Author : Bilyn Abdull Category : Romance
d'auke hankalinsa, gaba d'aya yayi busy saboda kamfaninsu na k'ok'arin fidda wata waya sabuwar k'ira.
Abinda ya faru kuwa a Nigeria ya watsar dashi gefe, saboda gargad'in da doctor d'insa yamasa akan yarage yawan damuwa, saboda ciwonsa yana k'ok'arin tashi.
Haka yadage yacire komai d'in, amma har yanzu yasaka amasa aikin bincike ta k'ark'ashin k'asa, sannan iyalan manager sun ku6uta suma, yabar Nigeria da sati biyu suka sakosu.
Gaba d'aya ya ajiye duk wani abinda yashafi Nigeria a gefe, ko bikin salla bai hakarta ba, sannan zuwan dayankan yi duk karshen wata ma ya daina, Momma batace dashi komaiba akan k'in zuwan nasa.
Dan lokacin da mai martaba (mahaifin momma) yazo sun tattauna sosai akan abinda yafaru, shine yace Galadima yad'an tsahirta da zuwa Nigeria nawani lokaci, idan komai ya lafa sai acigaba da bincike, dan wad'anda suka aikata sumafa baza suyi barciba, yanzu idonsu abud'e yake akan komai, amma idan anyi burus dasu komai ya lafa sai a d'auki mataki. Wannan yasa bai sake zuwaba, gameda business d'insa nacan kuwa Harun yana tsaye akan komai.
Fitowarsa kenan daga office zaije gida yad'an kimtsa sannan yaje asibi, wayarsa tashi ruri, zarota yayi daga aljihu ya duba, ganin Muftahu a kan layi saiya maida wayar cikin aljihu kawai batare da ya amsaba.
Hannu yabama beejay abokin aikinsa sukayi sallama akan saikuma gobe. yana k'ok'arin shiga motar kiran yakuma shigowa, shiga yayi ya zauna sannan ya d'aga, suka gaisa da Muftahu, ya tambayesa jikin Abie.
Shikuma ya amsa da Alhmdllh.
Muftahu yace, “ALLAH yasa ban takuraka ba? Inason muyi magana ne dama?.
Kwantar da kansa yayi jikin kujera ya lumshe idanunsa, cikeda k'asaita ya furta “ina saurarenka?.
Daga can Muftahu yay murmushi, sannan yace “dama akan yarannan ne, d'aya daga cikinsu an fasa aurenta, wai Wanda zai auretan yace yafasa sabo...da sa... sa.... yakasa fad'a saboda maganar tamasa nauyi abaki?
Galadina yace “kafad'a mana, kasanfa bana son kwana-kwana a magana ni?.
“wlhy maganarce babu dad'in ji, ca yayfa wai ita karuwarka ce, yanzu haka yarinyar tana asibitima?.
Da k'arfi ya cije lips d'insa, zuciyarsa na suya, saikuma ya saki guntun murmushin takaci, yatashi zaune yana bud'e idonsa, “humm Muftahu waye shi yaron dazata aura d'in??.
“wlhy ban saniba nima?.
“o right karka damu, zanyi tunani akan lamarin, ni bamma duba bayanai daka turomin akan yarinyarba fa, abubuwa sunmun yawane wlhy. amma masu bibiyar tata basuga wani abunda ya shafi waccan maganarba??.
“Gaskiya basuga wani abuba sa6anin tunaninmu, ammafa bama yarinya d'aya bace ba, twins ne, kaduba bayanan kagani?.
“ok sai munyi magana kenan?.
Bayan sunyi sallama yay shiru yana tunani a ransa, da gani kasan ransa a6ace yake, ya furzar da huci daga bakinsa sannan ya tada motar yatafi. idonsa yayi jajir saboda bak'in ciki, yanzun har takai wani yafasa auren wata akansa? waye yamasa wannan abin? miya masa ne da zafi haka ya tozartashi? wlhy yayi alk'awarin duk Wanda keda hannu akan wannan tozarcin da akai masa bazai d'aga masa k'afaba, dolene yayi dana sanin saninsa.
