DR SAHEEB by Maman noorul Hudah

Author :  DR SAHEEB Category :  Romance

Chapter   6 / 12

15K to 18K   out of 33.7K words

a fitar da ita waje"domin bayan sati biyu da faruwar abu sai ta fara bleeding da mummy tayi magana sai Dr musty yace" al'ada take"sosai ta tsorata Amma ya tabbatar mata jinin zai tsaya haka ko akayi

Haka kawai Dr mustapha ya sinci kanshi da rashin jin dadin hakan sai dai bece komai ba

Haka fa ta kasance har na tsawon sati uku inda ake shirin tafiya da ita da yammancin yau

Mummy ta tafi gida shiryawa Dr mustapha ne ya shigo ward din ya zauna ya Kama hanun ta ya kalli fuskarta yayi murmushi yace"sleeping beauty"

Sunanta ya fara Kira yace"fareeda fareeda ki bude idonki bacci ta Isa haka,fareeda ki tuna iyayen ki,mama zata iya rasa rayuwarta baba ma zai Shiga wani hali saboda ke ki manta da abinda ya faru ki tashi ki cigaba da rayuwar ki"domin sanda yasan inda yayiwa Iman wayau yasan komai na fareeda haka kawai ya ji is interested a case dinta
.haka yayi ta surutai Kamar tana jin shi har ya gaji ya mike

Har ya bude kofa sai yaji na'urar jikinta ya fara kara

Juyawa yayi sai ya gan ta bude ido tana kalle kalle asibinti can dai kamar Wanda ta tuna wani abu sai kawai ta fara juye-juye da tsalle -tsalle a gado

Da sauri ya karasa kafin ta Kuma sumewa yace"fareeda baba ya zo"

Kallonshi tayi ta Kura me ido hawaye na bin kuncinta

Wani mugun tausayinta yaji ya rungumeta yace"you are save"

Kalle-kalle take yace"kiyi magana Mana "

Shiru tayi,kawai sai yayi murmushi yace"welcome back watan ki d'aya a asibiti"

Zaro ido tayi Amma Bata ce komai ba

murmushi yayi yace"no prob in baki son kiyi magana dani toh ko in Kira Miki Dr sahe...."

Ai be karasa ba sakamakon wani ihun da tayi jikinta na mugun rawa

Yace"Yi hakuri toh"gyra Mata hular kanta yayi domin ya tsane ya gan kanta

Jingina tayi da gado babu abinda take sai hawaye

Kallonta yayi zaiyi magana sai ga mummy

Da mamaki ta kallesu cikin farin ciki ta zo ta rungume fareeda tana hawaye

Tace"dota yaushe kika farka?"

Bud'a bakin fareeda sai Suka ji tace"a kaini wajen mamana"

Mummy tace"ai Nima maman ki ne"

Shiko Dr mustapha jin tayi magana yasa shi sauke ajiyar zuciya domin dama yana gudun kar trauma ya hanata magana"

Kuka ta fashe dashi tace"akaini gida zai kasheni yayi min fyade ya rabani da uztazu na "

Kamar Wanda ta tuna wani abu cikin kuka tace"har mafalki nayi zai aske min sumana be aske bako?"ta kare magana da tab'a kanta

Aiko taji shi sumul wani ihu ta sake tace"ya aske dan Allah ku taimakeni ku tada ni a mafalki na tuba"

Mummy ta rungumeta tana kukan tausayinta tace"

Maman
Noorul
Hudah
Luv u my fans
Pls share
[1/6, 6:19 PM] Maman Noorul Hudah: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
*_DR SAHEEB*_
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

🌟 GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

Home of gorgeous, interllingent,and expert writers we the best among the rest.

Dedicated to my fans
______________
πŸ…Ώ4⃣7⃣-4⃣8⃣
_________________
Bismillahir Rahmanir Rahim

Tace"kiyi hakuri ya'ta ki cire wanan tunanin a zuciyar ki kinji?"

