Author : Bilyn Abdull Category : Romance
[4/22, 2:13 PM] Zuraiyah Zuzu💖: *_Typing📲_*
*_HASKE WRITERS ASSO...💡_*
*_♦RAINA KAMA......!!♦_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!._*
👉🏻1?
*Matsanan cigar* hayaniyar dake tashi agidan ce taja hankalina, cikeda bak'in ciki natashi daga barcin safen dana koma, fitinar gidanmu dabance data kowane family House dana Sani kona ta6a jin labarinsa a rayuwata, haka gidan namu yake kullum tamkar kasuwar 'yan danbe, daga matan gidan zuwa 'yan mata da yara tamkar muna ganin hanjin juna, saika rantse badaga tsatso d'aya muka fitoba.
Kururuwar danaji maman Safara'u ta kurma yasani kuma jan dogon tsaki, sai kuma najiyo muryar gwaggon haleema Na fad'in “kai amma wannan lamari baiyi dad'iba, kekuwa maman biyu ya kamata ki canja wannan halin naki, dan tabbas inba wani abu kikayiba babu yanda za'ayi yaronan Sadeequ yadage shi cikinsu *MUNAYA* yakeso, duka yaushe aka gama maganar nan akan shafi'u amma shine zaki koma kan Sadeequ kuma yanzu??.
gaba nane ya fad'i, cikin zaro idanu waje nace, “ashema mu akanmu fitinar take yau??. yink'urin sakko nake daga gadon Munubiya tashigo tana share kwalla, binta nayi da kallo harta fad'a saman gadon ta kwanta rufda ciki tareda fashewa da kuka mai ban tausayi. Hakan Yakuma tabbatar min lallai mud'inne dai ake hargowar akanmu. a fusace Na dirgo daga gadon na nufi k'ofar fita, (ko kad'an banida hak'uri, musamman akan cin zarafin mahaifiyarmu da akeyi agidan lokuta da dama idan irin hakan ta taso), taku biyu nayi naji an damk'oni, najiyo cikin masifa dan nasan Munubiya ce.
“wlhy ki sakeni kafin nafara huce haushina akanki munu! yau saina gyarama kowacce 'yar iskar mata zama agidannan dan kutu.....
Bankai ga k'arasawa ba Munubiya tai saurin rufe bakina da tafin hannunta.
Kici-kicin kwacewa nafarayi amma nakasa, dan bak'aramin ruk'o taminba, raina yak'ara 6aci ainun danjin irin rashin kunyar da Safara'u ke zubama innarmu a tsakar gida, bansan na wancakalar da Munubiya gefe ba nafice da gudu.
Babu Wanda yaga fitowata sai dai saukar sautin marin dana zubama Safara'u a farar fuskarta sukaji.
Hakan yaja gidan yay tsit na wucin gadi, sai kuma hayaniya takuma 6allewa, Safara'u da mamarsu sukayo kaina danufin duka....
Tsawar da baba k'arami ya bugace tasaka kowa dakatawa tsakanin ni dasu, hakama matan gidan sai suka fara jan k'afafu danufin barin wajen.
A tsawace yace, “kar wadda tabar wajen!!?.
Tsitt kakeji gidan yayi, tamkar bashi bane d'azun ya cakud'e da hayaniya tamkar ana biki ko suna.
Jarabar gidanmu ba bak'on Abu bane a anguwarmu, danta rigada tazama tamkar ajininmu take (yo ajininmu mana zance) tunda kullumne babu fashi sai anyi hayaniya, kodai matan gidan kokuma mu 'ya'yan gidan. Babu mai d'agama wani k'afa koda na second d'ayane kuwa, yanzun zakaji gidan shiru, anjima k'ad'an kaji an doka gangar shaid'an, musamman ma fad'an yara dayafi komai saurin had'a fad'an matan gidan da a kulum, a rana sai ayi fad'a biyar akan yara kawai, innarmu ce kawai da Maman Fauziyya keda k'ok'arin K'aucewa irin wannan fitintunun dasuka zama tamkar shan ruwa acikin gidanmu.
