu kam maganar gsky bana fahimtar karatu, saboda damuwace tsatstsage da zuciyata, nasanma nida aure kuma har abada, kowa yafito haka za'a sokeshi ya janye, ita dai 'Yar uwata Munubiya ALLAH ya taimaketa na gidane yace yana sonta, itama nasan da yanzu an soki lamarin, musamman daba banbancemu jama'a sukeyiba. Nagodema ALLAH da abinnan bai shafi rayuwar Munubiya taba sarkin hak'uri, tabbas danafi haka shiga tashin hankali, bansan yanda zan musalta muku k'aunar danakema 'Yar uwataba, ina sonta fiyeda zaton mai tunani, wlhy zan iya fansar da raina awajen kare nata, kamar yanda nasan itama zata iya yin hakan agareni.

Yau ta kasance juma'a, dagani har Munubiya bamuje makarantaba, saboda tatashi da ciwonkai, tun muna primary idan d'aya bai da lafiya d'ayan bazaije school ba, komin zare idon ko dukanmu da za'ai kuwa, wannan abinne yazame mana jiki har girmanmu gashinan.
Bayan nagama gyaran 6angarenmu innarmu tace Na shirya naje nakaima wata k'awarta sak'o.
Badan nasoba Na kar6i sak'onnan natafi, saboda banajin dad'in tafiya nikad'ai arayuwata, tunda nataso nayi wayo ko ina zamuje sai nida Munubiya ne, mawuyacine kiga d'ayanmu tafita batare da d'ayaba.
Tafiya nake tamkar zan fasa kuka, gani nake kowa nikad'ai yake kallo, sanye nake da jallabiya bak'a datasha adon honey color d'in duwatsu, Na nad'a Veil ruwan zuma shima, haka ma takalmana masu d'an tudu ruwan Zuma, sai lady's bag d'ina, ahankali nake tafiyar cikeda takuruwa, ahaka nazo bakin titi domin samin abin hawa.
Banfi tsayuwar 15minutes ba saiga taxi, ganin babu kowa a taxi d'ina kamar karna shiga, amma sainayi addu'a kawai nashiga, gudun karnazo nayi sakin Na hannu kamun na guje.
Munyi nisa da tafiya naga mai taxi d'inan yak'i d'aukar kowa, gashi anata tsaidashi, kumani bance masa drop na d'aukaba gaba d'aya.
Cikin dakiyar zuciya nace “bawan ALLAH miyasa bazaka tsaya ka d'auki mutaneba? bayan kuma gashinan anata tsaidaka?.
Ta madubi ya kalleni yana murmushi, sorry hajiya, kekad'ai aka bani izinin d'auka ai?.
Da mamaki nace “kamar ya??.
Dariya yad'anyi sannan yace “karki damu da wannan, ina muka dosa yanzun dai??.
Yawu mai kauri na had'iye da k'yar sannan na fad'a masa inda zamuje.
Har k'ofar gidan ya ajiyeni, nabashi kud'i kuma yak'i kar6a, haryaja motar yabar wajen ina binsa da kallon mamaki, na sauke ajiyar zuciya nidai ina hamdala ga ALLAH dayasa na sauka lafiya.
A fili nace “k'ilama aljanine?. saikuma nace “wayyo ALLAH ya tsareni da hawa motar aljanu?.
Da wannan tunanin nashiga gidan, tun a soro nake kwad'a sallama.
Daga ciki najiyo ana amsamin, tace shigo mana baiwar ALLAH.
Shiga nayi inda ake amsamin sallamar, dattijuwar macece da zasuyi sa'anni da innarmu, ba yaune karon farko dana fara zuwa gidanba, tun muna k'anana muke zuwa yawon da innarmu ko idan munzo suna ko biki, (inna lami k'awar innarmu ce, a anguwarmu take, tun zuwansu innarmu gidansu innaro suka k'ulla k'awance da inna lami d'iyar makwaftan su innaro. harkuma yanzu akwai zuminci mai k'arfi a tsakaninsu).

“a'a a'a lalale marhabin da d'iyata, Munubiya ce ko munaya??.
Fuskata d'auke da murmuahi nace “inna munaya ce, munu.... tana gida bata jin dad'i?.
“Ayya ALLAH ya sauwak'a yabata lafiya, ya Ai'shar dasu Aryaan??.
“lafiya lau take, tacema na gaisheku. ga wannan tace na kawo miki?.
“to madallah, ina amsawa. ngd sosai kuwa?.
Murmushi nayi kawai bance komaiba, sai zuwa can nace “Ameera batanan? naji gidan shiru?.
“wlhy Ameera tafita d'azunnan gidan Mariya, amma nasan duk inda take tana hanyar gida yanzu?.
“ALLAH sarki, to a gaida min ita idan tadawo ni bara na tafi?.
“haba dai Munaya, daga zuwa kice zaki tafi?, Dan ALLAH ki zauna yanzu zakiga Ameeran tadawo aii. bara kiga nasa miki ko kallone kisamu abokin hira?.

