yafito wanka yagama shiryawa ta kallesa tanajin nauyi ta danne ta Kuma kallonsa tana qarasowa ciki tace"
Barka da tashi.
Kallonta yayi ya amsa Yana nufota itama taqi tafiya yaqaraso gabanta Yana kallon kayan jikinta Kamar zaiyi mgn saiya fasa ya nufi kofa Yana cewa"
Ki siya kayan sawa ta online su kawo miki.
Da wani kallo tabi bayansa kafin tabiyosa zuwa cin abincin
Takasa sakewa ta kallesa sai idanuwansa datake na yawo jikinta Haka suka Gama ta miqe ta tattara gurin tagyara ta dawo Palo ta tararda Yana waya saita zauna ta kunna tv takai murya qasa sosai sbd lurada bayason qara ko kadan.
Cartoon ta kunna sbd kewar farhat
Yana gani ya tsaya kallonta Yana aje wayar ya kalleta ya kalli TVn sai abin Bai bashi mamakiba saima murya daya qara Mata ta remote ta waiwayo ta kallesa tareda sakin wani kyakkyawan murmushi batareda tasaniba tana cewa"
Thank you.
Akaro na farko ya saki murmushi kawai Yana daukan wani file da Mr Omar ya aje Masa wainda zai sakawa hannu.
Zamansa gurin yasa takasa kallon yanda takeso yana lureda yawan kallonsa datake saiya dan dago ya kalleta ya nuna Mata kusa dashi ta taso ahankali tadawo Nan ta zauna ya miqa Mata wayarsa Yana cewa"
Ki siya kayan.
Karba tayi tana cewa" thank you ahankalin shima ya maida hankali kan aikinsa.
Da daddare yau da zazzabi takwana sbd sanyi daya 'dan shigeta yinin sbd rashin kayan arziki ajikinta shiyasa har asuba tana cikin jikinsa a lullube sai abin yazo Mata da sauki Dan duk Rabin zafin jikinta a nasa jikin ya shige duk da hakan sunsamu yin bacci sosai.
Guraren Sha daya Mr Omar yakawo Dr Damien yazo yadubata yabata yace wancan maganin daya Bata na farkoma zaiyi tashasa kawai zata ji sauki.
Da daddare da kanta tace adawo Mata da farhat baice Mata komaiba sbd baida tsarin komawarta yanxu so yake taji sauki gaba daya ta dawo normal kafin su tafi can sabon gidan.
Sabuwar rayuwar su biyu kadai aka bude a gidan Dan kuwa tuni ta warke ba wani sauran ciwon komai atareda ita sai period dinta da duka duka kwana hudu takeyi zuwa biyar ya dauke Dan Haka gobema takesa ran yin wankan tsarki.
Da daddare Mr Omar ya sanar dashi wata tafiyar gaggawa da ake buqatan maleek din Dan haka yau din batai wani bacci ba da safe karfe goma Mr Omar yazo daukansu ta shirya cikin riga da wandon pencil jeans da doguwar kimono suka fito Mr Omar yasaka kayansu mota suka shiga suka wuce har lokacin hankalinsa duka na kan waya sbd al'amarin babbane Dan ayanda takeji kaman daga gizah ne.
Zibrian suka Isa cikin qatoton sabon gidansa dake cikeda ma'aikatansu na tsohon gida kowa yakomawa aikinsa tun na tsohon gida hakama kayanta nacan duk ankwaso muta abinda duka,
suna shigowa har bakin kofar palon Shiga Mr Omar yayi parking mota suka fito Yana kallonta Yana karantar yanayinta
Suna shiga farhat ta qaraso da gudu ta fada jikin NURU tana cewa"
I miss you aunt.
Sakinta tayi tafada jikin dad dinta tana cewa"
I miss you both.
Janyota NURU tayi tana cewa"
Sweetie zo Naga kafanki
Ta warke ko?
Bata sakaki zazzabi ba ko?
Na warke aunt NURU kawai dai banajin Dadin bakya Nan Afia Bata nan daddy ma bayanan.
Murmushi NURU tayi tareda duba kafar tana cewa"
Shikenan ai gashi muntaho ko
So muje kifadamun me mum Sarah ke Baki Naga kin qara karfi.
Aunt kema me daddy yabaki kin qara kyau aunt, daddy Nima zanci abinda kasiyawa Aunt NURU.
Shiru NURU tayi cikin tsananin kunyar Mr Omar daya dauke Kai Yana sosawa da mum Sarah data Dan janyo farhat din tana cewa"
Muje mukaiwa aunt dinki kayanta dakinta.
