Ubayd Maleek 1 Complete Hausa Novel

Author :  Mamuhgee Category :  Love

Chapter   10 / 37

27K to 30K   out of 110.1K words

go go fast.

Karba tayi ta juya arude sbd ita duk Mr Omar dinne ya rudata ta yanda yake maganar dukkanin jikinsa na wani irin rawa ga tsoron shiga dakin na MALEEK Yana ciki Amma haka ta Isa arikice ta bude tashige qofar na rufewa shima Mr Omar Jan qofar yayi yakoma gefen qofar shiga palon ya dasa sabon zama.

Tana shiga yana qoqarin zubewa kwance batasan lokacinda ta qarasa da sauri ba cikin tsoro da rudewa ta tarosa dayake batada kauri sosai da qarfinda zata iya taresa musamman da jikinsa yariga yasaki sai takasa suka zube kan gadonsa gabaki daya.

##MAMUH#

_ZAFAFA BIYAR_💖💖💖

_Alkiblah--SAFIYYAH HUGUMA_

_Makauniyar qaddara--BILLYN ABDULL_

_Dalaal--MISS XOXO_

_Mabudin zuciya--HAFSAT RANO_

_Ubayd Maleek--MAMUH GEE_

_DUKA KUDIN WANNAN DADADAN BOOKS DIN SUNA KAN FARASHIN NERA 700. WATO KUDIN PAGES KENAN. DOCUMENTS IDAN AN KAMMALA SUMA KUDIN SU DABAN.._

Ɗaya___300

Biyu____400

Uku_____450

Huɗu____500

Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*_08085405215_*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  0903 234 5899

[9/8, 4:31 PM] Ummuanwar🥰: *_Mamuhgee 14_*

Kokuwar tashi takeyi daga kan gadon dukkanin jikinta rawa yake sosai sbd tsananin tsoro da tashin hankali tareda ma firgici duk ta gama rudewa Amma sbd jikinsa yasaki gabaki daya ko kadan takasa motsashi daga jikinta sai numfashinsa dake qoqarin barin qirjinsa da sauri ta lalubo inhaler din dake hannunta ta dago kansa daga qirjinta dake harbawa ta Dora cikin bakinsa ta Danna harso biyu zuwa uku taga kaman Yana responding saita sake daddannawa tana shafa bayansa ahankali kaman yanda takewa farhat tana dan hura Masa iskan bakinta a fuska har lokacin jikinta rawa yake sosai sbd fadar tsoron datake ciki baya misaltuwa ganinta kwance kan gadon da za'a iya raba gangar jikinta da kanta akan laifin hakan.

Wata irin rawa jikinsa ya dauka kamar Yana fizga sosai Sosai take hankalinta yayi mummunan tashi ta turesa gefe daqyar daga kanta ta tashi zaune tana gyara Masa kwanciya hannuwanta na rawa ta fara Kiran sunansa da DADDY cikin masifaffen tashin hankali ganin Yana jijjiga da qarfi.

Da gudu ta sauko gadon tana wurgi da kimonon jikinta ta fita da mugun gudu ta dauko wayarta hannunta na rawa daqyar ta iya riqe wayar ta Nemo sunan Dr Damien ta Danna Masa Kira tana dawowa dakin da gudu cikin firgici take koro Masa bayani muryanta na rawa tuni zufa yayi Mata sharkaf.

Cikin son Samar Mata nutsuwa Dan ta fahimci bayaninsa yace"

Ki kwantar da hankalinki please ki fahimci abinda zanfada miki.

Jijjiga Kai tayi tana saurarensa cikin qaguwa tana sake hada zufan tashin hankali ko qarasa sauran bayanin baigama yiba tayi cilli da wayar ta nufi gaban madubi tafara dudduba allaurar da Dr Damien din yace

Bata ganiba tahau bubbude drowers cikin tashin hankali take na rashin ganin allaurar

Tayo gurin luggage dinsa ta bude tahau yamutsawa cikin sauri da tashin hankali cikin sa'a kuwa ta ganta da sauri tayo kansa tana zuwa kaman yanda Dr yace tayi ta Zuqa Masa allurar take yasaki wani wahalalle numfashi dukkanin jikinsa na sakewa numfashinsa ya tsaya cak ya daina motsi.

