CHARBIN KWAE Sirrin Yaudara da Ramuwar Kaddara by Officialraah444

Author :  Officialraah444 Category :  Romance

Chapter   10 / 18

27K to 30K   out of 51.8K words

sae ya xamana shine abincinta safe dare a times har rana ma

"A haka su hajja sukayi sati anan, a ranar da xasu tafi da yake shima xae bisu saboda shirun da AUNTY ta masa duk ya Waga masa hankali tsakanin dan ko A baeji ba daga bakinta akan maganar cikin kuma duk nacinsa bata yarda suyi magana a waya dan haka ya tsara musu tafiya tare, wurin 1pm xasu wuce sun xaune a dinning lokacin daga shi sae ita suna Wan taSa hira"

"''yau su hajja xasu koma fa'' ya faWa hannunsa na cikin nata kamar wata ibada, ta maraeraece fuska tana cewa"

''kaee dan Allah tun yau?''

"''ehh wlh kema kinsan halin uncle Musa koda Abby xae juri nisan hajja banda shi'' bakinta ta Wan taSe xatayi magana wayan KONTO Win ta far ringing, daga kan table da take a ajiye ya Waga yana saka speaker"

"''barka da safiya man'' ya faWa a sake, dagacan shima Mahmud Win a sake ya amsa ya Wora da faWin ''uban Wa ko ´a'' hajja"

''yah uncle Win Wa'' dariya duk sukayi Mahmud Win na cewa

''ina mae kaya tana lfy dae koh?'' baki KONTO ya ri™e yana kallon yanda ta Sata fuska yace ''kaga ni ba ruwana tana jinka wlh''

''aaa'aa wannan dae haWinka ne kawae Malam'' ''haWina a ina? mata tanajin sunan da ka kirata da shi'' ''uncle muna murna'' cewar Hafsah (matar Mahmud)

''yah mum Alim muna godiya'' magana kaWan suka ™ara akayi sallama ganin 12 ta Wan nisa

"''bubbah, bara na shirya'' shiru tayi tanata kallonsa, ganin haka sae yayi murmushi yana jan checks"

Winta yace

''au ashefa ban miki tayi ba koh? xo muje kishiryani'' aekuwa dukata sakar masa a hannun tana hararansa

"Saeda ta rakosu har get tana tsaye cars Win sukayi drove up, ji take kaman kar su tafi cox this is the very first time data xauna da family Winta bata taSa sanin abun haka yake ba no wonder mijinta da yayyenta ke tausayinta sosae, ashe ita abar tausayi ce bata saniba? ashe bata more ™uruciyarta ba? lallae rayuwa tayi wasan kura da ita kam, but she hopes everything has come to an end"

''em Madam did u need anything?'' wani boy ya tambaya ganin tun Waxu da suka wuce take a

jingine ta™i komawa ciki

"''ehh lfy'' daga haka ta juya cikin, gidan wani shiru dashi, tv ta kunna tana Wan dudduba channel Tana xaune tana kallon almost an hour, jin kallon baya mata daWi sae kawae ta shiga ciki ta sako himar saman kayanta ta fito wayarta ri™e a hannunta ta shiga Wakinsa already tana inda yake ajiye keys duddubawa tayi ta Wauki key Win wata CorollaS red ta fito, guards Win duk sunanan dan shi kaWansa ya tafi dama, suna ganinta duk suka tashi"

"''xan fita xanje gidan sister na, so ba sae kun biyoni ba''"

"''no ma, we can't let u go by yourself we have to be with u'' batace komae ba ta buWe motan ta shige da sauri mutum 3 suka shiga wata motan sukabi bayanta dan har an buWe mata ta fice"