Wucewa maleek yayi Yana Hana murmushinsa bayyanuwa ya nufi hanyar zuwa dakinsa
NURU ta miqe tabi bayan farhat data Kama hanyar dakin dasukace nata.
Kofar da maleek yashiga Nan suka Shiga wani palon ne dayafi na farko tsaruwa sai kofofin bedrooms guda biyu na maleek shine kurya nata farko Kuma da Alama nashin zaifi nata girma sosai sbd ta fahimci shi mutum ne me raayin makeken daki kokuma tace daga sarautane hakan.
Dakinta ta bude tashiga sanyin AC Dana qamshin turarukanta dake jere a gaban madubi Kamar za'a bude shago dasu suka doki hancinta ta qaraso tsakiyar dakin tana kallon koina cikin burgewa sbd komai na tsarin dakin Kamar ansan raayinta.
Wardrobe ta nufa ta bude tana waiwayowa ta kalli farhat saitaga ba ita zata tambaya ba ta maida kallonta kan kayan dake shaqe da wardrobe din ta waiwaya gefen kayan bacci batasan lokacinda tasaki murmushi ba tana Jin kunyar abinda tagani ta rufe tana duba bangaren takalma Suma dai kusan duk kowane designer brand akwai.
Gurin wayarta dake gaban madubi ta Isa bayan ta jera kayan data dawo dasu a dauka tareda kunnawa zata Kira gidansu saiga farhat data fita tadawo dakin tace"
Aunt kizo daddy na Kira.
Aje wayarta tayi suka fito tare ta nufi palonsa na cikin kofar bedroom dinsa suka Shiga tareda farhat Yana zaune kan kujera Yana duba wayarsa yaji shigowarsu Bai dagoba saidata kusa isowa dab dashi ya kalleta kafin ya kalli farhat data naniketa Kamar zata gudar Mata.
Kashe wayar yayi tareda Miqewa tsaye da wayar a hannunsa Yana kallonta yace"
Gizah zamuje da Mr Omar duk abinda zai faru ki sanar Dani a waya.
Akwai tight security anan Babu Wanda zai shigo bada izininki ba dan Haka ba kowa za'a bawa izinin shigowanba.
Wani card ya ajiye Mata akan table ya wuce harzai gota ta ya tsaya tareda kallonta yayo qasa ahankali setin kunnenta yafada Mata password na card din Yana fada Mata lips dinsa na gugar kunnanta ta lumshe ido ta bude ahankali tana kasa dagowa ta kallesa sbd kunya ga farhat a tsaye tana kallonsu cikin burgewa duk da batasan meyake faruwa ba farin cikin kawai takeyi.
Kallonta yayi yaso sakin murmushi ya fuske ya wuce ta biyosa baya daf da zai fice palon ta tsaya bayansa ahankali tace"
Allah ya yadawo dakai lafiya.
Yace Amin batareda ya waiwayoba ya fice tabi bayansa da kallo.
##MAMUH#[10/2, 7:32 PM] Sadeeya: *_Mamuhgee 38_*
_*YERWA INCENSE & MORE*_
_(The scents with diff essence for YOU& your HOME)_
_(MASARAUTAR KAMSHI)_
_Ina masu neman kayayyakin kamshi yan nahiyar ketaran chadi da Senegal? Kai harma da ingataccen had’i yan bornu? To ku matso domin nesa tazo kusa..._
_YERWA INCENSE & MORE: Sun zo muku da kayayyakin turaruka kamar haka:_
_Khumra kowacce Iri._
_Turarukan Wuta_
_Mopping khumrah_
_Washing khumrah_
_Bathing khumrah_
_body mist_
_kullaccam_
_scented hair cream/spray_
_wardrobe balls_
_carpet spray_
_air-fresheners_
_scented pebbles_
_body sprays_
_oil perfumes_
_Perfumes_
_kabbasa_
_burners_
_coal igniter_
_tong_
_kasko_
_english coal_
_dilke&halwa set_
_scented body mist_
_kai dama sauran kayayyakin da bamu ambata, YERWA INCENSE AND MORE, Na tura kayayyakin su koina a fadin Nigeria da ketare. Domin tuntubar su. Suna instagram: _@yerwaincense_and_more. Ko Facebook site:YERWA _COLLECTIONs. Ko a duba su ta number su: ___08095215215/09044191709! _
_suna bada kayan su kan sari ko sayi dai-‘dai_
******************
Bayan fitarsa Haka ta tsaya a inda take tana bin inda ya fice da kallo zuciyarta na rarraba tunanin shin so ne takamu dashi me qarfi kokuwa Jin dadine kawai na kusantuwa dashi?.