Dauke wuta tayi itama ganin baya numfashi baya motsi a kidime ta haura gadon ta taba kirjinsa taji baya bugawa ta Dora kunnenta kan kirjin nanma taji tsit a haukace ta daga qafafunsa ta Dora kan cinyarta ta zare Masa safunan qafan tasaka tafin hannunta tana gogawa da qarfi tanayi tana kallonsa adduo a bakinta har batasan wainda takeyiba

Ahankali ahankali taga numfashinsa yafara dawowa ahankali

Wata irin wahalalliyar ajiyar Zuciya tasake sai alokacin hawaye suka gangaro Mata har batasan lokacinda ta qanqame qafafuwansa dake kan cinyartaba tana sake kukan tsananin tsoro da ace wani abu yasamesa Yaya zatayi?

Me za'ace?

Me 'yayansa zasuce?

Ta Jima ahaka tana kukan kubuta daga muguwar masifar data tashi afkowa zuriarta gabaki daya kafin ta Dan dago ta kallesa da jajayen idanuwanta taga yanzu Kam numfashinsa yagama daidaituwa Amma bai tashiba sai hakan yasakata Jin shakka ta gyarawa dogayen qafafuwansa zama akan cinyoyinta dake filin Allah,

Jikinta daya gama daukan dumin tashin hankali yafara shiga qafafunsa gakuma tafin qafafunsa datake gogawa da tafin hannunta 'Dan dumi yaringa shigar qafafunsa yasashi motsawa ahankali a wahalce batareda ya bude idanuwansa ba

Itakuma taci gaba da gogawa Wanda Dole yasashi bude idanuwansa dasukai ja a wahalce ya kalleta daqyar ya maida idonuwan ya rufe Yana sauke wani numfashin me fitarda siririn sauti.

Bata ankara daya Dan farfado ba taci gaba da goga Masa tafin qafafun

Ya sake bude idanuwansa a wahalce yanason cewa ta daina ya kasa sbd hakan datake Yana Masa wani iri temperature dinsa tana hayewa sama Amma yakasa mgn sai kawai ya maida idonuwan ya rufe bacci ya daukesa me qarfi a wahalce.

Qarfe bakwai na safe yabude idanuwansa ahankali Yana furta sunayen Allah da adduar tashi bacci cikin zuciyarsa,

Motsawa yayi ahankali tareda yunqurawa zai tashi zaune yaji qafafuwansa a riqe ya Kai idanuwansa zuwa gabansa yaganta kwance rungume da qafafuwansa baccin wahala ya dauketa.

Kallo daya yayi Mata ya dauke idanuwansa daga gurin Yana zame qafafuwansa ya zuro qasa tareda yaye labulen makeken gadon ya fito Yana tafiya ahankali duk da garau yake Jin kansa ba damuwar ciwo ko daya Amma akwai rashin qarfin jiki ya nufi toilet yashige.

Harya fito tana baccin Bata farkaba Dan haka Kai tsaye ya shirya cikin Ash Armani's ya fesa turarensa na imperial majesty rosalle ya saka takalmin _manolo blahnik_ ya fice Kai tsaye Yana kunna wayarsa ya Kira mr Omar daya kwana zaune zaman jiran yazata Kaya yana ganin Kiran maleek yayi wuf ya dauki Kiran a qage yace"

Good morning MALEEK.

Ka kunna mota ganinan fitowa.

Da gudu mr Omar ya sauko ya nufi mota yashiga ya kunna da sauri tareda gyara parking yayi saiti daidai kofarda maleek din zai fito

MALEEK din nafitowa ya bude Masa yashiga ya rufe ya zagaya da sauri yashiga suka wuce.

Qarfe Tara da mintuna ta bude idanuwanta dasukai mugun nauyi sbd kukan datasha dakuma bacci

Tafara jujjuya idanuwan taga inda take a zabure ta miqe jikinta na rawa ta wuntsulo qasa tana kallon gadon taga bayanan da sauri ta fito cikin gadon har tana tuntube ta fice ko ganin gabanta batayi Takoma dakinta jikinta na rawa.

Daqyar ta nutsar da kanta Dan yin sallah tayo alwala tazo tayi sallah zuciyarta na harbawa da qarfi

Kallo daya zakai Mata kasan a firgice take takasa samun nutsuwa tana zaune a daki tana tunane tunane har kusan 12 tayi Dole ta fito Takoma dakin ta dauko wayarta sai alokacin taga misscals din Imran da text din Mr Omar na cewan sun wuce komawa Paris MALEEK zaiga likita.

Ajiyar zuciya ta sauke duk da bawai tasamu nutsuwa bane dajin hakan sbd ita yanzu qaddarorinta yawane dasu yanzu dame zata Kira qaddarar datakaita hawa gadon MALEEK na DELAH Giza Wanda ko 'yayan sarauta bila adadin ba kowane yaga ko gurin zaman Shan iskansaba gata tsautsayi da qaddara yasata ganin makwancinsa dako 'yayan cikinsa Basu taba ganiba Dan daga afia har Farhat Babu Wanda yataba shiga bedroom dinsa nako Ina Bare suka shimfidar kwanciyarsa.

