Ubayd Maleek 1 Complete Hausa Novel

Author :  Mamuhgee Category :  Love

Chapter   15 / 37

42K to 45K   out of 110.1K words

yawane suke yawo cikin kanta wainda suka girmi tunaninta.

Suna Isa dukkaninsu jekadi daga waje suka tsaya daga ita sai farhat suka shiga bayan an wangale Mata kofar tana shiga aka rufe abal da amminsu dake zaune a Palo suka kallo qofar atare fuskokinsu na bayyanarda wani yalwataccen farin cikinsu daya kasa boyuwa itama kasa motsawa tayi sbd kasa gasgata mafarki take kokuwa gata ga iyayenta bayan wasu shekaru take idanuwanta suka ciko da hawaye suna Shirin gangarowa meryam data fito daga gurin padima tana ganin kyakkyawar halitta a tsaye cikin palon ta tsaya cak taqare Mata kallo ta tabbatarda NURUntace a guje tayo kanta tana Kiran sunanta NURU ta ware Mata hannu tareda dauketa cak suka qanqame juna tana jero Mata yarensu Wanda farhat ce kawai batasan me take cewa NURUn ba.

Daqyar suka saki juna kowanne farin cikinsa yakasa raguwa ta qaraso gurin amminta ta rungumeta tareda riqo hannun abal dinta cikin yare da muryarta me sanyi tace"

Abal ubana nagari nayi kewarku fiyeda komai da kowa nayi farin cikin ganinku cikin lafiya da wadata.

Murmushin farin ciki me sauti abal yasaki Yana dafa kanta yace"

NURU 'yata tagari munyi farin cikin ganinki cikin koshin lafiya da nustuwar rayuwa,

Bamu taba farin rayuwaba irin Wanda Kika bamu ayanzu na aurenki da muka gani cikin ahali me girma da daraja.

Amminsu kuwa sbd farin ciki takasa cewa komai sai kallon 'yarta takeyi cikin tsananin so da kauna tareda alfahari Wanda yasa NURUn Jin nauyin iyayenta musamman da abal ya dauko maganar auren yana Mata nasihar hakuri da nutsuwa tareda tawakalli daya santa dasu Kuma yake qara Jan hankalinta dasu akan ta rungumi wannan aure da hannu bibbiyu.

Cikin mamaki ta kalli ammi tace"

Ammi Ina padima?

Ajiyar zuciya ammin tasaki tareda Dan satar kallon abal din kafin ta kalli kofar dakin da padiman ke ciki tace"

Tana can akwance batada lafiya sosai gobema inshallah zamu koma gida sbd aje can abal dinku yasamu maganin Bata Wanda zaiyi Mata tunda ciwon na jiri ne.

Subhanallh"NURU tace cikin damuwa da kulawa kafin ta miqe ta nufi hanyar dakin bayan ta kalli farhat dake maqale da ita tacewa ammi ga farhat Nan su gaisa

Ammin tajawota ta Dora kan cinyarta tana tambayarta tana lafiya?

Tana Isa dakin tashiga Kai tsaye padima dataji zuwan NURUn tasake sassake jiki tana maqale murya tareda qaro nishin ciwonda babusa hadda hawayen da tun safe suka kasa tsaya Mata na abinda ya tsaya ya danne zuciyarta.

Da sauri NURU ta qaraso bakin gadon tana kamo padiman tana Kiran sunanta cikin tsananin kulawa Tama dungumota gabaki daya tana cewa"

Padima meya sameki bayan yau Ina cikin tsananin farin cikin ganinku ku duka.

Marairaicewa padima tayi itama tana rungumo NURUn cikin muryar datayi laushi ta ciwo tace"

NURU nayi tsananin kewarki wadda bantaba sanin haka nake kaunarkiba Saida Kika tafi nakasa nutsuwar zuciya,

Wlh NURU nayi kewarki fiyeda zato ga amed ya yaudareni yace yafasa aurena Amma tsoro yahani fadawasu abal Wanda hakan yasa suka tsangwameni"""kuka tasake Mara karfi sosai tana sake shigewa jikin NURUn tace"

Nidai NURU bansan ya zanyiba mutuwa kawai nakeson Yi sbd itace daidaini,

Dan Allah NURU ki yafemun abinda nayi Miki wlh nayi nadama tunda gashinan Naga ishara irin wadda bantaba tsammani ba.

Cikin mamaki NURU ta share Mata hawayenta tana cewa"

Kidaina kuka padima duk wannan yariga ya wuce Kuma shi amed kansa yayiwa sbd Allah zaibaki Wanda yafisa Inshallah idan har kin tsarkake zuciyarki.

