DR SAHEEB by Maman noorul Hudah

Author :  DR SAHEEB Category :  Romance

Chapter   4 / 12

9K to 12K   out of 33.7K words

gorgeous, interllingent,and expert writers we the best among the rest.

Dedicated to my fans
_______________
πŸ…Ώ2⃣9⃣_3⃣0⃣
_____________
Bismillahir Rahmanir Rahim

Washe gari da safe iyalan alhaji al'amin ne zaune a dining suna cin abinci

Daddy ne ya kalli mummy yace"hajiya har yanzu fa babu labarin yariyar nan fareeda na tausayawa malam Abdallah "

Mummy tace"Allah ya bayyanata gashi bikinta Nan da kwanaki kad'an ne ai irin haka sai ya haddasa zargi tsakanin mijinta"

Shidai saheeb shiru yayi Yana tunanin badai fareedar daya sace dady ke magana akai ba"

Daddy ne ya kalleshi yace"Kamal ai a asibitin ka take aiki ko kasan inda taje Kuma yaushe ne last ka ganta domin ance daga zuwa night har yau"

Kallon daddy yayi yace"asibitina kuma?nifa ban san wata fareeda ba,but daddy baka tunanin ko wajen saurayinta taje ne?"

Dakuwa mummy tame tace"gidan ku Kai meyasa babu alkhari a bakin ka ne?"

Daddy yace"nifa nasan fareeda yariyar akwai natsuwa bana jin zata aikata hakan fatan mu Allah yasa tana lafiya,zan Kara zuwa police station inji ko sun samo wani labari"

Mummy tace"Allah ya taimaka"

Yace"Amin"

Saheeb a ranshi yace"yau dai zanyi abinda zanyi kafin asirina ya tonu"

Tashi yayi mummy ta kalleshi tace"Ina zuwa?"

Yace"asibiti"

Kallon tuhuma tame tace"wai meke faruwa ne?Kai da baka son zuwa aiki suddenly yanzu kullum sai kaje,iam warning you don't act anything funny cause I won't spare you"

Gabanshi ne ya fadi Amma ta dake yace"kedai mummy babu abinda zanyi in birge ki da bana zuwa kullum kina fad'a Amma yanzu kuma ina zuwa kina magana toh ai dole zan sa ido a aiki ko"

Bata Kara magana ba ta mike tana had'a plates

Gidanshi yayi direct inda yaje ya Sami fareeda zaune ta hade Kai da guiwa tana kuka

Dariya yayi yace"tun yanzu ai banma Yi komai bako,yanzu dai karki b'ata min lokaci ki tashi ki tube da kanki I don't have time Dan na gan alamun kin yi wanka'

D'agowa tayi da jajjayen idonta tace"ai sai dai ka tsallake gawa ta kafin ka aikata Zina dani d'an iska kawai"

Karasawa yayi cikin mugunta ya mikar da ita ya wanka Mata wani Mari daya sata sakin kara ta fadi saman gado

Jan rigarta ya farayi sai ya yage

Kwantawa yayi samanta ya fara kokarin hade bakinsu ta damke nata

Aiko sai ya rufeta da duka ta saki kuka yace"Dan kawai Ina ta Miki dariya?ni ba a tab'a ni in kyale yau zan nuna Miki ke karamar Yar iska ce ke karamar Mara kunya ....."Ai maganar makalewa yayi sakamakon fashewar bedside lamb da ya ji akan shi tuni ya koma gefe wanda a take ya sume

Tsoro ne ya kamata jiki na rawa ta saka hannu a aljihun shi ta cire makulli da k'yar ta iya bude kofar ta sauka da gudu ta bude na falon

Har zata fita ta kuma dawowa ta Shiga kicin ta ciro ruwan sanyi ta haura ta zuba me a jiki

Wani dogon ajiyar zuciya ya sauke ya bude ido sai dai ya kasa motsi

Kallonshi tayi tame gwalo tace"serves you right sanan ta ruga a guje ta bar gidan

Shiko kanshi ya rike ga jini na zuba ya wanke me fuska

Yace"you won't get away with this"


Hmmm

*Wanene Dr saheeb?*

Maman
Noorul
Hudah
Luv u
Pls share
[1/4, 12:54 PM] Maman Noorul Hudah: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
*_DR SAHEEB*_
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

🌟 GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

Home of gorgeous, interllingent,and expert writers we the best among the rest.