Kiran Imran ne ya katse damuwarta da tunaninta sbd rashin daukan wayanta tun jiyan yasashi shiga damuwa Dole ta Dan sake suka hau magana sama sama qarshe dai Dole hakura yayi da wayar akan tayi bacci ta huta zai kirata zuwa anjima danma Bata fada Masa abinda yafaru ba bakuma tajin zata taba iya fadawa kowa har abada.

Wanka tayi sai alokacin yunwar dake cikinta tun ta jiyan ta taso Mata ta nufa kicin ta dumama sauran abincin dabaiciba jiyan taci Tasha orange juice Takoma daki sai alokacin takira Afia suka hau fira itama sama sama harsaida afian tagane tace"

NURU are you sure you're okay???

Numfashi ta sauke kafin tace"

Eh kawai ciwon Kai ne ke 'dan damuna shima sbd I didn't sleep well last night ne.

Ok tom kiyi bacci yanzu Koda na 1 hour ne you'll feel good inshallah.

Aje wayar sukai ta kwanta Dan tasamu tayi baccin Amma Sam takasa har lokacin zuciyarta Bata cikin Dadi qarshe jekadi ta Kira taji lafiyan iyayenta tukuna ma tasamu ta 'dan rintsa baccin ya dauketa.

Bata farka ba sai yamma tana tashi wanka tayi tayi sallolinta ta Sanya riga da guntun wandon jeans baqi ta fito ta dafa kwai da farar noodles taci Tasha ruwa ta dauko ledar crunchy chips chops tazo ta zauna kallo tana ci saiga Kiran Afia ta dauka Nan suka hau waya yanzu cikin sakewa Dan baccin ya taimaketa sosai.

Karatunta yadau zafi sbd tafara exams din kammalawa shiyasa yanzu batada wani lokaci sosai karatu ne a kanta ko lokacin fira ta waya batadashi Dan wani lokacin wayar a kashe take yini saitazo kwanciya ta kunna da afia kawai take waya kafin takuma maidawa ta kashe ahaka ta gama exams dinta kwana uku ta qara akai ta tattaro tadawo gida ranar murna da farin cikin farhat Bata misaltuwa hakama afia datai tsananin kewan NURUn kusan daima kowa yayi kewarta shiyasa ranar gidan kaf acikin walwala suke Dan Jin suke kamar rayuwar gidan tadawo sbd AFIA ko yaushe tana library gurin karatun batada lokacin kowa na gidan

Farhat ma haka take turata daki tace taje tayi karatu itakuma NURU tana shiga cikinsu tayi aiki harma tayi Wasa da dariya dasu uwa uba idan ta biyewa farhat gurin wasan yara na guje guje ko qasa a playground na gidan Wanda ka zuba komai na wasan yara domin farhat Wanda ita kanta farhat yanzu take morewa playground din data samu abokiyar dake tayata shiriritarta shiyasa yanzu batada kaman NURUnta.

Hutun sati biyu kawai NURU tayi Mr Omar ya kammala komai na karatunsu dazasu fara yanzu na cikan burirrikansu,

NURU lawyer itakuma AFIA likitanci.

##MAMUH#

_ZAFAFA BIYAR_💖💖💖

_Alkiblah--SAFIYYAH HUGUMA_

_Makauniyar qaddara--BILLYN ABDULL_

_Dalaal--MISS XOXO_

_Mabudin zuciya--HAFSAT

RANO_

_Ubayd Maleek--MAMUH GEE_

_DUKA KUDIN WANNAN DADADAN BOOKS DIN SUNA KAN FARASHIN NERA 700. WATO KUDIN PAGES KENAN. DOCUMENTS IDAN AN KAMMALA SUMA KUDIN SU DABAN.._

Ɗaya___300

Biyu____400

Uku_____450

Huɗu____500

Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*_08085405215_*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  0903 234 5899*_Mamuhgee 15_*