Kokarin tashi take son yi jiri ya kamata tayi kamar zata fadi a lokaci d'aya mummy da Dr mustapha suka riketa

Kallonshi mummy tayi domin kwayar idonshi ya gama tona Mashi asiri

Dukar da kai yayi cikin jin kunya ya janye hanunshi yace"Sannu"

Zama tayi mummy tace"me kike so toilet zaki?"

Tace"mummy Ina son in saftace bakina"

Dr mustapha yace"iam sorry I was carried away I guess shine dalilin da ya hana ki magana d'azu ko?"

Mummy ko tace"ba baki kadai ba kina bukatar wanka"

Har bakin kofa ta rakata ta shiga sanan mummy ta dawo ta zauna d'aga Kai tayi ta kalle Dr mustapha sai kawai ya Sosa kai

Murmushi tayi tace"nasan jira kake ta fito ka shafa mata mai ko son?"

Da sauri ya bar ward din cike da kunya,Yana fita tace"kayiwa kanka saheeb"

Ba a jima ba fareeda ta fito d'aure da zani a kirji

Mummy ta Mika Mata wani dogon riga tasa tace"kina ta kallona,Zaki ce waye wanan?"

Murmushi yake fareeda tayi Amma batayi magana ba

Mummy ta kama hanunta tace"ni ce mahaifiyar saheeb"ta kare magana tana kallon kwayar idon fareeda

A take fuskar fareeda ta canja babu abin da kake hangowa sai tsanan Saheeb

Mummy ma sanda ta d'anyi Jim tukkuna harga Allah taji ba dadin yanayin fareeda sai dai ya zatayi shi ya jawo

Cikin sanyi jiki tace"dear ya abin ya faru"

Jikinta ya fara ruwa ta rungume mummy tace"mummy kashe ni ya so yi yana ta dukana ya yaga min kayan jikina mummy na tuba ko wani na gan yanayiwa babba rashin kunya bazan kara cewa komai ba"cikin kuka ta kwashe labarin komai ta fad'a Mata ta kare da cewa"nidai Allah ya isana"

Mummy tace"karki damu kin ji yayiwa kanshi"

Tace"mummy su mama basu zo sun gan ni ba? Yama akayi na Kare a gidan saheeb shine fa ya sace ni kwanaki criminal ne"

Mummy tayi shiru na d'an lokaci kafin tace"an fasa aurenki ne da farouq shine akayi da saheeb bamu San abinda yake shiryawa ba kenan"

Tunawa tayi da ya fad'a Mata shi ya Kira farouq

Tace"mummy shi ya shirya komai shi ya Kira farouq ya fad'a me ni karuwa ce"

Mummy tace"ki kyaleshi Allah ya isanki"

Tace"nidai a maidani gida Ina son ganin baba"

Mummy ta zauna kusa da ita tace"ah'ah gidan mu zan kaiki kina son ciwon mama ya tashi ne jin labarin abinda ya faru dake zai iya sasu cikin damuwa and yan anguwa zasu bude shafin gulma kin San yanzu kiwon mutum akeyi ko kina son baba da mama su shiga damuwa an sakoki a daren auren ki"

Kallon mummy tayi cikin alaman tambaya mummy tace"hmmm yayi Miki saki d'aya Amma karki damu daga yau kin Zama ya'ta Amma dan girman Allah kiyi hakuri ki zauna damu karki Bari kowa yasan wanan maganar harda iyayen ki duk Wanda ya tambayeki mijin ki, ki ce ya tafi Karo ilimi a kasar waje,ke kuma za a saki a makaranta ki cigaba da karatun ki"

Tace"nidai bazan iya Zama a gidan ku ba na tuba Dan girman Allah ki barni in tafi gida ni bazan iya Zama gida d'aya da saheeb ba"

Rungumeta mummy tayi domin jikin ta har wani mugun rawa yakeyi

Tace"karki damu ya tafi inda aka haifesa bazan tab'a bari a cutar da ke ba"

