DR SAHEEB by Maman noorul Hudah

Author :  DR SAHEEB Category :  Romance

Chapter   10 / 12

27K to 30K   out of 33.7K words

ki ce Zaki aureshi"

Tace"wallahi Dr ka fita harkata ko miye yayi min Ina ruwanka?ai dai be kai naka ba kuma baza a kwatanta da naka ba"

Kallonta yayi cikin ido da taimakon fitilan wani kofar gida me hasken gaske yace"Koda kuwa ya kashe miki d'an ko ya'?"

Tace"me kake nufi?"

Kafin yayi magana Dr musty ya kwace zancen da cewa"sharri zaka min nidai ban zubar miki da ciki ba" domin duk ya rude"

Murmushi me ciwo saheeb yayi yace"ya kayi kasan abinda zan ma sharri akai?"

Kallon fareeda yayi yace"Ina son ki sani lokacin da kike kwance a asibiti da ya gane kina da ciki sai yayi flushing saboda son zuciya"

Har kanta taji wanan maganar jikinta na wani mugun rawa da k'yar ta saita natsuwarta Kar saheeb din ya gane ta Shiga wani hali "

Kallon Dr musty tayi,zaiyi magana ta katseshi

Saheeb ya Kama hanunta yace"muje please ki rabu dashi ki bani wani dama na gane kuskurena kowa a duniya be wuce kuskure ba Ka da kike tunanin rabuwa dani kin San hanun da Zaki fad'a nan gaba?"

Fisge hanunta tayi tace"


Maman
Noorul
Hudah
Luv u my fans
Pls share
[1/11, 6:09 PM] Maman Noorul Hudah: 👄👄👄👄👄
Dr SAHEEB
💋💋💋💋💋
By maman noorul
Hudah

Dedicated to my fans

_____________

🅿8⃣5⃣-8⃣6⃣
______________
Bismillahir Rahmanir Rahim

Kallonshi tayi tace"toh saime dan ya cire min cikin da bana bukatar shi,ai taimakona yayi domin da be cire ba da ni da kaina zan Kai kudi a cire min so in kana tunanin zan rabu dashi ne saboda wanan karamin dalili kayi karya"

Cikin tashin hali domin be tab'a tunanin tsanan ya Kai haka ba da har zata ce zata kashe jininta saboda tsananshi

Yace"farheeb dama abin ya kai haka da wanne zan ji dashi an kashe min jinina Nima ai an zalunceni ai ko wani irin so yake Miki be kamata ya cire cikin ba tunda bashi ya halliceshi ba Amma ba komai ni najawa kaina nagode "

Jikin Dr musty ne yayi sanyi sai yanzu ya gane yayi kuskure ya ma rasa dalilin da yasa ya aikata haka

Shiko SAHEEB kallonsu yake Yana ja da baya jiri na dibar shi har zai fadi

Dr musty yayi sauri zai taro shi domin ya mugun bashi tausayi

D'aga me hannu yayi ya karasa mota

Zama yayi yasa kanshi a steering Yana kuka zuciyarshi na Kuna

Wayarshi ne tayi Kara sanda aka me missed calls biyu ya d'aga

Iman ce tace"Yaya ka fad'a Mata me tace?"

Yace"Iman zan hakura ta tsane ni cewa tayi da ba a cire cikin ba ita da kanta zata je a cireshi"yanke wayar yayi sakamakon kuka da ya zo me duk maganganunta wanan kalman yafi b'ata me rai"

Jan motar yayi ya bar anguwan

Itako fareeda Dr saheeb na barin wurin

Ta kalli Dr musty da jajjayen idonta tace'meyasa ka cire min ciki?"