Da wannan tunanin ya k'arasa gida.
Babu kowa a gidan sai jakadiya, su Sauban suna makaranta, Aunty Mimi da Momma kuma suna asibiti, jakadiya ta rissina tana gaidashi, hannu kawai ya iya d'aga mata ya haye sama.
Binsa tayi da kallon tausayi, hakan da yayi mata ya nuna ransa a 6ace yake, danshi mutum ne mai girmama nagaba dashi, dukda tana a k'ark'ashinsu bai ta6a wulak'antata ba, wannan tarbiyar mahaifiyarsu ce kuma.
Koda yashiga rigarsa kawai yacire ya zauna a bakin gado, medical glasses d'insa yasaka sannan yajawo System yabud'e, Emailil na Muftahu ya shiga.
Dukkan bayanai da tarihin su Munaya ne awajen.
Gaba d'aya ya nutsu ga abinda yake karantawar, shi mamakima abin yabashi, sukuma wane irin gida wad'annan yaran suka fito haka? Wani abun yakan bashi dariya (sai dai yakanyi dariyar ne a zuciyarsa), wani kuma haushi, tsaf yagama karanta tarihin yaran masu kama da juna.
Ya mik'e yana zagaye d'akin da tunanin miye mafita, har yanzu zuciyarsa bata bar karanta masa da hannun wad'an yaran aka masa wannan abunba, sai dai shi kansa yana tambayar kanasa mizaisa su aikata? miye kuma ribarsu bayan suma hardasu aka tozarta?. yanzu kuma zuciyarsa na masa wani tunani daban bayan yaji tarihinsu.
Zuciyarsa na cigaba da tunzurashi akan yayi amfani da damar k'arshe wajen bincikensa, tunda yabi dukkanin sauran bai samu wani bakin zareba.
To amma kuma wannan ai ba tarbiyyar Malam bahaushe baceba, daga baya kuma idan komai yafitofa? wane kallo kuma za'a masa?, shinma zata iya fahimtarsa kuwa? dan irin wannan abun yakan farune a labaran films ko Novels, to amma wannan ce damarsa ta k'arshe ai kawai, dolene ya jefi tsuntsu biyu da dutsi d'aya kenan?.............✍?
Tirk'ashi, Nikam dai nakasa fahimtar wannan cirkud'ad'd'en tunanin na Galadima?, fan's koku kun fahimta Ku fassara mana🤔?.
*_Ya ALLAH ka gafartama iyayenmu😭👏🏻_*
[4/22, 2:17 PM] Zuraiyah Zuzu💖: *_Typing📲_*
*_HASKE WRITERS ASSO...💡_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_♦RAINA KAMA......!!♦_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
👉🏻1?4?
.......An kai ruwa rana kafin asamu na farfad'o, ina farfad'owa kuma sukamin allurar barci domin nasamu Hutu.
Sai a lokacin hankalin iyayena yad'an kwanta.
Baba k'arami da yagama birkicewa akan shifa bazai yardaba, saiya maka iyayen Haidar a kotu. wannan wane irin tozarcine haka? sunzo sun kar6i kayansu, anbasu batareda anduba wulak'ancin dasukayiba, shine kuma dan rashin mutunci shi Haidar d'in zai jamusu 'yarsu ta salwanta, to shifa bazai aminceba.
Hak'uri Dady da Abbanmu suketa bashi suna tausarsa akan yayi hak'uri, su d'auki hakan matsayin k'addara kawai, indai mijine ALLAH zai bani wani ai. k'ilama shid'in ba alkairi baneba agareni dama.
Innarmu dai tun tana kukan zuci harya fara fitowa fili, mama Rabi'a nata tausarta.
'Yan gidanmu babu Wanda ya biyomu sai maman fauziyya, har innaro k'in zuwa tayi.