*Mg's skincare*

Hi my people🙋‍♀️

Ina gaisuwa

Toh albishirinku😬ku karkade kunnuwanku kuji inamai sanarmaku cewa set dinmu ayanzu yazama available maiso yarugo aguje karya tsaya Sanya ayi babushi☺️kundaisan kayan *mg's* dabanne  ba karya indai tafannin gyaran jikine kunsan yanda sabulun mg's herbal whitening black soap kemaida fata tazama Babu kuraje, pimples, acne,eczema, stretch mark, knuckles,black head,spot,dama duk wani matsala daya danganci fata duk wnd yayi anfani dashi yasan yanda yake maida jiki yazama abun burgewa abun kwatance, fata tadinga haskawa tana walwali duk inda kikashiga sai anyaba😍 toh Inaga wannan zazzafan set Mai maida tsohuwa yarinya☺️Uwargida Takoma amarya😁 amarya Takoma tamkar yanmata❤️yanmata Kuma sudawo Yan Sha shida fata tadinga walwali tana daukan Ido 😉 wani abun ba'a magana shiru akeyi sai Wanda yajaraba shine zai karas😘bama cika Baki duk wnd yagwada shine zaifadi ynd product din mg's yake❤️Kuma munakara Fadi cewa kayanmu organic ne bana bleaching ba suna tsagwaran gyaranjiki ne fiye da tunaninku kuyi kokari kushigo Kuma adama daku Wanda bayada halin siyan set toh sabulun mg's kadai kukarike kankat ne insha Allah🤭

Set dinmu yakunshi

Soap,body cream,face cream,body nd face scrub, cleanser,

Price:13k

Kaman ynd nafadi Wanda bazasu iyasiya set ba sabulun kadai zaibaku mamaki shikadai kukayi anfanidashi zaigoge duk wn prblm na skin living the skin fresh,smooth nd make the skin to glow set din kawai zaikara murje fatane buh ko soap mutum yake anfani dashi ba'a magana🤭

Soap price:3k

Mai bukatan Kaya should chat:08062991549

Call:08064532391

To plc ur order

Munada komai available now so hurry nd grb urs before you hear sold out🤗

Karkubari abarku abaya ko abaku lbr domin kynm yanagyara ko fatan d Mai yabata komutum bashida komai zai iya using kayan zaisa jikin k yafidda wn kyau medaukan hnkl duk inda kikayi se ankalla,show ur skin some luv domin mata da gyara akasanmu😍just gv it a try nd ur skin will definitely/forever thank you❤️

Mn Kaya kowani gari buh delivery is not free🤗

Team glow🧖‍♀️

***************

Sunfara karatunsu hankali kwance saidai NURU da hidima takeson Mata yawa yanxu Dan karatun nasu duk me zafi ne Amma ita ga hidimar kula da farhat da lalurorinta gakuma na gidan Dan yanxu tasaba sosai take saka hannu a aikin kigan musamman ma abinci sbd ko su afia da farhat sunfi Jin dadin cin nata hakama dad dinsu duk da kaman canke ne sukayi kaman yafi ci sosai idan tayi din saiya kasance kobatayi kullum idan Yana gari ita keyi.

Ta bangaren Imran jalal kuwa yanzu soyayya suke gudanarwa afili cikin kwanciyar hankali musamman yanzu daya tabbatarda yagama dasa soyayyarsa a zuciyarta Dan haka yake biyeda ita kaman jela Dan kusan koyaushe Yana gurin daukota daga makaranta kokuma Yana gidan firar yamma,

Yan gidan kaf yanzu kowa yasan menene a tsakaninsa da NURU musamman daya fara kawo Mata maganar aure Dan shi Sam Jin yake kaman soyayyarsu na buqatan kiyayewan tsaro bayason wasa wani Abu ya gitta so yake kawai suyi aure tazama tashi daganan ne kawai zaijisa hankali kwance shiyasa ya takura Mata da maganar auren.

Juyowa yayi daga tuqin dayake ya 'dan kalleta da fararen idanuwansa cikin sauti me bayyanarda Sonta dake mamaye dashi yace"

Beauty yau MALEEK zai Paris gobe da safe zanshigo zamuyi maganar wasu takardun contract dinmu idan mungama zanmasa maganar zuwa neman aurenki gaskia bazan iya cigaba da jira ba is high time ace komai namu yazama dahir ma'ana samun tabbacin zamowanki matata shine agabana komai baya gabana yanzu kamar wannan.

Tunda yayi maganar zai fadawa MALEEK zancen neman aurenta gabanta yayi mummunan faduwa ta dago da sauri ta zuba Masa manyan fararen idanuwanta tareda fadawa cikin tunani me qarfi da firgici.

Wane irin sarkakiya rayuwarta take cikine?

Menene matsayar rayuwarta gabaki daya yanzu sbd batasan menene sunan dazata alaqanta kanta dashiba adaidai yanzu.

Har suka Isa gida batasaniba sbd tunani da tsoro me qarfi da zancen Imran din ya tado Mata.

Kiran sunanta yayi Yana kallonta gabaki daya sbd tayi nisa a tunani batasan sunfi mintuna biyar zuwa shida da isowa gidanba.