"Da yake sunada Wan taxara da gidan Aliyah so sun bi ta highway taga ana saeda rosted corn a gefe Wan lumshe ido tayi tana tsaeda motar suma tsaeda tasu sukayi ta fito daedae yaro Waya ya iso shima, batace ™ala ba ta nuna masa masaran da saurinsa ya buWe mata motan saboda ana Wan rana ta koma shikuma yaje sae gashi da ita har guda biyar, ganinta a back seat sae shi ya shige gaban bayan ya mi™a mata, aekuwa kafin su isa gidan Aliyah tacinye ta farko"

"Aliyahm kaWae ta iske dan yaran basunan Khadeer na gun nanny Aysha kuma na makaranta itama bata jima da dawowa daga aiki ba, gaesawa sukayi tana kallon hannunta dake Wauke da corn biyu ga teeth Winta duk ta Sata har ma da gefen bakinta alamar bata saba ci ba"

Officialraah444

CHARBIN KWAE

(Janka sae mae nutsuwa) Story and writing by Officialraah444

Page 24 Typing.

''xauna mana anty atuu'' Aliyah ta faWa trying so hard not to laugh

"''ina yaran ne naji gidan shiru?'' ta faWa tana cin abunta, ganin haka sae Aliyahn ta mi™e taje fridge"

ta Wauko mata ruwa ta kawo xata buWe mata tace

''indae ma ni xaki buWe wannan can Win banashan farin ruwa bani mineral'' gira Aliyahn ta Wage cikin Wan mamaki tace

''yaushe kika fara shan minerals banda labari?'' ajiye masaran tayi irin abun nema ya samu Winnan

tace

"''toh ae in faWa miki yanxu idan kinaso kiga amae na toh insha ruwa, indae nasha ruwa toh ba xaman lfy dan sae ya haWo hada abubuwan da nace ya maeda''"

''kae dan Allah'' Aliyah ta faWa hada su kama haSa irin mamaki Winnan

''wlh kuwa kinsan yanayin dama jinjirin ciki ance haka yake sae ayita faman laulayi idan Allah ya

"Wora miki, amma ni dae ina fatan wani cikin baxx. '' sae da ta kae nan sannan ma ta lura da yanda Aliyah ta xuba mata ido cike da mamakinta sae ta tuna abunda take cewa da kuma wacce ke gabanta, da sauri ta Wauki corn Winta tana ci gaba da ci, itama Aliyahn sae ta mi™e tana shigewa ciki,"

"A ™a'ida part Winsu ya kamata ya wuce da aka ajiye hajja amma sae yace a kaesa part Win mamy tukun, da sallama ya shiga sae ya tarar falon da ba™i da kaman ya koma tunda basu gansa ba amma da yake mutum ne mae hankali yasan dole xataji ba daWi ace baexo ya gaesheta ba a matsayinta na maman matarsa, ™arin kuma ga ™awayenta yasan xataji daWi when he shows some respect"

"''Assalamu Alaekum'' ya faWa da muryarsa mae daWi, dukansu idanu suka xuba masa tunda duk sun sansa, gaeshesu yayi a mutunce suma suka amsa a hakan, sae ya juya kam mamy daketa danna waya yace"

''barka da gida mamy mun sameku lfy''

"''a' a ni da Hajiyata kacemin kamar yanda ka saba daya fi min, kuma gida lfy lau'' ta faWa tana wani juya kae, Wan murmushi shima yayi yana mi™ewa yace"

''toh mamy bara naje kar AUNTY taga ban shigaba har yanxu tunda tasan tare naxo dasu hajj ''

"''su toh, to ya ita matar taka?'' mamy da taji yace baeje gun AUNTY ba ae batasan sanda ta fara ™o™arin jansa da firaba dan kar ya wuce akan lokaci, amma da yake shima ya iya sae ya murmusa yace"

"''tananan lfy mamy tana kuma gaesheki'' ya ™arashe yana yin gaba, da sauri tace"

