DR SAHEEB by Maman noorul Hudah

Author :  DR SAHEEB Category :  Romance

Chapter   11 / 12

30K to 33K   out of 33.7K words

ta duba

Haurawa tayi da sallama ta tura kofar d'akin

Shiru ta ji hakan yasa ta shiga kwance ta ganshi a kasan tiles cikin amai idonshi a lumshe jikin shi yayi mugun zafi

Karasawa tayi cikin tashin hankali tayi ta jijjiga shi tana cewa Dr ka bude ido Dr

Kuka ta fashe dashi da k'yar ya bude ido cikin zazaabi ya shafa fuskarta yace"karki damu iam fyn"

Bude drawer shi tayi aiko tayi sa'a ta gan wasu allaurai daya ajiye alamun ya dade yana jinya

Dubawa tayi ta had'a sanan ta zo tame da k'yar ta taimakame ya tashi ya haye gado ta shiga toleit ta ganshi yayi datti ta wankeshi sanan ta fito da ruwa da mopper ta gyra d'akin bayan ta gama ta cire me vest din jikin shi ta ciro wani tasame

Kicin taje ta had'a me fattan dankalin turawa tasa a tray ta kaime

Bacci ta tarar Yana yi sai ta rufe shi da bargo ta dawo falo tayi tagumi tana tunani ko tun yaushe ya fara rashin lafiya yanzu toh da ya mutu fa?"

Bayan awa biyu ta koma d'akin sai taji motsin shi a toilet Zama tayi bakin gado sai kuma ta tashi ta bude wardrobe ta ciro bedsheet ta shinfid'an me

Fitowa yayi yana murmushi yace"nagode"

Kallonshi tayi ta gan ya rame

Kasa-kasa tace" ya jikin?"

Yace"da sauki hanya farheeb kina ganin ba shawaranki zan d'auka na Kara aure ba Kar in zo in mutu ba a sani ba kin gan kwana na uku Ina rashin lafiya"

Haka kawai ta fashe da kuka yace"subhannallah meya faru"

Cikin kuka tace"aini nasan dole wata Rana ka ce zaka Kara aure tunda ni ka gama dani nidai Allah ya isana"

Murmushin samun nasara yayi a ranshi yace"ashe bata da wayau"a fili ko marairaicewa yayi yace"ai ba laifina bane kece baki Sona Kuma ke da bakin ki kika ce in Kara aure"

Ba tare da ta kalleshi ba tace" ga abinci ka ci sai da safe"

Bata jira me zaice ba ta bar d'akin Domi kuka ne ke niman sub'uce Mata tana zuwa d'akin ta shiga bayi tayi wanka ta fito tasa Kaya bacci ta kwanta tana kuka

Bayan ya gama cin abinci ya zo d'akinta tana jin motsinshi ta lumshe ido

Hawa gadon yayi ya rungumeta tana jin shi tayi pretending Kamar me bacci


Washe gari da asuba


Maman
Noorul
Hudah
Luv u my fans
Pls share
[1/12, 8:27 PM] Maman Noorul Hudah: 👄👄👄👄👄
Dr SAHEEB
💋💋💋💋💋
By maman noorul
Hudah

Dedicated to my fans
__________
🅿9⃣5⃣-9⃣6⃣.
______________

Bismillahir Rahmanir Rahim

Washe gari ya rigata tashi ya tafi masalaci ba laifi jikin da sauki

Itama tashi tayi ta d'auro alwala tayi sallah tana idarwa ta fita ta fara aikin gida da had'a breakfast ta gyra falon yana shigowa ya ganta harta jera abinci for the first time a rayuwar shi da ta fara gaishe Shi domin ko da take aiki a asibitin shi bata tab'a gaishe Shi ba daga harara sai bakar magana Amma sai gashi yau tace"Ina kwana harda ya karfin jiki?"

Kallonta yayi da mamaki ta gane irin kallon ta harare shi ta murgud'a me baki ta ruga da gudu ya bita

D'aki ta shiga ta rufe kofa tana dariya

Murmushi yayi ya cize labenshi yace"Zaki shigo hannu"

Wanka tayi ta fito cikin bakin jallabiya

Zaune ta ganshi a falo Yana kallo ba tare da ta kalleshi ba tace"abinci na dining table"

Murmushi yayi yace"iyeh Ashe yau na zama d'an gatan farheeb dina"

Bata amsashi ba ta zauna ta fara cin abinci yace"farheeb yau ba school ne?"

