sbd kada farhat din tatashi Bata kusa tana gamawa ta aje jere komai a dining ta nufi dakin farhat din tana waya da Afia data Kira a rude sbd Imran yafada Mata saita kwantarwa afian hankali tana cewa farhat din tasamu sauki inshallah.
Turo dakin tayi tashigo Kai tsaye tana ganin farhat din zaune kan gado ta qaraso da sauri cikin farin ciki idanuwanta na cikowa da hawaye cikeda qaunar farhat din me girma tace"
Finally Sweetie kin tashi""rungumeta tayi tana cewa"
I miss you so very much baby
Kinabani tsoro jiya sosai harbansan tunanin me zanyiba......
Idanuwanta ne suka sauka akan MALEEK dake tsaye gefen gadon daga dayan gefen fuskarsa nakan waya dayake dubawa na Kiran dayayiwa Dr Damien.
Wani irin mummunan firgici da tsoro ne yashigeta tayi Saurin gayara hularta data zame tana tashi daga kan gadon tana gyara wuyan rigarta ta sauke Kai qasa tareda zubewa qasa cikin tsananin girmamawa da sanyin murya tace"
Barka da fitowa.
Bai jita bane kokuwa ya akai itadai dataji shiru ta dago sai taga baya gurin saitaji jikinta yasake yin sanyi sbd wani lokacin mantawa takeda matsayinta na baiwa sai irin hakan ta faru take tunowa da ita din bakowa bace face baiwa 'yar bawa jikar bawa gadon bauta,
Allah ne yahada qauna me qarfi da tsafta tsakaninta dasu afia da farhat Wanda ta dauka hakan tamkar wata rahamace ga rayuwarta shiyasa dorewa da dawamammiyar qauna atsakaninta dasu afia yazama cikin adduarta tacikin sujjadarta.
Kamo hannunta taji farhat tayi ta juyo kanta tareda zama kusada ita tana kawar da tunanin damuwa tasaki fuska cikin kulawa tace"
Yaya kikeji yanxu sweetie?
Kwantawa tayi jikin NURUn tana gyada Mata Kai alamar da sauqi.
Shafa kanta NURU tayi tana cewa"
Baby muje ayi brush nahada Miki pancakes dinki kici ko kadan ne zakiji Dadi Dr ma Kuma Yana zuwa hakama uncle Imran na zuwa haddama AFIA nason Jin muryan princess farhat.
Kallonta kawai farhat din keyi sbd Bata iya ko dariya haka ta dauketa takaita toilet tayi Mata wanka da ruwa me zafi tayi Mata brush suka fito ta shafa Mata Mai da duk abinda yakamata ta shiryata cikin Kaya masu kauri sosai tareda hular sanyi da socks ta hannun da qafa suka fito Palo tana daukeda ita suna fitowa babban Palo Ana budewa Imran kofa Yana shigowa cikin kayan sanyi shima sbd yau gari akwai sanyi sosai tana ganinsa taji wani irin sanyi aranta sbd dama Wanda zaiyi magana da dadynsu farhat din take neman mafita.
Qarasowa yayi Yana karban farhat din ya kalleta lokacinda ta lafe ajikinsa cikin kulawa yace"
Sorry farhat baby.
Kallon NURU datai Dan zuru zuru yayi yaji jikinsa na mutuwa da wata sabuwar qaunarta me qarfi ya sassauta kallonsa Yana Mata kallon kulawa yace"
How are you?
Numfashi ta sauke tana kallonsa tareda tana nufar dining room tace"
Am gud,ya sanyin yau?
Munsaka tasowa da safe haka.
Zama yayi da farhat daidai tana dawowa daukeda tray din tea da pancakes tazo ta zauna kusa dashi tana daukan cup din tafara bawa farhat dake jikinsa zaune tana sake Masa bayanin Yan jikin farhat din yake jiya shikuwa sai binta yake da ido cikin kulawa Yana sauraronta yanaji acikin ransa kaman itada farhat din iyalinsa ne duk da dai Bata Isa haihuwan farhat dinba Amma sai yaji inama ace acikin gidansu suke da ita amatsayin matarsa da hadasu zaiyi su biyun ya ciyar dasu breakfast din.
Ahankali qamshin dataji da safe a hannunta hakama a kayanta kwanaki data rasa Ina tasamu taji Yana doso hancinta Yana shiga cikin sanyi Bata kawo komai akaiba taci gaba da bawa farhat din daidai tana gama Bata Imran yace"
Ok tunda farhat ta qoshi saura lewanta yanzu.