Tace"toh nagode"

Tea Mai kauri ta Bata ta Sha sanan ta fara had'a kayanta

Dr musty ne ya turo kofa

Mummy ta kalleshi tace"

Kuyi hakuri yau na ce bari inje break inyi bacci

Shima Dr saheeb yace"yau in muku horo domin ba laifi ya Sha zagi jiya shiyasa yace"in huta sai ya gan ta inda za a hukunta shi🀣😏😏tunda kowa gudun shi yake

Fans a gaskiya nagode da kaunar ku Ina mugun yin ku please mu hade gobe inshaallah a min uzuri yau ba haka na so ba
Maman
Noorul
Hudah
Luv u my fans
Pls share
[1/7, 11:15 AM] Maman Noorul Hudah: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
*_DR SAHEEB*_
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

🌟 GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

Home of gorgeous, interllingent,and expert writers we the best among the rest.

Dedicated to my fans
_______________
πŸ…Ώ4⃣9⃣-5⃣0⃣
_______________

Bismillahir Rahmanir Rahim

Mummy tace"Dr tunda baka sallame mu ba mun sallame kanmu"

Shafa kai yayi,yayi murmushi shi Mai kyau yace"Yi hakuri na gan jikin nata da saura ne"

Hararanshi tayi tace"toh mudai mun tafi"

Itadai fareeda dukar da kai tayi domin ya zuba Mata ido

Ganin ya takurata ya sata mikewa tace"mummy Ina hijabi na?"

Mummy tace"ga wani can"

D'auka tayi tasa ta d'ago kai sai su had'a ido

Mummy tace"muje daddyn ku na waje".


Dr musty ne ya amshi kayan hanun mummy ya bi bayansu har suka Kai wajen mota ta ansa tame godiya

Daddy yaji dadin farfadowan fareeda yayi Mata ya jiki tare da niman alfarma karta sanar da iyayenta in sun tambaye ta tace"kasar waje taje amma ta dawo"

Suna kaiwa gida mummy ta kaita wani had'aden d'aki babu abinda babu komai na d'akin sea green ne"

Tace"daga yau d'akin ki ne wanan kiyi wanka ki fito ki ci abinci kafin Iman ta dawo ga akwatunan da anty samha ta kawo na lafen ki cire kaya kisa"

Tace"toh"kawai tace ta zauna bakin gado

Mummy ko taje kicin dan girka masu abinci Mai lafiya domin tun bayan abinda ya faru yau ne zasu ci abinci hankali kwance

Tashi tayi ta shige toilet tsayawa tayi gaban madubi tana kallon kanta da gashi ya fara tsirowa

Hawaye na gangarowa tace"I hate you Dr saheeb I hate you"

Kuka sosai tayi kafin ta mike tayi wankan ta,ta fito d'aure da towel

Mai da ta gani gaban madubi ta shafa ta fashe jikinta da tulare ta saka atamfa riga da zani tasa hijab ta fita

Sauka tayi nan ta gan mummy zaune a dining

Tace"mummy shine baki jirani na taya ki ba"

Mummy tace"ah'ah ke da baki da lafiya"

Tace"ai naji sauki"

Mummy tace"haba dota Nan ma fa gidan ku ne ki cire wanan hijabin"

Zatayi magana mummy ta katseta da cewa bana son musu

Murmushi tayi ta cire sanan ta zauna mummy ta zuba Mata

Daddy ne ya sauko cikin jin kunya zata mike yace"Yi zaman ki ai ke na gidane

Zama tayi sai dai a takure take

Iman ne ta shigo da gudu ta rungumeta tace"lah anty Ashe kin farka"

Murmushi tayi tace"Allah yayi "

Iman tace"iam very happy today"

Daddy yace"Iman har yanzu a na sayar da foam a school dinku ko an rufe".