In Ina ya fara yi Yama rasa me zaice

Tace"a haka kake tunanin kana Sona?inda kana Sona zaka bar cikin ne mu raineta tare amma sai ka zab'i ka cireshi why?"ka ko San yin haka babban laifine?.wayasa ka kashe min gudan jini ai nima jinina ne a gaskiya ban tab'a tunanin haka daga gare ka ba"

Dr musty yace"nayi ne dan Ina sonki gudun kada kizo ki komawa saheeb shiyasa na wanke ciki dan Allah ki fahimceni"

Tace"babu wata fahimta domin ni a yanzu ka fita a raina zan dai aureka ne dan kawai in samu hutu wajen saheeb but bawai Dan ina sonka ba infact nama fasa Kuma Ina son ka sani ka shiga hakkin Dr ya ma za ayi ka cire d'an Sunnah wallahi ko shege ne ai shima yana da right na a haifesa tunda babu Wanda ya hallice shi cikin mu,honestly iam disappointed in you"ta kare magana da fashewa da kuka domin ji tayi tana tausayi abinda aka cire

Barin wurin tayi ta barshi baki sake duk jikinshi yayi sanyi da k'yar ya ja mota ya bar gidan

__________
Tuki yake kwata-kwata hankalin shi yayi nisa, yayi zurfi cikin tunani kawai ba tare da ya sani ba sai ya hau footpath ji kake kirrrrrrrrr ya bigi street light

Mutane ne suka taro a inda abin ya faru shiko kanshi ne a steerig jini na fita a goshin shi da alamu suma yayi

Da sauri aka kaishi asibiti sanan aka Kira number Iman domin number ne yayi dialling last

Da gudu Iman taje part dinsu mummy tana kiransu tana kuka

Mummy da daddy suka fito daddy yace"meya faru?"

Tace"Yaya ne yayi accident yana asibiti"

Mummy tace"what wani asibiti yake"jikinta na mugun rawa

Kallonta daddy yayi inda ta gigice yace"ai hankalinki ya kwanta wallahi tunani shi ya jefa yaron nan a halin daya sinci kanshi

Iman tace"mummy ya kamata kin janye ki yafe mishi haka domin shima an zalunce shi Dr musty da kike sopporting shima bashi da hali domin shi ya cire cikin fareeda a asibiti"

Kallonta duk sukayi tace"mummy kin tuna ranan da fareeda tayi ta bleeding a asibiti?Ashe shiya mata haka"

Maganar ya matukar gigita mummy amma ta dake tace"ai shi ya jawowa kanshi"

Ciki ta shiga ta shirya ta fito tace"nidai na wuce asibiti"

Shiko daddy yace"ai za ayi ta ta Kare ne na gaji da ganin d'an nan a wanan halin"

Ciki shima ya Shiga ya shiryo ya fita Iman kawai aka bari a gidan

Ko da Suka je an shigar da saheeb ciki ana bashi taimakon gaggawa

Dr ne ya fito mummy ta karasa gabanshi tace"Dr da dai sauki ko?'

Yace

Maman
Noorul
Hudah
Luv u my fans
Pls share
[1/11, 6:09 PM] Maman Noorul Hudah: 👄👄👄👄👄
Dr SAHEEB
💋💋💋💋💋
By maman noorul
Hudah

Dedicated to my fans
____________
🅿8⃣7⃣_8⃣8⃣
____________
Bismillahir Rahmanir Rahim

Dr yace"babu wata matsala kanshine kawai ya d'an bugu munyi dressing ciwon Kuma sai iya tashiwa at anytime"

Tace"al-hamdullilah"

Bari in duba shi yace"eh Zaki iya shiga an mayar dashi ward"

Tace"ok"

Ward taje ta ganshi kwance Yana bacci wahala

Kallonshi tayi duk ya rame ya rage Kai zama tayi ta kama hanun shi tace"sannu saheeb"

Daddy ne ya turo kofa ya ganshi yace"hajiya kiyi hakuri haka ki yafe me tunda duk su biyun masu laifine Kuma ai gomma ta komawa saheeb tunda shi ya fara saninta"

