Ubayd Maleek 1 Complete Hausa Novel

Author :  Mamuhgee Category :  Love

Chapter   6 / 37

15K to 18K   out of 110.1K words

/>
Cikin girmamawa Kai aqasa tayiwa AFIA bayanin inshallah zasuji dadin zama da NURU Kuma tana bada hkr amaimakon NURUn.

Murmushi me qayatarwa kawai afia tayi tareda cewa"

Ba damuwa ki dawo da ita dakina takwana.

Angama.

Wannan karon da sanyi tashigo dakin bayan tayi knocking ance tashigo.

Qarasowa ciki tayi ahankali ta iso har inda afia din ke zaune kan kujera tana karatu a iPad dinta batareda ta dagoba tacewa NURUn"

Ki zauna kokuma daima ki kwanta tunda agajiye kuke.

Gyada Kai kawai NURUn tayi tareda zaunawa a qasan kujera afia na ganinta batace Mata komaiba ta qyaleta sbd ganin kamar zata takurata da yawane idan tace yasake dasu lokaci daya duba da irin matsayin dasuke dashi dayasa kowa ke Basu tsananin girma dama mutum take buqata akusa da ita akoda yaushe so ko Babu sakewa atsakaninsu ba laifi tunda dai akwai mutum din.

A kan kujera NURU ta kwana AFIA da farhat dake kwana a dakinta suka kwana cikin makeken lafiyayyan gadon dakin lullube cikin bargo me taushi.

Farhat na zuwa makaranta da wuri shiyasa kusan gidan kowa yatashi da wuri sbd shirinta wannan yayi wannan wancan yayi wancan haka Shirin nata yake.

Bacci ne a idon afia sosai sbd ta Dade da daddare tana karatu Dan haka Bata tashiba NURU ce dake zaune jungum taga farhat din nata yaqin saka uniform ta taso tazo ta durqusa gabanta tareda karban uniform din tana Dan sake siririn murmushin tunowa da meryam dinta wadda Allah yasanya mata tsananin kaunar qanwar Tata shiyasa so da dama takeda son yara duk yaron data gani meryam dinta takeji cikin ranta musamman farhat datake kusan tsara da meryam din.

Ahankali tafara Sanya Mata kayan tana cewa"

Kintashi lafiya?

Kallon fuskanta farhat keyi tareda Kai hannu ta latso kumatun fuskar NURUn dakeda taushi sosai cikin murna tace"

you have a very beautiful face like my Barbie.

Duk da batasan me farhat din tafada ba yanda take kallonta da yanda ta taba fuskanta yasata sakin siririn murmushi tana shafa fuskan farhat din tace"

Lewa (you're beautiful too/kema kinada kyau/kyakkyawa)

Duk da basa wani Jin Amharic sbd mum dinsu Bata musu dad dinsu Kuma turanci ne mafi yaren dayake musu mgn dashi shiyasa Basu wani ji kakarsu ce kawai mahaifiyar dad dinsu ke musu yarensu na amheric Amma dai duk da haka tasan me ake nufi da lewa cikin murnar tasan menene NURUn ta fada tace"

Lewa means beautiful right?

Ido NURU ta zuba Mata sbd batasan me tace ba.

Kamo hannunta farhat tayi tajata tana cewa suje ta rakata cin abinci batason ci ita daya a dining.

Kamar jela haka tabita zuwa dining din saidai Bata zauna ba ta tsaya har me aikin abincin gidan dake tsaye ta zubawa farhat din abinda tasan shi takeci itadai tana tsaye tana kallon ikon Allah dayake jekadi ta Tara masu aikin gidan kaf tayi musu bayanin NURU itama daga delah take su girmamata Kamar yanda suke girmama su AFIA shiyasa me aikin me suna Fana tana gama zubawa farhat komai ta jawa NURU kujera Dan ta zauna cikin girmamawa tace"

Me za'a kawo Miki?

Kallon kujerar dining din dake zuba qyallin adon zaiba tayi tana kallon bakin Fana din kafin ta kalli farhat data kamo hannunta tana cewa"

Zanyi latti fa ki zauna.

Zama tayi a dosane tareda girgizawa Fana Kai alaman aa Bata buqatan komai.

