alokacin tasamu damar Dan cin wani abinci Takoma daki ta kwanta Dan hutu take tsananin buqatar yi ayanxun ko kyawun fuskarta ya dawo daidai na rashin hutu da bacci da nutsuwar dabata samuba tun shekaran jiyan sbd fitinar dake gabanta Dan haka zata huta sosai kafin tafara fitowa aganta asan haryanxu tana Nan a LAILAH MALEEK dinta kyakkyawar mace me lokaci.
Ta bangaren jekadi kuwa ganin yadda jikin padima yarikice yasata kebe kanta cikin dakinta ta nemi numbern Mr Omar tayi Masa bayanin dukkanin komai ta Dora cewa lailah na gizah ta iso.
Shiru Mr Omar yayi tareda sauke Dan numfashi sbd baiso katse hutu da Jin dadin maleek ba Dan kuwa hutun gaske maleek din keyi a kwanakin Dan ko ayyukansu tuni suka taru suna Nan Yana Dan kokari Yana rage masu rayuwar sbd maleek din yasamu hutawa dakyau Amma Kuma wannan zancen Dole ya sanar Masa dashi.
Sake sauke numfashi yayi yace"
Zan sanar Masa duk abinda yace zakiji Amma dai kafin Nan inaga ki Dan Bata maganin meriz din kadan tasamu karfin Koda kyakkyawan numfashi ne sbd na tabbatarda maleek bazaiso ta rasa ranta ba dama amfanin riqeta din asan asalin su waye suke aikin Amma dai zan sanar Masa yanxu Inshallah.
Kashe wayar yayi tareda sake fitarda numfashi me zafi Yana tunanin Dole ya isarwada maleek wannan sakon batareda Bata lokaciba duk da ba Haka yasoba
Yaso ubangidansa yasake samun hutu wadatacce Dan kuwa tsawon shekaru Basu samu irin wannan hutawarba sbd kullum cikin aiki da bincike suke matuqar ba ciwoba maleek baya sati biyu a jere zaune baiyi tafiya sai kwanakin Nan dayaga alamar kila har fiyeda watama zasuyi suna hutawa yanxu ga wani aikin.
Ajiyar zuciya ya sauke akaro na biyu kafin ya daga wayarsa ya Nemo numbern MALEEK ya saka Kira Yana nutsuwa tareda daidaita murya
Saidata kusa yankewa kafin maleek din ya daga cikin kamewa yace"
Yes Mr Omar.
Barka da hutawa MALEEK,
Dama saqone daga gizah, jekadi takira jikin yarinyar Nan yakasa daukan meriz tana cikin mawuyacin halinda kowane lokaci zata iya rasa ranta shine jekadi ke neman qarin umarnin taci gaba da aikinta kokuwa ta dakata daga Bata din?
Shiru yayi na wasu seconds daidai fitowar NURU daga wanka fatar jikinta na daukan ido ya zubawa fuskarta fararen idanuwansa batareda ta ankareba yaji tunaninsa na sauyawa akan padiman ya sauke boyayyan numfashi ahankali tareda Miqewa tsaye ya fice daga dakin ya nufi Palo Kai tsaye yace"
Kada ta Bari wani Abu yasameta ta Bata magani sosai
Zamu sauya tsarin bincikenmu batareda yarinyar ba ta jinyaceta ta warke a maidata gida gurin iyayenta
Kada abari iyayen su San abin daya faru da ita sbd kada su 'dagawa 'dayar 'yarsu hankalin.
Angama maleek.
Sai maganar Mahaifiyarsu li'iliti tana gizah ta Isa Kuma ga dukkanin bayaninda jekadi tayi Kamar da umarnin neges ta Isa can sbd bada umarninkaba,badana Anneti ba badana kaleeb ba to tabbas idan badakuba shikadaine yakeda ikon Bata damar zuwa tunda ba sauran ummnnn wannan a tsakakaninku."ya qarasa fada Yana Dan rawar murya fada sbd girmama auren MALEEK din duk da ya rabu.
Shiru maleek yayi Jin abinda mr Omar yace
Ya Dan sake gyara tsayuwa Yana tunanin Dole akwai dalilin neges na bawa Lailah damar zuwa gizah ta zauna itakuma gata idanuwanta sun rufe gabaki daya batada tunanin komai yanxu saita yanda zata farfado da kanta ta jikinsa take ya yanke shawaran zuwa gizah ya bude Baki cikin nutsuwar murya yace"
Kayi Mana Shirin komai gizah din zamuje wannan karon Ina buqatan tunatarda wasu waye maleek Incase idan sun samu mantuwa.
