Author : Bilyn Abdull Category : Romance
iyayenmu muka gaida yaa Fadeel, sannan mukaima Feena ya jiki, ta amsa tana murmushi.
Ayusher daketa antaya mana harara Na kalla, “kekuma lafiya kike wani hararmu??.
Harar takuma watsa mana tana mik'ama Feena kofin tafarnuwa, “ban saniba 'yan rainin hankali, tun k'arfe nawa kukace zaku taho amma sai yanzu??.
Munubiya tatashi taje inda take ta rungumeta, sorry habibati, wlhy mun biya shagon aunty ne munyi kitso, saikuma ta tsaremu wai sai munyi k'unshi, tamace a gaidaki?.
“kai shine baku kirani mun jeba? wlhy nima kan nan nawa yana buk'atar kitso, tana lafiya?.
Namik'e ina fad'in “Sumul- sumul, mukuka dafa? ALLAH yunwa nakeji??.
Cikin tsokana mama Rabi'a tace “tuwo?.
Na tunzuro baki gaba, kai mama wai keda innarmu kullum tuwo bakwa gajiya??.
“yo yaza'ayi mu gaji tunda shi mukaci muka girma, kajimin ja'iran yara, wai kukam bakuda mak'iyi sai tuwone??.
yaa Fadeel yace “yo k'aton ciki yake saka mutane, ina dalili?.
Dakuwa innarmu tamasa, “gidanku Fadeel, mu miyasa bamuyi k'aton cikinba??.
Feena tace “ALLAH innarmu gaskiya yaa Fadeel yafad'a fa?.
“lallai Nafeesa, kema ina ganinki salo-salo Ashe k'yallece?.
Dariya muka sanya gaba d'aya, akuma wannan lokacinne yaa Marwan yashigo da sallama.
Su Aiyaan sukaje da gudu suka taryoshi da amsar kayan hannunsa.
Waje yasamu ya zauna yana gaida su innarmu, muma muka gaidashi.
Ayusher datasan dokarsa ta yana shigowa a kawo masa ruwa ta kalli Munubiya, sis.... Please kibama yaa Marwan ruwa, ni nariga da na ta6a tafarnuwa?.
Kamar munubiya bazata tashiba saikuma tamik'e saboda harara daya antaya mata, shi zatonsa ma nice, dan yasan Munu.... Akwai sauk'in kai.
Mama da innarmu kam hirarsu suketa zubawa kamar basusan mi mukeyi ba.
Babu dad'ewa saiga Munu... da k'aramin tire tazubo ruwa mai sanyi a jug, ajewa tayi a gabansa, ta durk'usa ta tsiyaya masa tabasa, sai da suka had'a ido ta janye nata da Sauri, alokacin ya fahimci Munubiya Ce, yana gama shan ruwan yadire kofin yana mik'ewa, “ki kawomin abinci d'aki?. ‘yafad'a yana yin gaba abinsa?.
Tad'an bishi da kallo sannan tamik'e takoma kitchen d'in.
Kallon juna mukayi nida Ayusher muna d'aga gira, yaa Fadeel daya gammu shima saiya saka dariya, k'asa-k'asa yanda su inna bazasuji ba yace “muma ALLAH kabamu masu sonmo?.
Muma ahankali mukace amin nida Ayusher.
Feena tace “ALLAH ya shiryeku, dama yajiku wlhy?.
Yaa Fadeel yace “saidai su susha duka, nikam ai bani dokuwa?.
Nanma dariyar mukayi.
Da sallama tashiga d'akin, yana zaune bakin gado dagashi sai vest da dogon wandon kayansa bai cireba, wayace a hannunsa yake latsawa, ta dire tiren abincin a gefe sannan ta janyo k'aramin table d'in gefe gabansa, abincin ta zuba masa, har sannan bai kalleta ba, saida tagama zata tashi yace “wato k saima ance kibani ruwa ko??.
