tace"
Mum Sarah kikawo ruwan sanyi sosai da towel da sauri.
Hannuwanta har rawa sukeyi tafara ragewa jekadi kayan jikinta tabarta daga ita sai shimi
Ta karbi towel din da mum Sarah ke miqo Mata yadau sanyi sosai sbd ruwan kankarane aka saka Masa ta ya6a Mata ajiki take sanyin yafara shigarta tafara jero ajiyar zuciya a wahalce.
Ganin hakan yasa NURU ta miqe da sauri kafafunta har rawa sukeyi ta nufi dakinsu kota kan afia dake kwance a qasa batabi ba ta zari wayarta ta fito sauri ta nufi dakin mum Sarah tana Nemo numbern Mr Omar dayake shima acikin mansion din yake Yana ganin kiranta ya tashi zaune sbd koyaushe a shirye yake kullum dare Baya wani dogon bacci sbd tsaro.
Cikin girmamawa ya dauka da cewa"
Barka da.....a yamutse ta katsesa da cewa"
Mr Omar maleek da jekadi sunci ko guba kokuma wani Abu daban kaga kawai kazo yanzu yanzu matsalan babbane, maleek... maleek..jikinsa duka yayi wani...
Ko rufe Baki batayiba taji buga kofarsa
Ta dago a tsorace ta kalli kofar palon zuciyarta na bugawa da qarfi sbd tsananin tsoro
Ta cikin wayar dake kunnenta har lokacin taji yace"
Nine abude kofar da sauri.
Da gudu ta qarasa kofar ta bude Masa dukkanin jikinta rawa yakeyi Bai dago ya kalletaba yace"
Zanduba jekadi ta jikinta zamu gano ko menene.
Da sauri tayi gaba tana cewa'
Zo zo zo kaduba suna cikin tsananin azaba,
Maleek ya....shiru tayi tana kaucewa ya qarasa gurin jekadi da sauri
Kallo daya yayi Mata yasan menene
Da sauri ya daga hannunsa daya yakai bakinta saikuma ya kasa tabbatarwa ta hakan ya dakata cikin tsananin tashin hankali yace"
Idan na tabbatar garin asirin Kona jinine Wanda zai.....
Cikin tsawar dabatasan Tai Masa ba tace"
Mekake jira ka tabbatar Mana maleek na can cikin irin halin kayi sauri kafada mana abinda za'ayi kokuma Akira Dr Damien kaduba kaga halinda suke ciki...
Sake sauke Kai yayi cikin Dan Jin nauyin zancen yace"
Bakinsu za'a laso aji idan da daci sosai.
Wani irin kallo Tai Masa itama cikin tsananin Jin zancen wani iri daga sama.
Ganin kallonda mum Sarah Tai Mata ta sauke Kai haka shima Mr Omar din yasata Shan jinin jikinta sbd hakan na nufin itace Dole zataje ta dandano musu na maleek tunda dai Babu me iya Shan na jekadi hakama maleek Dole sai ita Dan dama irin wannan masifar idan ta samu mutum Miji ko Mata ke lasa bakin idan Kuma yarone iyayensu idan tsofine yayansu.
Juyawa tayi da sauri ta fita ta nufi hanyar sama zuciyarta na bugawa a qarfafe sbd tsoro haka ta qarasa dakin har lokacin Yana kwance lullube idanuwansa arufe ganin hakan yasa ta qarasa da sauri ta haye gadon Bata tsaya wata wataba takai fuskarta dap da tasa zuciyarta na harbawa tasa hannuwanta biyu ta tallafo fuskarsa ta rufe idanuwanta ta Dora qaramin bakinta kan nashi ta zura harshenta cikin bakinsa ahankali ta laso sai alokacin ta bude fararen idanuwanta ta kallesa ga mamakinta saitaga idanuwansa a bude hancinta yake kallo.
Da sauri ta zabura tareda zare bakinta tana saukowa gadon dukkanin jikinta na rawa tayi kasa da kanta zatai mgn can qasan maqoshinsa ya bude Baki a wahalce yace"
Idan jekadi ce ko mr Omar kice abinda suke zargine Mr Omar yasan password na inda maganinsa yake
Daga haka ya maida idanuwansa ya rufe sbd azabar abinda yakeji cikin jikinsa
Da sauri ta juya daga dakin ta fice zuwa qasan har tana hada bene uku uku gurin saukowa ta iso dakin da sauri ta kalli Mr Omar muryarta na rawa tace"
Yace shine duk abinda kuke zargi din kayi sauri ka dauko antidote din yace kasan komai please please please hurry Mr Omar...