Wasu sabbin hawaye tasaki tana satar kallon kofa tace"

NURU bazan taba daina kukaba sbd kuka yaganni.

Da tausayawa NURU tace"

Kidaina fadar hakan padima.

Padiman zatayi mgn saiga amminsu tashigo wadda takasa zama Jin sun Dade aciki tsaf hankalinsu Bai kwanta da kebewar NURU da padima ba Dan haka Bata Bari padima tasake mgn ba ta janye NURU suka fito inda ta zauna tsakiyar iyayenta suna sake zantawa Kamar kadasu tafi goben jintake Kamar tabisu kosu bita musamman Meryam wadda takeda burin dauka duk tayi aure Amma yanzu Kam ko ita Bata gama tantance matsayintaba bare harta dauko wani ya zauna a qarqashinta.

Saida jekadi taga lokacin kaita gurin maleek yayi tashigo ciki ta sanar musu tayi bankwana da iyayenta bayan anshigo da tarin kayan arziki anjere musu daga Kaleeb da Anneti sai babbar kyautar MALEEK wadda ko ciki baa shigo da itaba saidai idan sun Isa gida akai musu.

Dazata fice harda hawayenta padima ta riqo hannunta tana hawaye qasa qasa tace"

NURU ki taimakeni Banda lafiya mutuwa zanyi idan Ba'a nemamin magani ba ciwon zuciya me qarfi nake fama dashi tunda dadewa kullum bana iya bacci ki taimakeni ki tafi Dani ki nemamin magani NURU.

Kallonta NURU tayi a Dan tsorace tace"

Tun yaushe padima shine Baki fadaba idan yayi tsanani wani Abu yasameki fa?

Kallon abal tayi cikin damuwa da kulawa tace"

Abal meyasa ba'a fadamunba ko a wayane da anfadawa jekadi ta fadamun ta waya wannan ciwon ba abun Wasa bane zantambaya afia Inshallah zamu tafi da padima.

Wani mugun kallo ammi tayiwa padiman data bushe idonta ba wani alamar qarya ko yaudara atareda ita abal ya hade fuska tsaf yace"

Kije NURU Allah ya albarkaci rayuwar aurenki ya Hana duk wani Wanda beda fatan alkhairi sa'ar rabarki,

Padima bazata bikiba kowane irin ciwone zamu nema Mata magani Inshallah.

Kallon padima NURU tayi tana Bata hakuri ta ido da cewa tayi hkr Inshallah ta Mata alqawarin dawo da ita hannunta ta nema Mata lafiya idan nasu abal din baiyiba.

Da haka aka wuce da ita tabarsu suna binta da addua suka wuce ciki Babu Wanda yaceda padima dake tsaye idanuwanta sunyi jajir zuciyarta na wani irin zafi da harbawa.

Kai tsaye sashensu datake dasu afia aka maidata sbd saqon maleek daya Isa gurin jekadi ta hanyar Anneti cewar basai ankar NURU gurinsaba yau din gobe zasu koma,

Tana Isa ta tarar da Afia zaune tagama hada musu kayansu tsaf sbd suma dad ya sanar cewa gobe zasu koma dama amatse take dasu bar Nan din sukoma Kota samu kanta tayi tunanin abinda yakamata.

Tsayawa tayi daga bakin kofa tana kallon afia da duk damuwa da sanyin jiki ya bayyana atareda ita taji tausayinsu su duka ya dawo Mata sbd tafi kowa sanin burin afia akan dawo da mahaifiyarta gidan MALEEK gashi yanxu su duka qaddara ta bullo musu ta inda basa zato.

Qamshin NURUn daya cika gurin yasata dagowa sukai ido biyu kowa yakasa motsawa suka tsurawa juna ido kafin Afia ta taso ahankali ta qaraso gaban NURUn ga mamakinta saitaji afia din ta rumgumeta tana cewa"

Thank God you're back NURU nayi kewarki.

Mamaki yasata daskarewa batareda tace komaiba ko motsawa.

Afia kuwa tarigada tasan zaman aure ko rayuwar aure tsakanin NURU da dad dinta bamai yiyuwa bane har abada Dan haka Bata sawa ranta damuwaba Dan duk duniya Babu Wadda dad dinta zaiso idan ba mum dintaba Dan haka tasan shima idan har aka koma Babu wani maganar aure dazaibi hakama NURU tana komawa Imran yadawo bazata yarda ba Imran zataso komawa Dan haka ta daure tacire damuwar komai aranta.