Baba k'arami yafara fad'a tamkar zai ari baki, inda yake shiga bata nan yake fitaba, kowa yayi tsit yana saurarensa, (saboda kasancewar masifaffe shima) sai da yayi mai isarsa sannan yajuya yafita yana fad'in nida Safara'u mu sameshi falonsa. harda iyayenmu mata.
Duk abinnan da akeyi innarmu na kicin tana had'a Karin kumallon safe, kuma kalma d'aya bata tofaba a zancen nasu, datasan ma zan fito bazata barniba nima.
A falon baba jafaru yanemi jin ba'asin tushen fitinar, cikin d'aga muryar da hargowa maman Safara'u tafara fad'in “Alhaji wlhy kashiga tsakanina da maman biyu a gidannan, idanfa tanama sauran matan gidannan Yanda taske so, suna barinta nibazan bartaba, tasanni tasan waye ubana ehe, kum.......
Hannu yay saurin d'aga mata, “kinga Suwaiba nifa ba wannan ne yasani kiranku ba, sonake naji minene ya kawo hayaniyar??.
Cikin jin haushin an tareta tace, “Alhaji akan yaronnan Sadeequ ne, kowa yasan wajen Safara'u yake zuwa a unguwarnan, amma jiya da yamma sai ya aiko kiran Munaya, dayake ALLAH yatashi tonon asirinsu sabida bayaune na farko ba sai d'an Aiken ya kwatsa maganar a tsakar gida, babu dai Wanda yace komai, dan azatonmu ba Sadeeq d'in Safara'u baneba, goshin magriba saiga Safara'u tashigo tana kuka. Na tsareta da tambaya da k'yar tacemin cikinsu 'yan biyu tagani da Sadeeq a zauren gidan Malam halilu suna hira da dariya, kuma hardama mata gwalo akayi. Saboda na gaskata zancenta na sake aiken Rahma taganomin da idonta, harma taji Sadeeq d'in nafad'in ai koma miza'ayi bazai auri Safara'u ba, cikin wad'an nan munafukan yaran daba ganesu akeba zai aura, saboda darene yasani d'inne maganar a raina har safiyar yau d'inan, amma wlhy Alhaji da k'yar na iya barci nida Safara'u jiya.
“hummm? kawai nafad'a ina dafe kaina, saboda jin Yanda aka canja maganar.
Babak'arami ya kalleni yace, “Munubiya ce ko Munaya?? (dan basa ganemu saboda tsananin kamata da hassana ta).
Zuciyata cikeda bak'in ciki nace, “Baba Munaya ce?.
“yauwa Munaya, ina 'yar uwarki??.
“Tana ciki baba?.
Baba ya kalli Safara'u daketa matse kwallan munafurci tun d'azun yace, “k! Safara'u tashi kiramin Munubiya ?.
Batareda ta amsaba tatashi tafita, mintuna kad'an saigata sun dawo tareda Munubiya datasha kuka idanu sukayi luhu-luhu. tsaki naja a raina ina hararta ta gefen ido, rashin jarumtar ta na bani haushi, ta cika hak'uri da sanyin hali tamkar innarmu.......
Maganar baba ce tadawo dani daga tunanin dana tafi. nad'ago ina kallonsa saboda kiran sunana dayayi, muryar a dake na amsa da “na'am baba?. kallonsa ya maida kan Safara'u yana fad'in “wacece acikinsu kika gani tareda Saddik'un??.
Binmu da kallo Safara'u tayi, cikin matse kwalla tace, “baba niba ganesu nakeba, sai sun banbanta min Kansu sannan?.
Baice komaiba dan shima yasan da hakan, (ta hallaya ne kawai kowa ke banbantamu agidan, hatta da innarmu kuwa). Baba yabimu da kallo alamar son sanin wacece acikinmu.
Da sauri Munubiya tace, “baba nice?.
Nima na kar6e da fad'in “baba k'arya takeyi nice jiya Sadeeq ya aiko kira, kuma babu wata alak'a dake tsakaninmu, hasalima ya kirani ne akan Safara'un, sune dai suka maida zancen haka?.
Daga Safara'u har mamanta harara suka ballamin, babu ragi nima na rama kuwa.
Baba ne yakatsemu da fad'in “miya faru to Munaya??.