Murmushi ta 'dan sake zatai magana qamshin yashiga hancinta sosai ta waiwayo ahankali idanuwanta ayau cikin babbar rashin sa'a suka sauka cikin NASA daidai shigowarsa palon gabaki daya cikin wasu Armani's dark blue best color dinshi sbd kalar na fidda kalar fatarsa sosai,
Gabaki daya shekarunsa na dattijanka sun boye cikin hutu da izzarsa tareda kamewarsa dake yawo cikin jininsa na sarautar asali,
Babu Wanda zai kallesa Kai tsaye yace shine ya haifi zuqeqiyar budurwa kamar AFIA UBAYD MALEEK ba.
Inda suke bai kalla ba dukkaninsu suka miqe tsaye musamman NURU da tuni tayi ciki daukeda tray Imran yabita da 'dan satar kallo gashi jeans ne ajikinta Wanda yasa MALEEK qara muryan tv kadan tadawo da Imran din hankalinsa.
Dr Damien yazo tareda nurse yaduba farhat Sosai tareda Bata duk wani kulawan likita datake buqata kafin yatafi yabar nurse dazata cigaba da kulawa da ita harta warke tukuna.
Duk yanda yaso sake ganin NURU harya gama yininsa ya tafi Bata Kuma fitowaba saidai suka rage firan a waya sbd maleek na gida Kuma a palon farkon yake zaune yau Wanda yasa kaf gidan tsayawa iyakarsu sbd ba'a wilgewa idan Yananan.
Saida zai tafi NURUn ta rakosa har mota sbd maleek na sama sai lokacin Imran yaji bayason tafiya musamman yanda NURUn duk ta sukurkurce akan ciwon farhat din Amma haka ya tafi yabarta.
Da daddrema haka batareda sun saniba bayan sunyi bacci yashigo dakin wannan karon NURU kayan baccinta masu Dan tsayine Dan wandon kayan yakai gwiwowinta hakama rigar nada hannu Amma duk Rabin Samanta abude Dan haka ko zama baiyiba ya dubasu ya gyara musu lullubinsu yafice daga dakin.
Kwana biyu tana kulawa da farhat Sosai hartaji sauqi ta warware Takoma kiriniyarta sai alokacin hankalin NURU ya kwanta tasamu walwala itama sbd dama ita tafi zamowa kaman farhat din da dabiun yarinta akan afia data dauki girman Dole ta dorawa kanta na zama babba acikinsu.
Imran kuwa sai zuwansa na yanzu ya ninka na da Dan yanzu Sam yafara saka danne feelings dinsa NURU Dan kusan kowa yafara fahimtar hakan gashi karatunta na tafiya daidai shaquwanta da Imran yasa ta dauki burin zama lawyer itama sai hakan yasake bashi kwarin gwiwan soyayyanta.
**AFIA tagamo karatunta na shekara daya Wanda yayi daidai da gama na NURUn itama Dan haka itama saitaje Las Vegas tayi shekara daya kafin suje University Dan Afia tafadawa dad dinta zata jira NURU tagama tadawo kafin suje University tare
Sanin irin shaquwan dake tsakaninsu musamman yanzu daya sanyata jerinsu ma'ana tamkar 'yarshi sai bai musa da hakanba ya amince Mata aka fara yiwa NURUn Shirin tafiya Las Vegas itama musamman gashi Imran yadan shiga damuwa na tafiyan Tata sbd tun ba'ayi nisaba NURU tafara cike dukkanin wasu matakanda cikakkiyar budurwa me daukan hankali zata cike to inaga taje tayi zaman kanta idanuwanta da kanta sun bude sbd rayuwace ta wayewa Dan gidan MALEEK ne dake Vegas din zata zauna itama kaman yanda Afia tayi zama itama.
NURU da farhat sunshiga damuwan kewan juna dazasuyi musamman farhat da komai NURU ke Mata ko dadynta Saida yayi aikin rarrashin kewar NURU da farhat dinsa zatayi.