Tace"ai muna strike till further notice"

Murmushi yayi yace"Ashe muna li'ke da juna na ji dadi wallahi "

Bata amsashi ba ta cigaba da cin abinta tana gamawa tace" zanje in kwanta bacci Nike ji"

Tashi yayi ya Kama hanunta yace"mu dai je mu kwanta"

Zatayi magana yace"please ki bar abinda ya wuce mu fuskanci sabon rayuwa"

Haka fa rayuwa ta cigaba da tafiya inda suke nunawa juna kulawa tare suke girki in tana aiki Yana tayata shakuwa ce sosai ta Shiga tsakanin su ta sake me sosai,in fita sai ta ji ba dadi gashi har yanzu ana strike

Kwalliya tayi bayan ta gama girki tasa jeans trouser da top tayi kyau tayi parking sumanta tayi a tsakiyar sai ta zamo Kamar wata foreigner

Fita zatayi taje falo domin lokaci dawowar sa yayi

Kawai sai taji kunya da k'yar ta daure ta cire kunya taje falo ta zauna Amma tana jin shigowar motar shi ta saka hijab

Yana shigowa tayi me Sannu da dawowa

Ya kalleta da fara'a yace"baki ji ko ba na hana ki saka hijab a gida ba"

Rufe fuska tayi tana murmushi tace"kunya nike ji"

Yace"toh cire in gan kwaliyar"

Kin cirewa tayi tana dariya karasawa yayi ya cire Mata ai numfashin shi ne ya d'auke yace"wow kin Yi kyau"

Waya ya ciro a aljihu ya fara Mata selfie"

Bayan ta had'a me ruwa yaje yayi wanka ya sauko ya sameta Suka ci abinci

Da misalin karfe 8pm bayan ya dawo daga masallaci suka fita zuwa inda zai sayi kaza

A mota ta jirashi ya saya da fresh milk Suka koma gida

Da k'yar yayi da ita ta ci tsorone ya bayyana a idonta karara Domin ta lura dashi yau yana son karb'an hakkinshi

Bayan sun Gama ci ya d'auketa ya kaita d'akinta ya kwantar da ita

Fashewa da kuka tayi tana bashi hakuri

Yace"kiyi hakuri yau bazan iya hakuri ba karki damu bazai Miki zafi Kamar na da ba"

Cikin dabara ya fara Mata wasanin me Shiga rai Wanda tun tana nokewa ta saki jiki ta fara bashi hadin Kai

Sosai ya haukace Mata yana nishi da gurnanin dadi

Ganin ya fita haiyancinshi sai bude mata kafa yasa ta fashewa da kuka jikinta ya fara rawa

Ko jinta beyi ba ya bude kafarta ya fara niman hanya

A tare suka sake wani ihun nashi na dadi nata na zafi domin mummy ta gyrata ga kuma d'inki da akayi mata gashi ta dade da mu'amula da namiji shi kanshi in badan shi ya rabata da budurcinta ba da bazai gane ko ba budurwa bace

Bayan komai ya wakana a hankali ta bude idonta da Suka mata nauyi ta sauke akanshi tana cigaba da kuka

Kallonta yayi yace"ki Yi hakuri wallahi banso na baki wahala haka ba please"

Rungumeta yayi yana sa Mata albarka da kuma bata hakuri akan ta yafe me

Tare suka je yayi Mata wanka shima yayi ya fito da ita suka kwanta ya rungumeta

Washe gari aka tashi da shirin bikin Iman domin yau saura kwana uku

Ana gobe d'aurin aure ya kaita gidan mummy sai dai be Bari ta kwana ba ya dawo d'aukanta

Bata so binshi ba domin yana takura mata baya d'aga Mata kafa hakan yasa taje d'akin mummy ta kwanta

Mummy tace"ku fito ku tafi Yana jiranki kar ya shigomin d'aki kin San ba kunya ne dashi ba nace ya tafi wai bazai iya bacci shi kadai ba"

Tace"nidai mummy a nan zan kwana"

Mummy tace"nidai na wuce tsakanin ki da mijin ki"Aiko har d'akin ya bita ya ganta kwance domin tana jin kamshi tulerensa ta rufe bargo har Kai

Yaye bargon yayi yace"ki tashi mu tafi kina b'ata min lokaci "

Kuka ta fashe dashi tace"nidai ka barni a nan zan kwana"

Yace"farheeb kina gudu na ne?"