##MAMUH#

_ZAFAFA BIYAR_💖💖💖

_Alkiblah--SAFIYYAH HUGUMA_

_Makauniyar qaddara--BILLYN ABDULL_

_Dalaal--MISS XOXO_

_Mabudin zuciya--HAFSAT RANO_

_Ubayd Maleek--MAMUH GEE_

_DUKA KUDIN WANNAN DADADAN BOOKS DIN SUNA KAN FARASHIN NERA 700. WATO KUDIN PAGES KENAN. DOCUMENTS IDAN AN KAMMALA SUMA KUDIN SU DABAN.._

ÆŠaya___300

Biyu____400

Uku_____450

HuÉ—u____500

Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇

0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

*_08085405215_*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN qNUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇

  0903 234 5899*_Mamuhgee 22_*

Washe gari tunda safe sakon Anneti na gayyatarsu cin abincin safe tareda ita ya iso musu suka shirya dukkaninsu itadai jekadi dama tunda safe tazo da kayanda NURU zata saka tana Palo takasa ta tsare Dan kuwa komai daya danganci NURU yanxu saiya biyo ta gurinta kafin ya isa gun NURUn.

Da kanta tashirya farhat kafin itama ta shirya cikin doguwar royal gown dinsu me adon golden stones da sequence rigar ta tafine straight shiyasa ta fidda shape din tudun qirjinta zuwa shafaffen cikin har fadin hips dinta saidai adon sequence ne ya 'dan boye bayyanar shape din nata Sosai Sosai Amma duk da hakan yafito sai wuyan rigar dakeda Fadi sosai ta Sanya qaramar siririyar sarkar gold ta doro gyalen rigar akanta ta rufe gashinta dake daure Yana qamshin turaren hayaqin da akai Masa ta fito afia nabinta da kallon yaba kyawun datai Wanda duk be daga Mata hankaliba tunda dai duk abanxane suka fito jekadi na bayan NURU sai sauran masu Binsu suna bayansu kawunansu duk a soke kasa.

Afia ce ke kokarin janta da firar karatunsu da tun shekaran jiya yakamata su koma Amma Basu komaba itama NURUn abin sai lokacin yafado Mata musamman da tafara zuwa Court itama afian tana zuwa asibiti sama sama sbd karatun nasu.

Tun kan su qaraso aka sanarda zuwansu suna isowa suka tararda askarawan maleek kusan guda shida a sassan Anneti din afia na gani tasan dad dinsu na ciki ita Kam NURU batasaniba tunda Babu abinda tasani anan din Dan haka Babu tunanin komai dayazo Mata suna isowa aka wangale musu qofa Ana yiwa NURU gaisuwa ta musamman kafin aka juyo akaiwa AFIA da farhat suka shige.

Suna shiga palon farko duka sauran Yan rakiyarsu suka tsaya anan dagasu se jekadi suka wuce har cikin asalin palon hutawar Anneti suna shiga jekadi ta zube qasa cikin bada girma tace"

Allah yaqara MALEEK kyakkyawar zuciya data fuska,barka da fitowa.

Da hannu kawai ya amsa tareda juyowa Jin muryar AFIA na gaishesa cikin girmamawa itama.

Farhat kuwa kusadashi ta zauna tareda riqe hannunsa tana cewa"

Good morning Daddy.

Da sauri jekadi ta Raba gefen NURU data kusan sanqamewa a tsaye sbd shammatarta da abin yayi Sam ko kadan ko qamshinsa batajiba batama taba saka ran zata ganshi ananba.

Kallon afia yayi da idanuwansa masu haske cikin sautinsa na kamewa ya amsa Mata tareda cewa"

Kuna lafiya?

Gyada Kai tayi tana cewa"

Yes Inshallah.

Ahankali NURU ta tako ta qaraso ciki ta tsaya ta gefen NURU cikin sanyin murya batareda ta kallesa ba kanta na 'dan qasa tace"

Barka da fitowa.

Tsit gurin yayi kafin ya dago ahankali itama ya kalleta Wanda yayi daidai da fitowar Anneti tasaki murmushin ganinsu ta nufi hanyar dining room tana cewa"

Farhat zo ahau table cin abinci Afia zokiyi serving Dina.

Dan kallon NURU afia tayi ta sauke idanuwanta akan budaddiyar gaban rigarta daya bude sosai Dan idan har ba shedan ne yake Mata gixoba tana hango saman nonuwar NURUn kadan ta juya ta wuce tana Dan waiwayowa harta shige dama farhat ita tuni tashige.