Ahankali take taya farhat cin abinci ta hanyar Bata ruwan tea ahankali ahankali sbd zafinsa harsuka gama ta goge Mata Baki da tissue suka taso farhat har lokacin tana riqeda hannunta sbd Babu Wanda yataba zaunawa da ita tunda tafara wayo yabata abinci abaki sai yau sai hakan yamata Dadi sosai itakuwa NURU sbd tasabane da bawa meryam abinci abaki duk da tafara girma shiyasa ko yanzu tabawa farhat din musamman dataga gatan da farhat takedashi ko kwatan rabinshi Meryam batada to ai Bata abinci abaki kaman dolene ma.

Bayan tafiyan farhat makaranta saita koma daki ta zauna zaman zugum tareda fadawa tunanin rayuwarta,

Ko atunani da mafarki Bata taba kawo rayuwarta zata juya kaman haka ba daga negestati yanzu Kuma Ana maganar bauta kokuma tace Reno har wata qasa.

Ajiyar zuciya ta sauke tareda miqewa ta nufa toilet din afia din wanda badan 'yan watan nin data diba a delah ba kafin zuwanta Nan da Babu ta yanda zata iya amfani da wasu abubuwan wanka takeson Yi Amma takasa Yi sbd kada tafara jiqa toilet din AFIA Bata tashi tayi wanka ba wata qila batason wani yafara jiqa Mata toilet Dan itama a gidansu kusan haka take batajin dadin wanka idan wani yafara shiga ya jiqa bayi shiyasa kullum itake rigan kowa wanka a gidansu.

Dawowa tayi ta zauna daga Nan zaune wani baccin ya Dan dauketa sai guraren goma da rabi da AFIA ta tashi motsin shirinta yasata tashi itama tana bude ido ta tashi zaune ahankali tareda bude Baki cikin sanyin muryarta tacewa afia"

Aderiki (barka da tashi/good morning)

Kallonta AFIA ta juyo tayi tareda sakin murmushi tana qarasa Sanya dogon blue jean ajikinta tace"

Morning lewa(beautiful/kyakkyawa)

Shiru NURUn tayi tareda sakin murmushin yaqen dole sbd lewa din kawai tasani batasan meye dayar kalmar ba.

Gane batada ilimin turanci ko kadan yasa AFIA murmusawa cikin Yar hausar amhara da Bata gwanewa ba tacewa NURUn tayi wanka ta shirya suje cin abinci a dining.

Dama jira take ta miqe ta nufi toilet din tashige tareda rufowa tana sauke ajiyar zuciya.

Tana jimawa a wanka Amma dai yau ta taqaita kokuma tace daga yanzu zata ringa taqaitawa sbd yanxu ba Kamar gidansu bane datake cikin gatanta agaban iyayenta Nan Kuma a qarqashin ikon yara ma take sai abinda aka cemata tayi.

Doguwar riga purple tasaka sai qyallin sequence take ta nade gashinta da gyalen rigar ta daurasa kaman dankwali sbd cikar gashinta yasa tafi son daura gyale akan yafawa sosai tayi kyawunta duk da Bata kwalliya Sam batama taba yiba suka fito dining tana gefen afia din suka zauna Koda Fana tasake tamabayarta abinda zataci batasan mezatace ba afia ce tace kawai akawo Mata boiled veggies da kwai sai ruwan tea dinsu na gado wato bitter lemon tea me condensed milk da Zuma.

Babu Wanda yasamu damar cin abinci agidan Saida sukaci tukuna kowa yakeda damar karyawa Dan haka suna gamawa afia tayiwa NURU bankwana ta wuce school.

Yini NURU tayi adaki a kwance daga juyi sai tunani sai bacci har lokacin dawowarsu yayi farhat tafara dawowa Wanda yasa kadaicin NURU rayuwa ta jata dakinta acan ta tayata tubewa tayi wanka ta tayata shiryawa suna fitowa daga dakin AFIA na dawowa ganinsu tare yasata Dan Jin dadin ganin walwalar farhat Dan haka tace su jirata itama tayo wanka suci abinci.

Tare sukaci abinci farhat na zaune gefen NURU kusan ko yanzu abaki take Bata abincin Koda suka gama janta farhat tayi zuwa dakinta sbd tanada drowings dazatayi tana neman abokin dazai tayata iccen mangwaro akace ta zano Nan suka baje NURU na tayata cikin nutsuwa.

Sunfara Jan kwanaki da zuwansu jekadi tasaka ido sosai akan zaman NURU duk da dama ta yarda da NURUn nada natsuwar da kowa zaiso zama da ita musamman yanda su afian suka jata ajiki sosai Dan kuwa afia Jin take kaman tasamu babban aminiya yanzu qarin qaunarta da NURU shine yanda take tsananin qaunar farhat take kulawa da ita Dan kuwa yanzu kusan itace ke Shirin farhat na zuwa makaranta.