"''toh yarinyar taka fa tananan lfy koh?'' juyowa yayi cikin wani sanyayyen murmushi yace ''mamynah, anjima xanxo musha hira inaga anan ma xanci abinci'' daga haka yayi gaba abunsa ''wae hajiya Amina na kasa gane kanki, yanxunnan yaronnan kika gama haWe masa fuska sae kuma naga n sake har kina tambayarsa''"

''me kikeso ki fahimta ´an mata?'' mamy ta faWa tana kallon hajiya maimuna ''yaushe kuka Winke keda sirikin naki mukeso mu sani'' cewar wata Hajiya

''huum bawani abu bane kawae dae kun sanni inada son cusawa ma™iyi haushi shiyasa kukaga na Wan sauko ina tambayarsa niyyata in ri™esa kar ya tafi amma yaronnan da yake shegen wayone dashi kamar tsohon dila kunga ae ya tafin'' dariya duk suka sa suna sakin arerewa wata daga ciki tace

''toh da kike tambayarsa cikin ´arki yanxu kin sauko koh?''

"''kash! ku ae shiyasa baku iya cin moriyar rayuwar duniya ba, in banda abunki ae wannan duk shirine ae, ke ni kaena ban gano gata Alhaji yakeso yamin ba sae da ´ata da kuma aminiyata suka sakani a gaba suka nunamin wlh sannan na fahimta''"

"''toh fahimtar damu muma'' suka faWa suna gyara xama, itama gyarawan tayi tana cewa"

"''toh kun dae ga kaman yanda kuka sani ne kullum burina haihuwar mace, amma Allah bae bani su da yawa ba, a burina in haifi ´a´ana duka as mata in samu wani xaxxafan mae kuWi wanda yakecin gashin kansa in aura masa, shine babban dalilin da yasa na auri Wan kano saboda chan ne asalin arxi™i yake as u can see Abuja kaxo naxo ne,.toh unfortunately mutuwa ta raba amma still"

"ina Wauke da burina a wuyana har akaxo Aliyah ta isa aure, kunga a lokacin Wan minister of finance ne ya nemeta kuma bae dogara da dukiyar ubansa ba nasa yake nema, dama kuma shine irin gidan da nake mata buri amma kashh. ashe mama's boy ne, nikuwa a duniya babu mistake"

"Win da nake ganin xanyi na cutar da yarana kaman aura musu wanda uwarsa ce ke tsara xaman gidansa, banaso ko kaWan uwar miji ta xama gaba a lamuran ´a´ana a barsu suyi rayuwa da maxajensu cikin aminci, shiyasa na™i auren daga baya sae shi wannan Wan former governor Win yaxo nemanta a lokacin shima naso na hana saboda na raena income Win yaron saboda an sagantasa bae iya neman kuWi ba, duka imaninsa naga abunda ubansa ya tara shima naso na hana amma da yake Allah yayi sae suka sama masa babbar offer ya fara babban aiki'' Wan kallon kawayen nata mamy tayi ganin yanda suka maeda ita tv hakan yasata ci gaba"

"''sae akaxo kan babytah wacce samari suka mata chaa kamar xasu Wauketa ba aure, amma bata kulasu bata kuma taSa yarda su haWu, ina cikin binciken wanda ya kamata na bawa dama a cikinsu saboda am so confuse dan dukkansu cin gashin kansu suke, da kansu ne suke neman kuWaWensu ba ™ar™ashin iyayensu suke ba, kwatsam sae ga wannan yaron akayi ta shan fama daga ™arshe dae akaci galaba a kaena, sae me? ciki yaxo ya Sullu hankalina yayi mutu™ar tashi sae da aka xaunar dani aka nunamin wannan cikin shine mabuWin duk wani buri nawa, shine hanyar da xan yiwa Rabi xarce na har abada kuma shine hanyar da xan nunawa Habu nice nan mae ´ar kuma in nuna masa naxo daedae dashi''"

Kae mamy wannan dogon buri haka??