Cikin sauri sauri shima yace"
Ok ok Amma Dole saimun tabbatarda bakin nasa akwai "daci sbd ta hakan zansan idan yagamabin jininsa..
Rikicewa tayi tana rawar murya tace"
Eh"kawai sbd ita Bata wani gane daci acikin bakinsaba gabaki daya ta rude da wani irin dumi da qamshin _Vedshakti lemon mouth freshner_ data debo abakin nasa Dan haka bazata iya tantance komaiba.
Tashi Mr Omar yayi ya fice daga dakin da sauri haryana tuntube tabarsu cirko cirko a tsaye kowa kayan cikinsa na juyawa sbd fargaba.
Jin shiru shiru yasa NURU fitowa takalli agogo lokacin har qarfe uku da arbain tayi tafito Palo yafiso goma tana komawa dakin mum Sarah Jin take Kamar tayi Ari hauka ta dauko wayarta zata Danna Masa Kira sai gashi yashigo da gudu gudu ya miqa Mata Yana cewa"
Hada da ruwan zafi kikai Masa yasha inshallah zafin zai sauka gabaki daya bayan asuba saina Kira Dr Damien.,
Idan yasha zaiyi amai sosai karki basa komai bayan wannan sai bayan 2 hours.
Karba tayi tayi kicin mum Sarah na bayanta jikinta na wata irin rawa take dafa maganin harsaida mum Sarah ta matso cikin tausayi da damuwa itama tace"
Ki nutsu Inshallah maleek da jekadi Babu abinda zaisamesu.
Gyada Kai tayi kawai tana dauko cup cikin cups din MALEEK dake gurinsu daban ta zuba Masa ko a tray Bata tsaya dorawaba ta dauka ta fice da sauri tana cewa"
Mum Sarah ki zuba kiyi gaggawar bawa jekadi.
Tana Isa dakin ta ajiye cup din saidata qara sanyin AC kafin ta qaraso gadon ta aje cup din kan bedside ta kallesa tanajin nauyin yanda zata bashi sbd tagama fahimtar Dan idanuwansa na rufe bashine ke nufin Yana bacci ba.
Kafin tayi wani yunquri taga ya motsa tareda bude idanuwansa Yana tashi zaune batareda ya kalletaba ya miqa hannu daqyar
Dasauri ta dauko cup din ta matso ta miqa Masa tareda tsayawa akansa Kamar zata fasa kuka sbd Jin yanayin take har cikin ranta.
Kurbi daya yayi ya dakata sbd abinda yakeji ta matsosa sosai cikin kulawa da damuwa tace"
Yace duka za'a shanye.
Ko kallonta Bata samu damar yayiba yasake daga cup din yasha Yana rufe ido tareda shanyewa ya miqa Mata cup din da sauri Yana saukowa gadon ya nufi toilet yafara kelaya wani irin aman azaba Wanda yasata kasa hkr tabisa ciki idanuwanta na cikowa da ruwa musamman ganin Aman hadda jini sosai aciki ta rude tana dafa bayansa da har lokacin yake bayyane ba Kaya ajikinsa Dan abin kamar daurin Rai da dai towel dinsa har lokacin be kunce ba koya kunce akwai qaramin gajeran wando ajikinsa.
Saidayayi mugun amai sosai kafin taji take zafin jikinsa ya sauka gabaki daya ta zuba Masa ruwa ya wanke fuskarsa da bakinsa ta fito tabarsa aciki ta sake gyara Masa gadon da duk suka cukuikuye sbd rudewa ta dauki cup din ta fice daga dakin tun kafin yafito sbd ta lura tun cikin toilet din yadawo MALEEK dinsa.
Gurinsu jekadi ta Isa da sauri itama cikin sa'a ta tararda ta amaye komai gabaki daya ta shigo suka kamata tareda goggge Mata jiki suka kwantar da ita take baccin wuya ya dauketa sai alokacin dukkaninsu suka saki ajiyar zuciya me qarfi abinda takeji tokare a zuciyarta ya fada Mata ta dafe goshinta tana sake sakin jerin ajiyar zuciya kafin ta dago dmta kalli mum Sarah tace"
Menene yafaru bayan shigewata da daddaren?
Ajiyar zuciya mum Sarah tasaki tareda sauke Kai qasa cikin rashin sanin takamaimai na komai tace"
Bansaniba
Kawai dai abinda nasani shine jekadi tashigo dakina acikin wannan halin
Abu daya tace shine na jininta na quna.
Wani sabon numfashin takuma saukewa me zafi kafin ta bude Baki tace"
Shikenan zuwa da safe idan duk sunji sauki zamuji abinda ya samesu
Ki lura da ita Mr Omar zai Kira Dr bayan asuba.