Shiru Munu... tamasa, Dan batasan mizata ceba, yad'ago idanunsa irin nata (dan duk 'ya'yan mama Rabi'a kama muke da juna, saboda ita suka biyo, idan kacire Feena dake kama da babansu) yana kallonta, itadai kanta ak'asa tana wasa da zoben hannunta.
“baki jina ne??.
Ahankali tace “kayi hak'uri to?.
Shiru yamata bai tankaba, yaja abincinsa yafaraci anutse, baice ta tashiba itakuma bata tashinba, gashi bawata hira sukeyiba, ita tunaninma yanda zatayi zaman aure da yaa Marwan takeyi, Yaya za'ayi rayuwa tayi dad'i Dan ALLAH?.........
maganarsace tasaka ta d'ago ido tad'an kallesa, shima idonsa Na kanta. ta janye nata idanun.
Yakuma fad'in “nace yaushe zakije kiga gidanki??.
Saitaji maganar wata iri, wai gidanta, gidansa dai, muryarta a sanyaye tace ai basai najeba?.
Yace “ko??.
Kai ta d'aga masa alamar eh.
Yad'anyi wani munafukin murmuahi, Sanan yamik'e yanufi hanyar bathroom yana fad'in “ki shirya jibi zanzo na d'aukeki da yamma?.
Bai jira amsarta ba yashige abinsa. tadad'e zaune tana kallon k'ofar toilet d'in, tamkar nanne zata ganoshi, saida taji motsin kamar zai fito sannan tamik'e da sauri ta kwashe kwanikan ta fice.
Bamu bar gidanba sai bayan sallar isha'i, yaa Marwan da kansa ya kaimu har gida.
_____________________________
Yana kwance a falon gidan daya zama mafakarsa, waya suke da momma akan yaushe zai koma? dan doctors d'in Abie nason ganinsa.
“maybe ma gibe ki ganni Momma dan nagama abinda ya kawoni?.
“shikenan babu damuwa, amma kana ganin a masarautar ku babu Wanda yasan kazo??.
“babu Wanda yasani momma, hatta da Harun, sai Muftahu kawai?.
Cikeda mamaki tace “Muftahu kuma??.
“eh Momma miya faru??.
Tayi d'an jim sannan tace “babu komai, amma ka dinga kula dai Muh'd?.
Shima yad'anyi shiru yana nazarin maganarta, sai kuma yace “ok Momma insha ALLAH?.
Yana ajiye wayar kuwa saiga Muftahu ya shigo, kallonsa Galadima yayi.
Muftahu dake shirin zama yace “yalla6ai barka da rana?.
“ykk??.‘cewar galadima?.
“wlhy Alhmdllh, dama akan yarinyarne, kagafa har yanzu bamuji daga gareta ba?.
Murmushin gefen baki Galadima yayi, sannan yabud'o massage d'in da Munaya ta turo masa yamik'ama Muftahu wayar.
Babu musu Muftahu ya kar6a, saida ya gama karantawa sannan ya d'ago yana kallon Galadima fuskarsa washe da murmushi, “Alhmdllh yalla6ai ta amsa Ashe??.
Kallonsa kawai Galadima yakeyi cikeda nazarinsa, yana mamakin yanda Muftahu ke d'okantuwa da wannan maganar auren, tunda yabashi damar binciken su Munaya bai barsa ya hutaba, haka kawai sai zuciyarsa ta d'arsa masa wani Abu, musamman idan yay dubi da yanda Muftahu ya nuna tsantsar farincikinsa dayace zai auri yarinyar na shekara 1. to koma dai miye, zai sanya masa idanu.
Muftahu yace, “yalla6ai to yanzu ya za'ayi dasu mai martaba ne??.
Galadima dake latsa d'ayar wayarsa yace, “no, karka damu da wannan, zan k'arasa komai kawai?.
Kamar Muftahu baiso hakanba, amma saiyayi murmushin yake, “shikenan ALLAH ya tabbatar da alkairi, yasa ayi damu?.
d'ago ido Galadima yayi ya kallesa, “to miye kuma na wannan doguwar Addu'ar? Saikace wani auren gaskiya??.