Dedicated to my family
_____________
πŸ…Ώ3⃣1⃣&3⃣2⃣
____________

Bismillahir Rahmanir Rahim

Kamalundeen Al'amin shine asalin sunan shi Amma ana kiranshi da saheeb saboda ya ci sunan kakanshi watoh mahaifin daddy shi

D'an ne ga alhaji Musa al'amin da mahaifiyarshi Rukayya Wanda in ka ganta sai ka rantse balarabiya ce Kuma ita fulani ce fulanin taraba

Iyayenshi auren soyyaya sukayi inda ko shekara Basu da aure basuyi ba Allah ya Basu haihuwa suka haife shi

Alhaji Musa d'an kasuwa ne Yana da kamfannoni mutum ne me son jama'a ga iya Zama da mutane

Su biyu ne a wurin iyayensu shi da kanwarshi Iman

Saheeb da Iman sun taso ne cikin so da gatan iyayen su kasancewar mahaifinsu attajiri ne Wanda yake da kamfanoni dayawa

A Niger State (Minna) suke da Zama Amma asalin mahaifinsu d'an kano ne Amma mummy taraba a makaranta Suka had'u da daddy har sukayi aure

Hajiya Rukkaya barrister ce sai dai bata aiki

A minna saheeb yayi primary da secondary dinshi inda ya gama al-amin international School Yana gamawa Daddy ya turashi kasar waje inda ya karanta likitanci ya Zama cikeken likita watoh medical doctor Wanda yasan aikin shi

Sai dai saheeb bashi da halin kirki domin tun Yana karami ya tsane talakawa ga rainin wayau da rashin girmama na gaba dashi,mummy tayi iyakar kokarinta na ganin ta seta shi Amma abin ya faskara domin ita kadai ke fama daddy be damu ba, irin mutanen Nan ne I dont care duk da shima wani lokaci ya kan me fad'a

Tun Yana turai daya kusa Gama makaranta Daddy ya fara Gina me asibiti babba me girman gaske domin ya faranta mishi

Saheeb Yana shaye-shaye tun Yana secondary school kuma iyayen shi sun sani mummy dai tana iyakar kokarinta na ganin ta gyra me rayuwa sai dai kamar a banza takeyi domin komin fad'an ta in yayi niyar yin Abu baya fasawa sai dai wani lokaci Yana mugun shakkata kasancewata no nosense ne ita"

Kamanin saheeb d'aya da mummy shiyasa mutane ke me kallon balarabe domin fari ne tas ga kyau kamar mace ga gashin kanshi kwance

Ranan daya farawa zuwa asibiti kenan ya had'u da fareeda har tame wanan Marin Wanda da tasan ko waye saheeb da Bata kuskura ta wanka me wanan Marin ba,saheeb irin mutane nan ne da basu da tunani da rashin Imani balle in yayi shaye-shaye,saheeb har wiwi yana sha,saheeb bashi da yafiya ko kadan domin ko Iman ne tame laifi sai ya rama hakan yasa shi d'aukan alkawarin b'atawa fareeda rayuwa at all cost

Shekaran saheeb 27 ita kuma Iman 23

Wanan shine kad'an daga cikin labarin saheeb sauran zaku ji Nan gaba sai dai fa kuyi hakuri da abinda zaiyi wa fareeda

Wanan kenan
Cigaban labari

Maman
Noorul
Hudah
Luv u
Pls share
[1/4, 6:51 PM] Maman Noorul Hudah: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
*_DR SAHEEB*_
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

🌟 GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

Home of gorgeous, interllingent,and expert writers we the best among the rest.