Juyawa tayi ta fice jikinta a matuqar mace sai yanxu takejin tsamin jikin guje gujen dataitayi daga sama zuwa qasa ta nufi dakinsu ta fada kan gado tareda lumshe idanu tana godewa Allah dayasa komai ya tsaya nan Amma Kuma zuciyarta na Bata wani irin yanayi Mara Dadi na afkuwar al'amarin sbd idan har ciwon maleek ne kaman yanda yasaba to ita jekadi fa?
Gabaki dayama wannan ciwon wani babban abune na daban sbd azabar dasuka Shiga sai me qarfin jini ne kawai zai iya dauka dan kuwa taga tsananin azabar dasuka shiga musamman MALEEK.
Bude ido tayi ahankali tasake lumshewa har lokacin tanajin dumin jikinsa daya Shiga jikinta sbd ba qaramin full body contact suka samu ba Dan ita yacire rigarta shikuma dama Babu anasa jikin.
Saurin rintse ido tayi da qarfi tana cire tunanin cikin ranta ta gyara kwanciya Dan tasamu bacci ya Dan dauketa kafin asuba.
##MAMUH#
_ZAFAFA BIYAR_💖💖💖
_Alkiblah--SAFIYYAH HUGUMA_
_Makauniyar qaddara--BILLYN ABDULL_
_Dalaal--MISS XOXO_
_Mabudin zuciya--HAFSAT RANO_
_Ubayd Maleek--MAMUH GEE_
_DUKA KUDIN WANNAN DADADAN BOOKS DIN SUNA KAN FARASHIN NERA 700. WATO KUDIN PAGES KENAN. DOCUMENTS IDAN AN KAMMALA SUMA KUDIN SU DABAN.._
ÆŠaya___300
Biyu____400
Uku_____450
HuÉ—u____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
*_08085405215_*
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
 0903 234 5899*_Mamuhgee 29_*
_*YERWA INCENSE & MORE*_
_(The scents with diff essence for YOU& your HOME)_
_(MASARAUTAR KAMSHI)_
_Ina masu neman kayayyakin kamshi yan nahiyar ketaran chadi da Senegal? Kai harma da ingataccen had’i yan bornu? To ku matso domin nesa tazo kusa..._
_YERWA INCENSE & MORE: Sun zo muku da kayayyakin turaruka kamar haka:_
_Khumra kowacce Iri._
_Turarukan Wuta_
_Mopping khumrah_
_Washing khumrah_
_Bathing khumrah_
_body mist_
_kullaccam_
_scented hair cream/spray_
_wardrobe balls_
_carpet spray_
_air-fresheners_
_scented pebbles_
_body sprays_
_oil perfumes_
_Perfumes_
_kabbasa_
_burners_
_coal igniter_
_tong_
_kasko_
_english coal_
_dilke&halwa set_
_scented body mist_
_kai dama sauran kayayyakin da bamu ambata, YERWA INCENSE AND MORE, Na tura kayayyakin su koina a fadin Nigeria da ketare. Domin tuntubar su. Suna instagram: _@yerwaincense_and_more. Ko Facebook site:YERWA _COLLECTIONs. Ko a duba su ta number su: _*08095215215/09044191709*! _
_suna bada kayan su kan sari ko sayi dai-‘dai_
**********
Harta Gama zuba Masa ta ajiye Bai Bai Kuma waiwayowa ba amfani yake da wayarsa sai farhat dayake tankawa ahankali,
Juyawa tayi zata fice batareda ya kalla inda take ba yace"
Kijira ki tafi da kayan.
Dakatawa tayi tareda sauke ajiyar zuciya boyayya sbd atlas dai yanuna yasan da shigowar mutum ba farhat kadaiba.
Juyowa tayi ahankali tadawo daga gefe ta tsaya tana Dora kallonta kan tv dake aiki Sam bama murya kusan gabaki daya Wanda ta fahimci qaidar iya muryar tv dayake buqatane ahakan.
Ganin tsayuwar Kamar zata damesa saita sulale ahankali Takoma palonsa na farko ta zauna tana kallon tsari da haduwar palon Wanda kusan komai na palon milk ne.
Juya idanuwanta tayi kan wani qaramin hoton LAILAH dake cikin qaramin milk frame tana tareda maleek din dukkaninsu cikin qananun Kaya black shi Yana zaune gabaki daya hankalinsa nakan wayar dake hannunsa itakuma ta rungumosa tana dariya fararen haqoranta tas a bayyane sunyi kyau.