Tace"eh,da last week za a kulle sai kuma suka Kara one weeek"

Yace"ok gobe ki siyowa fareeda medicine Nike son ta karanta,sanan anjima zan kawo Miki sabon waya ki kira su baba ki fad'a musu dama tafiya kikayi Amma yanzu kin dawo domin ko basu fad'a ba hankalin su a tashe yake"


Tace"toh abbana"

Yayi murmushi

Zama Iman tayi ya fara cin abinci suna gamawa ta ja hanun fareeda zuwa d'akinta

Ta kalleta cikin ido tace"fareeda!fareeda!!fareeda!!! So nawa na Kira ki?"

Fareeda ta dukar da Kai"

Tace"in nine ke zanyi amfani da wanan second chance din in gyra kuskurena ta hanya sa ido a karatu in Zama abin al'fari ga iyayena zanyi amfani da wanan daman in nunawa maza masu hali irin na Yaya cewa ni macece zan iya juya duniya inda na so,Mata ba abin rainawa bane "

Ina son kullum in kika kalli madubi kika kalli kanki sumanki da ya kwashe ya tuna Miki cewa kullum kina da task a rayuwa kina da aiki da zakiyi sanan kina da makiyi da Zaki nunawa bazakiyi give up ba"

Fareeda ta fashe da kuka ta rungumeta

Tace"faree ina son ki zama wayayya mace,wayewa baya hana
Addini,ki cire duk wani tunanin abinda ya faru a baya ki wasar sanan wanan kuka da kikeyi ki daina shi cigaba muke nima kuma shi muke so,Ina son ki daina tunanin baya gaba kawai zakiyi ta tunawa ina son abinda ya faru a baya ya zame Miki tarihi karki Kara waiwayanshi ki kasance ke tunanin gaba kikeyi ki daina tuna farouq ,ki kuma manta da saheeb da ya maiyar dake karaman bazawara only focus just focus"

Cikin kuka tace"ai ba laifin uztazuna bane Kiran shi akayi ak ......"katseta Iman tayi da cewa"har yanzu kina gani uztazun ki bashi da laifi?toh inda Yana sonki kome aka ce kinyi wallahi bazai fasa auren ki ba duk a cikin wanan lamarin nafu ganin laifinshi domin be yarda dake ba kuma ki godewa Allah da baki aureshi ba,Ina son ki sani fareeda komai ya faru da bawa toh Allah na da dalilinsa na haka "

Cikin sanyi jiki tace"haka ne"

Iman tace"yauwa ko kefa"

Tayi murmushi kuma ta d'au alkawarin mantawa da komai Amma saheeb bazata tab'a mantawa dashi ba"


Soyyayen nama taje kicin ta debo a plate ta kawo suna ci suna hira dan sosai fareeda ta saki jikinta

Har daddy ya dawo Mata da sabon waya me sadar gaske tayi murna sosai tana me godiya

Yace"karki damu ki saki jikin ki ki d'auke mu a matsayin iyayen ki"

Tace"toh a take ta Kira number mama dan tana dashi akai

Bugu biyuta d'auka tace'


Maman
Noorul
Hudah
Luv u my fans
Pls share
[1/7, 11:15 AM] Maman Noorul Hudah: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
*_DR SAHEEB*_
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

🌟 GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

Home of gorgeous, interllingent,and expert writers we the best among the rest.

Dedicated to my fans
______________

πŸ…Ώ5⃣1⃣&5⃣2⃣
_____________
Bismillahir Rahmanir Rahim

Mama ne ta d'auka da sallama

Fareeda tayi murmushi tace"lah mama kiyi hakuri ba Kira ku ba"

Cikin farin ciki mama tace"lah fareeda ce"

Fareeda da ta danne hawayenta tace"eh nice Mama"

Mama tace"Kai fareeda baki kyauta ba kin samu cikin tashin hankali"

Da k'yar cikin kokarin karta fashe da kuka tace"nayi kewar ku"

Baba ne ya fisge wayar yace"badai matsala ko fareeda?"