##MAMUH##
_ZAFAFA BIYAR_💖💖💖
_Alkiblah--SAFIYYAH HUGUMA_
_Makauniyar qaddara--BILLYN ABDULL_
_Dalaal--MISS XOXO_
_Mabudin zuciya--HAFSAT RANO_
_Ubayd Maleek--MAMUH GEE_
_DUKA KUDIN WANNAN DADADAN BOOKS DIN SUNA KAN FARASHIN NERA 700. WATO KUDIN PAGES KENAN. DOCUMENTS IDAN AN KAMMALA SUMA KUDIN SU DABAN.._
ÆŠaya___300
Biyu____400
Uku_____450
HuÉ—u____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
*_08085405215_*
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
 0903 234 5899
[9/8, 4:31 PM] Ummuanwar🥰: *_Mamuhgee 13_*
_Las Vegas_
Sabuwar rayuwarsa NURU Bata taba koda mafarkin samun yiba Koda kwatance itace take gudanarwa a Vegas sbd wani yalwataccen 'yanci da gata datake samu ta bangare biyu wato Imran da Kuma su afia da mahaifinsu Wanda shine ya dauki nauyin komai nata sbd 'yayansa.
Wata irin tsadaddiyar rayuwa takeyi a Vegas acikin lafiyayyan qaramin flat din maleek dake cikin wani babban building na masu Vegas da kanta.
2 bedrooms ne manya sosai agidan kowanne da toilet dinsa shima babba sai Palo 'daya da kitchen sai dining area shikenan,
Komai na gidan farine sai Yan abubuwa qalilan daba farare ba Dan kasancewar gidan Dan kuf kuf yasa bayada wani kadaici ko tsoron zama Kai daya saidai uban zallar dukiya da aka narka gurin gyaran gidan.
Tunda tazo bus takebi Bata taba amfani da motar da aka Bari Dan fitarsuba Dan tuqinta bai wani gama riqewaba Amma dai tsarin tuqin ne anan Bata ra'ayi tafison idan Takoma gida.
A school tunda tafara zuwa Bata samu matsalar karatun da mutanen makarantarba ko daya Dan haka saita maida hankali kawai tana karatun saikuma gyara jiki da harkan fashion da sabuwar qawarta 'yar Morocco take janta suna Dan fadawa ahankali ahankali.
Karatunta yayi nisa tagama gane kan farin Vegas Dan haka saita saje Takoma tamkar wata baturiyar qasar danma banbancin ita haryanxu kusan fiyeda Rabin suturarta sunanan jallabiyane saidai mafi yawanci na Turkish da Kuwait ne tafisonsu sbd mayafansu daurawa takeyi kaman scarf bata yafawa sai jeans da riguna masu har qasa Amma masu tsaga Suma da scarf take sanyasu sai handbags takarmanta Kuma mafi yawansu loafers ne masu tsada saidai Kuma yanxu tana Sanya heels musamman idan tasaka Kuwait gown.
Yau a gajiye tadawo gida tana waya da Afia taqarasa shiga cikin palon tareda rufo qofa ta wuce bedroom dinda yake nasu Dan dayan ko key dinsa Babu a gidan sbd ba'a shigarsa shiyasa ko bakin gurin qofar Bata taba zuwaba.
Ajiye Jakarta tayi tareda waya ta tube tafada toilet tayi wanka da ruwa me zafi Sosai jikinta ya saki ta fito tanajin wata irin yunwa Kuma.
Neutrogena oil kawai tashafa ajikinta sai body mist ta Sanya straight English riga Mara nauyi wadda ta zaune daidai fadin jikinta daga sama har qasa ta Sanya qaramar hula bayan tayi sallolinda bataiba tana gamawa ta miqe tareda zaran wayarta ta fito Palo ta aje wayar kan kujera ta nufi fridge Dan dauko drink da biscuits koshi tafara ci kafin ta Dan dafa ko noodles taci Dan batada qarfi ko kadan tana buqatan qarfin dahuwar noodles din Dan tun safe bataci komaiba.
A kujera tazo ta zauna tareda daukan remote ta kunna tv ta Nemo tashar cwtv Ana wani American series the arrow.
Tana fara ci tagyara zama kenan taji doorbell din yayi ringing ta fara kallon agogo kafin ta kalla qofar ta ajiye cup din hannunta tareda Miqewa ta nufi qofar tana tauna sauran biscuit din dake bakinta ta bude qofar Kai tsaye.
Mr Omar ne a tsaye riqeda wata qaramar brief case da wata luggage qarama
Cikeda mamaki ta saki murmushin farin cikin ganinsa Dan bayan Imran Babu Wanda yataba kawo Mata ziyara daga gida cikin muryarta me Dadi da sakewa tace"
Mr Omar you.......Bata qarasaba qamshin da zuwa yanzu tagama sani da tabbarwa Kona wanene taji ya doshi hancinta Yana shiga take ta hadiye sauran maganar tana kallon bayan Mr Omar.
