DR SAHEEB by Maman noorul Hudah

Author :  DR SAHEEB Category :  Romance

Chapter   12 / 12

33K to 33.7K   out of 33.7K words

shi had'iye miyau cikin rashin kunya na ji tace"in anki fa?"

Murmushi yayi yace"Yi hakuri matu kap garin nan kin fi kowa kirki"

Ko kulashi batayi ba ta fara tafiya kamar zata tashi sama ta Isa gaban motar Burnet ta bude cikin kwarewa ta fara gyra

Tana cikin gyran ne sai ga illu ya shigo da gudu Yana Kiran sunanta

Kallonta yayi yace"matu ansha dake please ki zo muje da sauri ki kalli show"

D'angowa tayi ta kalleshi tace"me ake kira haka?"

Yace"au ni nama mance ke hamago ce ba turanci"

Cikin b'acin rai ta kalleshi tace"illu karka gan Ina raga maka ka nima ka cimun fuska"

Yace"Yi hakuri kedai kin fiya matsifa zuwa nayi in fad'a Miki cewa wata ce ta zo daga birni take fad'awa su Indo wai ta fiki iya rawa Kuma wai in ki Isa ki zo a gwada"

Wani mugun dariya ta bushe dashi tace"ita wacece da zata ce zata gwada Dani?"

Illu yace"oho ai shine nace karya take kawata ta fita iya rawa zan Kira ki shine na taho"

Oga Saleh da tunda ya gan illu ranshi ya b'ace domin ya San zuwa yayi ya hana matu aiki '

Wani saurayi dake zaune a gefen yana jiran a gyra me mota tunda ya shigo garajin ya ji matu ta birgeshi tunda yake a rayuwarshi be tab'a ganin makaniki mace ba sai yau"

Murmushi yayi ya karaso gabansu ya kalli matu

Yace"Hy"

Kallon illu tayi tace"bashi amsa kasan ni ban iya karatun arnan ba"

Maganar ya matukar bawa Hafiz dariya

Yace"turanci ne karatun arna?"

Ko kulashi batayi ba ta cigaba da cire rigar aikinta babu kunya harta Gama cirewa ya rageta da riga da dogon wando Pakistan

Hafiz yace"haha keko ya Ina Miki magana kin share ni?"

Cikin kosawa tace"Kai malam ai ko bashi na ci maka ka shafamim Lafiya ko?nifa na tsane mutum me shegen iyayi da turanci harda wani ha"

Yace"Allah yabaki hakuri birgeni kikayi shiyasa ni dama Zaki aureni dana ji dadi"

Kallonshi tayi sama zuwa kasa tace"ni?rufa min asiri har guda nawa nike da za a wani ce za a min aure nifa barni da gyran mota"

Yace"toh bani number ki"

Kallon illu tayi kawai sai ta gan yana kuka tace"Kai ya haka Kuma? kodai hauka ne ya motsa?"

Cikin kuka yace"ba ke bane kike kula wani ba"

Tsaki tayi tace"kawai shine na kuka? kai nifa ban fiye kula irin yan birnin nan ba babu karya da turanci babu abinda suka iya haka sukeyi su narkawa yara ciki in ba iskanci ba ni yar shekara goma shabakwai wai zai aureni Kai muje kafin raina ya b'ace,yau na ji ma wai zamuyi baki daga birni"

Illu yace"muje"

Shidai hafix murmushi yayi sai dai fa ya d'au alkawarin dawowa dole sai ya samu abinda yake so

A hanya suka had'u da wata mota da ya lume cikin laka
Ganin me motar tsaye sukayi kallo d'aya matu tayi me ta d'auke Kai

Shiko Yana ganin su ya kira illu da hanun

Itako kau da Kai tayi,karasawa illu yayi Yana murna d'an birni ya kirashi

Gyran murya yayi yace"please ka taimaka mu fitar da motar nan mana I will reward you"

Kafin illu yayi magana matu ta kece da mugun dariya tace"kwaji d'an rainin hankali toh tunda turanci zakayi Mana da karya banza ai sai turanci ya taimaka maka Mara kunya banza yanzu ko kunya baka ji ba harda turanci"

Kallonta *Hydar* yayi yace"amatu ni kikewa rashin kunya ko baki gane ni bane?"

Tace"fes kuwa na gane ka,ko ba Hydar bane wanan d'an rainin hankalin da karya ba? toh sai mu ga Wanda zai taimaka maka"

Kallon illu tayi tace"toh inka taimakame daga yau na daina kula"

Illu yace"tuba Nike ranki ya dade"

Tsaki tayi tace"muje ka barshi da turancin shi ya taimaka me aini tunda ka kirani da Yar kauye mara aji nasan zamana da kai"

Murmushi yake yayi yace"ai zan rike ki ne"

Tace"in ka kamani ka kashe ni,kazan turawa kawai,in banda baffa Ina ni Ina wanan"

Cikin b'acin rai ya....

Ku biyoni a naira d'ari biyu kacal zaku Sha dramar

Karki Bari a baki labari 200only

Please patronize your writer


domin
biyan kudin karatu pls ku min magana tawanan 09090112846

Karku bari a baku labari

Dan girman Allah ba dan niba in kin San zaki fitarmin da littafi ki rike kudin ki

Sai naji ku mu had'u a NIDA YAYA HYDAR palace😀🤣

12 / 12