Author : Bilyn Abdull Category : Romance
hanya suka shigo falon, duk suka zazzauna.
Muduka muka durk'usa muka gaisasu, yayinda suka kuma gaisa dasu innarmu cikin mutunci.
Fita baba k'arami yayi yasa yaa Anas ya kunna Gen..... dayake babu nepa. Shikuma yakuma fita da hanzari domin nemawa wad'annan bak'i masu bazata kayan tarba, bayan yakira Dady da Abba ya Sanar musu.
Kaf matan gidanmu suka shigo, kowa yanason jin daga ina kuma.
Mukam d'akinmu muka koma muda su Ayusher muna hasashen bak'i daga ina haka? da gani dai kasan jinin sarautane, ko kad'an ban kawo Galadima a rainaba ma, dan narigada Na shafe labarinsa ni.
Suna cikin gaggaisawa da matan gidanmu saiga innaro tashigo, kai kace an wurgotane. baki tarik'e tana fad'in “o ni Marwanatu, manyan bak'i irin wad'annan surasa gurin sauka sai 6angaren Ai'sha? kuko bayin ALLAH daga ina haka? ?.
Su aunty Mimi basu fahimci zancen taba, dan haka duk sai sukayi d'an murmushi, matan gidanmu kuwa kowacce tayi k'asa da kai dariyar mugunta Na cinta, Innarmu dai bata tankaba, hakama mama Rabi'a, sai inna lami ce tace, “yo inna in banda abinki waka hana rana fita idan lokacin fitar tata yayi??.
Kallonta innaro tayi zatayi magana baba k'arami yashigo da sallama, su Yaa Anas na biye dashi da kayan ciye-ciye nik'i-nik'i, bayan sun ajiye suka gaishesu cikeda girmamawa suka fita.
Zama baba k'arami yayi suka sake gaisawa, sannan yace, “kufayi hak'uri, mukam duk kun sakamu a duhu wlhy?.
K'asaitaccen murmushi aunty Mimi tayi, domin dama papi yamata bayani akan komai na 6oye musu dasukayi. ta gyara zamanta sosai “Alhaji daga masarauta muke, munkuma zo kawo kayan k'anwatane Gimbiya munaya?.
Kusan kowa dake falon saida ya waro idanu waje, domin jin furicin aunty Mimi, wasuma zuciyar tasu kad'an tarage tayo tsalle waje.
Aunty Mimi bata damu da yanayin nasuba tacigaba da fad'in “kuyi hak'uri fa, nasan nakuma sanyaku a wani duhun, mai martaba sarki Abdul'fatah da maimartaba sarki Jalaludden Abubakar, sune sukazo Neman auren yarinyar Ku Munaya wa d'ansu Galadima Muhammad Sameer Saifuddeen Abubakar, sun 6oye muku kansune saboda wani dalili, amma sun aikomu da sak'on ban hak'uri a gareku, yanzu dai mun kawo kayan lefen Munaya ne gasunan?.
Jin jina kai kawai baba k'arami ke iyayi, bakinsa yakasa rufuwa saboda d'unbin farinciki da al'ajabin dake dank'are a zuciyarsa, yanzu nan daman manyan sarakunane agabansu a wancan karon sukazo Neman auren d'iyansu, lallai sun godema ALLAH dabasu aikata wani Abu Mara k'yauba agaresu, lallai ya yarda kwarjinin mulkine yasakasu mik'a Auren d'iyarsu ga mutanen dabasu saniba.
Ai su madam innaro sai aka zauna k'asa babu nauyi, muryarta har zuga take tace “ranki ya dad'e wai gaskene saboda ALLAH?, kokuwa wasa kikeyi??.
Murmushi aunty Mimi tayi, sannan ta kalli su Ummu hasheem da suma suketa murmushi, kallonta ta maido akan innaro, “hajiya kaka mizaisa muzo muyi muku wasa irin wannan akan magana mai muhimmanci irin ta aure, tabbas maganar nan gaskiyace, munama fata gobe idan ALLAH ya kaimu iyanzu Munaya tazama d'aya daga cikin zuri'ar masarautar gagara badau?.