MALEEK ne sanye cikin Louis Vuitton suits dark blue as usual,
Sai waya dake kunnensa Wanda alamu ya nuna da mahaifiyarsa yake mgn sbd yare dayakeyi Wanda sautin muryarsa daya kusa sumar da ita sbd tsoro da nutsuwar dake cikin muryar tareda wata irin kamewa Dan yaune Rana ta farko datake Jin muryarsa Kai tsaye Yana magana.
Daburcewa tayi tareda tsorata tashiga hankalinta sosai tareda rabewa gefe tana kame jikinta musamman kayan dake jikinta hakama kanta duk rabi a bayyane.
Mr Omar yariga yasan wacece ita ma'ana matsayinta na negestatin MALEEK Dan haka ko gangancin dagowa yayi Mata ko kallo daya baiyiba Dan sanin babban laifin aikata hakan musamman a irin yanayin datake damashi ko acan gida baya iya dagowa ya kalleta sbd sanin laifine hakan su sauran tunda Basu saniba nasu me sauqine.
Kai tsaye MALEEK yashigo har lokacin waya yakeyi Dan haka ko lura da ita baiyiba bare yaji gaisuwarta ya wuce ciki Kai tsaye har lokacin itadai kanta na qasa kirjinta na dokawa da qarfi qarfi
Mr Omar ne yamiqa Mata waya batareda ya kalletaba kansa a qasa Yana cewa"
Jekadi ce akan wayar.
Karba tayi jikinta amatuqar sanyaye ta Dora wayan a kunnenta tareda miqawa jekadi da gaisuwar"
Barka da yau jekadi.
Barkanki da yau Allah yaqara Miki lafiya da kyau da Nisan kwana NURULHUDA.
Tsit tayi tana sauraron jekadin sbd zuwa yanzu kusan tasaba da kirari da irin gaishe gaishen da jekadi ke Mata Wanda ta dauka hakan amatsayin 'dan wani girma daya shafeta na 'yayan MALEEK su AFIA datake taredasu musamman dayake itama da sunan ake Mata amfani a makaranta wanda da farko ko a makaranta aka Kira sunan tsoro kamata yakeyi hartazo tadan saba Amma duk da hakan har yau har gobe idan aka kirata da NURU MALEEK sai gabanta ya Fadi.
MALEEK yazo wani mahimman taron dare da zasuyi da wasu abokanan huldansa masu mahimmanci Dan haka kinsa Babu masu hidimarsa anan kece zakiji da komai musamman yanzu da dakinsa ke buqatan gyara kasancewan yadan Kwana biyu bai ziyarci farin ba Dan haka ki gyara komai atsarin yanda yakeson komai kada kiyi kuskure ki kiyaye.
Bakinta yayi nauyinda bazata iya magana ba saidai Kai kawai ta daga tareda miqawa Mr Omar wayarsa ta juya ya biyota abaya ya ajiye kayan hannunsa ya juya ya fice bayan yace Mata idan MALEEK ya nemesa Yana can qasa a mota ya ciro key card na bude master bedroom din maleek yaja qofar ya fice.
MALEEK na balcony din dayake fes fes tsare dawasu lallausan kujeru guda biyu da table a tsakiya sai glass door din dayake Hana iska shigowa ya damesu kullum acan take karatu itama Dan haka gurin agidan ma kaman yafi samun gyara sbd ko Imran yazo anan suke fira harya tafi nada gidan.
Ganin Yana can ta dauki jakukunanda mr Omar ya ajiye ta nufi dakin da sai yanxu ta fahimci nasa ne ta Dora card din budewa akan qofar dakin ta bude.
Ahankali ta tura zuciyarta da qafafunta tareda hannuwanta Babu Wanda baya rawa sbd daburcen datake.
Girman dakin da makeken royal bed din dake ciki me wata irin transparent labule fari tas data zagaye gadon tayanda bazaka baccinsa ba saidai inuwarsa idan Yana ciki.
Mirror dinsa tamaida ido akai girmansa yasata juyowa gaba daya tana kallon kanta aciki ta yanda take firgice.
Komai na dakin fari ne shima Kuma komai tsaf tsaf yake ba wata qura sbd ba gurin shigowarta kamar dai akwai mutum aciki kullum.
Qamshinsa ne dai wadda tafara haddacewa sbd tsoro shine yake tashi takowane lungu da saqo na dakin.