Officialraah444

CHARBIN KWAE

(Janka sae mae nutsuwa) Story and writing by Officialraah444

Page 24 Typing.

Meenal na xaune hannunta ri™e da wani samplena material da aka fitar daga manufacturing

"company da take managing wani ™aramin na'ura ne kaman microscope tana dubawa jikinnan fesa anata ™amshi, Wan tsayawa yayi daga ™ofar yana kallonta duk ta faWa itama da gani shes'nt alright ajiyan xuciya yayi yana yin sallama da ™arfi yanda xataji, aekuwa tajin harda Wan xaburanta dan bataji motsinsa ba"

''hajiya minee mene akeyi?'' wani irin kallonsa ta rin™a yi kaman lokacin ta fara ganinsa cikin Wan rawan murya tace

''ya khaleel welcome''

"''thank u dear, ina AUNTYN?'' ya faWa yana adjusting A.C"

''AUNTY taje Kaduna gun taro'' Wan kallon meenal Win yake da mamaki dan he can't remember AUNTY'S visiting to kd

"''taro na me?'' bakinta ta taSe tana buga hannyenta alaman 'oho' idanunta duka a kansa, jin yayi shiru yana sosa tafin hannunsa yasata cemasa"

''a kawo maka abinci ne?''

''no na ™oshi'' wani shirun suka kuma yi sae chan tace ''yaa khaleel ya matarka ashe an samu ™aruwa?''

"''ehh an samu ™aruwa alhmdlh, kekuma mene yake damunki?''"

''me ka gani?''

''gani nayi kin Wan faWa''

''a'a ni lfy lau nake'' tayi saurin faWa tana tattare kayanta ta wuce sama

"5pm dot ya bar Abuja, da yake yayi waya da boys Winsa yana isa Lagos gidan Aliyah ya sauka, suna xaune a falo ita da yaran adawiyah kuma na Waki, gaesawa sukayi a mutunce as usual"

"''ka shiga ciki yaya, ae tana ciki ta kwanta tana gama Sallah'' ''did she eats?''"

''ehh na mata tuwo kuma taci sosae''

''ko xaki tasota toh sae mu wuce gida dare na ™arayi'' mi™ewa Aliyah tayi tana murmushi ta shige

dan dama tasan baxai taSa shiga Win ba

"Idanunta duk bacci haka ya ri™eta har gun car, da kansa ya sakata ya juyo yanawa Aliyah sallama"

dan khareem bae dawo ba

''toh anty sae da safe koh?'' Aliyahn ta faWa tana le™a adawiyah da ta jima da komawa

''toh yaya khaleel sae da safe'' kansa kwae ya jinjina mata yana shigewa suka tafi

"Šago kanta data kwantar jikin window yayi ya maedasa kan laps Winsa yana matsawa yanda xa'a samu space, ya Wauke ™afafunta daga ™asa ya mayar kan seater ya xare mata kan hijab Win ya gyara mata hulan yana shashafa gashi dake goshinta kwance a haka suka iso gida, yanxu kam da kansa ya Wauki kayansa yayi ciki da ita, sae da ya kwantar da ita bayan ya mata yanda xataji daWi sannan ya fita ya danna bell dake bayan ™ofa daga ciki suka shigo suka kawo mishi luggage's Winsa"

"Washe gari baeje ko ina ba, dan wunin da yayi jiya a Abuja ji yake kaman yayi wata bae ganta ba suna xaune yana fiddo mata da abubuwan da su mamy suka bashi wae ya kawo mata, dariya kawae take tana kallon yanda yaketa bubbuWe mata ledojin, shima murmushin yake yana nunnuna mata abubuwan da kowa ta bada"

"''wae toh ita wannan jakan a ina ka sameta?'' ''Hajiyan Alii ce ta bani, kayan yamin yawa'' ''Allah sarki Ummah, she's so kind''"

"''ehh hakane kam, she's different acikin gidannan'' ya ™arasa faWa yana saka mata kwakumeti a baki"

''yayi daWi kuwa'' ta faWa tana buWe baki ya ™ara bata wani

"''kamar sun san xanje kuwa, au ban faWa miki ba a part Winku nayi lunch'' ya faWa yana bata albishir, sae ta janye kanta cike da mamaki tace"

''a part Winmu kuma?''