Ban farfad'oba sai gabanin magriba, lokacin su Abba na shirin tafiya masallaci, na bud'e idona ahankali, da innarmu na fara tozali, sai mama Rabi'a da maman Fauziyya a gefenta, Munubiya na gefen gadon danake kwance rik'e da hannuna ta kifa kanta ajikina alamar barci ya saceta ahaka.
Nan komai yashiga dawomin sabo a zuciya, fashewa nai da kuka mai tsuma rai, cikin dasashiyar murya nace “shikenan innarmu, shima na rasashi, Haidar yatafi, yakuma ce har abada bazai ta6a dawowa gareniba, mi muka musu suka za6i mana wannan sharrin dabazai ta6a barin rayuwarmu ba? yarigada yazame mana tabo a tarihinmu, ya ALLAH ka gaggauta saka mana akan duk mai hannu akan buga jaridarnan, wlhy Haidar ban aikataba, sharri sukaimin, dan ALLAH karka barni, ina sonka wlhy, sosai nake sonka, dan ALLAH mama Rabi'a kuce masa sharrine, ban aikataba, Munubiya dan ALLAH karkubar haidar yatafi, ina sonsa wlhy.......?.
Kuka Munubiya takeyi sosai, dan tunda na fara magana ta farka, dama barcin nata bawani nisa yayiba. Innarmu kam tashi tayi tafita tana share hawaye, maman Fauziyya na rik'e dani tana lallashi. Mama Rabi'a ma kuka takeyi saboda ganin 'Yar uwarta Na kuka.
A haka su Abba suka shigo suka samemu inata wannan sambatu, da rok'on akiramin Haidar, dan wani masifar sonsa nakeji a lokacin, fiyema da son Dana masa muna tare.
Duk saida nabama su Abba tausayi, Dady ya zauna akujera tareda rik'e hannuna.
“Munaya ya isa haka kinji, kiyi hak'uri, ki yarda da k'addara, dama can ALLAH ya rubuta shid'in ba mijinki baneba, insha ALLAHU mijinki nanan zuwa soon. Ubangiji nason bayinsa masu hak'uri, wata rana komai zai zama labari tamkar ba'ayiba kinji?.
Ahankali na fara sassauta kukan danakeyi, ina sauraren lallashin Dady, sai ajiyar zuciya danakanyi lokaci-lokaci.
Bayan doctor yazo ya dubani yace abani abinci nasha magani, sunaso nakuma samun isashen barci danna samu na kuma hutawa. Saboda jinina yahau gaskiya.
Hankalin su baba k'arami yakuma tashi, ace 'Yar k'aramar yarinya dani amma da hawan jini, (ALLAH yay gaggawar sakamin akan duk mai hannu akan wannan tushen matsalar).
Da k'yar aka samu nasha shayi, nasha magani barci yakuma kwasheni.
Sai kusan 10pm su Abba suka tafi gida, akabar Mama Rabi'a da Munubiya zasu kwana dani.
***°••?***°•••?***°••?***
Yana shirin fita asibitin sai ga Momma tadawo gida, tun yana sakkowa daga benen ya hangota zaune afalo itada jakadiya, da alama magana sukeyi.
Takun takalmansa da k'amshin turarensa yasasu juyowa suka kalleshi gaba d'aya, ya k'araso cikin falon cikeda takunsa na asalin jinin sarauta cikakke. Kujerar gefen Momma ya zauna yana fad'in “Momma yaushe kika shigone??.
Idonta akan d'an nata tana nazartar yanayinsa tace, “ban dad'e da shigowa ba, nama zata barci kakeyi ai? danJakadiya tacemin tuni kana gida?.
Guntun tsaki yayi yana lumshe ido, tare da kuma jingina kansa jikin kujerar, ahaka yace, “wlhy kuwa Momma, nad'an tsaya wani aikine aciki?.
Idanu ta tsira masa domin hango damuwa k'arara a fuskarsa. “Muh'd mike faruwane? mike damunka??.
Idanunsa da har yanzu suke da sauran ja ya bud'e, yasaki murmushin gefen baki, “babu komai Momma, mikika ganine??.