Batayi magana ba ta tashi tana gogewa saheeb goshi inda jini ya bushe

A daren ranan Bata runtsa ba har ya bude ido tsakiyar dare ya ganta zaune da al-qurani tana karantawa

Fashewa yayi da kuka yace"mummy kiyi hakuri ki yafe min Koda kuwa bazan samu fareeda ba Ina bukatar yafiyarki domin in gan dai-dai da a ce na bi shawaran da kika bani randa aka d'aura aurenmu da yau ban rasa gudan jini na"

Mummy tace"kayi shiru bana son surutu"

Shiru yayi yana hawaye tace"wanan kukan zaisa kanka ciwo fa,namiji yayi ta kuka kamar mace"

Washe gari da asuba daddy ya je gidansu fareeda sallama yayi baba ya fito

Bayan sun gaisa yake sanar da baba komai daka faruwa har zuwa kwanciyar saheeb asibiti sai dai shima ya b'oye me wasu abubuwan da zai b'atawa baban rai

Hakuri sosai ya bashi duk sai kunya ya Kama baba

Yace"baba dan girman Allah ka bani auren fareeda a Karo na biyu wanan Karo nayi maka alkawarin za a rike ta amana

Baba zaiyi magana kawai sai ya gan daddy na kokarin sunguna me

Baba yayi saurin dakatar dashi badan ya so ba yace"alhaji kaima ai yar ka ce kayi duk abinda ya dace"

Godiya yayi me sosai tare da tabbacin za a Bata farin ciki kuma za a maida auren nan da sati d'aya

Da yamma ranan su mummy Suka koma gida sai dai fa saheeb ya ki magana da kowa abin ya dame mummy amma ta basar

D'akinta ta shiga tayi wanka ta fito ta shiga kicin ta same Iman na girki

Mummy tace"kin kusa ne?"
.tace"eh yanzu zan jera su a dining"

Tace"ok bari inje in Kira Kamal"

Ko da taje d'akin shi ta samu yayi wanka yayi sallah ya zauna a dadduma yayi tagumi"

Tace"in ka gama ka fito mu ci abinci"

Yace"ni bana jin yunwa"

Tace"bana son in maimata magana na, ka riga ni zuwa dining"tashi yayi yana kunkuni

Suna zaune ya fito ya ja kujera ya zauna Iman ta zuba me abinci

Daddy ya kalleta yace"hajiya kiyi hakuri nayi magana da mahaifin fareeda ranan juma'a za a maiyarda aurensu"

Kallonshi tayi tace"akan me kenan za a had'a ta da wanda bata so?"

Yace"hajiya zai koya Mata sonshi in Suka tare"

Tace"shi kuma Dr musty fa?"

Yace"na Kira shi ya sameni zan bashi hakuri"

Mummy tace"wallahi bazai yiwu ba sai dai a had'a shi da Iman "

Tashi Iman tayi ta dafe kirji tace"


Maman
Noorul
Hudah
Pls share
[1/12, 12:48 AM] Maman Noorul Hudah: 👄👄👄👄👄
Dr SAHEEB
💋💋💋💋💋
By maman noorul
Hudah

Dedicated to my fans
____________
🅿8⃣9⃣-9⃣0⃣
________________

Bismillahir Rahmanir Rahim

Mikewa Iman tayi tace"nidai bazan aure shi ba"

Daddy yace"hajiya ki barshi a bashi hakuri kawai"

Tace"saboda me kenan"

Yace"ki duba fa har ciki ya zubarwa fareeda Kuma ki ce Zaki had'ashi da yar'ki wani me tsoron Allah zai zubar da ciki ai dai-dai yake da kisa"

Tace"shi d'an naka tsoron Allah yake dashi da za a had'a shi da yar'wani look alhaji please kar ka d'au ko na rainaka ne but ya kamata mu cire son zuciya inda aka bawa Kamal second chance shima a bashi domin dukaninsu masu laifine dan bazai yiwo mu rabashi da fareeda mu kuma hanashi Iman ba ni na lura ba halin shi bane,sharrin shaidan ne in kuma baza ka yarda ba zanje gidan iyayen fareeda a d'aura da Dr musty"