Ta bangare daya ita kanta AFIA yanzu kusan komai fadawa NURUn takeyi Bata iya riqe bakinta idan suna zaune Jin takeyi kaman ta amayo Mata dukkanin damuwar data shiga da yanda iyayenta suka rabu Amma tana riqe kanta sbd sirrin iyayentane saidai kusan duk wani abu yanzu NURU tasani akansu musamman labarin dad dinsu da tsawon lokacin Nan bai dawoba saidai kullum suna waya dashi bama Kamar farhat da yagama haddace sunan lewa abakinta Dan qiri qiri suka maida sunanta lewa.

Abu dayane matsalarsu da ita gurin fira rigima sukesha sbd batajin turanci ko kadan sukuma yaren bai kamasu ba shiyasa idan suna fira sukeshan dariya sbd wani abin kafin tagane kwatancen kurame sukeyi da ita.

Ganin komai inshallah yayi yasa jekadi tattarawa Takoma tabar NURU da kewa saidai tayi Mata alqawarin ringa zuwa dubo Mata iyayenta akai akai tana bugowa tafada Mata.

##MAMUH#

_ZAFAFA BIYAR_๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–

_Alkiblah--SAFIYYAH HUGUMA_

_Makauniyar qaddara--BILLYN ABDULL_

_Dalaal--MISS XOXO_

_Mabudin zuciya--HAFSAT RANO_

_Ubayd Maleek--MAMUH GEE_

_DUKA KUDIN WANNAN DADADAN BOOKS DIN SUNA KAN FARASHIN NERA 700. WATO KUDIN PAGES KENAN. DOCUMENTS IDAN AN KAMMALA SUMA KUDIN SU DABAN.._

ฦŠaya___300

Biyu____400

Uku_____450

Huษ—u____500

Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

*_08085405215_*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

ย  0903ย 234ย 5899[9/6, 6:12 PM] Anty Rabi'at: *_Mamuhgee 9_*

Sun Dade a can Saida afia taduba agogo taga lokacin fitowan dad dinsu yayi yasata aje karatun tana kallon NURU data dage tana kallon dabbobin duniya wainda wasu batama taba sanin akwaiba bare ganinsu sai take kallon abin cikeda mamaki da burgewa fuskarta ma ta nuna hakan

Afia ta dafa littafin tana cewa"

Ma'am Muje saikuma gobe mudawo ki Dora daga inda Kika tsaya.

Murmushi NURU tasake tana cewa"

Inason sanin sunayensu duka.

Karki damu ko farhat zata koya wannan yanxu dai muje inajin yunwa.

Fitowa sukayi NURU nasake wanyewa da qaton gidan sbd saiyau tun zuwanta ta fito ta zagaya cikinsa AFIA kuwa sai sake Mata bayanin komai takeyi tana nunnuna Mata.

Suna shigowa MALEEK UBAYD na gab da shigewa dining room tareda farhat dake gefensa cikin sauri AFIA tace"

Dad NURU na gaidasheka.

Jin haka yasa NURU saurin durqusawa muryarta na rawa tace"

Barka da fitowa cikin yarensu sbd a rikice take batasanma wane kalar yare shi yakejiba ko yake amfani dashi.

Batareda ya juyoba ko ya tsaya ya daga Kai tareda qarasa shigewa yana fiddo hannuwansa dake zube cikin alhijun qananan kayan dake jikinsa na _Stuart weitzman_ dark blue dasuka fiddo hasken fatarsa da asalinsa.

Miqewa NURU tayi kanta aqasa ta nufi hanyar qarmin Palo dazata Kai dakinsu ta shigewarta Dan tasan bama abune me yiyuwa cin abincinta dasu afia ayau.

Itama afian bayan wucewan NURU Bata damu da cewan tazo cin abinci ba sbd ba abune me yiyuwaba cin abinci a table daya da maleek ubayd idanba su 'yayansaba to saidai matarsa ko iyayensa ko 'yan uwansa akwai wainda baya yiyuwa cin abinci table daya dashi Dan haka ta wuce dining room din tareda kallon Fana tace idan tagama serving dinsu ta hada abinci a tray akaiwa NURU daki.