Janye idona nayi daga Kansu na maida gareshi, kaina ak'asa Nace,
“baba ya kirani ne yana tambayata minene abinda Safara'u tafiso a rayuwarta, dan yanason yabata gift na birthday d'inta, kuma soyake yayi mata bazata. shinefa nake lissafa masa muna dariya saboda ina cewa ya had'o mata da gyad'a soyayya dan ita mayyarta ce, a dai-dai lokacinne kuma na hangota zata shigo gida, nifa dama tsokana namata gwalon, Ashe ita ta d'aukeshi wani Abu. Kuma wlhy Rahma k'arya takeyi, lokacin data fito tareda yaa Hameed ta ganni yana bani kayansa nakai masa ciki shi zai shiga masallaci salla. Wannan shinefa abinda yafaru, shine suke cewa nakwace mata Sadeeq, har ana cin zarafin innarmu da farar safiyar nan?.
Ajiyar zuciya innarmu ta sauke a hankali, taji dad'i daba abinda suke zargin baneba.
Wata uwar harara baba jafaru ya watsama maman Safara'u, “kai Suwaiba kedai ALLAH ya gyaraki, dan ALLAH kuringa bincike akan Abu idan yara sun fad'a muku, tokinji dai abinda yafaru, kekuma Safara'u dayake bakida tarbiyya har bakinki yana iyama Ai'sha rashin kunya ko, ki tabbatar saina saka Abdulhameed yacimin ubanku keda Rahama yau a gidannan. Ai'sha kiyi hak'uri dan ALLAH ?.
Innarmu ta yink'ura zata mik'e tana fad'in babu komai babansu, ALLAH ya kauda fitinar gaba?.
“Amin? muka fad'a muma muna mik'ewa mukabi innarmu a baya.
Koda muka fito, sai matan gidan suka zubo mana ido suna kallo tamkar yau suka fara ganinmu, a raina nace munafukai, haka zaku k'are.
Ran innarmu ya6aci matuk'a a wannan karon, amma kasancewarta mutum mai hak'uri da shanye damuwa sai bata nunaba.
Nida Munubiya kam kasa shanye 6acin ranmu mukayi, munsan koma wace irin wulak'antawa za ai mana agidan *KAKARMU* ce taja mana, itace tabada kowacce iriyar k'ofar tozartamu, idan kaga abubuwan da ake mana saika d'auka ba jinin gidan baneba, tunda muka taso a haka muka tsinci kanmu, hakama mahaifiyarmu a wannan halin muka risketa tana fuskantar k'ask'anci da wulak'anci daga Kakarmu da matan Abban mu, harma da matan k'annensa, bamuda 'yanci irin na 'ya'ya, mahaifiyarmu batada kima irinta matar gida (Uwargida), hakan yasamo asaline dalilin................✍?
👎🏻
Tofa masu karatu dalilin mi? Dani daku duk muna buk'atar jin wannan dalili a bakin MUNAYA!, saiku kasance dani danjin Yanda wannan labari mai d'unbin harmutsi da tsalle-tsalle zai kaya, miye manufarsa? ina kuma ya dosa?.
Amsa d'aya zan iya baku.👇🏻
*_LABARIN MAI TSAWONE_*
saikun kasance dani a hankali zancigaba da warware muku lauje cikin nad'i.
ALLAH yasa zaku bani had'in kai, tabbatarwata shine yanda zaku kar6i wannan labarin.
Dan haka kumuje zuwa🥺✍🏼✍🏼
Zamu cigaba Monday insha ALLAH, wannan d'and'anone.
Sannan wannan karon zandinga typing ne Monday to Friday kawai insha ALLAH, kunga banda weekend kenan😊.
One luv🥰
*_ALLAH ka gafartama mahaifanmu😭👏🏻._*
[4/22, 2:13 PM] Zuraiyah Zuzu💖: *_Typing📲_*
*_HASKE WRITERS ASSO...💡_*
*_♦RAINA KAMA......!!♦_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
👉🏻3?
.........Fad'a sosai innarmu tamin akan Marin Safara'u danayi, sannan ta d'ora da nasiha kamar yanda tasaba, wani kam yashiga kunnena, wani kuwa tabaya yabi, dan harga ALLAH Na daina zama kowa yana taka mana mahaifiya a gidan.
