Author : Bilyn Abdull Category : Romance
“kinga tashi kije kawai, amma wannan maganar tazama iyamu ukunnan, idan najita awani waje saina zubar miki da hanjin ciki waje, duk shawarar dakika Yanke da zuciyarki zaki iya nemanmu daga nan zuwa kwana biyu kawai?.
Da sauri Munaya tazaro idanu waje tana kallon Galadima.
Harara ya zuba mata yace “karki cinyeni?.
Baki ta zun6ura gaba tana k'unk'uni, bayajin mitake fad'a, sai motsin la66anta kawai yake gani.
Sai da aka rufemin iso sannan aka baro gidan dani, bankuma kwanceba saida motar ta tsaya, Wanda yake tare dani yacire k'yallen sannan yace na fita.
Ko kallonsa banyiba saboda tsoro nafice amotar da sassarfa.
Gudu-gudu sauri-sauri na Isa gidanmu, mutane sai kallona sukeyi, ALLAH ma yasoni babu kowa a tsakar gida, inaga matan gidan duk sun shige sallar magriba yaran kuma basu dawo daga islamiyya ba.
A 6angarenmu ma innarmu na d'akinta, hakanne yabani damar shigewa d'akinmu wuff, na iske Munubiya na barci itama, na sauke ajiyar zuciya mai k'arfi ganin ALLAH ya tsareni babu Wanda ya ganni, kayana nacire daketa kamshin turaren Galadima, bayi nashige nida kayan, nayi wanka sannan suma na wankesu na shanya a bathroom d'in.
Harna fito Munubiya bata tashiba, nayi sallar magriba sannan nafito wajen innarmu.
Da mamaki take kallona, “yoni har ina shirin kiranki naji lfy baki dawoba had dare yarufa??.
Zama nayi ina murmushin yak'e, dan abinda yafaru tsakanina dasu Galadima d'anzu ya min kane-kane a zuciya. ganin abin nakeyi kamar a mafarki. “ayya innarmu ai tun d'azun nashigo, lokacin kina salla, harfa nayi wanka ma nad'an huta. tace tana gidaki, yaya jikin Munubiya??.
Jikinta Alhmdllh, tad'an watsa ruwa takoma ta kwanta bayan taci d'an abinci?.
To Almdllh, ALLAH yak'ara afuwa.
Amin innarmu ta amsamin, daganan muka koma hirar gidan Inna lami.
Munkai tsawon lokaci afalon muna hira da innarmu, sai dai nifa bama fahimtar hirar nakeba, dan fili kawai nakeson samu nayin tunanin maganar su galadima.
★★★★
Tun bayan tafiyar Munaya Galadima yakoma kan doguwar kujerar yay kwanciyarsa tamkar mai barci.
Muftahu dake kallonsa yace, “Amma miyasa kace ta tafi? batareda ta bamu gamsashshiyar amsa ba kuma??.
Shiru Galadima bai amsaba tsawon mintuna uku, sai zuwa can yabud'e idonsa yana kallon Muftahu, baki yad'an ta6e “karka damu kanka, tama yarda, amsa ce kawai bata bamuba, itama kuma zata bayarne, tuni naga yardarta cikin kwayar idonta, akwai abinda take shakku akansa shiyyasa tak'i amsa mana?.
Kai Muftahu ya jinjina kawai, yasan tunda Galadima yafad'i haka to hakanne kuwa, amma sai yace “to amma bamu bata koda number ba, tayaya zata sanar damu amincewar tata kenan??.
Murmushi kawai Galadima yayi baice komaiba.
Hakanne ya tabbatarma Muftahu murmushin Galadima shine amsar tambayarsa. Daga nan bai sake cemasa komaiba shima.
Falon yay tsit.