Innarmu da mama Rabi'a juna suka rungume suka fashe da kuka, yayinda innaro tamik'e ta callara gud'ar data jawo hankalin tawagar jama'ar 'yan biki, sai kawai tashiga taka rawa.
Dariya sosai tamaba su aunty Mimi, shi Kansa baba k'arami dariyar yayi yana girgiza Kansa da mamakin innar tasu mai kayan arzik'i Dana tsiya.
Matan gidanmu kam ba'a magana, kowacce tayi d'if takasa koda kwakwkwaran motsi, kowaccensu jitake tamkarma tafasa ihu take a nan.
Muryar gwaggon halimatu na rawa tace “wai da gasken dai Munayar gidan sarauta zatayi aure??.
“kwarai kuwa?. ‘innaro tafad'a tana mata wani kallo, “jikata sai gidan sarauta, masu bak'in cikin kuma sai a mace?.
Lallai maganar innaro tadaki zukatan dukkan matan gidanmu, Sanin halin innaro da baba k'arami yayi saiyace duk afita abama bak'i waje susha koda ruwane.
Jiki babu kwari sukaita Jan k'afa suna fita Su da danginsu 'yan biki da gud'ar innaro tajawosu shigowa. bak'in cikin kuwa k'arara a fuskokin wasunsu, maman su yaa hameed tayi taga-taga zata fad'i saida aka taryota.
Gwaggo Safiyya tace “lallai jama'ar gidannan yau ake *RAINA KAMA KAGA GAYYAFA* duk Wanda kake Kallon bai kaiba to tabbas watan watarana shine zai kereka, babu ruwan arzik'i da mugun gashi, Wanda yace shine to tabbas bashi baneba?.
Su Ayusher suka shigo suna gumtsa mana, kallonsu kawai nakeyi amma badan na gaskataba, munubiya ta rungumeni ta fashe da kukan dad'i, kallonta kawai nakeyi nakasa koda motsi, to murnar Auren shekara d'aya zanyi? Kokuwa murnar Ashe galadimane mijin nawa? bawani can da ban ba kamar yanda muketa hasashe?.
Ban iya ta6uka komaiba wata k'yak'yk'yawar budurwa tashigo, daka ganta kaga wadda Hutu yagama ratsawa, babu shakka zamu iya zama sa'anin juna da ita, fuskarta d'auke da murmushi tace, “to ina amaryar Uncle Sam d'in??.
Feena ta nuna ni da hannu itama tana murmushi.
Gadon ta hayo batareda jiran abata iziniba, ta mik'amin Chocolates guda biyu tana kuma fad'ad'a murmushin nata.
Cikin mamaki muryata a sanyaye na girgiza mata kai nace “yar uwa namiye??.
Hannuna takamo tasakamin tana 'yar dariya, “inji Uncle Sam yace nabama matarsa, sunana Samha, d'iyar yayar Uncle Sam ?.
Duk da mamakin daya cika zuciyata, hakan bai hani mata murmushiba, nace “nagode Samha?.
Tad'an langa6e kai alamar itad'in shagwa66iyace tace , “zan dai fad'ama Uncle Sam kin gode, lallai Uncle ya iya za6en k'yak'yk'yawar sarauniyar gagara badau mai jiran gado insha ALLAHU?.
dariya su Bilkisu sukayi, nidai nakasa cewa komai, sai d'an murmushi danayi.
Ta dafa munubiya takuma fad'in inason twins sisters arayuwata, dan ALLAH nima kuna sona??.
Yanzun kam kasa daurewa nayi, nima saida na dara kamar yanda su munubiya ke dariyar, nakula ko kad'an Samha batada girman kai irinna 'ya'yan sarauta, sannan tanada surutu gaskiya?.
Cikin shagwa6a ta langa6e kai gefe, “ALLAH da gaske nake kubarmin dariya, ina addu'ar ALLAH yasa nanda wata 9 aunty ki Haifa mana twins muma?.
Amin su Ayusher suka amsa atare.
Matsowa tayi kusa dani tafara mana hotuna, nidai nakasa ma magana, lallai Samha akwai rawar kai, ta tubure da shagwa6a wai sainayi murmushi kamar yanda munubiya tayi, tanason taje tabama Galadima tagani kozai iya banbancemu. Babu yanda na iya dole na murmusa akayi, sannan mukayi gaba d'aya.