Dedicated to my fans
___________

πŸ…Ώ3⃣3⃣-3⃣4⃣
______________
Bismillahir Rahmanir Rahim

Da k'yar ya jawo waya ya Kira Mahmud ko minti ashirin ba ayi ba ya zo gidan

Abu kamar Wasa sanda saheeb ya Sha ledar ruwa hakan ya kara sashi saka mugun kudiri a ranshi na ko me zai faru sai ya wulakanta fareeda tunda har tayi sanadin da yayi jinya

Fareeda ko tana fita ta tare me adaidaita gida tayi direct inda ya sauketa ta Shiga ciki domin anso me kudi

Baba dake zaune yayi tagumi Yana ganinta ya mike yace"fareeda Ina kika Shiga har tsawon kwana bakwai kuka ta fashe dashi

Tace"saceni akayi baba yanzu dai bani kudi in kaiwa me adaidaita"

Kudi ya bata ta kaiwa me a daidaita a kofar gida ko sai kallonta ake Bata kulasu ba ta shige gida

Zama tayi baba ya kalleta yace"Ina jin ki"

Kallonshi tayi tace"baba Ina mama tunda na dawo ban ganta ba"

Yace"tana d'aki an Samata ruwa hawan jini ya kamata"

Mikewa tayi ta shige d'akin ta rungume mama dake bacci bude ido tayi tana ganin fareeda ta fara kokarin tashi

Tace"mama karki damu na dawo kenan"

Mama cikin muryar marasa lafiya tace"Ina kika shiga kika barmu cikin damuwa?"

Tace"wallahi Rana nan Ina dawowa wasu Suka sace ni Suka saka ni a mota yanzu ma da k'yar na kubuta"

Baba zaiyi magana sai yaji sallama daddy

Fita yayi suka gaisa daddy yace"yanzu kenan na fito daga ofishin yan sanda Amma har yanzu shiru karka damu nasan za a dace"

Cikin ladabi baba yace"ai mun gode Allah yanzu ta dawo"

Daddy yace"ikon Allah alhamdullilah Kira ta"

Fitowa farida tayi ta durkusa har kasa ta gaisheshi

Kallonta yayi yace"fareeda ya akayi haka kuma?"

Shiru tayi a ranta tace"d'an ka shi ya saceni"Amma a fili sai tace"wallahi Abba saceni akayi aka kaini wani gida"

Yace"ikon Allah Amma waye yayi Miki wanan aikin domin nasan da kidnappers ne da sunyi demanding ransom"kallonta yayi yace"Zaki iya gane ko in ce kin San Wanda yayi Miki wanan aikin"

Shiru tayi tana tunanin ta fad'a me gaskiya ne ko ta b'oye me"

Maganar shi ce ta katseta da yace"kin Yi shiru"

Kawai sai ta yanke shawaran ta b'oye me d'anshi ne yasa aka sace ta saboda dalilai uku,na farko bata son abinda zai kawo rashin fahimta tsakanin daddy da baba domin tasan halin baba da zuciya ba karamin b'aci ranshi zaiyi ba in ya San gaskiya Kuma zaice zai Kai Kara station domin zaice dan saheeb d'an me kudine bashi zai bashi damar wulakanta yar'shi ba,dalili na biyu shine Bata son surutu yayi yawa a ce tayi rayuwa a gidan wani namiji har na tsawon sati d'aya Bata ma son uztazunta ya San gaskiya dama ta lura ya fara canja Mata tasan aikin fauziyane,dalilin na uku shine bata son ta Kara shiga harka saheeb ko aikin ta hakura tana gudun ta fadi gaskiya ya zo yayi Mata abinda yafi nada"

Kallon Abba tayi tace"ban sanshi ba"