“bakaso dai nasani kawai Muh'd?.
Yad'an narke face alamar shagwa6a, “please Momma ki yarda dani mana?.
Girgiza kai kawai tayi tana murmushi, “to na yarda dakai. yanzu sai ina??.
“dama zanje hospital ne, dan inaga zanje Goa gobe idan ALLAH ya kaimu, maybe kuma na kwanama?.
“ok. ALLAH ya kaimu to, dama muna magane da jakadiya akan akawo wasu sabbin bayin, kaga aikin yanama su Samha yawa a gidannan Muh'd, gakuma makaranta, idan suka fita kaima ka fita sai gidan yay shiru, gashi mukuma muna Asibiti?.
6ata fuska yayi yana gyara zamansa, “Amma kuma Momma bakwa tunanin a kuma samun matsalar datafi ta baya? kiduba kiga dad'ewar da mukayi da wad'ancan, amma hakan bai hanasu munafuntar muba?.
“Humm Muh'd kenan, wancan karonma bawai dabararmu bace ta tsaremu, muyi hak'uri akawo koda guda 20ne, maza 10 mata 10?.
“kai Momma, amma har 20 ma?, ina laifin 5 kawai, idan sukayi yawa gidanan hayaniya zaiyi yawane?.
“wane irin 5 kuma Muh'd?, yanzu badan laluraba data kawomu nan ta ajiyeba konan da can ka isa matsawa batareda bayi ko dogaraiba, sha'anin gidan sarauta sai hak'uri, wlhy tunda aka kwashe bayinan gidan saiyayi wani iri, tamkar bana masu sarauta ba, yanzu haka kullum k'orafin Mimi kenan adawo da bayin gidanan?.
“momma kenan saboda Aunty Mimi za'a maidosu??.
“kusan haka to, saboda ita saboda buk'atunmu muma ko?.
“shikenan, sai a dawo damasu min hidima idan naje ko??.
“a'a baza'ayi hakaba, idan an kwasosu kaikuma idan kaje kuma fa? wad'ancan munriga da mun yardaba da amarsu, idan mun maidosu nan kafin mu samu masu amanarsu zamusha wahala,, amma idan nan aka kawo mana wasun zamu saka ido sosai akan su yanzu ai??.
Kai kawai ya gyad'a mata batare da yace uffanba. saikuma zuwa can yace “inaga nima next week zanje Nigeria ?.
“Nigeria kuma Muh'd? mizakayi??.
“murmushin gefen baki yayi yana kallonta, kwantar da hankalinki Momma, 3days kawai zanyi na dawo, wani d'an aikine zai kaini, ko masarauta bazasu San najeba ma Dan ba a can zan saukaba?.
“Amma Muh'd baka kudin abinda zaije ya dawo? kuma kana ganin zaka iya Shiga Nigeria kafito batareda kowa yasani a masarautarku ba??.
“kimin addu'a Momma, insha ALLAHU lafiya lau d'anki zanje ya dawo kinji, kuma zanyi taka tsantsan d'in yanda bazasu San najeba insha ALLAHU?.
Murmushi Momma tayi, tace “to shikenan, ALLAH yabada nasara akan abinda za'aje, yakuma tsare mana kai. amma nikam Muh'd yamagar yarinyar nan da aka muku 6atancinnan tare??.
“ban saniba Momma, dan ni ba saninta nayiba fa?.
“amma dai gaskiya ba a k'yautaba, yarinyarnan dukda anazargin da had'in kanta yakamata anemi iyayenta ai, amma ba ayi burus da lamarinta ba, kuma wannan aikin Kaine yakamata kayishi tunkan kabaro k'asar alokacin?.
“Nima nayi tunanin hakan daga baya Momma, amma wlhy a time d'in hankalinane yatashi sosai, sai dai karki damu, a wannan karon zansa amin bincike akanta?.
“hakan yafi kam gaskiya, bara na kimtsa saimu wuce k'ila kafin mu tafi su Sauban sun dawo. antafi d'akko Khaleel kuwa??.