Tace"babu jiya muka dawo inshaallahu zan zo in na huta"

Yace"toh ya mijin naki baki dai Yi fushi da ni bako?"

Tace"eh baba nasan komai kayi kayi shine Dan farin cikina"

Yace"toh nagode sai kin zo"

Tace"toh baba"

Suna Gama magana ta shige d'akinta har zatayi kuka ta tuna da maganganun Iman kawai sai tayi murmushi ta kunna tv ta shige bargo tana kallo

B'angaren Saheeb ko wata d'ayan Nan a daddafe yayi shi domin in ya rufe ido babu abinda yake gani sai lokacin da yake muamula da fareeda duk ya rame yayi baki,kuma shidai yasan ba sonta yake ba toh meke faruwa dashi ne

Kawai sai ya yanke shawaran cigaba da karatunshi ya karo illimi domin ya dagana abinda ke damunshi da rashin aikinyi

Aiko ya samu aka d'aukeshi ya fara makaranta sai dai fa abin girmama yakeyi kullum Yana cikin tunanin ta balle in ya tuna ya saketa sai ya ji ba dadi domin gani yake zata kula wasu

Abin har ya Kai ga ko namiji ya gani sai ya kira da fareeda

Shidai har yanzu be yarda sonta yake ba ya d'au may be sha'awa ce kawai.

Abin takaici ko bacci baya samu da ya rufe ido sai ta zo me
_____________
Bayan wasu kwanaki fareeda ta saki jiki sosai tayi kiba tayi bulbul cikin ikon Allah suman Nan ya fara fitowa yayi kyau

Mummy na Bata kulawa kuma ta samu admission an bata 200level da result dinta na midwifery

Iman ko na kokarin mayar da ita classic lady


Shiko Dr musty ya kasa samun natsuwa tunda suka bar asibitin dan haka yau ya yanke shawaran zuwa gidan tunda yasan ba aure a kanta

Yau dai ta tashi da kewar humaira dan haka wajen mummy taje ta amshi tsohon wayarta ta dawo d'akinta ta kwashi number hummaira ta kirata

Humaira na d'agawa tace"Kai kawas baki da mutunci a ce ko Kira babu"

Humaira cikin jin dadin jin muryarta da ta dade tana son jin tace"lah shegiyar d'ari Ina kika Shiga ne?"

Murmushi fareeda tayi tace"na leka lahira ne na dawo"

Hummaira tace"ban gane ba"

Tace"ki zo please zan turo miki da address kin ji Ina jira"

Humaira tace"ki bani Nan da awa d'aya Ina da lectures '

Tace"ok"

Sauka tayi ta fad'awa mummy zatayi bakuwa

Mummy tace"toh ki shiga kicin ki dafa Mata abinda zata ci"

Tace"ok"

Zuwa tayi ta fara had'a girki"

Kafin minti 40 ta gama domin taliya ta dafa da miya

Komawa tayi d'aki tayi wanka ta saka wani riga da wando da Iman ta siyo musu anko

Tayi masifar kyau gyra guntun sumanta tayi dake kwance tayi sai ya kwanta Kamar sumanda akayiwa Jerry curl sai tayi Kama da irin classic iya muran nan

Kallon madubi tayi ta gan tayi wani kyau sai kawai tayi murmushi tace"bari inyiwa kaina selfie"

Waya ta ciro ta seta camera tayi masifar kyau a hoton a take ta sashi a screen saver

Iman ne ta turo kofa ta ganta tace"wow kin gan inda kikayi kyau kuwa ko Nima zan aske sumana ne dan inyi irin wanan kyau din"

Hararanta tayi tace"sis banson haka fa"

Tace"allah kinyi kyau Bari in Miki selfie"

Tace"ok muyi tare"

Hotuna sukeyi da wayar Iman sai fareeda ta ji sallamar humaira da gudu ta bar d'akin tana dariya

Binta Iman tayi,tana sauka ta rungume ta tace"nayi kewar ki"

Humaira da harga Allah Bata gane fareeda ba ta turata tace"nifa fareeda Nike nima ko ba Nan bane gidan alhaji al-amin ?"