Bata bar d'akinba saida mama Rabi'a tashigo kiranta zasu tafi, aikam kamar tayi kuka, dan bataso tafiyarba, sai dai tace anjima zasuzo wajen brothers and sister's event.
Har k'ofar gida su Ayusher suka mata rakkiya, dan lokacin su aunty Mimi harsun fita, sunso ganina amma sukayi shiru kar aga kamar dawata manufa sukayi hakan, sun hak'ura tunda dai insha ALLAH gobe ina cikinsu.
Basuci komaiba dai a kayan da'aka jibge musu sai ruwa, dan haka baba k'arami yasaka aka bisu dashi mota, yace inhar ba wai bazasu iya cin cimar tamu bane to dan ALLAH suje dashi koda bazasuci ba su bada.
Godiya sukayi, suna mai yaba halaccin wannan gida mai cikeda karamci, dukda dai sunkula akwai lauje cikin nad'i gameda wannan family d'in, musamman yanda wasu suka kasa 6oye hassadarsu, aunty Mimi ta murmusa a zuciyarta tana fad'in Ashe ba masarautar mu kawai baceba keda irin wannan kitimurmurar ta family.
Mukulin farar motar da aka zubo akwatinan suka dank'ama baba k'arami sukace ta amaryace.
ai yanzu kam rasa abin fad'a baba k'arami yayi, yak'agara 'yan uwansa su dawo suga wad'annan tarin baiwa da hikimar ubangiji da yayma d'iyarsu, wadda akulum ake ganin mahaifiyar yaran a k'ask'ance acikin gidan, sai gashi tazama *RAINA KAMA.....*
Bak'i na tafiya gwaggo Safiyya tasaka aka baje manyan tabarmi a tsakar gida, aka fiddo akwatinan domin kowa yagani, makwafta duk sun shigo suma kam dan kar ayi babusu.
Gaba d'aya gidan yacike da shewa da hayaniya, tun anama irga kayan har aka bari, saibi da idanu, 'yan bak'in ciki kam sun kume waje guda, sai kukan zuci, wasuma kasa daurewa sukayi suka bar wajen.
Kasancewar su Ayusher duk suna can nashige toilet d'inmu nashiga raira kuka, nifa bammasan yanda zan fasalta muku yanda nakejiba wlhy.
★★★★
A 6angaren sister's d'ina kam su Safara'u harda kukansu, fauziyya ce kawai ta nuna farincikinta, dan har d'aki tashigo ta rungumeni tana ALLAH ya sanya alkairi.
maganar tashin hankali ga jama'ar gidanmu ba'a magana, sunma rasa yanda zasu masalta lamarinma, maman yaa hameed data kasa hak'uri saita saka masifa da zage-zage wai ai munafurcine su abbanmu suka shirya, wannan zancen k'aryane akwai magana a k'asa, 'yan koranta ma irinsu momy Hadiza suna tayata.
Nanfa gidan ya hargitse da hayaniya, kowa da abinda yake tofawa, innaro dai Abu biyune ya dameta, farinciki dakuma damuwar abinda tayita ma innarmu shekara da shekaru, yau kuma gashi ALLAH ya d'aga darajarta, ita dawanne ido kuma zata kalli Ai'sha.
Babu Wanda ya tanka a 6angaren innarmu, saima farinciki dasu mama Rabi'a ketayi abinsu, inna lami kuwa da aunty salamah sunata callara gud'a dawasu acikin matan anguwarmu, hakanne yakuma harzuk'a su maman Safada'u, suka murje idanu sunata zuba tsiya, danginsu na tayasu.
Innarmu dai tana daga cikin d'aki abinta, sai zuba murmushi take tana sharar hawayen dad'i, yau kokad'an rashin mutuncin 'yan gidanmu bai 6ata rantaba, saima wani farin ciki dasuke sakata.
🤣🤣
Maganar sisters and brothers event kam ai bai yuwuba yau, dan gidanmu gaba d'aya a harmutse yake, ga 'yan anguwa sunata turuwar zuwa ganin kaya harda mota.