Waiwayowa tayi ahankali ta kalli farhat dake gefenta tana kallonta kamar Bata santaba sbd ganin bayan sabon gida da aka sauya musu hadda aunt NURU da daddy dinta kaman suma sababbine aka kawo musu.
Murmushi me qayatarwa NURU tasaki tana juyawa takoma cikin palon ta zauna tareda kunna tv da remote tana Nemo tashar waqoqin yarensu ta Amstar farhat tazo ta zauna jikinta tana cewa"
Aunt NURU Zaki fassara Mana waqan da akeyi ko?
Da mamaki ta kalli farhat din tana murmushi tace"
Sweetie bazan iya fassa Miki dalla dalla ba kawai dai suna waqan soyayyarsu ne.
Da Haka ta rufe zancen farhat din sbd bazata iya bi tana fassara Mata suba kalaman sunyiwa kunnuwanta nauyi bama zata ganeba ko fassarawar tayi Mata sbd kalaman so din ko ita datake sabon Shiga sun Mata nauyi.
Saida lokacin sallah yayi ta miqe ta nufi ciki da farhat a dakinta sukai sallar bayan tayi wankan tsarki
Suna gamawa suka fito babban Palo gaba daya cin abinci daga ita sai farhat din akan dining Haka sukaci suka tashi tunanin afia yadawo Mata
Tanajin kewarta sbd akwai shaquwa da kauna a tsakaninsu ta haqiqa Dan haka takejin kewarta tun ranarda suka baro can saidai tana Mata uzuri sbd Babu Wanda zai zabi wani yabar uwarsa koman lalacewarta Dan hakan yasa Bata ganin Jin illar afia ko kadan kawai dai laifinta daya shine
Barin mahaifinta ta zabi mahaifiyarta daba itakeda gaskia ba ko acikin matsalar ta iyayen nata cire tunanin zancen tayi daga kanta sbd wannan ba huruminta bane dazata shiga tsakanin 'ya da iyayentane.
Ranar dasu mum Sarah suka baro gidan bayan kowa ya fidda kayansa anzo andaukesu akabarsu su kadai har lokacin a palon suke afia na kukan rasa cikin mum da dad din wazatabi
Lailah dakejin wata masifaffiyar hauka na bijiro Mata Jin take kamar ta Dora hannu akai tayita rusa ihu tana tsinewa maleek sbd tunda Allah ya halicceta ba'a taba muzanta taba da wulaqanta taba harma agaban bainar masu aikinta dake tsoronta da Bata girma Kamar zasu bauta Mata sai yau maleek yayi Mata wannan mummunan tabon,
Cikin tsananin ihu da masifa tareda tashin hankali ta miqe tana cewa"
Allah ya Isa tsakanina dakai MALEEK Kuma wlh bazan yardaba wannan wulaqancin dakamun kanka kayiwa Dan saina tabbatarda ka fuskanci tozarci fin wannan Kuma wlh zama matarka ko zan rasa Raina saina dawo matarka alokacin karuwarka zatasan matsayinta da nawa bazai taba zuwa dayaba Dan kuwa wlh ko zata samu damar zama cikakkiyar matarka to saidai idan Ni Lailah bana raye.......
Da sauri afia ta rufe bakinta cikin tsananin baqin cikinta da wannan karon yakai maqura baya boyuwa hawayenta na tsiyaya tace"
Mum mekike fadarwa kanki Haka?
For God's sake meye amfanin hakan?
Tun farko nayi gudun hakan mum ba kalar rokon daban mikiba karki tafi sbd duk duniya Babu abinda zakije kisamu dayafi Miki 'yayanki da mijinki Wanda mum ga dukkanin abinda nasani nake Kuma gani dad bazai taba dawo dakeba kema kinsani sbd kinsan wayeshi,
Kin Mata umarnin da kaleeb yabaki mum duk Kika shure Kika tafi?
Mum na rokeki ki hakura ki aje komai tunda yabar Miki Nan din kiyi zamanki tareda Gina sabuwar rayuwa ki maida hankali kan aikinki I promise to be with you aduk halinda Zaki shiga matuqar Zaki janye wainnan kalaman naki ki hkr da abinda zai ringa jawo Miki wulaqanci dacin fuska,
Mum menene amfanin wainnan maganganun na cewa saidai idan bakya raye
Mum ba'a yiwa Allah ganganci wainnan maganganun har daureki zasu iyayi Dan Allah mum Ina rokonki kadakiyi abinda zai cutatar da dad ko NURU sbd ita ba laifinta bane
Idan akwai me lefi nawane nice na hada auren...