Badan nasoba na zauna har ameera ta dawo, sosai tayi murna da ganina, dayake munsan juna, school d'aya mukayi a secondary, kuma ajinmu d'aya, nan muka zauna mukasha hirarmu, har ta soya mana wainar fulawa mukaci muka k'oshi abinmu.
Ban bar gidanba sai bayan an sakko masallaci, har titi ta rakoni, da k'yar muka samu taxi kasancewar anguwar tasu tad'an shiga lungu abin hawan yana wahala.

Saida muka hau titi na fad'ama driver inda zamuje.
'Yar dariya yayi yana fad'in “aina sani hajiya?.
Cikin fad'uwar gaba nad'ago na kalleshi, Dan naji kamar muryar driver n d'azun, ido na zazzaro waje da dafe k'irji dan ganin shine kuwa.
Na ware baki zan maka ihu ya jehomin farin Handkerchief a fuska. luuuu nayi da baya na kwanta a kujerar, tun ina ganinsa dishi-dishi har na daina gaba d'aya................✍?




Tofa jama'a ana wata ga wata wanene yasa a kwamushe Munaya🙆🏻😭?.







*_ALLAH ka gafartama mahaifanmu👏🏻😭_*
[4/22, 2:17 PM] Zuraiyah Zuzu💖: *_Typing📲_*



*_HASKE WRITERS ASSO...💡_*
_(Home of expert and perfect writer's)_




*_♦RAINA KAMA......!!♦_*
_{Kaga gayya}_




*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*



👉🏻1?5?


.......Tunda yafara tafiya bai tsaya ko inaba sai a wata sabuwar anguwa, shiru anguwar take babu yawan hayaniya, dan gidajenma tsilli-tsilli suke tamkar rugar Fulani, wani gida dakecan nesa da sauran gidajen yanufa, gidane babba mai k'aton bak'in gate, yay horn sau biyu akazo aka bud'e masa. a babbar harabar gidan yay parking, yana cikin motar bai fitoba har kusan 10 minutes bayan yagama waya yace ya iso.
Idanu na zaro waje saboda ganin Muftahu yafito daga wata k'ofa yanufo motar, gaba d'aya mamaki yahanani kwakwkwaran motsi harya k'araso.
Mai taxi yafito ya risina ya gaidashi, sannan yace nagama aikina Oga.
Murmushi Muftahu yayi, sannan ya lek'a Munaya dake barci kashir6an ta glass, janye kansa yayi sannan ya zaro wayarsa daga aljihu yay kiran wani.
“Umh yalla6ai akwai 'Yar matsala fa, dan barci takeyi sosai, kona d'akkota?.
Da sauri yace “No ina zuwa, amma wannan driver dayay aikin yabar wajen, dan bana buk'atar ya ganni?.
Murmuahi Muftahu yayi, tare da fad'in “angama ranka ya dad'e?.
Muftahu ya sallami drivern daya kawo Munaya, yace zai kirashi ya maidata zuwa anjima, yaje yabar motar anan.
“babu damuwa Oga, saina jika?.