Sake Kiran sunanta yayi Yana cewa"

Are you ok?

Waiwayowa tayi dukkanin jikinta a matuqar sanyaye ta kallesa ta gyada Masa Kai batareda ta iya bude Baki tayi maganaba

Zai sake mgna ta bude kofar motar ta fice daukeda handbag dinta da wayarta a hannu.

Bin bayanta yayi da kallo cikin 'yar damuwar sauyawarta atake cikin motar.

Baishigoba sbd a yanda take dinnan bazai samu damar ta kulashiba yanda yakamata sai kawai ya tada motar ya juya ya fice daga gate din gidan ya wuce.

A palon ciki ta tararda farhat na kallon cartoon ta taso da gudu ta fado jikinta tana Mata sannu da zuwa

Qaqalo murmushi tayi ta shafa kanta tana cewa"

Sweetie Aunt NURU batajin Dadi kanta na ciwo zanje na huta ko.

O o sorry aunt.

Gyada Kai tayi tareda sake shafa fuskan farhat din tana wucewa zuwa daki sbd AFIA Bata dawoba sai zuwa yamma.

Tana zuwa daki ta zube kan kujera tareda watsarda Jakarta da wayarta kan daya kujeran tana dafe goshinta tareda rintse ido tana.

Ta Jima ahakan cikin tunani me zurfi har wani wahalallen bacci ya dauketa Bata farkaba sai yamma da Afia tashigo.

Tashi zaune tayi kanta na tsananin sarawa ta miqe tsaye ta nufi closet ta tube ta shige toilet.

Wanka tayi tareda alwala ta fito ta shirya cikin doguwar Bahrain gown mara adon komai Mara nauyima kwata kwata,ta nada mayafi ta tada sallah.

Bayan tagama sallolinta miqewa tayi ta nufi kicin Dan aikin abincin dare sbd Imran yace yau dad dinsu afia zai dawo.

Acikin sanyi takeyin komai sbd rashin walwalar datake ciki na dawo da ita tunaninta da Imran yayi Dan kuwa Dole wata Rana duk cigaban rayuwar dazata samu saita dawo inda asalin rayuwarta take tsaye wato baiwa Kuma negestati.

Meyasa ta shagala hartaso manta wacece ita?

Ta Yaya zatai aure bayan batada wannan damar ko ikon,

Shin ita ayanzu ma menene matsayinta a masarautar delah?

Menene sunanta anan gidan? Yar aiki kokuwa me Reno kokuwa me debewa 'yan gida kewa.

Tayaya Imran zai mallaketa amatsayin matarsa bayan ita din negestatin wani ce Wanda haryanzu batamasan ko wayeba.

Ta Yaya zata Bari Imran yayi maganar aurenta gurin maleek bayan tasan hakan bame yiyuwa bane.

Kammala komai tayi ta diba nata ta jera a tray ta fice daga kicin din tabarwa Fana ta jeresu a dining.

Koda taje daki ta aje abincin tafaraci tana amsawa afia firarta sama sama

Dataga ma ba iyacin abincin zatayiba saita shanye drink din kawai ta bar abincin.

bayan sallar magriba motar data dauko MALEEK daga airport tana shigowa gidan su Kuma lokacin sun gama sallolinsu suna zaune a Palo na biyu farhat na kwance jikinta tana kallon cartoon AFIA Kuma na gefensu itama riqeda wani hardcover t book tana karantawa ita Kuma NURUn tayi nisa sosai a tunanin abinda yake damunta hankalinta gabaki daya yabar jikinta zaune kawai take.

Karan doorbell yasa AFIA kallon farhat sbd sanin Babu masu aiki ko daya yanzu a part din lokacin shigewarsu yayi sun koma part din masu aiki saikuma gobe tace"

Farhat kije ki bude kofa I think Imran ne yazo yanzu.

Sunan Imran din da AFIA ta fada yasata dawowa hankalinta ta juya a hankali ta kalli afia murya a Sanyaye tace"

Kina magana ne?

Batareda ta juyoba hankalinta na kan littafin datake karatu ita afian tace"

Eh inaga Imran Yana bakin qofane doorbell Yana qara.

Kallon hanyar fita palon zuwa palon farko NURU tayi cikin nazari saidai Kuma dama tasan zaiyi wuya Imran din yaqi dawowa yau din sbd sauyin daya gani tattareda ita dakuma nacinsa akan maganar aurensu.

Zame farhat tayi daga jikinta tareda Miqewa tsaye ta nufi daki ta doro qaramin mayafin doguwar riga akan kayan

10 / 37