Dauke idonsa yayi daga kanta tareda Miqewa baice komaiba ya wuce ciki.

Ajiyar zuciya ta sauke a boye sbd idan har akwai abinda yafi takura da firgici tashiga sbd taji idanuwa akanta saidai Babu tabbacin nasane Kona afia.

Kokarin zama takeyi taji Anneti takira sunanta tafasa ta nufi hanyar dining room din a sukwane tana Dan sauke Kai tana shiga Anneti ta nuna Mata kusada ita ta qaraso ta zauna kirjinta na bugawa sosai sbd duk wannan abin wani iri takejinsa Yana Mata nauyi sbd zuwan komai lokaci daya.

Afia ce tayi serving kowa Nan suka hau cin abincin Babu me mgn musamman itadai gabaki daya bataci abinda ya wuce Loma hudu ba sbd amatuqar takure take.

Maleek ne yafara tashi ya fice kafin Anneti saisu daga baya suna fitowa tuni aka fitarda komai na tafiyarsu suka dunguma zuwa ainihin fadar NEGES inda yayiwa NURU kallon tsaf kafin ya kalli MALEEK Dan kuwa yatabbatarda NURU bazatayima sa'ar afia ba Amma maleek ya aureta.

Yanaga Dole akwai dalilin dayasa MALEEK auren wannan yarinyar wadda akace asalinta ma 'yar bawan kaleeb ne,

Idan har da akwai dalili saiya bincika yaji Dan kuwa wannan karon bazai dagawa MALEEK qafaba Dan Bai shirya sauka mulkiba ya bawa MALEEK kujerarsa Dan haka zai binciki asalin ita yarinyar da zuriarta dole baza'a rasa abinda zaiyi amfani dashiba daga ciki ya rusa maleek gaba daya saiya mallaki kejeran da hujja.

Kyauta me girma yayiwa NURU tareda su afia kafin aka fito da NURU sai alokacin kowa yaganta 'yan jaridu kuwa sukaita dauka wasuma a sace suke daukar hotunan hadda maleek batareda sun saniba.

Kayan aure da aka bawa NURU Dole saidai aka barsu anan a hannun jekadi data riga yanxu tadawo gizah sbd sassan NURU daza'a fitar a tsara itace zata zauna Dan duk lokacinda NURU zataxo tananan Dan haka kayan acan sassan NURUn za'a ajesu.

Har airport jekadi ta rakasu tana sake jaddadawa NURUn wasu bayanan na cewa wannan aure ba saki ba warwarewa,aurene daya qullu har abada Dan haka ta nutsu ta rungumi abinda Allah yabata ta riqe da kyau tareda kiyayewa Banda Kuma yarda da kowa sbd za'a iya biyowa ta gurinki a cutatar da maleek.

Itadai saurare take kawai Dan batamasan wane turn rayuwarta zata daukaba daga yanzu Kuma.

Harsuka shiga jirgi suka miqa tana cikin tunanin yanda zatai rayuwa agidan amatsayin matar dadynsu afia gashi haryanxu bataga wani Alama daya nuna afia bataji dadin abinba ta bangare daya ga Imran datasan yanacan Yana jiran dawowarsu batasan me zatace masaba ya fahimta.

Sai dare sosai suka sauka motocin daukarsu suna airport jiransu Mr Omar sai wani rawar jiki yakeyiwa NURU Wanda yasa MALEEK yimasa kallo daya ya nutsu ya daina aka barta cikinsu afia kamardai yanda suka Saba tun ada.

Suna isowa gida su mum Sarah suka tarbesu suna zubewa yiwa MALEEK barka da dawowa Kai tsaye ya wuce samansa bayan ya amsa musu da hannuwa.

NURU suka jiyo sunawa barka da dawowa taredasu afia wadda tayi gaba sbd sai yanxu taji tasamu nutsuwa harwani ajiyar zuciyar nutsuwa take sakewa farhat mum  Sarah takama hannunta suka nufi dakinta Dan wanka da hutawa.

Koda NURU tashigo daki afia harta shiga wanka Dan haka itama a qage ta cire kayan jikinta ta dauko towel ta daura tana warware gashinta afia ta fito tana gama warwarewa ta nufi toilet din tashige ta sakarwa kanta ruwan zafi tana rufe ido itamadai kusan dawowa gidan yabata nustuwa.

Tana fitowa ta Sanya kayan bacci ta saka jallabiya akai tayi sallolinta tana gamawa ko ruwa Bata nemaba ta cire jallabiyar ta haye gado ta shige bargo sai bacci Wanda afia tuni tayi nata baccin.