Abba yace"ok zan Kira Yan sanda ayi bincike ai nasan kin San inda suka kaiki"

Tace"daddy a sume Suka kaini kuma da na gudu ban lura da anguwan ba saboda saurin karsu kamani bazan gane ba"

Daddi yace"Yan sanda zasuyi aikin su"

Tace"nagode"

Cikin kankanin lokaci surutai ya cika anguwa kowa na fadin albarkacin bakinshi wasu suce yawo taje wasu Kuma suce dama sun San irinsu

Bayan wasu kwanaki saheeb sanda yayi Kwana uku be koma gida ba

Ran mummy yayi mugun b'ace d'aya dawo sai ta ganshi da bandage tayi me tambayar duniya Amma yaki fadin meya sameshi da ta masa ne sai daddy yace a barshi Mana ai shi ba yaro bane"badan taso ba tayi shiru

Bayan wasu kwanaki bikin fareeda da uztazu ya rage kwana biyu tunda ta dawo Bata koma wurin aiki ba sai dai uztaz ya mugun canja Mata baya zuwa gidansu ko yaje ita kadai ke magana

Shiko SAHEEB hankalin shi a tashe yake ganin har zatayi aure be samu ya d'au fansa ba sai dai fa ya d'au alwashin baza a d'aura auren nan da farouq ba

Zuwa yayi ya d'au katin bikin da aka bawa daddy

Number dake cikin katin ya kwashe ya Kira

Yace"Dan Allah Ina magana da farouq ne"

A d'ayan b'angaren aka ceme ah'ah

Yace"pleaes number shi nake so ne domin Ina son muyi wata magana ne"
.Abbas abokin farouq ba tare da tunanin komai ba ya tura me number

Murmushi yayi a take ya Kira number

Farouq na d'agawa da sallama

Saheeb yayi murmushi yace"saurayin fareeda ne na kirane in maka kashedi ka fita hanyar karuwata in ba haka ba toh Ina tabbatar maka mu biyu zamuyi ta hawanta domin ko ka aureta bazai Hana mu had'uwa ba"

Ai wani fadiwar gaba uztaz ya ji yace"

Maman
Noorul
Hudah
Luv u my fans
Pls share
[1/4, 6:51 PM] Maman Noorul Hudah: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
*_DR SAHEEB*_
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

🌟 GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

Home of gorgeous, interllingent,and expert writers we the best among the rest.

Dedicated to my fans
___________
πŸ…Ώ3⃣5⃣-3⃣6⃣
_____________
Bismillahir Rahmanir Rahim

cikin mugun tashin hankali farouq dake tsaye cikin d'akin shi ya zauna yace"bawan Allah karka Mata sharri fareeda ba haka take ba"

Dariyar rainin hankali saheeb yayi yace"Ashe kaima kana cikin mahaukata Wanda fareeda ke yaudara ta Sha fad'a min Kai Wawa ne shiyasa tace"muje muyi sati d'aya mu huta kafin auren Ku ta Kuma cemin indai Kaine ko wani karya ta shimfid'e maka yarda zakayi,ka tab'a tunanin meyasa da Bata night duty sanda na dawo ta fara nine Dr saheeb ai babu abinda mukeyi sai hulewa"

Hawaye ne ya fara gangara daga idon uztaz jinshi shiru yasa saheeb yin murmushi samun nasara

Yace"nidai na dai Kira kane in baka shawara ka fasa auren nan in ba haka ba fareeda matar maza biyu ne"

Yanke wayar uztaz yayi ya kwanta Yana jin wata tsanan fareeda

Shiko SAHEEB yayi dariya yace"kin Yi kuskure yariya"

Bayan kwana biyu

Yau ta kama juma'a kuma yaune d'aurin auren fareeda da farouq gidan ya cika da makota da abokan arziki

Amarya ko tayi kwaliya cikin wata atamfa Wanda ta tsaya da kudinta domin ba laifi ta dade tana tanadi su humaira ne zaune suna Mata tsiya

Bayan sallah juma'a aka cika a cikin massalacin kofar gidansu fareeda

Sai dai fa an share awa biyu ba a gan ango da walihi shi ba babu jama'arsa

Daddy daya gaji da jira yace"wai malam Abdallah meke faruwa ne?"