Cikin kuka tace"ba Kai bane kayi ta min mugunta"

Yace"Yi hakuri yau ba abinda zanyi"da k'yar ya lallabata ta yarda ta bishi

Bayan kwana uku aka d'aura auren Iman da mustapha biki yayi biki an ci an Sha daga Nan aka Kai amarya gidanta

Suma Suka bude shafin soyyaya

Bayan wasu watani

Toh kaikuma saheeb me zai faru da kai kuma? na gaji ka barni in huta
Maman
Noorul
Hudah
Luv u my fans
Share
[1/13, 9:36 AM] Maman Noorul Hudah: 👄👄👄👄👄
Dr SAHEEB
💋💋💋💋💋
By maman noorul
Hudah

Dedicated to my best friend maman fareesa Allah ya raya ya bawa Ana's tsawon rai ya Kare shi daga sharrin mutum ko al-jan,a shafa min kanshi
____________
🅿9⃣7⃣-9⃣8⃣
_______________
Bismillahir Rahmanir Rahim.

Bayan wasu kwanaki sosai fareeda ta fara sabawa da jaraban saheeb Kuma yanzu sun koma makaranta shi yake kaita yake dawo da ita

Sai dai fa baya yarda ta fita babu hijab harda nikab kullum cikin hijab take mummy tayi magana ta gaji hakan be wani dame ta dan dama ta Saba

Yau dai ta tashi da rashin lafiya sosai take rawar sanyi kallonta yayi cikin damuwa yace"baby Sannu zai bari it matter of days"

Tace"wani days month dai wasu laulayi suke har su haihu nidai na Shiga ukuna,Allah ya isa..."shiru tayi tsakamakon kallonta da yayi

Hade rai yayi yace"Allah in nakara ji wallahi zan fasa bakin Nan"turo baki tayi

Dariya ta bashi yace"mun dai shiga uku domin inda kike da son jikin nan wata rana har goya ki zanyi"

Kwanciya tayi tana nishi gashi komai ta ci sai tayi aman shi

Drip yasa Mata da k'yar bacci ya d'auketa

B'angaren humaira ko ansa bikinta da Mahmud kuma tana zuwa gidan fareeda lokaci zuwa lokaci

Sai dai fa kwata-kwata saheeb ya fita harkan Mahmud a cewar shi ba abokin kwarai bane

Cikin fareeda ko ba karamin wahala yake bata ba tana matukar bawa saheeb tausayi kullum maganarta be wuce Dr kodai mutuwa zanyi?"

Sai yace"ah'ah karki damu zaki samu sauki "

Su mama ko yanzu hankalinsu kwance ganin Yar su cikin kwanciyar hankali Kuma saheeb ya bawa baba jali ya fara wani sana'a ya daina gadi

Saboda tausayinta yasa in zaije aiki sai ya kaita gidan mama in zai dawo sai ya biya ya d'auketa

Cikin na kaiwa wata uku ta fara samun saukin laulayin

A wata na hud'u taji sauki sosai tayi kyau kuma tana karatun ta cikin kwanciyar hankali in ka ganta da k'yar zaka gane tana da ciki domin hijab ne jikinta always

Da cikinta taje bikin humaira tare suka je da saheeb inda ana d'aura aure ya kirata Suka koma gida duk da taso wuni haka ta hakura ta bishi

Bayan wata biyar ta haiho yar'ta mace shi da kanshi ya karbi haihuwar matarshi ba karamin wahala Tasha ba

Sanda ya gyrata ya fara Kiransu mummy

Mummy da fushi take dashi akan yaki bari farida taje gida wanka tace"bazata je ba saidai ya kawota "

Aiko yace"yi hakuri mummy please"

Ganin da gaske yake yasa taje ta gyra jaririya ta Mata wanka ta had'a kayanta ta dawo da ita gida shima kayan nashi ya had'a ya bisu

Ranan suna anci an Sha anyi shagali Iman da tsohon cikinta wata bakwai ta zo

Zumunci ne tsakani Dr musty da saheeb sun manta abinda ya faru a baya

(Haka ake son mu kasance masu yafiya)

Bayan shekaru uku abubuwa da dama sun faru ciki harda gamawa makarantar fareeda Kuma yar'su ta girma Rukkaya takwaran mummy Amma suna kiranta samha soyyaya take gani a gun iyayenta sai dai fa saheeb nashi ta daban ne domin ji yake bazai iya rayuwa babu ita ba har fad'a suke da fareeda wai ya fiya b'ata yara

Fareeda ne zaune a falo tana kallo sai ga samha ta zo da gudu tana nuna Mata hanunta tace"ummi kin ga zafi"

Kallon wurin tayi ta gan kuraje ne sunyi ja tace"Sannu ta Bata magani ta sha"(anti biotic)