Washe gari sai guraren 11 dukkaninsu suka fito kowanne a shirye Banda farhat da har ankaita school sukuma sai zuwa gobe zasu fara zuwa.

Kai tsaye dining suka nufa suka zauna breakfast afia na fadawa nuru suna buqatan zuwa shopping sbd kusan turarukansu da mayukansu dasu shower creams dinsu duk sunyi qasa gashi ita tana buqatan wasu books na karatunta data siya tun last month sun iso ankirata tazo ta karba.

Ruwa NURU Tasha ta aje cup din tana cewa"

I also need some books zanbincika idan munje.

Miqewa tayi ta nufi daki tana shiga wayarta na ringing ta qarasa ta dauka cikeda mamaki da tsoro ganin Imran ne me Kiran ta ajiye wayar tareda kifewa hankalinta na neman tashi,

Me Imran keyine dazai kirani bayan nasan yariga yasan abinda yafaru.

A musulunce a al'adance duk laifine me girma Amma duk da hakan zatai magana dashi tafada Masa Dole hakuri zasu dauka haka Allah yaso Babu aure atsakainsu.

Tana daukan wayar tana tsinkewa sai kawai ta ajiye tareda kashe wayar gaba daya ta nufi closet dinsu ta janyo dogon pencil jeans da riga doguwa har qasa saidai daga qasan a tsage take har cinyoyi Wanda yasa ake Dan ganin jeans din idan tana tafiya ta janyo veil ta daura harta dauki wayarta sai ta fasa ta ajiye ta juya ta wuce.

Afia Dama a shirye take suka fito afia da kanta zataja motar yau suna sako qafafuwansu waje NURU ta tsaya cak wani tunani Yana fado Mata na sanin yanzu fa ita Matar aurece batada ikon fita kona kanta.

Waiwayowa afia tayi ta kalleta tana cewa" lafiya Kika tsaya?

Numfashi NURU ta sauke tana basarwa kada afia tagano dalilinta saita riqe gefen cikinta tana Dan yamutsa fuska kadan tace"

Marata tana ciwo inaga period Dina zaizo kije Bari nakoma na kimtsa najira zuwansa Dan kowane lokaci zaizo.

Da wani irin kallon mamaki afia tace"

Amma ai ba lokacin period dinki bane.

Sake yamutsa fuska tayi tace"

Eh ba lokacinsa bane Amma inaga abubuwan da akaita banine a gizah dama tun can sunata sani ciwon ciki.

Kallon mamaki da tsoro afia Tai Mata takasa cewa komai sai kawai ta juya tana cewa"

Shikenan ki koma Ni zanje nadawo.

Juyawa tayi Takoma ciki tana shiga Palo tana ta sauke ajiyar zuciya ta nufi daki ta cire rigar ta sauyo da qarama Mara kauri tabar wandon ta nufi kicin direct Dan aikin abincin Rana Kota samu abinyi dazai hanata zaman tunani.

Tanayi su Fana da mum Sarah na tayata harta gama tafito ta jera a dining tana baro dining din saiga farhat andaukota daga school tun daga Palo tana shigowa tace"

Aunt NURU yau akwai drwing dazamuyi babba na _Eiffel tower_ competition ne inason nazama 1st.

Yes yes sweetie Inshallah zamuyi shi babba me kyau Wanda zaisa ki cinye afterall who's gonna help you drw????

Da qarfi tana tsalle tace"

Our beautiful Aunt NURU.

Hmmn that sounds like a bribe sbd bantaba Jin kince our NURU ba saidai kice your NURU to yau kenan kinyadda keda afia.

Suna qarasawa kofar shiga palon kurya farhat na cewa"

No not afia,Ina nufin me and my dad since you are his wife now.

Tsit NURU tayi sakamakon hada ido datayi da maleek dayake saukowa tayi saurin dauke kanta tana riqo hannun farhat wadda ta kwace tayi gurinsa tana cewa"

Daddy barka da fitowa.

Kama hannunta yayi Yana nufar hanyar dining Yana cewa"

Hw is daddy's little princess?

alhmdlh dad but today I have.......kallonta yayi cikin nustuwa yace"

Go and freshen up first kafin kizo naji menene.

Da gudu tayi ciki tabarsu tsaye sai alokacin NURU tadan gyara tsayuwa tana rage murya qasa qasa tace"

Barka da fitowa.

Kai kawai ya gyada Mata ya nufi dining Wanda yasata Dole binsa Dan serving tunda dai Babu kowa agurin.

Zama yayi taqaraso

15 / 37