Yes maleek"Mr Omar yafada Yana kashe wayar maleek din take yakira ya sanarda tafiyar maleek aka garzaya karban tickets da komai.
Yaso barinta anan gidan yaje yadawo tukuna Amma Kuma bazai iyaba sbd duk tsoron dazai Bata hankalinsa zaifi kwanciya idan tana cikin mutane shiyasa ya maidata can gida zibrian gaba daya kafin suka wuce.
A gizah kuwa sosai yakoob yagano akwai abinda jekadi ke boyewa musamman Dama sunsan Dole itakadaice tasan inda padima take sbd itace wadda tashigo gizah din da ita Dan Haka ya kasa ya tsare cikin taku sosai harya gano inda take zuwa acan bayan sassan maleek duk da Bai Isa cikin sassanba ya isa kofar yasan akwai babban abinda maleek yasakata take boye gurin dangane da padima Dan Haka yakoma yafadawa neges komai
Cikin wani irin yanayi neges ya murmusa Yana jinjina Kai yace"
Ayi aike gurin tsohuwar matar maleek lailah cewa nabata damar zuwa muyi mgn.
Allah yaqara ma girma da lafiya."yakoob din yafada Yana yin baya baya ya juya ya fice.
Ta bangaren lailah kuwa yau ta samu damar Isa gurin hutawar neges Dan maganar aurenta da maleek data kawota har cikin palon akai Mata iso ta qaraso gabansa ta gaidashi cikin girmamawa kafin ta zauna cikin tata isar ta zamtowarta Matar asalin me mulkin
Take aka fara shigo da kayan marmari dasu Zuma da kayayyakin tabawa aka cike gurin tsab ta dago ta kalli kayan tareda dauke Kai sbd hakan tamkar cin fuskane ga maleek ace macen dake matsayin matarsa tana zaune gaban wani Wanda ba maleek ba har akawo Mata abinsha Dana ci Ana nufin taci gabansa wannan rashin darajar yayi yawa tana matsayin Matar maleek guda.
Numfashi ta sauke tareda waiwayowa ta kallesa Kai tsaye cikin tausasa harshe tace"
Allah ya taimaki neges me gizah ta yanxu ina maka barka da hutawa tareda barka da ganin wannan lokacin.
Kallonta yayi daka zaman hakimcen dayake ya Dan saki fuska wani murmushin dattijantaka na sauka kan fuskarsa yace"
Neges ya amsa Kuma Yana biki barka da fitowa medakin maleek na gizah.
Lailah tunda tashigo cikin zuriarsu take tsaye a wuyansa sbd mace ce me tsananin son mulki da Isa tareda kwadayin komai yazama Yana qarqashinta da ikonta Dan kuwa Jin take kamarma itace maleek din sbd sosai ikonta da gadararta ke bayyanarda mijintane me kujerar sosai take shigar Masa hanci Yana dannewa sbd taku da zamanta sirikarsa amma zai Bata darasi daidai da ajinta sbd ita takawo kanta gurinsa yanzu neman mafitar matsalarta da maleek.
Cikin nutsuwa da kulawa ya Dan juyo da Kai a kame yace"
Abu dayane akan matsalar aurenku da maleek shine karkata da hankalinsa yayi ta wani bangaren
Ma'ana wani Abu daya rinjayi tunaninsa akan iyalinsa.
Dagowa tayi cikin mamaki tace"
Akwai abinda ya rinjayesa kuwa bayan wannan auren da yayine...
Wani murmushin yakuma saki Yana cewa"
Mace bazata juyarda maleek ba ko wacece kuwa nafi sakaran wani Abu daban Wanda Banda sani akai Amma Dole saikin Saka ido kin bincika kin gano kafin asan inda gyaran zai faro.
Shiru tayi tana nazarin zancensa sbd Bai wani shigetaba zancen Dan kuwa duk me lafiya ya kalli al'amarin dakyau zai fahimci cewan Babu wani dalilin sauyawar maleek zallar halinsane rashin daukan reni ko kadan sai aure daya qara take hasaso wani abun daban Amma tunda yafadi hakan zata bincika tagani Dan a shirye take da maganin dukkanin abinda zai shata Mata layi da zamowa Matar maleek.