“Hakane kuma yalla6ai, sorry?.
Shiru Galadima bai amsaba. falon ya d'auki shiru kowa da tunaninsa.
★★★★
Harda safe inata yawan duba wayata kozanga replay daga Galadima amma shiru, hardai munubiya tace “wai miye bini-bini saiki duba waya??.
Kallonta nayi ina k'ak'alo murmushin yak'e nace “babu komai fa?.
Badan ta yardaba ta k'yaleni, cigaba mukayi da aikin da innarmu ta samu.
Aryaan yashigo yana kuka, muduka mukace miya faru kaikuma?.
Cikin kukan yace “ba Abdul bane ya dakeni, wai dan Zainab ta zubamin ruwa na rama?.
Nace “ina Abdul d'in??.
“Suna wajen fanfo?. ‘cewar Aiyaan daya shigo yanzun?. “Auntynmu kuma wlhy sosai yabama Aryaan mari a fuska, sannan ya halbeshi ga k'afarsa har yafad'i?.
Da hanzari nafice daga sashenmu, na iske Abdul da sauran yaran gidanmu a bakin fanfo suna wasa da ruwa, rankwashin Abdul nayi tareda murd'e kunnensa, “mi Aryaan yamaka ka dakesa dan k'aniyarka??.
Hannuna yadafe saboda zafin dayaji na murd'ar kunnen, cikeda tsiwa yace “yoba Zainab ya daka ba danta watsa masa ruwa bata ganiba?.
K'eyarsa na mangara, “to ina ruwanka, Zainab d'in ba k'anwarsa baceba? kokuwa dan kai mama d'aya ta haifeku? daga yau kasake dukan wani acikinsu saboda yadaki Zainab ko Fahad saina lallasaka agidannan, masu shegen 'yan ubancin tsiya, iyayenku duksun 6ataku da k'in 'yan uwanku jininku?. nak'are maganar dakuma rank'washinsa.
Aikam ya daddage ya kwantsama kuka, kaikace wani uban bugu namasa.
Kamar jira gwaggon haleematu keyi tafito tana tambayarsa miya faru?.
Fad'a mata yayi waina mareshi da murd'a masa kunnen saboda ya daki Aryaan, harda cewa na zageta.
Hummm tamkar dama kad'an take jira damu, har k'ofar d'akinmu taje tana zazzaga masifa da zagina.
Innarmu tafito tana tambayar miya faru? dan ita bama tasan an bigi Aryaan d'in ba.
Maimakon tama innarmu bayani saita koma kanta da cin mutunci, kamar innarmu tayi shiru amma yau saita kasa.
Ta kalli Goggon haleema tana murmushi, Sadiya bakinki yasan mizai fad'a, inba hakaba zan baki mamaki agidannan wlhy, bakinki ya tsaya iya maganar yara, idan kika kuskura iyayena suka kuma shiga a furicinki zakiyi nadamar sanina?.
Innarmu nagama fad'a tashigewarta.
Galala gwaggon haleematu da duk matan gidanmu sukayi da mamaki, duk kuma sai shakkar innarmu ya shigesu, Ashe akwai ranar dazata iya maidama wani murtani acikin gidan?.
Murmushi nasaki, sannan nabama Munubiya dake kusadani hannu muka tafa, nace “ho innarmu, kina aljanna ina binki da addu'a, haka nakesonki agidannan, kiringa watsema kowa aniya?. naja hannun Munu.... muma muka shige ciki.
Abbanmu dake kallon komai ta window d'akinsa yasaki murmushi yana girgiza kai, yasan gaba d'aya halayen Munaya nashine, yarinyar batada tsoro, amma yau Ai'sha ta birgeshi datama Sadiya haka, koba komai tasaka musu shakkarta azukatansu.
Aikan kowa jiki babu kwari taja k'afarta tashige d'aki tana gulma da zuciyarta.
