ta koma ciki bayan Dr musty ya gama komai ya kalli mummy yace"zata farfado nan da awa uku a sa ido a kanta"
Tace"thank you very much zanyi ma transfer"
A tare suka fito suka tarar dashi a tsaye
Dr musty yace"mummy zan shigo zuwa anjima in duba jikin nata"
Tace"please in ka samu lokaci ka turo magabatar ka bana son auren nan ya wuce nan da sati uku"
Cikin jin dadi yace"nagode mum sai na zo"
Yana tafiya ta koma d'akin saheeb din ta gyrawa fareeda kwanciya
Sanan ta fito ita Iman ko kallon inda yake batayi ba balle yasa ran zata me magana
Mummy ne ta fito ta gan be motsa daga inda yake ba ta kalleshi tace"dan tana d'akin ka bashi zai sa ka shiga ba kayi hakuri da ta farka zan d'uketa a d'akin"
Kallonta kawai yake har ta bar part dinshi
Tana wucewa ya shige ya kulle kofar
Kallon fuskarta yayi tabbas ta Kara kyau ga wayewa suman kanta ya kalla ya gan sun kwanta gashi da tsayi an Kama shi wuri d'aya
Yace"alhamdullilah "
Zama yayi gefen gadon ya Kama hanunta Yana Wasa dashi
Yace"baby iam sorry please forgive me nayi alkawarin saki farin ciki har karshen rayuwata"
Hanunta ne ya d'an motsa sai ya kalleta yayi murmushi nasan Zaki soni please karki bari a shiga tsakanin mu"
Wani mugun rungumeta yayi gam Yana sauke ajiyar zuciya da k'yar ya kwantar da ita sanan shima ya kwanta
Bayan awa uku da rabi cikin bacci yaji tana magana idonta a rufe sai cewa take mummy nayi mafalki ya dawo,mummy ni gidan mu zan tafi mummy ki taimakeni zai kuma min aski,mummy wurin be warke ba"surutai take sosai
Jikinshi ne yayi sanyi cikin sanyi jiki yace"farheeb ki bude idonki Zaki iya komawa ki bude idonki"
Kin budewa take sai surutai take da gudu yaje ya debo ruwa a toilet ya dawo ya watsa Mata
Firgit ta zabura ta bude idota ta sauke a fuskarshi
Wani ihu tayi tace"wayyo mummy na Shiga uku ki zo ki taimake ni
Karasota yake tana matsawa baya tana bashi hakuri kuka take sosai
Hawaye ne ya cika idonshi domin ya San ya shiga tara
Yace"farheeb listen to me please"
Cikin kuka tace"ku taimakeni nidai Allah ya isana"
Dunkulewa tayi a karshen gado ta rufe kanta da bargo daga bargon kana ganin inda jikinta ke b'ari
Har zai yaye bargon yaji ana buga kofa ba kowa bace mummy ce
Tace"ka bude,wallahi ranka zai b'ace"
Ko ta kanta bebi ba ya yaye bargon wani ihu fareeda tayi jikinta ya cigaba da b'ari
Jawota yayi ya rungume yace"ni ba abinda zan Miki"
Kwace kanta take Amma ya matseta,mummy ko sai zazzage me matsifa take
Gajiya tayi ta bar wurin tana jin haushi
Fareeda ko wani karfi ne ya zo Mata ta
Maman
Noorul
Hudah
Pls share
[1/9, 10:37 AM] Maman Noorul Hudah: πππππ
*_DR SAHEEB*_
πππππ
By maman noorul
Hudah
Dedicated to my fans
π
Ώ6β£5β£-6β£6β£
Bismillahir Rahmanir Rahim
Wani karfine ya zo mata ta tureshi ta sauka ta gudu
Bugun kofa sosai mummy takeyi tace"ka bude wallahi in baka bude ba zan Kira maka yan sanda
Itako fareeda zubewa tayi a kofar tana kuka tana cewa mummy ki taimakeni
Hankalin mummy ya tashi ta d'au fyade yake shirin mata
Shiko kukanta ne ya dame shi domin jinshi yake har cikin zuciyar shi
Karasawa yayi ya bude Mata kofa ya koma gado ya kwanta
Mikewa tayi ta fita ta rungume mummy
Tace"mummy Dan girman Allah a bari in koma gida bazan iya ba"
Kama hanunta tayi Suka tafi falo ta dibo Mata ruwan sanyi ta ba