★★★★
Gaba d'aya a kwanaki biyunan banida wani sukuni, tunanin maganar yak'i barin zuciyata, a kowacce dak'ik'a zuciyata tunzurani takeyi akan Na amince kawai, dan banida wata mafita sai wannan, ni kaina inason sanin Wanda ya aikata mana wannan abun, sannan bana fata sauran 'yan uwana suyi aure su barni a gidannan, hakan ba k'aramin tozarci zai zamarminba, ga Munubiya tadage akan innarmu ta sanarma Abba itama ad'aga bikinta har saina samu miji nima ahad'a ni da ita, na nuna mata 6acin raina akan maganar amma abanza, tanuna Sam ita tana a kan bakanta, nikuma harga ALLAH ba zanso hakan ta kasanceba.
Ita kanta innarmu nakula danne zuciyata kawai takeyi akan fasa aurena, amma tana cikin matsananciyar damuwa.
Yanzu yazanyi kenan? Na amince ko karna amince? gashi ya gargad'eni akan kadda Na nemi shawarar kowa, ni kaina nama kasa sanarma koda Munubiya, kuma kullum cikin tanbayata take mike damuna? duk da ita zatonta akan maganar Haidar ne har yanzu nake cikin damuwar.
Yau dai kwanaki biyu kenan da faruwar abin, har yanzu kuma nakasa tsayawa a matsaya d'aya.
Kusan tashin hantsi muna tsakar gida a baranda muduka 'yan matan gidan, kowa da hidimar dayakeyi, sai wasu daga cikin k'annenmu dake wasa agefenmu, iyayenmu kuma Na daga can k'arshen barandar suma kowa da hidimarta, innarmu ce kawai babu tana gidan mama Rabi'a taje duba feena da jikinta yad'an motsa.
Tsayuwar mota mukaji a k'ofar gida, yara suka tafi da gudu dansuga wanene? azatonsu cikin su Dady ne.
Mintuna baifi 10 ba saigasu suna shigowa da ledoji, saikuma ga Zarah tashigo cikin kwalliyar kece raini, tana taku d'ai-d'ai, daka ganta kaga mai yaron ciki, cikeda muran muka hau mata sannu dazuwa, itako saiwani ciccijewa take tana kuma Jan kai, ita adole matar manya.
Abin kallo bai k'areba saida mamansu yaa Hameed ta iso da d'an gudu ta rungume Zarah a jikinta, duk mukai galala muna kallon wannan sabon salo.
“masha ALLAHU Zarah sarkin haske, kinganki kuwa, da anganki anga matar manya yarinyata, kai ai aure Ni'ima ce babba, duk wacce ALLAH yabama 'yarta miji matan gidannan ta godema ALLAH, Dan wlhy yana sonta?.
Caraf Momy Hadiza ta kar6e da fad'in “wlhy kuwa Yaya, ai babu babban bak'inciki irin kanada gandamemiyar budurwa a d'aki tayi kwantai takasa auruwa, aimu sai godiyar ubangiji wlhy, babu ta inda ni'ima bata saukar manaba, Zarah zoki zauna ki huta kinji 'yar albarka?.
Maman safara'u da gwaggon haleema da maman su Fiddausi suka kwashe da dariya.
Kowa yasan damu ake wannan gugar zanar, amma sai mukayi murmushi kawai bamuce komaiba, maman fauziyya ma batace komaiba, nama godema ALLAH da innarmu bata nan balle ranta ya 6aci.
Tsam namik'e nabar wajen zuciyata Na suya, Na danne kukan dake shirin tahomin...
Maman Safara'u tace, “to yanzu ke bazaki iya danne zuciyarki ba saikin nuna hasaadarki a filin ALLAH?, to Ashe ranar auren 'yan uwanki mutuwa kuwa zakiyi?, dan kina gani za'a d'auke kowacce abarki agidan.
Wani k'arfine yazomin a zuciyata, Na had'iye kukana, najuyo ina kallonta ido cikin ido, wani murmushin takaici nasaki, sannan nace “maman Safara'u ke uwace agareni, sannan innarmu takoya mana tarbiyyar girmama kowacce mace agidannan, badan hakaba dana fad'a miki maganar dabazaki ta6a mantawaba, kuma ba hassadar tasani tashiba kamar yanda tunaninki yabaki, natashine Na d'aukama Zarah ruwansha, naga tashawo rana kuma babu Wanda yayi yink'urin bata?.