Nikam ma zazza6ine yagama rufeni tunda nagama kukan, duk wannan kacaniya da akeyi ina cikin bargo k'udundune, su munubiya kam sunacan tsakar gida sun kasa sun tsare akan kayan gudun masu suruf bahana😜🤣.
Da k'yar aka tartare kayan aka kaisu falon baba k'arami kasancewar magriba ta gabato, sai bayan isha'i su Abba da Dady suka gani, ranar Abbanmu shima saida yayi kukan dad'i, ALLAH Sarki Ai'sha, nagodema ALLAH da wannan babban al'amari yashigomin ta 6angaren tsatsonki, kema yanzu k'ya samu 'yancin kanki agidan mijinki, 'ya'yanki zasu samu 'yanci a gidan mahaifinsu, dama akance ka yarda da k'addara kakuma godema ALLAH a yayin da ya jarabceka, Ashe sharrin da akama d'iyarsa zai zame mata alkairine, sun had'ata da babban mutum domin 6atanci agareta dashi kansa Ashe zai zama sanadin alkairi a rayuwar yaranne, dan yasan inba dan wannan abin yafaruba ina Galadima zai ga munaya har iyayensa sunema masa aurrenta? hikimar ubangiji yawane da ita, yakan jarabeka domin kankare zunibinka, kokuma danya d'aga darajarka ta inda bakayi zato ko tsammaniba.
★★★★★★
Labarin tarbar mutunci dasuka samu tuni ya karad'e masarautar, wasu kam dariyama abin yabasu, ina wata tarba dazasu samu ga talakawa fak'irai. suna dai fad'ane dan kar amusu dariya.
Mama Fulani koda labarin yaje kunnenta saita ta6e baki tana murmushi k'asaita, Wanda ita kad'ai tasan fassarar kayanta.
Tsaf yagama shiryawa zaije sashen da aka sauke abokansa a cikin masarautar, dan babu damar saukesu a 6angarensa, saboda angama masa gyara tsaf amarya kawai ake jira, su aunty Mimi ma dasuka kai lefe sun Sanar da amaryarsu kawai suke buk'ata, basai su Abba sun wahalar da kansuba wajen kaita da komai. Wannan dalilin yasaka aka yanke shawarar k'arama munubiya kayan munayar kawai, da safe za'aje a kuma jera mata su a gidanta😄.
Cikin takunsa na kasancewar cikakken namiji mai tashen k'uruciya ga jinin mulki dake yawo ajikinsa yafito, waya ce manne a kunnensa, yayinda d'ayan hannunsa ke cikin aljihun jeans d'insa, bayi da hadiman gidan sai zubewa sukeyi suna kwasar gaisuwa, kansa kawai yake d'aga musu yayinda yake cigaba da wayarsa da Momma wadda tana India ita batazoba.
Samha tak'araso gareshi a hanzarce, “Uncle ka tsaya mana please ?. ‘tayi maganar a shagwa6e saboda ganin ya basar da ita tamkar baima gantaba?.
d'an juyowa yayi ya kalleta sannan ya d'auke idonsa yana cigaba da Murmushin sa na k'asaita saboda addu'ar da Momma ke jero musu ta zaman lafiya da samun albarka ta har abada acikin auren daza'a d'aura a gobe. jiyake tamkar yace Momma ta dainama auren shekara d'ayannan addu'a irin haka, shifa harma tausayi suke bashi yanda suke nuna farin ciki da zumud'insu akan auren, musamman idan ya kalli yanda masarautar tagama cika tab da dangi takowanne 6angare, ga tawagar wasu masarautu dasukayo gaba tun yau, hakama 'yan siyasa ba'a magana, dan ba k'aramar gayya papi da Sarki sukaima wannan aurenba, kasancewar shine jika namiji na farko dazaiyi aure a masarautar, Wanda kuma kowa ke saka ran shine magajin sarautar masarautar.
Ita dai Samha tana tsaye tana kallonsa harya kammala wayar da Momma ya kashe.