Dokawa taji qirjinta yayi ta dauke kanta daga kallon hoton tareda Dan hadiye yawu tana qoqarin Wasa da yatsun hannunta.
Kasawa tayi tasake juyowa gabaki daya ta qurawa hoton ido tana qarewa LAILAH kallo.
Kyakkyawace da kyanta yake a bayyane,gata da kyawun jiki Kamar ba ita ta haifi afia ba Kamar dai yayarta,
Wayewarta ko acikin hoton a bayyane take sbd yanayin shigarta da yanda take nanuke ajikin MALEEK Wanda son datake Masa yake bayyane afili shima alamunsa da yanda hankalinsa ke kwance qarara a hoton ya bayyanarda soyayyarsa ga matarsa.
Sake dauke kallonta tayi daga hoton jikinta nayin sanyi bugun zuciyarta na qaruwa ta waiwaya gefenda kofar dakin lailah din saitaji jikinta na Gaza Mata ta miqe tabar gurin ta koma cikin palonsa wannan karon sallamarta daqyar ta fito qasan maqoshi sbd shaqewar dataji maqoshinta yayi.
Qarasowa tayi kanta a qasa ta dauki tray din ta fice batareda tabi takan farhat ba dasukazo tareba.
Tana saukowa kitchen takai kayan ta wanke da kanta ta maidasu gurinsu ta fito ta nufi daki batareda Takoma gurin padima ba.
Tana zuwa daki ta fada kan gado takwanta tareda rufe idanuwanta tana sauke ajiyar zuciyarda batasan Kota mececeba.
Har dare Bata sake fitowa daki ba Koda padima tazo ta tambayeta ce Mata kawai tayi kanta na ciwo hutu take buqata.
Padima Bata damu da hutun da NURUn tace tana buqataba ta zauna gefenta tareda kallonta Kai tsaye tace"
NURU inason zankoma gida Kuma cikin gaggawa sbd kwana biyun Nan inata mafarkai marasa Dadi na abal da ammi kaman dai da akwai babbar matsala Dan haka Ni inaga zankoma gurinsa kada ya zamto babuke akusa Babu Ni.
Tashi zaune NURU tayi tana kallonta da yanayi na damuwa tace"
Amma ai nayi waya da abal ko dazu Kuma banji alaman matsala ko wani damuwaba bayan haka meye amfanin zuwanki kema idan Baki ga likita ba akan Taki lafiyan.
Yamutsa fuska tayi tana cewa"
Kibar maganar nawa ciwon sbd bana tunanin zan tsaya ganin likita naji sauqinsa sosai Dan dama kila hadda damuwar rashinki akusa ne yasa abin yayi tsanani yanzu Dana zauna dake naji saukin komaima kawai damuwata anan iyayenmu ne kiyi tunani kema kinsan Koda damuwa abal bazai taba Bari kiganeba barema Koda na baro fa bayajin Dadi kwana biyu Yana fama da ciwon tari...
Da wata sabuwar damuwar NURU ta kalleta tana cewa"
Amma meyasa tun zuwanki Baki fadamun abal bayajin dadiba padima?
Kinga shine ya gargadeni akan kada na fada Miki Kuma ko yanzu kada kiyi Masa maganar Dan zaisan cewa nafada Miki
Nidai gida zankoma jibi kiyi Shirin duk abinda Zaki bani da Wanda Zaki karbomin daga MALEEK,
Ni bana wannan ba NURU meyesa nakeganin kaman ba zaman aureba kike a gidan nan??
Dan Babu wani alamari daya danganci aure danaga Yana faruwa dake.
Shiru NURU tayi tareda dagowa ta kalli padiman tsawon mintuna sbd batasan me zataceba tunda kusan gaskia padiman tafada, ta sauke numfashi tareda Miqewa tana cewa"
Kidaina wannan tambayar padima
Ba lallai komai ake bayyanawaba
Tunda dai akwai auren komaima ahankali za'ayi.
Miqewa padiman itama tayi tana cewa"
To dai iyayenki saisu daina dukan gaban 'yar so tana auren MALEEK na delah gizah Dan kar ayi zaton wuta a maqera ajita a masaqa.
Juyowa NURU tayi ta kalli padiman da manyan idanuwanta ta matso daf da ita harsuna shaqan juna tace"
Ko a kasuwa za'a jita ba ruwanki bane ki Kama bakinki kadaki fadawa su abal abinda zaisasu damuwa sbd padima ba ruwanki da abinda zai kawo musu bacin Rai ko damuwa.