Ina gama fad'ar haka nabar wajen. tsit banji kowa yasake maganar ba, bansan miyasa ba, maganar tawace tasakasu yin shiru kokuwa oho.
Ina shiga falonmu Na fashe da kuka, anzo ga6ar da kawai zan amince da buk'atar Galadima, insha ALLAHU aranar datake fad'ar za'a tafi abarni, aranar nima zanbar gidan, Na gwammace nayi auren shekara d'ayan nafito.
Tunanin tawace hanya zanbi Na fad'ar musu Na amince na farayi, dan basu bani number ko wata hanyaba dazan iya nemansu, gashi kuma bazan iya gane gidan dasuka kainiba.
Tunawa dawata farar takarda nayi, wadda nagani a bag d'in dana fita da ita a ranar, kuma nasan ni bani Na ajiyeba.
Da Sauri Na d'auki bag d'in na zazage, saiga takardar tafad'o, na d'auka na bud'e, Number wayace ajiki kawai.
Jikina har rawa takeyi na d'auki wayata na kwafe number, sai kuma nakasa kira, na fara zagaye d'akin.
Motsi naji kamar na tafiya, da Sauri na shige bathroom d'inmu dan nasan Munubiya ce.
fanfo na kunna yanda zata d'auka wanka nakeyi.
Sha warar tura massage kawai na yanke. dan haka na rubuta
*_“na amince inhar bazai zama ka wulak'anta rayuwa taba?._*
Haka kawai natura masa na cire kayana nafara wankan gaskiya...........✍?
⛹🏻♀⛹🏻♀⛹🏻♀time d'in wasa yafara.🤸🏻♀
*_Ya ALLAH ka gafartama iyayenmu_*👏🏻😭
[4/22, 2:17 PM] Zuraiyah Zuzu💖: *_Typing📲_*
*_HASKE WRITERS ASSO...💡_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_♦RAINA KAMA......!!♦_*
_{Kaga gayya}_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
👉🏻1?6?
.......Zaune yake cikin wata runfar bunu dake harabar gidan, dagashi sai wando 3quarter da t-shirt mara nauyi, k'afafunsa hard'e saman table dake tsakkiyar kujerarun, an yisane da ainahin siminti kamar kujerun, sai dai anmusu ado da katifa a sama wadda inma bakayi kallon tsaf ba zaka d'auka na katakone.
Laptop ce ajiye asaman cinyarsa, yayinda idanunsa ke sakeye cikin siririn farin medical glasses d'insa Wanda har kana iya hango fafaren k'wayoyin idonsa aciki.
Gaba d'ayan hankalinsa naga aikin dayakeyi a laptop d'in, lokaci-lokaci yakan d'auki fresh milk na hollandia dake a cikin kofin glass ya kur6a ya ajiye. d'an k'aran da wayarsa tayi yasashi waigowa ya kalli wayar, saikuma ya d'auke kansa ya maida ga system d'in. Saida yagama duk abinda yakeyi sannan ya ajiye laptop d'in bisa table ya sauke k'afarsa d'aya k'asa.
Ruwa ya d'auka yasha sosai sanann ya ajiye ya d'akko wayar da sak'o yashigo d'azun yana k'ok'arin dubawa. sabuwar number ce, dan haka yabud'e cike da mamakin waye?.
*_na amince inhar bazai zama zaka wulak'anta rayuwata ba._*
Shiru yayi yana nazarin massege d'in, dan yakasa fahimta India ya dosa, Yakuma maimaita karantawa har sau biyu, ana ukunne yarinyar shekaran jiya tafad'o masa arai.
Murmushin gefen baki yasaki, tareda d'age girarsa d'aya yana ta6e baki da fad'in “iyimm!. kingama Jan ajin kenan? Well dama nasan zaki amince ai?.