Innarmu tace, “ku shirya gobe idan ALLAH ya kaimu Ku tafi gidan mamanku Rabi'a Ku k'arasa hutunku, banason zamanku a gidan nan tunda fitina yake kawowa?.
A sanyaye Munubiya ta amsa da “to innarmu?.
Amma ni saina tunzuro baki gaba ina k'unk'uni, dan banason tafiya ko ina, canma saboda d'an mama Rabi'a d'inne Marwan, ko kad'an bama shiri dashi, saboda masifarsa. “kai innarmu, yanzu dan ALLAH saboda wasu can bazamu mik'e kafa yanda mukeso ba agidanmu, duka fa hutun sati biyu ne kacal, amma saimunje wani waje?, ni wlhy inkika barni babu mai k'ara mana koda kallon banza a gidannan, harma innaro bazan bartaba.........?
Maficin danaga innarmu tajawo yasani tashi da sauri nabar gurin, Na tabbata shirin bugamin takeyi. Munubiya ta saka dariya tana kallona, “ke ga rashin arzik'i ga tsoron tsiya, dukan maficin kikema wannan gudun??.
Harara Na balla mata, “yo k'ya fad'i haka mana tunda ba jikinki baneba, tsoro kam kinsan waye matsoraci acikinmu ai?.
Munubiya ta ta6e baki “naji dai, koma mizaki ce kije kiyita cewa, inama kayana dakika saka jiya? na wanke, dan dasu zanje?.
Wayar innarmu Na d'auka ina dannawa, batareda na bata amsaba Na nuna mata laundry basket d'inmu.
Innarmu tace, “to Aljanar waya ajiyemin kafin ki k'ararmin kud'in ciki, ina taki??.
“kai innarmu, please mana, zan kira Ayusher nefa nasanar mata muna zuwa gobe, ALLAH wayata babu ko nera aciki Munu ta cinye min jiya?.
“kiji tsoron ALLAH munaya, Nina cinye mini kud'in waya? bake kika kira Balkisu ba da kanki??.
“to dana kirata sai nace kuyita surutu har kud'ina ya k'are?
innarmu Na shirin yin magana muka jiyo kururuwar kukan Safara'u da Rahama. dariya Na k'yalk'yale da ita, ina fad'in “o, ALLAH ga yaa hameed can yana gwajin kwanji a jikin gayu?.
Harara innarmu ta ballamin, saikuma tamik'e tana shirin fita, nasan kar6arsu zataje, nai saurin fad'in “kai innarmu, kid'an barsu su lallasu mana?.
Dakk'uwa ta watsomin tareda fad'in “K'aniyarki Munaya?.
Dagani har Munubiya dariya muka sanya harda tafawa kuwa.
Ba'a rufa mintuna 3 da fitar innarmu ba muka fara jiyo hargowar Maman safara'u (dama ita bata magana a hankali) Yaa hameed takema masifa akan dukansu safara'u dayakeyi, maman su yaa hameed babu hak'uri, itama tafito suka fara cacar baki, yaa hameed kam ficewarsa yayi bayan innarmu ta kwaci su Rahama a hannunsa da k'yar. kafin kace mi gidan yakuma kaurewa.
Munubiya tace, “kai jama'a ko breakfast ba'ayi agidanba har antafi wrestling zagaye na biyu?.
Na fad'a saman gado ina Dariya, danni mamaki 'yan gidanmu nakeyi da bala'insu. wayar Innarmu tayi ringing, da Sauri Na duba sainaga Abbanmu ne, cikeda d'oki Na amsa tareda masa sallama sannan Na gaidashi.
Yace, “Munubiya ina maman takune??.
“Abba ba munu bace, nicefa?.
“to to munaya ce? hayaniyar mi nakeji haka agidanne Munaya??.
K'yafta min ido da zungurina Munubiya tashiga yi wai karna fad'a masa (dayake a Hans free nasaka wayar, tana jin komai) amma saina harareta da murgud'a baki nace, “Abba Mama Ce da maman safara'u suke fad'a?.
Tsaki yaja da fad'in “ALLAH ya shiryesu to, ina maman taku ne??.
“Amin Abba, Innarmu tana can wajen rabon fad'an ai?.