Gwaggon Haleema kam ai saida Nusaiba taja hannunta sannan ta iya d'aga k'afarta.
Koda muka Shiga sai innarmu tahau mana fad'a akan dukan Abdul d'in da nayi, hak'uri kawai na bata danni yau raina fes, innarmu tafara maida murtani.😅
★★★★?
Da k'yar ya iya bud'e idonsa ya janyo wayarsa dake ringing, batare da ya dubaba ya amsa yasaka a kunne.
“Assalamu alaika Muhammad kana lafiya??..
Zaram ya mik'e zaune tareda watstsayewar dole saboda jin muryar mai martaba mahaifin Momma papi.........✍?
To ko mai martaba zai amince da auren Munaya? duk da baisan kai tsaye auren yarjejeniya baneba🤔?.
Karku manta Amincewar mai martaba itace ta kowa.
Muje zuwa my guys⛹🏻♀⛹🏻♀⛹🏻♀⛹🏻♀⛹🏻♀⛹🏻♀
*_ALLAH ya gafartama iyayenmu_*😭🤚🏻✋?
[4/22, 2:17 PM] Zuraiyah Zuzu💖: *_Typing📲_*
*_HASKE WRITERS ASSO...💡_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_♦RAINA KAMA......!!♦_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
👉🏻1?8?
..........A Asibiti gado suka bani, sunata fad'an yanda jinina ya hau sama, su mamakima suke yi 'yar k'aramar yarinya dani amma inada hawanjini, shin miyayi zafi haka?.
Su Abba dai kasa cewa komai sukayi, dan su kansu abin na yata6a zuciyarsu.
Wannan karonma Mama Rabi'a da Munubiya ne suka kwana a wajena, washe gari da yamma saiga 'yan gidanmu wai sunzo dubani, bamuyi mamakiba Dan munsan ba domin ALLAH sukazoba, kawai sunzo ganin kwafne.
Duk suncika d'akin da surutu akan wai suna mamakin miya samin hawan jini?. daga mama Rabi'a har Munubiya babu wanda yabasu amsa.
Doctor ne yashigo yace sud'an ragu wasu su fita baranda dan ALLAH, duk fita sukayi harda mama Rabi'a aka barmu iya mu yaran kawai, dansu Fiddausi duk hadasu akazo.
Ina daga kwance kan gado ina sauraren hirar dasukeyi, wai safara'u da Halimatu ne sukaje gidan su Siyama tai tamusu yatsina da d'aukar kai, saikace ba 'yan uwanta ba, mijinta yadawo sukayi shigewarsu suka barsu afalo har yamma sannan suka fito, mai makon tabasu hak'uri sai cewa tayi wai dama basu tafiba🤣.
Wannan abun daya faru shine yajawo rigima a gidanmu jiya da daddare, har saida su Abba suka tsawatar.
Murmushi kawai nayi Na gyara kwanciyata, a zuciyata ina fad'in maganinku ai, baku masu dangiba..........gabana yafad'i, saboda jin tamkar k'amshin turarensa. da sauri Na d'ago kai saboda jin su Fauziyya ma sunyi tsit daga surutun dasukeyi suna kallon bayanmu.
Wani yaam naji a raina domin ganin Galadima da tawagar dogaransa, sai wani dake gefensa amma ba muftahu bane, (Harun ne). Sanye cikin k'ananun kaya wad'anda suka fidda ainahin k'irarsa ta cikakken namiji, fuskarnan kamar kullum babu walwala.
Mu 4 ne kawai a d'akin, dan haka yana tsaye a gadon farko da alama tanbayoyi yakema matar dake jiyya a gadon. gani nai yasaki wani guntun murmushin gefen baki sannan ya kalli harun, bansan miya cemasaba nagadai yabaro wajen yana tunkaro gado Na biyu.
A hankali Na lumshe idanuna wani Abu Na tsikarar zuciyata mai kama da tsoro da rud'ani.