Bayan tafiyar driver Galadima yafito, dama duk yana kallon abinda ke faruwa ta window.
Taku yake cikin tsantsar nuna jinin mulki dake yawo ajikinsa, ga wata izza ta zamowarsa cikakken namiji mai isashshiyar lafiya. fusakarnan babu walwala kamar kullum, ahaka ya k'araso wajen motar, Muftahu ya bud'e masa murfin inda Munaya ke kwance tana kwasar barcinta.
Kallonta yayi na tsayin mintuna uku, sannan ya janye idonsa ya rankwafo da kansa cikin motar, saida yad'an cije lips d'insa sannan yasaka hannayensa biyu ya tallafota ahankali ya fito da ita, tamkar 'Yar baby haka ya d'akkota acikin hannayensa, sai wani kuma d'aure fuska yakeyi yana kauda kai, kaikace anmasa dolene ya d'auketa.
Hannu Muftahu yasaka yatoshe bakinsa saboda dariyar dake Neman kwace masa.
Wai yau Galadima gudane d'auke da mace a hannu, mutumin da ko kallon mata bai cika yiba, inkaga yana walwala ko dariya wa mace to Momma ce ko aunty Mimi.
Jakarta ya d'auka shima yabi bayansa.
Ya iske harya shinfid'eta a doguwar kujerar dake falon, yana gyara hannun rigarsa daya nannad'e yana jan k'aramin tsaki, ganin Muftahu na murmushi saiya kuma had'e fuska, Muftahu ya ajiye bag d'in yana had'iye dariyar da k'yar saboda gudun yin laifi.
Hannu yamik'ama Muftahu.
Muftahu yabashi handkerchief d'in daya zaro a aljihu, rankwafowa yayi kanta ya d'ora Handkerchief d'in bisa hancinta, tsayin minti 2 ya janye.
Tari tafarayi, saikuma ta fara k'ok'arin bud'e idanunta tana lumshewa, Muftahu ya mik'o masa gorar ruwa mai d'an sanyi.
Cikin hannunsa ya tsiyaya kad'an ya shafa mata a fuska, ahankali ta fara bud'e idanun ta, shikuma yaja da baya yakoma ya zauna bisa kujerar mai zaman mutum d'aya.
d'ora k'afa yayi d'aya kan d'aya ya jingina kansa jikin kujerar ya lumshe idanu, saika rantse idonsa arufe suke, amma ya zubasune akan Munaya dake ta mutsu-mutsun tashi zaune.
Da k'yar ta iya tashi ta samu ta jingina da kujerar tana k'arema falon kallo, yayinda hawaye ke zirara a kumatunta.
Ruwa Muftahu ya mik'a mata, babu musu ta kar6a dan wata kishirwa takeji, tunda tafara shan ruwan bata ajiyeba saida ta shanye tas, nan wata zufa tafara karyo mata kuma.
Mik'ewa Muftahu yayi yak'ara gudun AC n.
Ahankali zufar tafara tsanewa, saikuma tad'anji k'arfin jikinta, Muryarta na rawa alamun kuka tace, “Please Ku suwaye? miyasa kuka kawoni nan? dan ALLAH kuyi hak'uri karku cutar dani, karku lalatamin rayuwa dan girman ALLAH, Ku tausayama mahaifiyata, damuwar damuke ciki kad'ai ta ishemu, wlhy daku keta mutuncina gwamma Ku kasheni yafimin sauk'i?.
Daga Muftahu har uban gayyar kallonta kawai sukeyi, ita ko kad'anma bata gane Galadima ba, saboda yayi sama da fuskarsa.
Muftahu ne yace “ki kwantar da hankalinki, kuma ba abinda yasa muka d'akkokiba kenan?.
“to miyasa kuka d'akkoni? bawan ALLAH, mina muku??.
Muftahu ya juya ya kalli Galadima, amma saiyaga ko motsawa baiyiba, bashima da niyyar tanka musu.
Itama Munaya saita maida kallon nata ga Galadima, a kuma lokacinne yad'ago kansa zai gyara zama.
Wata razananniyar k'ara Munaya tasaki saboda tsorata, da Sauri Galadima ya toshe kunnensa, shima tsawar ya Daka mata wadda tasakata nutsuwar dole.
“k!!! Dalla karki ciremana dodon kunni!!!!?.
Dole Munaya tayi shiru jikinta na 6ari da k'yarma.
Yaja wani wawan tsaki, tare da janye hannayensa daga kunnensa yana harara Munaya. “k wace irin shashashace ne??.
Sukda halin da take ciki saida ta watsa masa harara, amma bata iya cewa komaiba.
Hannu yakai tamkar zai maketa saikuma ya FASA, komi yatuna oho.
Komawa yayi inda yataso ya zauna, ya maida k'afafunsa yay crossing d'insu.
Shi dai Muftahu yana kallonsu yakasa cewa komai, bakajin motsin komai saina shashshekar kukan Munaya Dana k'arar AC.
Cikin kuka tace “minamaka kasa aka kawoni nanan? ko sokake kakuma jamin wani sabon 6atancin bayan Wanda yafaru abaya? wane Abu na tare maka waishin aduniyarnan dan ALLAH bawan ALLAH??. takuma rushewa da kuka mai tsuma rai.