Wayar ya ajiye gefen table d'in, yazame ya kwanta a kujerar idonsa na kallon rufin bunun, yanzu dai yarinya ta amince, amma tayaya zai tunkari ahalinsa kuma da wannan batun? Mai martaba mahaifin Momma ne matsalar farko, saikuma k'anin mahaifinsa Sarki, Momma bashida matsala da ita inhar papi ya amince, yad'an cije lips d'insa yana lumshe idanu, dole yay gaggawar nemo mafita, dan bak'aramin aiki baneba agabansa, musamman daya zam duniya tagama saninsa da yarinyar a yanayin da bai dace da d'iyan bahausheba musulmi.
Ya sauke ajiyar zuciya mai k'arfi, kafin yaja kuma siririn tsaki.
Zumbur yamik'e saboda wani tunanin daya zo masa a zuciya. waya ya d'auka ya lalubo wata number da aka rubuta my second Momy. kusan mintuna biyu yana kallon number d'in batare da yayi dailing ba, saikuma ya danna cikeda jimami.
Ringing uku aka d'aga daga can.
bayan yayi sallama aka amsa daga can tace “a'a yarona dama kana k'asar??.
Murmushi yayi tamkar yana gabanta, yad'an zame ya kwanta jikin kujerar yana shafa kansa. “Sorry my mom, wlhy 2days kawai da shigowata, kuma babu ma Wanda yasan nazo, wani d'an aikine ya kawoni?.
Dariya tayi daga can, cikin tsokana tace “yo dama ai kai kullum cikin aiki kake katafila?.
“oh my mom sunan dakika samin kenan? to nagode?.
“ai shine yadace dakai, yaka baromin 'Yar uwa da jikin yayana??.
“Everything Alhmdllh mom. wlhy nakiraki muyi wata muhimmiyar maganane, ALLAH yasa ke kad'aice??.
“ni kad'aice yarona, inama bedroom kwancene, miya faru??.
“uhmmm mom inason nayi a...? saikuma yay shiru yakasa k'arasawa.
“ina jinka mana?.
“ai mom maganarce bansan yanda zaki fahimceta ba, amma zancene inason nayi auren ?.
Zumbur tamik'e zaune, saboda jin maganar tayi tamkar daga sama, dan bata ta6a jin makamanciyar wannan maganar daga bakin Galadima Sameer d'in ba, hasalima bata ta6a jin ance yanada budurwa ba, kullum cikin yimasa maganar aure suke yana basarwa da cewa akwai sauran time, shiyyasa koda maganar jaridar nan tafito kai tsaye ta k'aryata zancen. “yarona wasa ko gaske dan ALLAH??.
murmushi mai sauti ya saki tareda ajiyar zuciya, har yanzu hannunsa na yawo bisa Kansa yana shafawa “mom da gaske nakeyi, aiban ta6a kawo miki irin wannan maganar ba?.
“hakane, to 'Yar wace masarautace ka samo mana??.
Sai da yad'an ta6e bakisa sannan yace “no mom, babu kowacce masarauta?.
“tofa, d'iyar waye to??.
“ba 'Yar kowa baceba mom, yarinyar Nance dai da aka mana 6atanci tare?.
“Sameer ban gane mikake nufiba? kana haukane? Koma kafara shaye-shaye bamu saniba??.
tashi yayi zaune sosai, ya d'auki ruwa yad'ansha, “ban fara shan komaiba mom, inason ki fahimceni da k'yau, dan kece ta farko Dana fara sanarma maganar, sannan kinsan Ku ukune kuka iya Sanin damuwata kai tsaye aduk duniyarnan. nasan zuciyarki zata kawo miki abubuwa dayawa akan maganarnan, to duk ba haka baneba...............?.