Hmmn abu Kamar Wasa bayan kwana uku kurajen sun mamaye ko Ina na jikin samha harta halshe da baki babu inda babu ko magana bata iyayi

Hankalin saheeb ya tashi domin har allura yayi Mata ya kaita skin care a banza duk asibitin da ake sa ran samu sauki anyi ina mummy ma nimo musu take amma abin sai karuwa yake

Fareeda kullum sai kuka gata da sabon ciki

Da abin yayi sanani fareeda ta kaita gida baba na gani yace"ai wanan sai maganin gargajiya Kuma yasan Mai badawa"

Baba yace"a Bari gobe tunda dare yayi zasu"

A ranan a gidan ta kwana sai dai fa gari na wayewa ta tashi da zazzabi

Baba yace"toh ta zauna a gida su tafi da saheeb"

Saheeb ne ya zo da mota ya d'auke baba da samha Suka tafi barkin saleh

Parking yayi ya d'auki yar'shi a hannu

Domin babu hanyar mota da zaije gidan

Da sallama suka Shiga sunman gidan domin d'aki d'aya ce tak a gidan

Saheeb na kallon gidan inda yayi kaca-kaca da datti Yana mamaki wai yau shine ya zo neman taimako a wajen talakawa ikon Allah

Wata budurwa ce ta fito ta kallesu ta gane baba dan haka ta gaishe Shi

Yace"tsoho na Nan?'

Tace"eh Bari in Kira shi yana ciki"

Kallon saheeb nayi sai na tuna lokacin da wanan tsohon ya zo niman taimakon waje shi haka shima d'anshi ya rike yar'shi

Hmmm what goes around always comes around muna rayuwa ne but at some point wallahi komin kudin mu da mulki wata rana sai mun nima taimakon na kasa damu,karki gan ko ka gan kana da kudi da mulki kace zaka wulakanta mutum ba a wulakanta mutum toh in Allah daya hallice mu be wulakantamu ba then who are we to look down on each other? Yan uwa ya kamata mu gyra zuciyoyin mu mu, sowa Yan uwanmu abinda Muka sowa kanmu,because in kayi Mai kyau zaka gan Mai kyau

Allah yasa mu dace ya rufa Mana asiri duniya da lahira ya raya Mana ya'yan mu,ya raba mu da shaarin masu sharri ya tsarkake zuciyar mu ya bamu lafiya da abinda lafiya zata ci,ya Allah muna tawasali da sunayen ka tsarkaka masu Nima haihuwa Allah ya basu,Yan Mata Allah ka Baku miji na gari masu aure kuma ka Kare mazajen mu ka raba su da matan banza,ya rabbi ka raba mu da aikin dana sani,Amin )

A raina nace ikon Allah ba a raina mutum ko Yaya yake domin kowa da baiwar da Allah yayi me waya tab'a tunanin yau saheeb zai nimi taimakon tsohon daya wulakanta hmmn mu bi duniya a Sannu


Maman
Noorul
Hudah
Luv u my fans
Pls share
[1/13, 9:36 AM] Maman Noorul Hudah: 👄👄👄👄👄
Dr SAHEEB
💋💋💋💋💋
By maman noorul
Hudah

Dedicated to 80k's
_____________
9⃣9⃣-1⃣0⃣0⃣
______________

Bismillahir Rahmanir Rahim

Tsohone ya fito da murmushin shi sai dai yana ganin saheeb ya b'ata rai

Shima saheeb wani kunya da dana sani ne ya lullubeshi

Tsoho ya kalleshi yace"me ya kawo ka gidana Mara mutunci ko zuwa kayi ka Kara kwallo dani?"

Saheeb ya duka har kasa yace"baba dan girman Allah ka yafe min na tuba wallahi na tuba"

Baba ya kallesu yace"Ina kuka San juna?"

Tsoho ya kalli baba yace"ai shine ya tab'a kwallo dani akan naje niman taimako asibitinshi "

Saheeb ya fashe da kuka ganin samha ta fara Mika yace"baba dan girman allah ka taimakeni ka bawa ya'ta magani "

Tsoho yayi dariya yace"ashe ka ji inda ake ji kenan toh ni ka nimi wani wuri ba nan ba ka tuna Nima dana kawo nawa yar'ka wulakanta ni?"