Wani mahaukacin kallo lailah tajuyo tana yiwa afia da idanuwanta dasuka fiffito sukai jajir kamar me bori tace,
Kikace mene afia?????
Kallon mum din tayi tana dakewa tace"
Nice na hada auren batareda raayin ko dayansub......
Wani gigitaccen Marine akaro na biyu ya sauka a fuskarta Saida tayi baya ta zube kan kujera a dimauce ta dago lailah tace"
Wannan na tabbatar min da kikai bare tafi Miki uwarki
Dan kuwa kece silar duk komai daya faru ayau tsakanina da dad dinki.
Juyawa tayi a masife tayi ciki ko gabanta Bata gani sosai ta nufi dakinta tana shiga ta rufo wani irin kuka dataketa dannewa tsabar baqin ciki ya subuce Mata ta zube kasa tana sakinsa tareda rufe bakinta da hannuwanta kada afia ta jiyota abin ya Mata yawa.
Afian ma kasa bin mum din Tata tayi ta zauna agurin tana kuka ahankali ahankali.
Da daddare daqyar kowannensu ya iya kwantawa Babu ci bare Sha hakama kwanciyar kawai sukayi Babu Wanda ya samun bacci ya daukesa sbd fargaba da tashin hankalin rashin ko masu gadi Babu ko motsin komai aduk girman gidan sai rashin tsaro da motsin yasa sukaji basa cikin kwanciyar hankali musamman afia data rasa tunanin me mum dinta keyi tareda tunanin meye niyarta.
Washe gari Lailah tarigada ta yanke shawaran zuwa gizah Dan takasa hkr a Daren takira NEGES datasan shikadaine yanxu zai iya saka Baki a maganar sbd kaleeb ko Ana Mata dukan mutuwa bazata fara tunkararsaba bare Anneti datasan duk duniya bazatabi bayan kowaba indai akan 'dantane MALEEK,
Tariga ta yanke zuwa gizah sbd dawo fry da matartabarta na matsayin Matar maleek bazata taba yardaba 'yar bayi jikar bayi tasha gabanta harta karbi matsayinta.
Koda afia tashigo dakin da safe lailan na zaune tana duba agogon hannunta Dana wayarta akai akai sbd tayi booking din ticket na tafiya jira take lokaci yayi ta nufi airport
Drivern dadyn Imran takira aturo Mata shi take jira yakaita airport din
Shigowar afia yasata dagowa ta kalleta da idanuwanta dasukai jajir sbd rashin rintsawa da tashin hankali tareda masifar datake ciki ta dauke Kai daga afian tana Dan yamutsa fuska tace"
Afia idan kinzo Nan danki dameni da koke kokenkin Nan kokuma wani shirmen daban kadaki fara sbd inada ciwon kan danake fama dashi already bana buqatan wani sabo Dan bama zan dauka ba kece naki ran zaiyi mummunan baci so just get out of here"taqarasa fada tana nuna Mata kofa da ido.
Tray din da afia ta jero Mata tea da soyayyan kwai takawo Mata ta kalla tana tsiyayar hawaye takasa cewa komai ta juya ta fice hawayenta na sake gudu tana zuwa kitchen ta ajiye tray din ta juyo ta fito kenan mum din tafito janye da akwati da handbag dinta sai wayarta a hannu
Da mamaki afia ta qaraso tana share hawayenta dasuka kasa tsayuwa ta bude Baki muryanta na rawa tace"
Mum Ina....
Bata qarasaba lailan ta katseta da cewa"
Gizah zantafi idan Zaki iya zama anan ne to saina dawo idan bazaki iya ba ki nema gidan dad dinki ki koma can dama kece Kika hada auren saikije ki qarasa cike ladarki ta qara musu dankon zama.
Juyawa tayi ta fice tabar afia sandare a tsaye cikin 'dibbin mamaki da tsoron mum din Tata da sauyawarta.
Da gudu taqarasa ta riqe mum din tana cewa"
Mum Dan Allah na rokeki kada kije ki wulaqanta kanki acan
Tozarci da sake tonarda asirinki kawai Zakiyi Anneti bazata karbekiba Dan Allah kada kije mum,
Mum na rokeki Dan Allah...