Da sauri saheeb yace"mum you are right"kallon Iman dake kuka yayi yace"please my sister"

Kuka ta fashe dashi tace" ya zan auri wanda ban sani ba kuma cikin kankanin lokaci"

Yace"sorry "

Daddy yace"hakane hajiya "

Tace" ni damuwa na d'aya ya fareeda zata d'auki lamarin Amma zanje in d'aukota yau"

Saheeb yace"nima zanje"

Tace"no ka jirani"

Yace"amma yanzu zaku dawo ko?"

Hararanshi tayi kawai sai ya tsosa Kai yana murmushi

Itama murmushi tayi for the first time da zai gan murmushin ta tunda ya dawo

Makullin mota kawai ta d'auka tasa hijabi

Ta koyi sa'a ta same baba gida bayan sun gaisa

Tace"Ina fareeda take"

Yace"tana ciki yanzu ta dawo makaranta"

Tace"baba alfarma nike Nima"

Yace"toh inaji"

Yace"baba please so nike a bani fareeda ayi komai wajen mu tunda ba kowa yasan abinda ya faru ba kuma nafi son muyi komai cikin sirri basai an gane ba saboda gudun surutu da bakin mutane auren ma a masallacin kofar gidan mu za a d'aura bayan sallah asuba ba sai anyi wani taro ba domin koni yan uwana basu sani ba saboda irin haka yasa bamu sanarwa kowa ba dan gudun haddasa zargi domin wasu zasu iya zargin ko fareeda akwai abinda tayi ne yasa ya saketa kuma kasan ga saceta da aka tab'ayi wanan ma sanda ya kawo cecekuce shiyasa Nike son mu tafi da ita"

Baba yace"toh babu damuwa Allah ya bada zaman lafiya "

Mama tace"ko yanzu da ta dawo ana ta gulmace gulmace nidai banbi ta kansu bane wasu har shigowa suke suji me ya dawo da ita"

Mummy tace"ai mutane basu da tunani komai sai anyi ta gulma akai"

D'akin fareeda ta Shiga ta tarar da ita tana kuka Zama tayi a gefen gadon tace"fareeda saboda za a had'a ki da d'ana kike kuka?"

Fareeda da tausayin mummy ya kamata domin tasan bata jin dadin tsanan da take nunawa d'anta tace"ah'ah ni mummy na yafe me ina dai kukan rabuwa da mama ne"

Mummy da tasan karya takeyi tace"oh ni ba maman ki bane"

Tace"ke mamata ce mummy"

Mummy tace"toh tashi ki d'au kayanki mu tafi _

Tashi tayi tana goge hawaye a ranta tana jin haushin saheeb"

A zaune a harabar gidan suka tarar da saheeb

Motar mummy ne ya fara shigowa sai na fareeda parking tayi ta fito Yana ganinta ya taso Yana murmushi

Akwatinta ya fito dashi ta hade rai kamar hadari

Karasowa yayi dan tuni mummy ta shige ciki'

Yace"welcome back farheeb"ya Kare magana da Kai hanun akwatin da niyar amsa ta rike gam

Yace"haba kawo Mana in tayaki"

Tace"stay away from me"

Yace"how can I stay away from you? Karki manta ke matata ce"

Tsaki tayi tace"na tsane ka"

Yayi murmushi yace"and I love you baby"ya Kare magana da mata flying kiss"

Wani haushi ne ya kamata ta ture shi ta wuce"

Ya kyakyale da dariya yace"Kuma dole a zauna dani ba ka ji yariya na niman kasheni da sauran kwana,shegen taurin kan tsiya da rainin hankali Allah zaki gane ne"