Had'e fuskarsa yayi yana hararta, “to maganatu miya faru kuma? kike kwalan kira tundaga wata uwa duniya?, wai sai yaushene zakiyi hankali Samha??.
Baki ta tunziro gaba, idonta harya cika da gwalla “amma dai Uncle aina fara yin hankalin ko, kumafa wani Abu Nazo na nuna maka, naje Sashenka wannan sarkin k'ofar yawanice kana wajen mai martaba?.
Kansa kawai ya girgiza yana kallonta, saida takai aya sannan yace “to aini inada abunyi, yanzuma ba wai sauraren naki zan zauna yiba, dan nan ba India bane, ba'a ganina available ko yaushe OK??.
Harya juya zai tafi tarik'o hannunsa tana daddaga k'afafu idonta na zubar da hawaye.
Kansa ya dafe domin sanin fitinar Samha, tace,
“please Uncle Sam 2munutes to?.
Juyowa yayi tamkar zai maketa, saikuma komi ya tuna ya fasa, d'an cije lips d'insa yayi yana hararta, “ke wai wace irin fitinanniyace ne?, Uwarmi to zaki fad'amin??.
Dariya tayi tana share hawayenta dan ganin tasami nasara, wayarta ta daddana sannan ta mik'a masa.
Nanma Harar tata yayi kafin ya kar6a, itace yagani a photo da 'yammata biyu masu kama d'aya, kamarma yarinyar dasuke shirin auren contract, harya yatsina fusaka zaice suwaye? saikuma yatuna. d'an murmushi basarwa ya saki kafin ya kalli Samha da ta tsaresa da idanu. “Uncle ina aunty Munaya anan? ?.
Wayar yamik'a mata yay gaba abinsa yana fad'in titsiye zakimin ma kenan? an fad'a miki bazan ganeta baneba??.
Baki ta turo tana k'unk'uni, “waikai Uncle Sam bazaka ta6a canjawa baneba? kai kenan kullum sai jan ajin tsiya, shiyya sama ALLAH yayoka jinin sarauta wlhy, Aunty Munaya kin bani da wannan mijin naki mai k'asaitar tsiya, aiko wlhy tunda kace haka saina had'a maka mugunta gobe a wajen dinner ?.
Ta tuntsire da dariya saboda tuno mizata shirya masa.
★★★★?
*Rana bata k'arya........*⛹🏻♀
Yau mun wayi gari safiyar d'aurin aure, gida yakuma d'inkewa da jama'ar dukda d'aurin Auren na Azhar ne bayan sakkowa masallacin juma'a.
Tun jiya banida lafiya, amma na hana su Ayusher fad'ama kowa, sai Magani suka samo min nasha, itama dai Munubiya duk sukuku take, babu abinda ke damummu sai jimamin rabuwa da juna, dan itama kusan zazza6inne ma ta kwana dashi, sai dai dayake nawa ya had'a da damuwa saina fita nuna jin jiki.
Jama'ar gidanmu dai a harmutse suka kwana, wasuma ko barcin basu sami damar yiba saboda ciwon hasada dake cin zukatansu, gashi gida d'inke da jama'ar babu damar matsawa koda nan da canne sai an gane, bare sufita neman mafitar tarwatsa Auren, waddama suke d'an samin tallafinta kwad'ayinta yasaka canja shek'a (innaro🤣), dan jiya da suke zuba tijara shigowa tayi tamisu tas, harma tana Neman tone musu asiri gaban tawagar 'yan biki, badan gwaggo Safiyya ta lalla6a taba ba'asan inda jarabar innaro zata tsayaba kam.
Ko karyawa ban iya tashi nayiba bare aje maganar wanka, ina kwance cikin bargo sai shar6ar kuka nakeyi babu wanda yasani.
Ahaka gwaggo Safiyya tashigo kiranmu nida Munubiya, da k'yar su Ameera suka samu natashi zaune ina tangad'i, gaba d'aya nayi wujiga-wujiga dani, da taimakon Munubiya dake rik'e da hannuna muka iso gidan innaro inda su Abba suke jiranmu.
Gaba d'ayanmu ne amaren aka had'a, abin mamaki saiga innaro ta kamani ta zaunar tanamin sannu, harda lallashina wai na