“ai da sauran time Momma, kuma nifa yanzu nace aringa kawoshi a school bos, dan kinga mu ba kullum Muke gidaba, ga khumar har yanzu bai dawoba, inaga jikin mahaifiyar tasa yayi tsanani shima?.
“kama tunamin wlhy Muh'd, yakamata koda kaida Sauban ne kuje Ku dubata, wannan shine adalci da zakama Wanda yake k'ark'ashinka idan wani Abu yasamu rayuwarsa?.
“Hakane wlhy Momma, zamuje insha ALLAH, miye ma sunan k'auyen nasune??.
“nikam nad'an manta, amma bari zan tanbayi jakadiya kota rik'e?.
“ok tom shikenan?.
Tunda Momma ta shige saiya maida Kansa ya kwantar jikin kujerar, yacigaba da tunaninsa datum d'azun yake cin zuciyarsa da ruhinsa. baya buk'atar shawara da kowa akan wannan maganar gsky. to amma koya fad'ama Harun?. kai a'a, inma fad'arne Muftahu yakamata ya sani, tunda shine ya d'ora akan aikin, kuma shi kad'ai yasan komai akan yaran, to amma ba komai ne Na sirrinsa Muftahu ya saniba ai. (zuciyarsa tace, to ai wannan baikai girman sauran sirrikanka ba, kuma abune daza'ayi Na k'ank'anin lokaci yawuce, tunda ka yanke shekara d'aya ne ko biyu), iska ya furzo daga bakinsa yad'an dafe kansa dayakejin yana Neman fara masa ciwo.....
★★★★?
Washe gari natashi da d'an sauk'i, sai dai har yanzu hawayen sun kasa barin fuskata nida 'yar uwata Munubiya. mama rabi'a ce keta lallashinmu da mana nasiha, ahaka su Ayusher sukazo kawo mana break fast itada Feena, ya Marwan ya kawosu.
Daga gidanmu kam ko ruwan zafi babu Wanda yakawo har kusan 10, sai kuma ga Fauziyya itada Jameela k'anwarta, sukace inji mamansu, tace ayi hak'uri Mubarak ne shima babu lafiya.
Mukace mun gode ya jikin Mubarak d'in?.
Fauziyya tace, “da sauk'i, tare suke da maman tasu, sunacan zasuga likita?.
Anan su Fauziyya suka zauna ana hira dayake weekend ne babu school, kusan hirar duk akan abinda haidar yayine shida iyayensa, dagani har munubiya bamu saka musu baki, ni hirarma k'onamin zuciya takeyi.
Yaa marwan dake zaune a gefe yanata latsa waya tamkar baya jinmu yamik'e, kallon Munubiya yayi yace “zo mana?.
Saida yafita sannan ta mik'e tabi bayansa, su Ayusher suka sanya dariya suna fad'in soyayya ruwan Zuma.
Nidai bance komaiba, saibin 'Yar uwata da kallon tausayin zama da wannan mai shegen miskilancin nayi. zama da irinsu yaa marwan sai mai hak'uri wlhy.
A ranar da daddare aka sallameni muka koma gida, sai dai 'yan gidanmu maman Fauziyya ce kawai tazo, amma ko innaro batazoba. sai bayan an sallamemu su Dady sukaji babu Wanda tazo dubani. kuma Maman fauziyya Ce kawai me kai mana abinci, dukda ba ranar aikinta bane haka take dafa mana su fauziyya sukai.
Aiko ranar sunga tsantsar bala'i, dan su Abba birkice musu sukayi suduka ukun, har Dady da ake gani mai hak'uri. ita kanta innaro saida tasha jinin jikinta ga 'ya'yan nata.
Nacigaba da samun kulawa wajen innarmu da 'Yar uwata Munubiya, duk hanyar dazasubi Dan samamin farin ciki ita sukebi, burinsu kawai suga Na manta komai, hakama iyayena maza, sai