Shigewa tayi ta je d'akinta direct ta kwanta

A daren ranan Dr musty ya zo daddy yayi me bayani tare da bashi hakuri

Beyi musu ba ya yarda yace"ya amince da auren Iman"domin yasan ko ya auri fareeda bazata tab'a yafe me ba kullum in sukayi fad'a saita tuna da laifin da yayi Mata"

Daddy yace

Maman
Noorul
Hudah
Luv you my fans
Pls share
[1/12, 12:48 AM] Maman Noorul Hudah: 👄👄👄👄👄
Dr SAHEEB
💋💋💋💋💋
By maman noorul
Hudah

Dedicated to Hussein Abu Sameer
____________
🅿9⃣1⃣-9⃣2⃣
__________

BismillahirRahmanir Rahim

Daddy yace"toh ka turo magabatan ka yace"inshaallahu gobe zasu zo sai dai a sa bikin nan da sati uku"

Daddy yace"ba damuwa"

Nasiha sosai mummy tame jikin shi yayi sanyi yace"mummy tabbas mahaifiyata ta rasu amma a yanzu kin cika gurbinta Ina alfari da ke"

Tayi murmushi sukayi sallama

Duk inda saheeb ya so da nacin shi ya gan fareeda abin ya faskara domin kulle kofa tayi taki budewa ba shi kadai ba babu Wanda ya gane kanta a gidan daddy yace"a kyaleta she need space"

Cikin kwanaki biyar gyra sosai mummy take masu harda Iman da kullum Dr musty ke zuwa zance harga Allah yanzu yana son iman itama ta fara sake me

Amma tsakani fareeda da saheeb ba cigaba domin duk inda tasan zai ganta Bata zuwa wurin yanzu a d'aki take cin abinci ko a hanya suka had'u sai ta canja hanya da gudu abin ya dame shi"

Yau dai ya d'au alwashin ko ta halin ka'ka sai ya ganta hakan yasa yayi ta patrol a kofar d'akin

Tana fitowa ta ganshi ta koma da wuri sai dai kafin tace"zata kulle kofa ya tura da karfi"

Kallonta yayi yace"wai me kike nufine?ke har yanzu baki hakura bane ya kamata ki gane ko Allah muna me laifi ya yafe Mana balle mutum"

Kuka ta fashe dashi tace"ni ka kyaleni bana son ganinka"

Yace"ai ganina ya Zama wajibi domin ko mutuwa nayi inda Nike jin sonki sai na miki fatalwa"

Cikin kuka tace"nidai Allah ya isana"

Yace"nima Allah ya isana ai bake kadai kika iya Allah ya isa ba"

Komawa tayi ta ajiye jaka ta kwanta ta rufe jikinta da bargo "

Zama yayi bakin gado yace"Yi hakuri please ki kulani ko zan samu natsuwar komawa aiki asibitin da yanzu bansan me ke faruwa dashi ba"


Ko kallonshi batayi ba sai ma bacci da ta fara

Murmushi yayi ya tashi ya fita

Bayan kwana biyu aka d'aura musu aure a massalaci kamar inda mummy ta fad'a haka akayi

Itadai fareeda an Mata kitso da lalli ga d'inki da mummy ta mata

Da daren ranan ta tarasu ta musu nasiha

Daddy ma ya jawa saheeb kunni akan Kar ya sake basu kunya

Jan fareeda dake kuka mummy tayi zuwa d'aki tace"nasan kin tsane Kamal but ya kamata ki gane yanzu yana da hakki akan ki Kuma dole ki saukesu in kina son kanki da rahama ki natsu ki bashi hadin kai dan ku gina rayuwa mai inganci wallahi fareeda banso yi Miki haka ba duk da Ina son ki da Kamal na so baki farin ciki but abinda na duba shine ke fa bazawara ce zaiyi wuya saurayi da be tab'a aure ba ya aure ki ya rike ki da daraja bana son Dr musty ya aure ki yanzu daga baya yayi tunani yi miki kishiya domin maza Basu da tabbas shiyasa na amince Amma ki yafe min"

Rungume mummy tayi tace"nagode"

Mummy tace"Yi sauri kije yana jiran ki a mota"

Har mota mummy ta raka ta ta Shiga gidan gaba

Mummy ta kalli saheeb dake zuba murmushi tace" shugaban marasa kunya ko sallama babu?"