Bakinsa ya ta6e a zuciyarsa yake fad'in daganin yarinyarnan akwai tsiwa dai, saikuma uban tsoro kamar farar kura. banza yamata, azahiri idonsa a lumshe suke, amma kuma abad'ini yana kallon Munaya ne, kukanta Neman saka masa ciwon kai yakeyi, dan haka yay maganar cikeda izza da mulki.
“kinutsu muyi abinda ya kawomu, inba hakaba zaki kwana anan gidan ne?.
Da Sauri Munaya ta share hawayenta, “indai kukane na daina wlhy, kayi hak'uri ka sanarmin, dan ALLAH ka maidani gida kafin hankalin innarmu ya tashi?. tak'are maganar da share hawaye.
Dariya taso bashi amma saiya gimtse, saikace ba itace tagama tsiwa ba yanzun.
Muftahu dai kasa hak'uri yayi saida yad'an dara, Galadima ya balla masa harara, hakanne yasashi yin shiru ya had'iye dariyar.
“kin shirya tafiya kenan??. ‘galadima yafad'a tamkar an masa dole sai yayi maganar?.
Munaya tace, “wlhy na shirya ranka ya dad'e?.
Yace “good girl? yana ta6e baki.
“ki fad'amin waye yasaki aikin nan??.
Cikeda rashin fahimta Munaya tace, “wane aikin??.
Shiru Galadima yayi bai tanka ba, sai Muftahu ne yaymata bayani dalla-dalla akan abinda yafaru a plaza kwanakin baya?.
Cikeda k'unar zuciya Munaya tace “ni babu Wanda yasakani, saima tozarci da hakan ya jawo mana muda mahaifiyarmu, bansan komaiba, amma tunda al amarinan yafaru muka kuma tsintar kanmu a k'unci, kullum da irin abin kuka dazamu gani agidanmu, yanzu haka akan waccan abin maganar aurena sau biyu tana lalacewa, yanzu haka satina guda kenan da baro asibiti saboda tashin hankalin dana shiga a dalilin fasa aurena da cin zarafi dana fuskanta daga Wanda yafasa aurena nawa, wlhy Ku yarda dani bansan komaiba?.
Muftahu ya juya yana kallon Galadima da idonsa ke a rufe, amma yana sauraren Munayar.
Kusan mintuna 3 sannan ya bud'e idonsa, akan Munaya ya zubasu, bazata iya jurar kallon kwayar idonsa ba dan haka tayi azamar janye nata, shima janye nasa yayi ya gyara zamansa. “kince babu hannunki? amma miya kaiki plaza a wannan time d'in daya kamata duk yarinyar kwarai tana gidansu??.
“Muna bikine, bayan munkai amare mun dawo sai fu'aad yamatsa akan saimun shiga, ba dan nasoba nayarda, kuma bani kad'ai baceba, harda 'yan uwana su uku?.
“waye shi Fu'aad d'in??.
“Saurayinane, awajen bikin muka had'u dashi?.
da sauri Galadima yace “miye kamaninsa? kuma ya kukayi dashi bayan abin ya faru??.
A nutse Munaya tabasu labarin komai, sannan ta zano musu kamannin Fu'aad dalla-dalla, danma bawani kallon tsaf tamasa ba a cikin kwana biyun.
Muftahu yace “kozamu iya samun Horton shi Fu'aad d'in??.
“banida hotonsa, dan bai yarda munyi ko photo d'aya ba awajen bikin, amma zamu iya samu a video d'in da akayi maybe awajen dinner? ?.
“galadima yace “a ina zamu CD d'in yanzu??.
“gaskiya wannan shine mai wahala, dan bansan taka maimai cikin angunan waye yasaka ayiba?.
Galadima ya cije lips d'insa da k'arfi, sai kace zai hudasune.
Kusan mintuna 3 kowa baice komaiba, sai can munaya tace “kunji na fad'a muku gaskiya, Ku maidani kafin afara nemana?.
“zamu maidaki bisa sharad'i guda d'aya?. ‘cewar Muftahu ?.
“wane sharad'ine??. ‘Munaya ta tambaya?.
“Sharad'in shine zakuyi auren 1year keda Galadima?.
Cikin zaro idanu waje munaya tace “kamar ya? ban fahim cekaba fa??.
“ina nufin Auren yarjejeniya zakuyi na shekara 1 ko 2, ta wannan hanyarne kawai zamu iya kamo bakin zaren, sannan kekuma zaki sama ma iyayenki kwanciyar hankali, nanda kafin adadin da aka d'ibama auren yacika kinga komai ya wuce, saiya sakeki kiyi idda ki sami Wanda kikeso sannan kuje gida a d'aura miki aure dashi, Galadima ma zai iya sawa har auren a d'aura muku, daga baya sai kuje ya warwarema iyayenki komai, yakika gani??.
“tabd'i, wannan wace irin maganace saikace labarin Novels ko films? to tayayama za'ayi hakan yafaru? bayan nama sanarma iyayena banida wata alak'a dashi?.
Murmuahi Muftahu yayi, yace “dan wannan duk mai sauk'ine, kedai amincewarki kawai muke nema?.
“amma dai kun maidani wawuya wlhy, to ban aminceba, gara na dawwama banyi aureba ai?.
Baki Muftahu ya bud'e zai k'ara magana Galadima ya d'aga masa hannu alamar yayi shiru ya barta.

14 / 36