''ehh mamy ce taso na tsaya muyi hira sanda naje shine na mata al™awarin komawa cin abinci''

"kanta kawae ta girgixa dan ta harbo jirgin mamyn, sae kuma tayi Wan murmushi tace ''ae ta musamman ce, she knows her hand''"

''yah na yarda dan abincin kam is extendly woow'' dariya ta saka ganin yanda yayi da fuskarsa ''kaci abincin maya dole ka ruWe ae''

''huum kin ma san da naci a xuciyana me nace?'' da sauri ta girgixa masa kanta

''toh cewa nayi shiyasa Abby duk abunda xaije ya dawo baya taSa yarda matarsa ta rabu dashi ashe yasan garan da ake haWa masa yana jaa'' dariya suka saka sosae tana bashi hannu sukayi high five

"A haka rayuwan take Wan tafiya, yau gashi har su hajja sunyi wata da komawa, wanda kuma har a yanxu bae samu magana da AUNTY ba dan ta™i yarda, sosae abun yake cinsa amma yana ™o™arin dannewa baya nunawa kowa he always include his wife first amma hakanan ya kasa faWa mata, tunda kusan itace sila inda bae aureta ba they can not came to this extend, Mahmud kawae ya faWa wanda shine ya basa shawaran ya kuma xuwa Abujan though dae ya koma sau biyu a cikin watan but still ana making masa excuses"

"Duk abunda yake ciki tana sane kuma kallonsa kawae take dan tasha farkawa daga bacci ta iskeshi a xaune gefen bed yayi tagumi wanda ba haka yake ba, baya ™arar da darensa a bacci wannan ta sani amma kuma sallah yake ba tunani ba, daren ranar da xae tafin ma bae yi bacci ba yanata faman tunani itadae da yake harkan gabanta ta isheta tana gama haWa masa bag Winsa ta kwanta, washe gari kuma koda ta tashi har ya wuce, duk da bataji daWi ba amma tanata ™arfafa xuciyarta ko tunaninsa ta™i yarda tayi"

Wato har yanxu dae ajinnan na nan kaman yanda yake

Officialraah444

CHARBIN KWAE

(Janka sae mae nutsuwa) Story and writing by Officialraah444

Page 25 Typing

"Hakanan taji tanason cin alala, Wan taSe baki tayi tana shafa cikinta"

"''nikam yaushe ma nae ganin alala har naci bare naji inaso?'' ta tambaya tana kallon cikinta, sae kuma ta taSe baki tana mi™ewa tayi kitchen Win, da yake tayi zuhr sae kawae tayi xamanta a kitchen Win har ta gama ta xubo ta fito tana hurawa da baki, wayarta daketa vibrate ta kalla 'H' idanunta ta Wan fiddo da mamaki sae kuma ta Waga kiran"

''H mae abun mamaki'' ta faWa tana xama

''anty kin wuni ™lau'' aka faWa daga cikin wayar ''lfy''

"''masha Allah, kina gida ne? munaso xamu xo kawo miki IV Win Naanah ki turamin address'' ''dan Allah? abun yaxo kenan''"

''ehh wallahi xanyi hanging yanxu dan ina driving ne ki turomin yanxu hope kuma kina gida'' ''ehh ina gida sae na ganku'' daga haka ta ajiye wayar

''alalana kar kiyi sanyi dan Allah'' ta faWa tana kaewa baki daedae kiran KONTO ya shigo ™in Wagawa tayisae da ya mata kira na biyu sannan ta Waga ta saka speaker ta

10 / 18