Cikin sauri da gaggawa tahau aikin daya shigo da ita take ta gyare komai tsaf tareda wanke toilet ta goge ta kunna AC da turaren daki dake fita ahankali sbd Bata budeshi duka ba kadan ta bude ta yanda kamshin zaifi bada nutsuwa sbd kadan kadan yake fita Kuma saiya Jima kafin ya feso kadan din.
Gadonsa ne kawai batayi gangancin ko tabawa ba sbd sanin hukuncin laifin hakan Dan ko yau da a delah ne ko gizah Allah ne kawai yasani idan zataga safiyar gobe sbd mugun babban laifine ganin makwancin asalin jinin DELAH bare MALEEK guda matuqar ba negestatinsu ba ko matayensu Suma sbd sune abokanan kwanciyar tasu Dan haka kallo daya tayiwa gefen gadon Bata kumaba harta gama ta fice dakin zuciyarta na sake shiga rudu.
Tana fitowa palon tahau tattare kayan biscuits da drink dinda takeci tayi kicin dasu tasake tattara palon ta gyara hakama cikin take tahau gyaransa takuma Dora Masa abincin daren dazaici.
Sanin kalolin abincin dayakeci yasata hada Masa gasashen flat bread da boiled veggies aciki sai ruwan lemon tea masu zafi da qamshin lemon leafs da ginger takawo dining ta jera ta bar palon gabaki daya ta shige daki ta rufo Dan batasaka ran zata sake dogon motsiba a gidan har gari ya waye yatafi.
Yakai mintuna talatin Yana wayar dayake Yi kafin ya kammala tareda kashe wayar gabaki daya ya nufi hanyar master bedroom dinsa dinsa yashige Kai tsaye tareda rufowa.
Wayar hannunsa ya ajiye gaban mirror ya nufi closet dinsa ya rage kayan jikinsa duka ya daura brown towel a qugunsa lafiyayyan fatarsa da hutu da kulawa yagama bayyana atareda ita Kamar ta sabon saurayi me sabon jini ajika.
Babban toilet dinsa daya kusa girman dakuna biyu yashige.
Bayan fitowarsa yayi duk abinda zaiyi ya Sanya fararen kayan bacci masu Dan kauri na _roughbay_ da socks din sanyi a qafafuwansa yazuro slippers yafito dining tea din kawai yasha sai rolled flat bread din guda daya yasha ruwa kadan ya koma daki yayi brush ya kwanta tareda Jan duvet cover take qura ta Dan tashi sbd Bata taba komaiba na gadon bare kakkabewa da sauya su bedcovers.
Muguwar shaqa yayiwa kurar wadda zai iya cewa tun Yana yaro rabonsa da shaqar Kura irin hakan sbd mummunan attack din datake basa take yafara tari ahankali ahankali Yana rufe hancinsa da bakinsa ya yaye bargon gaba daya Wanda yasa qurar sake tashi take tarinsa yafara qarfi idanuwansa na fara sauyawa ya sauko da qyar numfashinsa na sauyawa da sassarqewa ya isa gaban mirror ya lalubo wayarsa ya kunna zuwa lokacin yafara samun attack Dan kuwa numfashi yafara dauke Masa Kiran Mr Omar ya Danna daqyar ya iya furta"
My inhaler.....
Yana fadar hakan ya saki wayar Yana durqushewa agurin cikin tsananin azabar toshewar numfashi da wani irin zufan wahala daya jiqasa cikin qanqanin lokaci.
Mr Omar najin muryar MALEEK da abinda yafada yasan attack ne zai samu a rikice yabude inda ake aje inhalers dinsa cikin duka motocin dayake hawa ya ciro jikinsa har wani rawa yakeyi da gudu ya nufo ciki tsabar sauri da rikicewa ko lift kasa tsayawa shiga yayi ta staircase yabiyo Yana hada stairs uku uku gurin hayewa.
Danna doorbell yake ba kakkautawa Wanda yasa NURU dake waya da Imran akewa ba shiri ta fito sbd gudun 'karar ta damu MALEEK.
Kayan bacci ne ajikinta qaramin guntun wando da rigarsa Mara hannu Dan haka saita sanyo doguwar kimono akai ta riqe gaban ta fito da sauri ta bude tana cewa"
Please stop ringing the bell Ina zuwa.
Tana budewa taga mr Omar ciki mamaki take kallonsa kafin tayi mgn ya dunguro Mata inhaler din cikin gaggawa yace"
MALEEK yasamu attack na asthma kiyi sauri ki Kai Masa idan yayi nisa ki shaqa Masa please go