Batareda ya kalleta ba yasake Dora Mata tunanin bibiyar daddaqin abinda maleek ke tunani ta hanyar bibiyar jekadi sbd itace mafi amintar maleek a duk gizah da rayuwarsu bayan kaleeb da Mr Omar ko mahaifiyarsa Anneti batasan sirrinsaba sai wainnan mutanen uku.
Da wannan tunanin sosai lailah tasakawa jekadi ayar tambaya Dama tajima da sanin jekadi maqiyiyarta ce ba kauna atsakaninsu munafukartace kodan yanda tasamu cikakken bayanin jekadi itace tsaye akan komai na NURU a rayuwar maleek Dan Haka ta kanta zata fara saita rusa yardar dake tsakaninsu da maleek bayan tasan menene matsalar tukuna.
Bayan tabaro can sassan Anneti ta nufa akaiwa Anneti shelar isowarta tashigo cikin shigar alfarmarta kamar koyaushe ta zauna ta gaida Annetin Kamar dai yanda suka Saba cikin yanayi na Ni Matar neges nikuma Matar MALEEK Babu wata qarin Hira akai sbd Lailah har cikin ranta duk tsanarsu da qiyayyarsu takeji sbd sune munafukanta dasuka tsayawa NURU akan auren MALEEK Dan Haka Bata wani tsayaba ta wuce tabar Anneti da bin bayanta da kallon mamakinda baigama sakintaba saidai bazatani takan zancen lailah ba zata jira maleek yazo tana buqatan bayanin dawowan lailan.
##MAMUH#
[10/2, 7:32 PM] Sadeeya: *_Mamuhgee 41_*
Are you guys looking for where to buy ur skincare product @ mg's skincare is the best plug for you🤗
Do you wish to have that flawless skin that's free of all skin prblm
Do you wnt to achieve that milky skin that turn heads wherever you go😉
Try mg's product nd I assure you you'll never use any other product except mg's product✅
Mg's will gv you the best out of all
With mg's product ur skin is 💯 clear,fresh,smooth nd ur skin will absolutely glow all day💃
We have herbal whitening black soap now nd beauty set available
Nd both the soap nd the beauty set is for all skin type everyone can use it🤗
Just gv it a try now nd see wonders✅
Chat:08062991549
Call:08064532391
Soap price:3k
set:11k
Follow us on
Instagram@glow_with_mgs
Facebook:mg's skincare
Nd guess wht🦻
Duk Wanda zesiya Kaya daga yau Alhamis 30-9-21 zuwa Nanda 5days that is ranar talata there will be 20% off discount a soap nd the set😍so what are you guys waiting for hurry nd grab urs💃 now is the time to glow🧖♀️
Pamper ur skin🦵
Shine like a bride 👰
be part of the glow team karkubari abaku lbr
Just chat 08062991549 to plc ur orders😘
Do not forget to follow us👆
Like nd comment pls dearies😘
Patronize us🙏
mg's always serve you the best✅❤️
*****************
Tun dasukai magana da neges tasakawa jekadi ido sosai akan motsinta takai har bibiyarta tafarayi Amma sbd jekadin ta iya takunta fiyeda tunani lailan Bata taba samun damar sanin komai dangane da wani baqin yanayi ko sirri atareda jekadin ba harta fara sarewa daga bin daddaqin na jekadi sbd Sam ba dabiarta bace Dan ita ta dauki kanta tanada abinyi hakama ba girmanta bane tsayawa irin wainnan labe laben ga abun duniya yafara sakota gaba sbd yanzu rayuwarta ta wayi gari kowa baya tareda ita tun daga kan mijinta har yayanta su danginta ba'a magana sbd ta Jima da watsar dasu dama mahaifiyarta ta Dade da rasuwa mahaifintane kawai shima tsufa yacisa sosai har baya gane kowa sai anfada Masa wannan waye shiyasa batada lokacin kowa saina Gina rayuwarta sbd gidansu kaf kowa yazamo wani hamshaqan kansu duk da ita kadaice mace sai tana alaqanta kanta da matsayinsu suda suke maza bazata taba yadda itama ta zauna tana amfani da alfarmar wani ko sunansa so take ta Gina kanta da kanta ta yanda za'a fadeta da matsayin datake dashi badai da matsayin wani datake a qarqashinsaba shiyasa ta rufe ido ta watsar da 'yayanta da komai Amma yau ta wayi gari ko 'yan aiki batadasu sai guda biyu kacal da ganinsuma baqin ciki yake sanyata sbd Kamar Saida aka zabo wainda suka fi Muni da rashin kakkamtuwa aka Aiko matasu batada 'da, batada miji, batada gidan kanta bare matsayin kanta ko sunan Wanda zatace a qarqashin alfarmarsa take batada Dan Haka gabaki daya yanzu Jin take kamar ta rasa nustuwa da tunaninta Bata iya tunanin komai kanta ya toshe zuciyarta bayan kwashe kwashen tunane tunanen duniya dasuka kusa haukatata Babu abinda takeyi tarasa wazata zauna dashi ko masifa tayi ta rage abinda takeji bare.