Murmushi fareeda tayi tace"ke banson iskanci ba ganinan ba"

Kallonta humaira tayi da kyau kuma tabbas muryar fareeda ce tace"ke ya haka?"

Fareeda ta ja hanunta tace"muje d'aki

Iman dake gefe tana kallonsu tace"humaira meya kawo ki gidan mu?"

Kallonta humaira tayi sai kawai ta saki ihu tace"lah Iman me kike a Nan"

Tace"gidan mu ne ai"

Fareeda ta kallesu da mamaki tace"Ina kuka San juna?"

Tace"
Department dinmu d'aya kuma ko d'azun muna tare"

Tace"toh muje ciki"

Suna Shiga humaira tace"nifa ban gane ba na gan duk kin canja min kuma meyasa kika rage suman kanki?"

Murmushi fareeda tayi tace"is a long story Bari in d'auko Miki abinci sai in baki labari a lot has happened"

Tace"ok"

Abinci ta kawo duk suka had'a hannun Suka ci a tray

Humaira tace"toh Ina jin ki"

Ajiyar zuciya fareeda ta sauke ta kwashe komai ta fad'a Mata

Babu abinda humaira keyi sai kuka tana tsinewa saheeb

Iman da duk jikinta yayi sanyi Bata jin dadin maganar humaira ba

Fareeda ne ta lura da haka domin koya naka yake naka ne"

Ta kalli humaira tace"


Maman
Noorul
Hudah
Luv u my fans
Pls share
[1/7, 4:28 PM] Maman Noorul Hudah: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
*_DR SAHEEB*_
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul
Hudah

🌟 GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

Home of gorgeous, interllingent,and expert writers we the best among the rest.

Dedicated to my fans
_____________
πŸ…Ώ5⃣3⃣_5⃣4⃣
____________
Bismillahir Rahmanir Rahim

Ta kalli humaira tace"kedai a bar maganar kawai"

Humaira da a sane take dibewa saheeb albarka hararan Iman tayi tace"barni in fad'a karta kashe ni"

Murmushi yake iman tayi tace"ai gaskiya ta fad'a"

Hira suka cigaba dayi fareeda tace"wai har yanzu shiru ke da Umar"

Tsaki humaira tayi tace"tuni Muka rabu cewa yayi beso inyi karatu toh ni ina zan iya shiyasa nace ya nimi wata zamanin nan da tsofofi da sufar su suna niman ilimi balle ni ai karatu tayi da a ce bakiyi karatu ba wanan d'an iskan yayi Miki iskanci Nan da daga Ina zaki fara"

Fareeda tace"kedai kin fiya fad'a"

Tace"na kaiki? ai kin fini shiyasa kika shiga abinda bana naki ba ya janyo Miki matsifa tsohon na nan hankali kwance gashi an raba ki da wanan suman larabawan"tayi kwafa fad'a take sosai babu abinda ke bata haushi sai suman da ya yanke

Tun abin na bawa Iman haushi har ya fara bata dariya kallonta kawai take,in humaira tayi shiru sai ta Kara kallon fareeda tace"wai da gaske ya aske suman?"

Tashi tayi tace"bari in Yi alwala inyi sallah"

Shiga toilet tayi tayi alwala ta fito rike da d'an kwali da tulin ribborn na a cuce maza

Kallon kanta Iman tayi tace"no wonder yanzu na gane dalilin fad'an ki ashe dai babu suman ne kamar na gemu"

Hararan ta tayi ta d'aura d'an kwalita tasa hijab

Itadai fareeda dariya takeyi

Tana idar da sallah ta d'auki Jakarta

6 / 12