Sha tayi mummy tace"yanzu saboda shi Zaki tafi ki bar mummyn ki?ke Ina ruwanki dashi?in kika ce Zaki barni Nima tafiya zanyi"mummy ta kare magana cikin hawaye
Rungumeta fareeda tayi domin tabbas tasan ta yarda mummy na kaunarta
Mummy tace"je ciki kiyi wanka ki fito mu ci abincin"
Mikewa tayi Iman na ta bin bayanta suna Shiga d'aki Iman ta kalleta tace"faree magana nike son inyi dake in ya b'ata Miki rai kiyi hakuri"
Tace"inaji "
Zama Iman tayi ta kama hanunta tace"faree nasan ya saheeb ya Miki laifi da bazaki tab'a yafe masa ba but Ina son ki gane abu d'aya wanan dama ce da zaki rama abinda ya miki domin soyyayar ki ce ta dawo dashi domin tunda ya gan hotunan ki da Nike posting wallahi kullum sai ya min tambaya game dake nidai kawai basarwa nike kuma nagan son ki a kwayar idonshi yau domin har kuka yayi kiyi amfani da wanan dama ki koya me hankali,bawai kiyj ta sumewa da kin ganshi ba ki cire wanan tsoron get rid of the fear in you and move on,and abu na gaba shine wallahi bana jin dadin yanda kike nuna tsanan Saheeb a gaban mummy Ina son ki gane komai lalacewarshi d'anta ne and babu wata uwa da zata zo ana nuna tsanan d'anta karara haka ko batayi magana ba nasan tana jin ba dadi koni wallahi bana jin dadin ki sani mummy na Miki soyayar gaskiya karki bari ke ki kasance me rama alkhari da Sharri"
Jikinta ne yayi sanyi tace"nagode Iman gaskiya kika fad'a zan kiyaye"
Iman tace"good,kiyi kokari ki daure ki zauna a nan din"
Tace"toh amma gobe zani gida in gaida iyayena"
Iman tace"sai muje tare"
Tace"toh"tashi tayi ta Shiga wanka itama Iman ta bar d'akin
Wanka tayi ta fito da alwala tasa dogon riga tayi sallah
Tana gamawa ko Mai Bata shafa ba ta bar d'akin ko da ta sauka ta tarar da Abba har ya dawo tayi murmushi tace"Abba ka dawo ashe"
Yayi murmusji yace"eh yanzu mummy ku ke fadamin baki ji dadi ba ya jiki?"
Tace"da sauki"
Iman tace"ai taga Mai d'aukan raine ta razana"ta kare maganar cikin sigar zolaya tana murmushi
Zaiyi magana sai ga saheeb ya sauko cikin 3qter da armless
Tun daga nisa daddy ke kallon inda ya rame kallon mummy yayi sai ta harare shi kawai sai ya kau da kai
Zuwa yayi ya ja kujera tuni faree ta sure tana niman yin kuka
Take Mata kafa Iman tayi harta d"an saki kara
Abinci yayiwa kanshi serving kad'ai domin da yayi gaisuwa babu Wanda ya amsa mishi harda daddy
Suna fara cin dinner sai wayar faree yayi Kara ta kallesu tace"Bari in d'auka
Tashi tayi ta koma falo ta d'aga wayar
Murmushi tayi tace"Dr naji sauki fa I saw your text da sauki"
Kome yace Mata oho sai naji tace"toh sai ka zo"
Dawowa tayi ta zauna mummy ta kalli daddy tace"alhaji munyi magana da Dr musty zai turo magabatansa "
Daddy yace"toh sai sun zo"
Mummy tace"bana son bikin ya wuce Nan da sati uku"
Ai ji sukayi saheeb ya mike ya
Maman
Noorul
Hudah
Luv u my fans
Pls share
[1/9, 10:37 AM] Maman Noorul Hudah: πππππ
*_DR SAHEEB*_
πππππ
By maman noorul
Hudah
Dedicated to my fans
___________
π
Ώ6β£7β£-6β£8β£
______________
Bismillahir Rahmanir Rahim
Yayi wurgi da komai na table din yace"matar nawa za a aurawa wani wanan wani irin rashin adalci ne?"
Jikin faree ne
Ya fara rawa ta b'oye bayan mummy "
Daddy yace"Kai fa ka saketa toh miye dan zata Kara aure?"
Yace"toh ai saki d'aya na Mata kuma tun daren ranan na maidata shine dan an tsane ni za a wani had'a ta da d'an iska?"