Tunanin 'yarta afia ne yafado Mata Rai take taji idanuwanta na neman cikowa da hawaye ta hadiye tana miqewa zuwa bakin window ko zataji sanyi sanyi Amma takasa Saida hawayen suka tsinke Mata ta zauna bakin windon tana fashewa da wani irin kuka Mara sauti tana buqatan mutum atareda ita Wanda zai dubeta ya saurari damuwarta.
Afia take tsananin buqata ayau din sbd ta Dan duk duniya yanzu 'yartace kawai me iya rarrashinta ta rungumeta ta saurari duk haukar dazata iya fada da wadda zata iyayima kaf duniya yanzu 'yartace kawai me iya Mata wannan bayan ita ko maleek tasan bazai taba kallonta da idon sauki Kona mutunciba
Dan Haka hankalinta yaqara tashi tana jinta cikin mummunan yanayi na baqin cikin rayuwarta da Kamar tayi hasara.
Ta Jima Yana boyayyan kukan daya Gama kumbura idanuwanta da fuskar datake masifar ji da ita sunyi jajir sunyi suntum duk da hakan bataji wani sauki ko sassaucin komaiba ta miqe ta nufi toilet jiki amace ba kwari ta wanko fuskarta tareda yowar alwala Dan ko wankan batada karfin Yi tafito ta goge fuskarta ta tayarda sallar ishai da akai tun dazu bayan tagama akaro na farko bayan tsawon lokaci yau ta daga hannu tana rokon Allah sassauci da mafita sbd ada ganin tagama samun komai na rayuwa yasa sallah data zama Dole kawai takeyi Amma adhkar da sauran adduoi gurin ubangiji basa gabanta sbd duk abinda takeso tagama samu.
Agurin take zaune tana tsiyayar hawaye ta gefen fuskarta batareda ta iya tashiba takai hannu ahankali ta dauki wayarta ta Nemo sunan afia akaro na farko bayan tsawon lokaci taji qaunar 'yayanta na dawo Mata sbd haryanzu tasan kome zata zama arayuwa 'yayantane kawai bazasu taba iya guduntaba musamman afia datake kaunarta fiyeda komai saidai takasa duba kaunar da yarinyar ke Mata sai yanzu take ganewa Dan kuwa a yanda takeji yanzu ko 'yayanta abata ta zauna dasu zataji saukin duhu da kuncin da zuciyarta ke ciki.
Numbern afia takira tayita ringing No answer harso biyar take jikinta yasakeyin sanyi hannuwanta sukai sanyi ta juyar da kanta ahankali tana kallon qasa kafin ta daga wayar ahankali ta shiga gurin saqo ta rubuta mata" _Kiyi hakuri afia_
Tura Mata tayi tareda ajiye wayar tana rufe idanuwanta zuciyarta na wani irin nauyi da kunci.
Jekadi jin tsarin na barin padima tareda tattalata tasamu lafiya amaida gida yasata sauya nata tsarin itama nabin umarninsa tafara bawa padima magani tareda kulawa da goge Mata fatarta data Gama konewa tana shafa Mata magani akai akai Wanda take padiman tafara dawowa hayyacinta Dan hartana Dan iya bude Baki Kuma tana iya zaunawa sai hakan yasaka jekadi sake bada himma sosai cikin kwana biyu padima tafara dawowa mutum sosai a ranar da padiman tafara iya bude Baki sbd tsananin farin ciki jekadi ta fita ta kebe tasake Kiran Mr Omar ta sanar dashi komai alokacin suna hanyar tahowa gizah suna cikin jirgi Amma Basu riga sun tashiba Dan Haka baida damar ganin maleek sbd Yana first class Dan haka yabari harsu Isa tukuna.