Murmushi padima tasaki cikin isashiyar muryarta tace"
Kiji da matsalar gabanki ta zaman aikin gida da renon mijin wata Ni kibarni zanji dasu abal din naki idanma labarin yakaimusu wata Rana Dan yanxu banjin zanyi lokacin isar musu da wannan labarin inada nawa sabgogin kawai dai kishirya min komai nafada Miki gida zankoma.
Wucewa tayi ta fice daga dakin tabar NURU nabinta da kallon takaici takaici sbd halin padima dai haka yake tun suna yara saidai kwana biyun Nan datazo musu tayi tunanin tafara sauyawane shiyasa taketa kiyayewa sbd kada suyi halinsu agabansu afia subarwa kansu abin takaici.
Zaunawa tayi kan kujera tana furzar da numfashi tace"
Zanyiwa jekadi magana ta maidaki tun kafin mufara halin acikin gidan Nan tunda kinji kingani kinfasa neman lafiyar ai shikenan kije ko Dan lafiyar iyayenmu.
Da daddare har daki tasamu jekadi zata zauna jekadi tayi saurin miqewa tana cewa"
Ba girmanki bane mushrah idan kinason ganinane duk inda kike zan sameki naji bayaninki ko umarninki.
Murmushin yaqe kawai tayi sbd duk ranta a jagule yake yau din daga wannan sai wannan.
Daga tsayen ta kalli jekadi da taushin murya da zallar gajiya da damuwar komai tace"
Jekadi padima zata koma gida jibi nafadawa Mr Omar yayi muku komai na tafiyar,
Idan kunje kibata wadataccen kaso acikin wainnan dukiyar dake can na dukiyar auren......kasa karasawa tayi sbd Jin nauyin fadar kalmar aurenta
Itakuma jekadi Jin tayi shiru tace"
Yanda kikace haka za'ayi Inshallah"sbd ta fahimci abinda take fada.
Gobe ku shirya saimu fita akaiku kuyi siyayyar abinda kuke buqata.
Godiya jekadi keyi Allah yaqaro girma da kusanci tsakainki da MALEEK tareda tabbaciyar qauna.
Shiru tayi batareda tace komaiba saima sanyi da jikinta yayi ta juya zata fice jekadi tadago takalleta cikin tausayi da kaunarta saitaji bazata iyaba ta gyara tsayuwa tareda aje matsayinta na jekadi takira sunan NURUn cikin tsananin kulawa kaman yanda ta Saba a da.
Tsayawa NURUn tayi tareda waiwayowa ta juyo gaba daya damuwarta na raguwa sbd tasan jekadinta ta Da ce kafin tazama Matar maleek.
Takowa jekadi tayi tazo har gabanta takamo hannunta tajata zuwan kan kujera ta zaunar da ita kafin itama ta zauna ta fuskanceta cikin kulawa a natse tafara cewa"
NURU aure da kike gani Kona soyayyane saika dage da kulawa da naci akan wasu abubuwan sbd kusan a rayuwar aure ke mace kece zakija ragamar Kama hanyar zuwa wani mataki,
NURU kinshigo wata irin baudaddiyar rayuwar aure wadda kike buqatar juriyada kokartawa kafin kisamu matsayinki na Matar gida idan ba hakaba rayuwarki da quruciyarki zasu qare su tsufa cikin tausayi me tsanani,
Aure gidan sarauta musamman irin naki auren dayake da qalubalai da tazarori masu yawa,
Shawara daya anan itace ki maida hankali ki dage karki dage a Gina karatu kawai ki zauna kiyi nazari aurenkima kina buqatan dage Masa Dan bawa kanki suna da matsayi a gidanki sbd karki tsufa agidanki bakisan suna ko matsayinki a gurin Wanda kike aureba Dan kuwa wannan wata rayuwace da Kika shigo ba Babu fita sai mutuwa hakama akwai qalubalai agabanki Dan haka ki nutsu kiyi abinda yakamata kiyiwa kanki yaqi kema Dan tabbatarda zamanki acikin aurenki sbd auren MALEEK babban rabone agareki ki,
Kibude idanuwanki ki daina yadda da kowa da komai sai abinda zuciyarki ta nutsu dashi NURU.
Sai alokacin ta dago ta kalli jekadin jikinta duk yakuma yin sanyi ta bude baki ahankali tace"
Nagode jekadi.
Gyada Mata Kai jekadi tayi tana miqewa tace"
Ranki ya dade Zaki iya tafiya.
Miqewa tayi ta nufi kofa tana Jin gabaki daya gajiya takeji sbd sanyin da jikinta ketayi ayau din daga wannan sai wannan.
Dakin farhat ta wuce kawai sbd acan zata samu nutsuwa yanzu kawai
Tana shiga ta nufi toilet tayo alwala ta