Anutse ya zayyane mata tarihin su Munaya, har zuwa maganar aurenta data lalace, yad'ora da fad'in mom banason nazama silar tawatsewar rayuwar yarinyar da bata jiba bata ganiba, ki fahimta mana, inason na bibiyeta ta hanyar auren Nata kozan sami wasu evidence akan case d'inan?.
Ajiyar zuciya mom ta sauke daga can, “to na fahimceka, amma ni mikakeso nayi yanzun??.
“yauwa momyna, sonake kisamu inno da mai martaba da maganar, amma kinuna kamar kece kikayi tunanin su Sani na auri yarinyar?.
“iyim nagane, kenan dai yazamto kamar kaid'in bakasan komaiba??.
“yes my mom, kin fahimceni dai-dai?.
Murmushi tayi, “ok babu damuwa, kamayi sa'a zanje gidan anjima dama na duba inno datayi mura?.
“wayyo 'Yar tsohuwarnan, karfa ta wuce bataga 'ya'yanaba?.
“k'aniyarka Sameer, aiko zan fasa kenan?.
“no please, sorry mom, nabari, ALLAH ya k'arama ginbiya inno lafiya?.
“zan kamakane fitsararre?.
Dariya yayi yana kissing d'in wayar sannan ya yanke kiran Yana cigaba da murmushi, yasan inhar inno da papi suka amince komai yagama yuwuwa, dan ko masarautarsu dolene kowa ya amince.
★★★★
d'aure nafito da zani ina goge ruwan goshina, Munubiya data zubamin ido tace “kuka kikayi ko sweetheart? ?.
“lah a'a wlhy, aini basukai namusu kuka ba wlhy Sweetheart, dan haka kima share batunsu. nifa kitsoma nakeson muje wlhy, kaina yagama yin datti har d'an tsami-tsami yakeyi?.
“kice kawai kin zama k'azama baby??.
janbaki na d'auka na wurga mata, tai saurin cafewa tana dariya. nima dariyar nayi ina fad'in “kin tsira yanzu, amma next time bazan barkiba?.
“hhhh idan na zauna ko? kinga shirya kawai muje wajen aunty Salamah mu wanke kai, daga can saimu biya muga jikin feena ma ko??.
“ok, hakan yayi?.
Shirina nayi cikin zani da Riga na wata oxblood d'in atanfa da ratsin milk, nakawo milk hijjab na saka batareda na d'aura d'an kwaliba, itama Munubiya irin kayan nawa ta canja. tsaf muka fito damu, saida Munubiya takira Innarmu ta sanar mata sannan muka tafi.
Mun tarar duk sunbar tsakar gidan, kowacce tashige 6angarenta, 6angaren su fauziyya muka lek'a domin sanarma mamarsu zamu fita.
bamu wani jimaba muka fito muka tafi.
Tunma a layinmu muka sami napep. har k'ofar shagon Aunty salamah ya saukemu..
Kamar yanda ta saba haka tamana tarba ta mutunci da d'oki. muma hakan ne daga garemu, dan muna k'aunar auntynmu data koya mana aiki, tace ?'yan ukuna ina hasaanar to??.
Dariya mukayi, dan munsan Ayusher take nufi, mukace bama tasan mun tahoba amma daga nan gidansu muka nufa.
An wanke mana kai, sannan mukayi kitso bawani mai yawaba, aunty ce tace dole sai ammana kunshi ko kad'anne, dole badan mun soba aka mana Jan lalli sai bak'i daya zamo kad'an, bamu baro shagonba sai bayan la'asar, dan mund'an taya aunty aiki.
Kai tsaye gidansu Ayusher muka nufa, mun iskesu gaba d'aya afalo suna hira, Ayusher na tacema Feena tafarnuwa dazafa sha. yayinda innarmu da mama Rabi'a ke zaune kusada juna suna hira k'asa-k'asa. Aiyaan Ahmad da Aryaan kam hankalinsu nakan wasa a can gefe.
Yaa fadeel ne yafara fad'in “oyoyo 'yan biyunmu?.
Dariya mukayi, sannan muka k'arasa cikin falon, bayan mun gaida