Dayake da daddare ne sosai jekadi ta fito tayi wayar adaidai lokacin lailah Tana zaune taji motsi me girma ta window din dakinta Kuma Kamar harma da mutum tagan gilmawarsa saita tashi zaune dakyau tana kallon windon zuciyarta na Dan harbawa Amma takasa riqewa ta miqe tsaye ta nufi windon tana Dan daga manyan dogayen labulayen windon saitaga kaman sake gilmawar mutum Kuma idan idonta ya gani kamar da kyau jekadi tagani.
Kallon hanyar tayi tana dawowa cikin dakinta zuciyarta na gargadarta da bin jekadin saidai Kuma wata zuciyar tana ingizata ga zuwan ta rintse ido tana komawa ta zauna saidai Kuma takasa nutsuwa tanason bin jekadin
Ta miqe da sauri tareda daukan wayarta ta fito sanyeda slippers tabi hanyar baya ta fice daga sassanta tabi inda jekadin tabi tana tafe tana waige waige har tayi Dan nisa saitakasa gane inda jekadin tabi tafara waigawa koina tana dubawa saikuma tsoro yashigeta ta juya da sauri zata juya saiga jekadi ta fito ta wata hanya tabi hanyar Nayan sassan maleek tana tafiya cikin nutsuwa sbd kada tabar qarar sawu.
Da fargaba da mamaki me tsanani take kallon jekadin tareda rintse idanu tabude mamakinta na neman komawa tsoro sbd kayan dake jikin jekadin bashine kayan data ganiba ajikin jekadin data wurga ta windontaba Kuma tabbas Bata Isa ace yanzu yanxu ta sauya kayanba.
Kodai idanuwanta ne ke Mata gizo kokuma wanine ya wurga ta windon ba jekadiba?
To idan wanine waye?
Meyasa yayi irin shigar jekadin?
Girgiza Kai tayi da sauri cikin tsananin tsoro dason tabbatarwa tabi bayan jekadin cikin sanda tana Nemo camerar wayarta tareda kashe hasken flashlight sbd idan ba tabbarwa tayi da wacece jekadin acikinsu hauka zata iya kamata Dan haka a sidade sidade tabi bayan jekadin tana waiwaye cikin tsananin tashin hankali sbd Jin kamar Kuma Ana binta itama san'da san'da abayanta.
Wata boyayyar kofar dataga jekadi ta fita yasata zare idanuwa cikin mamaki da tabbatarda zancen neges kenan dai da akwai wani Abu da maleek ke boyewa¿Aikuwa yau saitaga ko menene to Amma Kuma ta Yaya tunda jekadi rufe gurin zatayi..
Tunani tafara ta yanda zata samu Isa cikin dakin Kota halin qaqa taga abinda kila zai dawo da aurenta da maleek Dan Haka bazata Bari wannan damar ta wucetaba.
Waige waige tahau Yi cikin sauri Idonta ya fada kan wani qaton katako Wanda batama tsaya mamakin ganinsa a guri irin wannan ba ta dauka da sauri ta lallaba taqarasa bayan jekadi dake kokarin rufe kofar da mukullin ta waje bata tsaya wata wataba ta daga katakon ta buga Mata akai bada karfi ba sbd Jin bazata iya da qarfinba sbd kadata illatata sai kawai ta tureta gefe ta Fadi ta qarasa dakin da gudu ta tura kofar ta fada ciki tana dubawa.
Faduwar da jekadi tayi ganin lailan ta nufi cikin da gudu yasata miqewa da sauri tana Kiran sunanta saidai kafin tayi wani yunkuri wani mummunan duka ya sauka akanta me tsananin azaba take ta sulale agurin ta zube a some jini na fita ta goshinta batareda taga Wanda yayi Mata dukan ba.
Lailah kuwa ganin mace a kwance cikin dakin cikin wani yanayi na Kamar majinyaci yasata takowa ahankali zuciyarta na harbawa cikin tsananin mamaki da tsoro ta iso har gabanta zata Kai hannu ta tabata padiman ta bude idanuwa ahankali baccin daya fara daukanta na sakinta ta zubawa lailah idanuwanta ahankali tana kallonta da mamaki Jin motsi abakin kofar shigowan yasa padima kallon bayan lailah mamakin ganinsa nasata kaikata Kai tana kallonsa dakyau ahankali ta bude Baki tace"
AMED????
Da sauri lailah ta juya zata waiwaya wani mugun duka ya sauka a tsakiyar kanta batareda ta waiwayo ba ta