“shike Nan, idan tashigo kice takirani muyi magana?.
“to Abba bye?.
Yace, “ok dear bye?. Sannan ya yanke wayar.
Ina yanke wayar Munubiya ta kaimin bugu, Na kauce ina dariya “yo da bakina a hanani fad'ar gaskiya?.
“ba hanaki akayiba, amma kinsan idan Allura ta tono garma mune tushen fad'an ai, kinkuma san halin Abba da d'aukar zafi kamar baba k'arami?.
“tab, ta k'are musu dai suda suka takalo wlhy, jarababbu dangin masifa?.
“kina ciki kenan tunda kema dangin kine ai?.
Dariya muka Sanya nida munubiya.
*washe gari*
Tafiyar mu gidan mama Rabi bai yuwuba, saboda dawowar Abbanmu, da innarmu ta sanar masa a waya zamuje can muk'arasa Hutu sai yace a'a muyi hak'uri mu zauna, Dan akwai bak'in da zaiyi a k'arshen sati (weekend), kuma yanason dukkan yaran mukasance muna nan.
Innarmu tace shikenan.
Wannan dalilinne ya hanamu tafiya Hutu, dama ni ba so nakeba, Munubiya ce keta zakwad'in tafiyar.
Yau ta kasance alhamis, tunda safe muka tashi da himmar wanki nida Munubiya, ina sharar sashenmu Munubiya na fidda kayan wankin, yayinda Aryan da Aiyan keta tara mana ruwa daga fanfo zuwa banbu.
Ina gama sharar na wanke hannuna na k'arasa bakin fanfo inda Munubiya ke k'ok'arin jik'a kayan. zama nayi bisa d'an dakali da akayi wajen saboda irin hakan, wanki ko wanke-wanke da sauransu, waya nake latsawa ina nemo mana wak'a, dan muji dad'in wankin, maganar aunty khaleesa kawai mukji a kanmu tana fad'in,
“k! Munaya tashi kije ki gyaramin d'akinmu, akwai wani zanina nan ki d'akkosa ku wankemin?.
Banza namata ban d'agoba, sai Munubiya ce tace, “to aunty khaleesa?.
Shirun danayi ina kuma tamke fuska yasata gane nice munaya, Dan haka ta kalli Munubiya dahar tatafi, “k Munubiya!... dawo, bakece zakiyiba, k! Dan uwarku Munaya tashi kije kimin?.
Da sauri Munubiya tace, "Aunty khaleesa ai nice munaya, waccan Munubiya ce?.
Hararta tayi, “mai dani 'yar iska to, ko kina tunanin ban ganeku nima d'in??.
Banyi niyyar d'agowa ba, amma jin abinda tafad'a yasani sakin guntun murmushi, nasan k'arya takeyi tace tana ganemu kai tsaye, yanzu ma dan kawai na nunu halin nawane shiyyasa tagane nice, kawai tafad'ane dai, mai da kaina nayi nacigaba da abinda nakeyi.......
Wata ashar ta lailayo ta makamin, tareda zaburowa tamkar zata dakeni, dai dai nan sallamar innaro ta karad'e tsakar gidan. mu duka kallonta mukayi, nikam kallo d'aya namata na d'auke kaina, (dan nikam natsani kakarnan tamu) Munubiya da aunty khaleesa suka gaidata, nikam a d'age nace “ina kwana?.
“kin yima uwarki Ai'sha dan Ubanki?, cewar innaro ta na nunani da d'anyatsanta manuniya👉🏻, tacigaba da fad'in “ni zakima gaisuwa a haka? kamar wata sa'ar uwarki?, aiko Aisha da ubanki basu isa sumin gaisuwa hakaba balle ke haihuwar yanzun?.
Baki na la6e, ba tareda na kalleta ba natashi nahau wankin, Munubiya kuma tawuce danta gyarama su aunty khaleesa d'akinsu. abinda nayi na nuna halin ko in kula saiya kuma tunzura innaro, ta fara hayagaga da matse kwalla wai naci zarafinta.
Wannan yasaka matan gidanmu da yara fara fitowa d'ai-d'ai suna kallonmu (dan al'adar gidanmu ce hakan, da anji kaya-kaya kowa zaiyo waje yaganema