Baba dake kiran number farouq a Karo na ba adadi

Sai yanzu ya d'aga baba yace"ya na jiku shiru Kuma na Kira number kawunan ka akashe"

Farouq yace"fasawa mukayi "

Baba besan lokacin da yace"kun fasa Kuma?"

Tasowa saheeb daya nace sai ya biyo daddy yayi yace"baba meya ce?"

Baba da ya rike Kai idonshi ya canja kala ya kalli daddy yace"wai sun fasa"hawaye ke gangarowa a idonshi yace"sun b'atawa ya'ta rayuwa,har cemin yake wai shi bazai auri karuwar da taje karuwanci har na tsawon sati d'aya ba"

Daddy yace"karka damu za a San abinyi"

Saheeb yayi saurin cewa daddy me zai hana ni a d'aura dani?"

Baba yace"ah'ah karka damu zamu yarda da kaddara bana son ka zo daga baya ka wulakanta min ya'ta tunda a araha ka sameta ko kamata gori".

Daddy yace"karka damu na dade Ina son haka ta faru domin na yaba da hankalin fareeda"

Baba zaiyi magana daddy ya dakatar dashi

Shidai saheeb addu'a yake baba ya yarda

Daddy yace"muje ka gan ai mu bar jamma'a kuma ka hakura ayi auren Nan gashi mun tara jama'a

Yace"toh"

Suna komawa ba tare da b'ata lokaci ba aka d'aura auren

KAMALUDEEN
~Da~
FAREEDA

Akan sadaki dubu hamsin

Su dai yan cikin gida Basu San meke faruwa ba ciki kuwa harda fareeda ga Daddy ya roki alfarma Kar a sanar da ita a bari ta gani da idonta


Shiko SAHEEB ana fitowa daga d'aurin auren ya Kira wani mutm

Yace"ka min booking flight din?"

A d'ayan b'angaren akace 12:am zai tashi

Yace"good"

Kira Mahmud yayi yace"ya maganar maganin da kace zaka bani na gargajiya?"..!


Mahmud yayi dariya yace"kace plan din yayi kenan?".

Yace"eh Mana"


Mahmud yace"

Toh fans ya kuke ganin zai kasance?miye plan din saheeb nidai shawarata team fareeda a zauna da shiri karya shnmace ku

No my water inside wooo Kar a zo a ce na fiye muguntaπŸ€ͺ
Maman
Noorul
Hudah
Pls share
[1/5, 9:33 AM] Maman Noorul Hudah: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
*_DR SAHEEB*_
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

🌟 GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

Home of gorgeous, interllingent,and expert writers we the best among the rest.

Dedicated to all my fans
____________

πŸ…Ώ3⃣7⃣_3⃣8⃣
_______________

Bismillahir Rahmanir Rahim

Mahmud yace"ok zamu had'u zan baka maganin zaka iya 4hrs kanayi zaka ajiye tarihi a rayuwarta da ko ganin ka tayi wallahi sai ta firgita balle ya Kai ga,ta d'aga hannu ta mare ka"

Yace"good Ina gamawa zan bar gari wallahi"

Mahmud yace"in kana so sai in Taya ka"

Tsaki yayi yace"kaifa d'an iska ne matar nawa"

Daddy ne ya taho inda yake yace"muje toh muyiwa mummy bayanin komai kasan ba musan da bikin ba"

Yace"toh"

Zuwa sukayi wajen baba da kwata-kwata harkan auren beyi me ba ya dai jin kunyar alhaji ne Amma shifa harga Allah baya son aje a wulakanta me ya'