Tsosa Kai yayi Yana murmushi

Har suka kai wani gida bana da ba kuka fareeda keyi taki kallon inda yake jikinshi yayi mugun sanyi Amma beyi magana ba

Shiga falon sukayi ta zauna tayi tagumi

Haurawa yayi ya tube manyan kayan jikinshi ya fito daga shi sai vest da 3qter

Ganin ta yayi kwance ta lumshe ido Yana tab'ata ta firgita

Murmushi yayi yace"matsoraciya ba abinda zan Miki ki je ki kwanta dare yayi is after 9"

Tace"ni a Nan zan kwanta"

Yace"saboda me fa?"

Tace" haka kawai"

.yace"ok wallahi in bakitafi ba abinda kike gudu shi zan Miki"

Da sauri ta mike tace" Ina ne d'akin?"

Yace"ki lalleka ai gidanki ne"

Zuwa tayi ta duba aiko ta gan Wanda take sa ran nata ne ta shiga tayi kulle"

Kulle gida yayi yaje d'akin tura kofa yayi ya jita a rufe

Babu inda beyi da fareeda ba amma taki budewa haka ya hakura ya koma d'akin shi

Bayan sati d'aya

Maman
Noorul
Hudah
Luv u my fans
Pls share
[1/12, 8:27 PM] Maman Noorul Hudah: 👄👄👄👄👄
Dr SAHEEB
💋💋💋💋💋
By maman noorul
Hudah

Dedicated to my fans
__________

🅿9⃣3⃣-9⃣4⃣
__________
Bismillahir Rahmanir Rahim

Bayan sati d'aya wasan b'uya sukeyi da fareeda ko kad'an bata Bari ya ganta kafin ya tashi ta tafi makaranta ko girki bata masa balle yasa ran wata kyautatawa ga wani iskanci da ta kawo in zata fita bata zuwa da mota sai adaidaita sahu

In ma yayi sa'a ya ganta ko kallonshi batayi a gabanshi zata girka abinci dai-dai ita ta cinye hakan yasa ya kirata yayi Mata magana Amma sai tace"ya Kara aure in be zai iya Zama da ita ba"

Duk ya rame ya sukurkuce domin shifa a gaskiya Yana bukatar matarshi kusa dashi ko a asibiti baya gane kan aiki"

A daddafe sukayi sati uku kowa na harkan gabansa in suna gida wickend shi kadai zaka gani a falo ita tana d'aki a lokacin an fara shirin bikin Iman Wanda yanzu suke zuba soyyaya da musty

A yau ta kama wickend da sassafen ta fito Kamar inda ta saba kafin ya tashi ta gyra gida da sauri-sauri domin bata son ya fito ya tarar da ita

Kicin ta shiga ta had'awa kanta breakfast ta fito ta zauna ta ci ta koma kicin ta wanke abinda ta b'ata ta koma ciki

Gajiya tayi da kwanciya kadaici ya lullubeta ta fito falo ta kunna tv tana kallo sai dai abin mamaki yau ko da asuba bata ji motsinshi ba alamun be fita masallaci ba kenan"

A ranta tace"ko be kwana bane a gida?"a fili Kuma tace"toh ni Ina ruwana?"

Zama tayi amma zuciyarta ta kasa samun natsuwa d'aga Kai tayi ta kalli kofar d'akin sai kawai ta kau da kai ta cigaba da kallonta

Abu kamar Wasa har dare bata ji motsin shi ba

Kawai sai ta sinci kanta da son zuwa d'akin

10 / 12