Team farida ku ji rainin wayau wai tun daren ranan ya maidataπ€π€£
Mummy ta wanka me Mari ta nuna shi da yatsa tace"zan iya hakuri na zauna da kai a gida d'aya amma bana son ka Kara shiga lamarin
Fareeda tunda Kai ishashene ka saketa a daren aurensu ka mayar damu kanana mutane a idon duniya shine sai yanzu zaka zo kana niman raina mana hankali a idon duniya,toh ta ishe ka haka karka Kara in ba haka abinda zan maka sai duniya sunyi tantama koni na haifeka "
Kama hanunta yayi yace"mum beat me slap me but iam begging you karki rabani da farin cikina nasan ni mai laifine a hukunta ni amma Kar a rabani da farheeb dina"
Janye hanunta tayi tace"wallahi ko zaka mutu bazaka samu fareeda ba kaje ka nimi wata mu kuma zamu tsaya maka a matsayin mu na iyayen ka domin hakki ka ne a kanmu but wallahi ba fareeda ba kuma in ba so kake in tsine maka ba toh ka fita hanyarta"
Daddy ya kalla a zatonshi ko zaisa baki ga mamakin shi sai ya gan daddy ya mike yace"hajiya nidai komai kikayi dai-dai ne"
Kallon fareeda tayi tace"kina son musstapha?"
Fareeda tace"eh"
Mummy tace"ki zauna da shiri za ayi bikin ku Nan ba dadewa ba"
Wani ihu saheeb yayi yace"nidai wallahi Allah ya isana saboda an tsane za a rabani da matata toh wallahi zanje har gidan nasu in roke baba nasan in kin kini shi ba zai kini ba"
Wani Mari mummy tayime tace"dan gidan ku wa kakewa Allah ya isa?"nuna shi da yatsa tayi tace"saheeb Ina fad'a ma ka fita daga idona fa kuma kaje in ka isa je gidan wallahi sai na tsine ma watoh tozarta mu da kayi be ishe ka ba sai kaje ka tona Mana asiri wajen iyayenta yariya tarufa mana toh kaje Ina jiran ka"
Tana gama magana ta haura sama
Fareeda ta ja kafa zata wuce ya kama kafa ture shi tayi tace"stay away from me"
Yace"meyasa kike fadin haka? Eh farida kowa fa yayi laifi a wanan maganar amma laifina kadai ake gani toh kiyi hakuri dan girman Allah ki rufa min asiri mu zauna lafiya"
Jan kafarta tayi tace"karka kuskura ni dama ba sonka nike ba asalima bansan da Kai aka d'aura min aure ba, dan haka kaje ka nimi wata kowa Allah had'a shi da rabonsa"tana Gama magana ta shige da gudu
Zaman dirshen yayi a kasa ya fara kuka, takaicin shi d'aya shine inda mummy ta dage tana goyon bayan farida kamar ba ita ta haifeshi ba
Kasa tashi yayi ya zauna Yana kuka
Da misalin karfe 8:pm motar musty ya danno kai cikin gidan
Kiranta yayi a waya tace"yanzu zata fito"
Wanka tayi ta sheka ado sai kyalli take domin yau tayi adon da tun da take Bata tab'a irinsa yau tana son ta tabbatarwa Dr musty tana sonsa domin ta dade da kamuwa da soyayyarsa daurewa take da jame aji tana son suyi aure kafin wanan azallumin ya Kara nasara a kanta
Gyale ta d'auka ta aza a saman doguwar rigar atamfa dake jikin ya tayi bala'in kyau
D'aukar waya tayi ta fito ba karamin mamaki tayi da ta ganshi zaune a inda ta barshi d'azu ba gyangyadi yakeyi
Kamshin tularen da ya jine ya sashi bude ido ya sauke a kanta
Murmushi tayi tace"Sannu Yaya baka Shiga d'aki ba ka zauna a kasa kana gyagyadi Kamar wani mara gata"
Dariya Iman dake falo tana kallo tayi kasa-kasa ta kalli fareeda ta kashe mata ido
Mikewa yayi yace"you see ni nasan kina Sona ne shiyasa kika damu dani"
Tace"Kai kuma haka akeyi daga magana sai kamin sharri ni bana son ka ban tab'a sonka ba tunda wuri kasan inda dare yayi maka,Bari ma in tafi karka b'atamin lokaci "
Yace"Ina zaki?"
Tace"yawo"
Ai binta yayi yace"muje in raka ki"
Kallonshi tayi tace"
Maman
Noorul
Hudah
Luv u my fans
Pls share
[1/9, 5:02 PM] Maman Noorul Hudah: πππππ
*_DR SAHEEB*_
πππππ
By maman noorul
Hudah
Dedicated to my fans
______________
π
Ώ6β£9β£-7β£0β£
Bismillahir Rahmanir Rahim
Tace"ah'ah yi zaman ka bako nayi"
Kafin yayi magana tayi tafiyar ta,binta yayi a baya
Tana kaiwa wajen motar Dr musty tace"lale da zuwan masoyina,barka da zuwa muradin zuciyata bugun numfashi na"
Wani numfashi saheeb ya ja saban tashin hankali kasa kwakwaran motsi yayi
Itako ta kalleshi da gefen ido tace"muje ciki"
Shiko musty sai washe hakora yake Yana zuba murmushi
Yace"baby kinyi kyau"
Murmushi tayi tace"Allah ko?"