Baba ne ya fara rokonshi amma tsoho ya rufe ido yace"besan zancen ba"

Hankalin saheeb ya tashi yayi nadama wulakanta d'an Adam watoh Ashe kowa na da ranan shi a duniya "

Duk magiyar da zaiyi tsoho kin taimakon su yayi

Baba yace"saheeb muje kawai Allah ya raya ta"

SAHEEB dake zaune a kasa ya rungume samha yace"baba Ina nan har sai ya taimaka min bana son ratsa ya'ta"

Gajiya baba yayi ya tafi ya barshi a zaune tsohon ma shigewa yayi ya barshi

Jama'a ku duba lamarin Allah yau ga medical Dr itama matar shi Dr Yana rokon Wanda beyi karatu ba magani
Allah yasa mu dace

Komawa gida baba yayi fareeda na ganin shi ta taso tace"baba an dace?"

Baba yace"Ina kuwa tsohon yaki bayarwa a cewar shi Kamal ya tab'a wulakantashi a asibiti da ya Kai yar'shi"

Farida ta fashe da kuka tace"ka kaini kila in ya ganni ya bamu taimakon"

Baba yace"da kamar wuya"

Labari ta bawa baba jikin baba yayi sanyi yace"shiyasa Yana da kyau mutum ya aikata alheri muje"

Suna zuwa ko Suka tarar da saheeb zaune yayi tagumi

Sallama fareeda tayi budurwar d'azun ta fito saf fareeda ta gane itane aka kawo asibiti

Murmushi tayi tace"Ina ka'ka"

Tace"Yana ciki"

Tace'yi min sallama dashi"

Ciki ta shiga sai gashi ya fito Yana ganinta yace"ya'ta ashe rai kan ga rai?"

Tayi murmushi dole ta gaishe Shi ya amsa

Dukawa tayi tace"baba ka dubi girman Allah ka taimakawa ya'ta"

Yace"ina take haba ba sai kin rokeni ba ki shigo da ita"

Nuna me saheeb dake kallonsu tayi tace"gata shine mijina kayi hakuri ka taimaka"

Yace"ya'ta saboda ke zan dubata in ba haka ba wallahi sai dai inda Allah yayi "

Tashi SAHEEB yayi da sauri Suka shiga baba ya Basu na wanka da shafawa

Fareeda ta amsheta ta goya

Har kasa ya sunguna ya sake niman gafara baba da k'yar yace"albarkaci fareeda ya yafe me"

Abu dai kamar al'mara da suka fara mata magani ko kwana 7 ba ayi ba samhat ta fara samun lafiya tana wasan ta

Nan fa darasin rayuwa ta kara shiga saheeb ya tuba sosai

Komawa yayi yayiwa tsoho alkhari Kuma ya tabbatar me duk lokacin da yake niman taimako ya zo wajen shi

Bayan sati biyu samhat ta dawo dai-dai

Mahmud har gida ya zo da humaira Suka roke saheeb ya yafe me

Bayan wasu shekaru abubuwa da dama sun faru ciki harda haihuwar fareeda inda yanzu yaransu hud'u Iman nada uku humaira biyu soyyaya suke nunawa juna da girmamawa yanzu saheeb har gidan marayu yake dashi ga taimakon talakawa shiko tsoho Allah yayi me rasuwa saheeb ya d'auki nauyin karatun d'anshi kuma yanzu budurwar yar'shi a gidansu fareeda take har sun Mata miji

Toh fans a Nan na kawo karshe wanan labarin kuskuren dake ciki Allah ya yafe min please ayi amfani da darasin a watsar da Wanda beda amfani

Nagode da kaunar ku


*NIDA YAYA HYDAR*

Babban gareji ne Wanda kap kauyen kwaita babu gareji daya kaishi girma Kuma gareji ne me tashe saboda kwarewar ma'aikatarsu

Gareji ne da yake bakin titi garin kwaita dake under kwali area council Abuja Shiga nayi dan somo labarai domin sunan garejin ne ya ja hankalina domin a gaban garejin na gan anrubuta *MATU GARAGE*

Wani bakaniki ( makaniki)na hango kwance da kayan aikinsu yellow watoh irin kayan nan biri da wando

Aiki take cikin kwanciyar hankali a karkashin mota wani dattijon ne ya zo ya jingina da motar yace"matu ki fito gashi an kawo motar alhaji Kuma kin San baya so kowa yayi me gyra sai ke"

Abin ya bani mamaki domin na ji yayi maganar ne kamar da mace

Aiko fitowa tayi daga karkashin mota tsanye da hula baka ganin sumanta but zaka gane macece

Suman tsaye nayi ganin macece Ashe

Zaro ido nayi nace mace Kuma da irin wanan aikin

Muryar oga sule naji yace"matu Yi sauri ki duba motar nan kafin driver ya dawo d'auka

Wani kallo tayi me da yasa

11 / 12