Duk daddy ya lura da yanayin shi kallonshi yayi ya dafa shi yace"malam Ashe duk tsawon shekaru da muka kwashe muna tare baka yarda dani ba Kamal d'an na ne kuma ai a gaban ka ya nuna da kanshi ba dole akayi me ba Yana son auren fareeda ka kwantar da hankalin ka inshaallah za a rike ta Amana"

Baba ya kalleshi ya Kama hanunshi yace"alhaji ba haka bane Amma Ina gudun aje a wulakanta min ya'ta wallahi bazan ji dadi ba nasan ya'ta na kuma yarda da tarbiyarta shiyasa Nike son in roke ku dan girman Allah ku rufamin asiri duk randa kuka gaji da ita ku dawo min da ita Amma Kar a wulakanta ta wallahi ko Karen gidana bazan Bari a wulakantashi ba balle ya'ta fareeda,alhaji ayi ta hakuri da ita kasan a gidan Rashi ta tashi sai dai ta yarda da karfin iyayen ta"ya Kare magana hawaye na bin kuncin shi domin beso a ce fareeda ta auri me kudi ba yasan halin ya'yan su"

Daddy yace"lallai na yarda yau baka d'auke ni d'an uwa ba Amma babu komai ni zan nuna maka ba haka Nike ba"
.shidai saheeb bece komai ba sai ma dukar da kai da yayi

Bayan yan d'aurin auren sun watse baba ya koma ciki daddy ya shiga mota da daddy shi

Baba na shiga ciki ya gan Mata ne cike duk inda ya so kebewa da mama yayi Mata bayani abin ya fassakara

Ganin fareeda yayi ta fito tayi kwalliya tayi kyau da ka ganta kasan tana cikin farin ciki

Haka kawai yaji tausayin yar'shi har ya fara tafiya zaije inda take sai ya gan hummaira ta fito tace"faree muyi selfie"tayi magana tare da d'aga waya

Ji yayi jikinshi yayi sanyi domin yasan duk wanan farin cikin dan Bata san abinda ya faru bane,kuma fad'a mata zai b'ata Mata farin ciki yasan halinta sai ta tada bikin

A ranshi yace"ki yafe min fareeda bansan Taya zan fad'a Miki farouq ya fasa aurenki ba saboda yana zargin ki"yanke shawaran bazai fad'a Mata ba yayi sanan ya bar gidan gaba ki d'aya

Su mummy ko daddy na kaiwa gida ya Mata bayanin komai ba karamin farin ciki tayi ba zaunar da saheeb tayi tace"d'ana ka godewa Allah daya baka Mata ta gari kamila Dan girman Allah ka rike ta amana ka ji Allah ya albarkaci auren ku"

Yace"Amin"

Kiran kad'an daga cikin danginta na kusa tayi dan zuwa d'aukan amarya tace"da an d'auketa a kaita gidan mijinta direct in ya so gobe saheeb ya taho da ita dan a fara shirin wata bikin da programs kuma tana son sanin choice dinta domin a fara had'a Mata lafe"

Cikin kankanin lokaci aka cika gidan da Yan uwa na kusa sai tsiya akeyiwa saheeb

Iman ko murna tayi sosai

Haka fa akayi yinin biki anci an Sha kuma babu Wanda ya fad'awa fareeda abinda ke faruwa

Da misalin karfe 6:30 motorcin alfarma Suka paka kofar gidansu fareeda

Abin ya matukar bawa mutane mamaki ganin matan da suka zo d'aukan amarya

Bayan anyi gaishe gaishe aka Kai fareeda d'akin mama nasiha ta Mata sosai kuka fareeda keyi mama nayi

A waje suka tarar da baba fareeda ta rungumeshi tana kuka ga mamakinta shima hawayen yakeyi yace"ki yafe min ya'ta kowaye kika gani a matsayin mijin

4 / 12