Cikin quluwa lailah ta cire jikinta daga nata tana cewa"
Baki fahimci abin Dana fada Miki kenan ba nace ki nemi dad dinki ki tafi gurinsa bazan iya wannan hayaniyarba afia please just go kina batan lokaci Ina buqatan Isa airport kan lokaci.
Rabewa tayi ta wuce ta miqawa driver akwatinta ya karba yasaka mota tareda bude Mata tashiga ta rufe ya zagaya ya shiga ya tada motar suka fice.
Ajiyar zuciya afia ta sauke ahankali tanabin inda suka wuce da ido tana rasa tunanin Yi akan mahaifiyarta sbd yau da mahaifiyarta tasake tsallakewa ta barta akaro na biyu ya rusa duk wani sauran hope datake dashi akan uwarta sbd duk uwar data tsallake babbar budurwa kamarta a qaton gida irin wannan Babu kowa ta tafi ta barta batareda tunani ko fargaban wani abun yafaruba tabbas babu 'yayanta cikin ranta,
Dad dinta tasani ta tabbatarda Koda Wasa bazai iya kwatanta wannan gangancin akantaba shida yake uba Amma uwarta mace takasa yadda ta runguma takuma yadda data zama uwa me nauyin 'yayanta akanta.
Sake sauke numfashi tayi tareda juyawa ahankali ta koma ciki tana daga qafafuwanta dasukai Mata nauyi daqyar.
Dakinta direct ta nufa ta zauna bakin gadon tareda dagowa ta kalli dakin tafashe da kuka ahankali tana sunkuyar da kanta sbd yau ta wayi gari batada kowa atareda ita bawai Dan tarasa kowa din ba.
Ta share awanni a hakan tana kuka cikin hali na ciwon dakecin zuciyarta kafin ta share hawayen ahankali ta miqe tsaye ta janyo akwatinanta tafara kwashe kayanta tana zubawa ciki harsaidata Gama kwashewa tadawo ta zauna tana tunanin Kiran mahaifinta datasan ransa abace yake da ita.
Kasa kiransa tayi Takoma ta kwanta kan gado tana tunanin meya hargitsa rayuwarta cikin kwana daya da awanni akai.
Kasa kiransa tayi Takoma ta kwanta har batareda tasan matsayar inda ta dosa ba sbd wata zuciyarta na Bata shawaran in mum dinta gizah sbd dakatar da ita ga wani abin dabai kamataba Wanda zai iya janyo zubewar mutuncin dad dinsu da ita kanta mum din saidai Kuma Tana Jin gwara ta qyale mum din tayi nisa zuciyarta batajin kira.
Wayarta ta dauka ta duba Babu available tickets na zuwa gizah Dan Haka ta yanke shawaran jira kwana biyu tagani.
Bayan kwana biyu haka tasake dubawa ba tickets sai jikinta yayi sanyi ta sawa ranta ba alkhairi cikin zuwan nata Dan Haka tasake daurewa ta zauna har gari yasake wayewa ta yanke shawara takira dad dinta saidai Bata samesaba sai kawai ta Nemo wayar NURU takirata Kai tsaye.
Da safe ne suna cikin bacci itada farhat a dakinta washe garin ranarda MALEEK ya wuce kenan,
Basu tashiba sbd guraren karfe takwas ne taji ringing din wayarta ta lalubo ta dauka batareda ta tantance sunan me kiranba saidataji muryar afia ta wartsake tana bude ido tareda dubawa taga sunan afia din ne cikin kulawa tace"
Afia kina lafiya kuwa?
Ajiyar zuciya afia ta sauke dagacan bangaren tareda bude Baki tace"
Kituromin Edward yazo yadaukeni anan tsohon gidan Ina jira.
Ahankali NURU tace"
Ok Bari nakirasa nafada Masa zaizo yanzu Inshallah.
Da haka suka kashe wayoyin kowacce cikin Jin nauyin 'yar uwarta.
Batareda ta sauko gadonba daganan kwance ta Nemo numbern Edward ta saka kiransa Yana dagawa ta sanar dashi yaje ya dauko afia yace ok.
Komawa baccinta tayi sbd Bai ishetaba kafin afian ta iso.
Cikin bacci tasakejin ringing na wayarta ta lalubo ta daga cikin bacci tace"
Mum Sarah lafiya kuwa?
Sorry na tasheki dama afia ce tazo nace zan sanar dake za'a Kai Mata kayanta asalin dakinta da aka ware Mata.
Guntuwar hamma tasake tana