Sauran 'yan uwana kam sun zuba masa idanu tamkar zasu cinyesa, kowacce takasa furta komai a fili saida a zuciyarta take tattaunawa da yaba Galadima d'in.
Annanma yayi kusan mintuna hud'u sannan ya tunkaro gadon takusa damu, dan nice ta k'arshe. duk da akusa damu yake banajin miyake fad'a, saidai motsin la66ansa kawai nake gani, tabbas Galadima naji da Girman kai da mulki, kallo d'aya zaka masa ka tabbatar da tsantsar sarauta da mulki dake yawo a jinin jikinsa....... tunda naga yanufo inda nake sai kawai narufe idanuna gaba d'aya.
Su Munubiya duk suka risina suna gaidashi.
Hannu kawai ya d'aga musu yamatso jikin gadon danake.
Tsantsar mamakine ya bayyana a fuskarsa, yad'anyi kamar zai nunani da hannu saiya kuma fasa, su safara'u kam duk sun zubo mana idanu suga yanda za'a kwashe.
Munubiya ce cikin k'arfin hali tace “Munaya ki tashi ana miki magana fa?. daka ganta kasan a tsorace take maganar.
Shima juyowa yayi ya kalli Munubiyar domin jin kuma Muryata, maganar Muftahu ta fad'o masa arai dayace yaran twins ne, kuma ba'a iya banbancesu.
Suma Kansu dogaran NASA da Harun duk sunyi tsuru suna kallonmu, domin babu wanda baiga jaridarba a wancan lokacin.
Maganar sace tasaka kowa maida hankali a kansa, nidai har yanzun idona arufe suke, cikin basarwa da nuna halin ko in kula yace, “ya jiki??. tamkar bayaso haka yayi maganar.
Nima cikin dakiya da shariyar kamar yanda yamin nabud'e idona nace “Alhmdllh?.
Kamar yanda yake tambayar kowa nima haka ya tambayeni miye matsalata?.
Na d'a6e baki sannan nace “masassara?.
Harun ya kalla, danshi baima fahimci minake nufiba.
Murmushi harun yayi, danya fahimci bai ganeba, cikin gyara tsayuwa yace “tana nufin fever?.
Caraf fiddausi tace, “ranka yadad'e k'arya take hawan jinine?.
Juyowa yayi ya kalli fiddausin da fararen idanunsa wad'anda suka nemi zautata, bai Ce komaiba ya janye ya maida kan Munubiya, “Sister naga drugs d'innan??. yafad'a kamar anmasa dole.
Ko kad'an Munubiya bataji maiya fad'aba, dan a saman la66ansa yayi maganar, tana shirin sake tambayarsa d'aya daga cikin dogaran ya maimaita mata a tsawace.
Nikaina saida Na bud'e ido saboda tsawar, Na bankama dogarin harara ina magana k'asa-k'asa yan da babu mai jina, kajimin shegen dogari, dan tace batajiba zakawani daka mata tsawa?, shi mizaisa bazai bud'e baki yayi magana yanda kowa zaijiba? Mutum sai azabar Girman kai mtsoww, koma R bai iyaba.
Duk maganar danake la66ana ne kawai ke motsawa, shikuma idon nasa nakan la66ana, dukda duba kwalin drugs dayakeyi, tsaf ya karanci duk maganar danakeyi. yayi wani munafukin guntun murmushi yana mik'ama Munubiya magungunan.
Juyawa yayi yama Harun magana, sannan ya juyo ya kalleni yana fad'in “ALLAH yak'ara lafiya?.
Harara Na zuba masa batare da tunanin zai ganiba, amma sai caraf muka had'a idanu.
Janye idanunsa yayi a kaina yajuya yabar wajen yana cije lips d'insa da mamakin yarinyar nan da batada tsoro.
su Safara'u Na zuba masa godiya, duk da zukatansu Na mamakin yanda yanuna tamkarma bai sanmu ba.
Ko kallonsu baiyiba ya d'aga musu hannu, sukuma sunyine dama danya tanka musu.