Yace"eh"
Tace"toh muje ka gaida mumy da daddy"
Yace"toh"
Wuce saheeb sukayi kamar Basu ganshi ba
Falon Abba direct ta kaishi Nan ta tarar dashi da mummy suna Hira
Har kasa Dr musty ya sunguna ya gaishesu
Cikin sakin fuska mummy ta amsa me
Tace"ka sanar dasu ko?"
Yace"eh inshaallah gobe zasu zo"
Tace"toh Allah yasa alkhari"
Yace"Amin "
Sanda suka fita ta kalli daddy tace"meyasa baka amsa me gaisuwa da kyau ba and ko kallonshi bakayi ba"
Kallonta yayi yace"look hajiya so so ne amma son kai yafi babu inda zai ayi a ce ina ji Ina gani d'an na na son abu kuma ni da kaina in d'auka in bawa wani shin hajiya kinma Lura da Yanayi Kamal kuwa?wallahi in bayi wani abu a lamarin nan ba komai zai iya faruwa dashi"
Tace"toh ya mutu Mana nifa ba irin matan masu d'aurewa yaransu gindi bane and in ina son saheeb ya canja dole sai ya rasa wani abu Mai muhimmanci zai San darajar d'an adam in ya rasa fareeda dole zai gane rayuwa Kuma zai shiryu zai daina bin rudin zuciya"
Daddy yace"hajiya kiyi hakuri a maida auren nan shine rufin asirin mu gaba ki d'aya domin hakan ne zai rufa mana asiri ba sai iyayenta da sauran jama'a sun gane meya faru ba,yanzu in an tashi aurenta da musty me Zaki fad'awa iyayenta?"
Tace"har gida zan je in sanar dasu in musu bayani in kuma nima yafiyar su nasan zasu fahimta"
Yace"hajiya ki barshi haka ko haka aka barshi ya Sha wahala wai hajiya baki tausayin shine?"
Tace"dan Ina tausayin shi bashi zai sa in tauyewa Yar mutane hakki ba Dan haka a bar wanan maganan a ce ni in zaunar da saheeb in me nasiha akan ya rike matarshi ashe jina kawai yakeyi toh zai gane ne"
_________
Guest falo fareeda ta Kai Dr musty ya zauna ta d'auko drinks da fara'a tace"ya aikin ne?"
Yace"alhamdulillah "
Yace"yanzu ki amince ayi auren"
Tayi murmushi tace"eh na amince"
Murmushi yayi yace"kina Sona kenan?"
Ta rufe fuska,kallonta yayi yace"faree please akwai maganar da nike son muyi please karki min mumunan fahimta"
A natse ta kalleshi tace"inaji"
Yace"a gaskiya banji dadin zamanki a gidan nan tunda babu aure tsakanin ki da saheeb toh me kikeyi a nan honestly iam not comfortable with this kamata ai su barki ki koma gida ki fuskanci sabon rayuwa"
Jan numfashi tayi tace"a gaskiya Nima nafi son in koma gaban iyayena but bana son hankalin su ya tashi wallahi in baba yaji wulakanci da Dr yayi min wallahi sai ya kusa had'iye rai dan zuciya ga mama da hawan jini Kuma bana son mutunci dake tskanin su da daddy ya lalace,and dady da mummy sun min alkhari musaman mummy wallahi ta nuna min kauna a kaina ta rufe ido dan ta samo min farin ciki ka ga da kunya in ce mata zan koma gida bayan nasan abinda zai haifar,but karka damu tayi alkawarin auran dani ga duk Wanda nike so"
Murmushi yayi yace"I trust mummy but daddy ban yarda dashi ba baki gan inda ya amsa min gaisuwa ba?"
Zatayi magana kawai suka ji
Maman
Noorul
Hudah
Love u fans
Pls share
[1/9, 5:02 PM] Maman Noorul Hudah: πππππ
*_DR SAHEEB*_
πππππ
By maman noorul
Hudah
_____________
π
Ώ7β£1β£-7β£2β£
_____________
Bismillahir Rahmanir Rahim
Kawai Suka gan saheeb ya shigo kafin suce zasuyi wani abu ya shake Dr musty babu abinda kake gani sai idanunshi
Fareeda taje da niyyar taimakabme ya tureta ta fadi a kujera
Idonshi yayi jajir kamar garwashi jikin shi har rawa yakeyi saban b'acin rai
Cikin kunan rai yace"tunda taki tafiya gidansu sai ka zo ka jata"
Dr musty ko ya ji maza zuwa yanzu da k'yar yake numfashi
Mikewa fareeda tayi ganin in batayi wani abu ba zai iya kashe shi
Ihu ta farayi tana niman taimako tana kuka
Sama-sama mummy da yanzu Suka gama fada da daddy har Yana ce mata in wani abu ya Sami d'anshi bazai yafe Mata ba
.itako tace"oh ita fareeda ba haifanta akayi ba ko ko bata da iyaye masu sonta toh in abin ya Zama haka washe gari zata mayar da ita gida"
Mikewa tayi tace"meya sameta take irin wanan ihun"
Jin muryata tayi tace"mummy ki zo zai kashe shi"
Da gudu mummy ta fita tana zuwa ta tarar da saheeb ya sheke wuyar dr musty zuwa yanzu ya fara fito da halshe"
Karasawa tayi ta wanka me Mari tace"sake shi"
Yi yayi kamar beji ba kuma ko motsi beyi ba
Kara me tayi tace"Kamal in nice na haife ka na ce ka sake shi"
Ko gizau,daddy ne ya shigo ya turashi kawai sai suka gan ya zube kasa kamar rubabben gwanda
Shima Dr musty zubewa yayi ya rike wuya yana wani irin tari
Da gudu fareeda ta karasa tana kuka bata San sanda ta aza kanshi a cinyarta ba ta fara me Sannu Iman ta kawo me ruwa
Shiko SAHEEB a zahiri idonshi biyu Kuma kallon fareeda yakeyi Yana hawaye sai dai ya kasa kwakwaran motsi ko hanun ya kasa d'agawa
Da gefen ido daddy ya kalli fareeda itako ko kallon inda saheeb yake batayi, ba daddy ba kadai har mummy ta ji ba dadi
A ranta tace"Ashe kiyayya ta Kai haka dole toh in aura mata Wanda take so Kar a shiga hakkinta"
Iman ne ke kuka tana kiransunan shi
Daddy yace"ta dibo ruwa"
Zuwa tayi da gudu ta dibo ruwa ya yayyfa me a fuska wani ajiyar zuciya ya sauke yace"daddy ka roketa wallahi nayi nadama nidai ta daina kula wani zan mutu zuciyata zafi yake min mummy ki bata hakuri"
Ba tare da tayi magana ba ta bar falon kuka ya fashe dashi yace"wayyo an tsaneni"
Fareeda ko bayan tayi amfani da basirarta na nurse da kuma student Dr ta taimakawa Dr musty ya dawo dai-dai
Kallonshi tayi tace"Sannu "
Da kai ya amsa Mata tace"da dai sauki ko?"
Yace"eh"
Juyawa tayi ta kalli saheeb shima ita yake kallo karasawa inda yake ta farayi
Ganin tana tunkaroshi yasa shi yin murmushi
Tana kaiwa gabanshi ta wanka me Mari
Cikin zafin rai ta nuna shi da yatsa tace"
Maman
Noorul
Hudah
Luv u my fans
Pls share
[1/10, 11:50 AM] Me Group: πππππ
*_DR SAHEEB*_
πππππ
By maman noorul
Hudah
π GORGEOUS WRITERS FORUMπ
Home of gorgeous, interllingent,and expert writers we the best among the rest.
Dedicated to my fans
____________
π
Ώ7β£3β£-7β£4β£
______________
Bismillahir Rahmanir Rahim
Tace"how dare you? Me nayi maka a rayuwa?meyasa baka son ganin farin cikina?meyasa ka tsane ni? Meyasa kake son ganin hawaye na?"
Girgiza Mata Kai yayi zaiyi magana ta katseshi tace"Dr Mari nayi maka Kuma ka d'au fansa fiye da laifin da na aikata ma,ka rabani da saurayin dana taso na fara so a ranan aurena ka mayar dani abin dariya ga al'uma,ka sace ni ka haddasa zargi a zuciyar mutane Wanda har in mutu bazan tab'a mantawa ba,wanan be ishe ka ba a daren aurena ka min abinda ko Kare bazai d'auka ba ka min caka-caka wanan be ishe ka ba,ka sakeni ba tare da kayi tunanin halin da iyayena zasu Shiga ba,as if that was not enough ka min aski"nuna shi tayi ta nuna kanta