Sunci abinci sungama yakoma sama inda suka bisa suka zauna palonshi Dan Basu lokacinsa na magana Jin idan da akwai wani abin saidai duk Rabin zancensu na NURU ne Wanda yasashi mamakin irin shaquwan qanqanin lokaci dasukai da qaunan dasuke Mata Wanda yasashi Jin ai shikenan tunda sunsamu wadda suke so yanxu yasamu Daman kansa tunda inshallah hakan ya nuna ba damuwa yanxu ataredasu musamman AFIA dama ita farhat tuni Bata damu da tafiyan mum dinsuba sbd batasan me hakan ke nufi takamaimaiba.

Koda afia tashigo daki NURU na sallan la'asar itama toilet ta wuce Dan alwala.

Ahankali ahankali Afia tafara saka NURU sakewa dasu sosai tana dariya yanxu acikinsu,tana iya kwanciya akan akan gado daya da afia tareda farhat a tsakiyansu wadda itama shaquwanta da NURUn ya ninku fiyeda farko.

Duk wani aikin gidan ahankali tafara sabawa da saka hannunta musamman bangaren girki da sosai take tayasu Dan tana son iyawa hardai bangaren baking hakama gyaran dakinsu Dana farhat tuni ta karbe itakeyi sai hakan yasake janyo Mata qauna da masu aikin,

Duk wannan hidimar datakeyi a gidan bata sake hada hanya dako inuwar dadynsu ba bare ganinsa dama idan Yana Nan masu aiki basa wilgewa to dama ita tasan Babu wani banbanci matsayi tsakaninta da masu aiki shiyasa itama idan Yana gida tana daki ko library gurin karatun da afia ke koya Mata Wanda ba laifi tana Dan fahimta.

Ahaka lokacin yaqara cigaba da ja sosai tuni sauyi yashigo rayuwarta ta sauyin jiki da lafiya tareda fara ilmantuwa Dan kuwa turanci yanzu kaman yaqi haka take gwamadawa suna dariya ita dasu musamman idan tanason bada labarin Abu to ko Yaya yazo watsoshi takeyi ganin hakan yasa AFIA yanke shawaran yiwa dad dinta maganar son asaka NURU makaranta Dan ita dake koya Mata yanzu karatunta yafara daukan zafi tana buqatan maida hankali.

Lokacinda tayiwa dad din maganar Kai tsaye yace tafadawa Omar babban amintaccen yaronsa.

Aikuwa tana yiwa Omar waya Babu Bata lokaci aka nemawa NURUn admission a wata school dake kusa datasu farhat inda zata fara daga farko.

Da farko taso zamewa zuwa makarantar sbd ganin kaman samun damar yayi yawa saida afia ta takura Mata tareda Bata qwarin gwiwan yin karatun tareda kwadaita Mata future me kyau na masu ilimi.

Ranar farko data fara zuwa daqyar ta iya bawa kanta qwarin fahimtar kalmar da ake fada Amma haka tadawo Bata wani fahimci komaiba shiyasa a salube tadawo driver na ajeta tana shigowa daki ta wuce ta zube kan gado kife tana sauke ajiyar zuciya tace"

Afia zakuyi hasaran kudi ne kawai banasaka ran kaina zai iya daukan karatu irin wannan.

Koda aka dauko farhat daga makaranta tana dawowa taga NURUn da gudu tayo kanta tana cewa"

My Lewa 'yan makaranta.

Dariya kalman tabawa NURU ta jawota tana zare Mata school bag daga bayanta tana cewa"

Farhat lewanki kanta a toshe yake kidaina murna ma tun wuri.

Kumatun NURUn dakeda laushi suke burge farhat ko yaushe su farhat din ta matsa tana cewa"

Lewa bazatayi kyan banza ba zata zama me qoqari nasan wata Rana lewa zata zama abin mamaki.

Murmushi tayi tareda kissing goshin farhat din tana cewa"

Kinada yadda sosai haka akan zan iya?

Yes beauty Zaki iya daddy ma zai jinjina Miki sbd qoqarinki zai siya Miki duk abinda kikeso sbd daddy nason me kokari a school sosai.

Murmushi kawai tayi tareda Jan hannunta zuwa daki Dan tubewa ayi wanka.

Suna dining taba bawa farhat abinci Afia tadawo da sauri ta aje jaka ta qaraso tana cewa"

Fana ki kawo mun cheese cream zanci abinci dashi.

Cikin kulawa take kallonsu bayan ta shanye cup daya da juice tace"

NURU ya school da Dadi ko?""taqarasa cikin tsokana sbd Babu wani alamun school yayi Dadi atareda NURUn.

Kallon afian tayi tareda 'Bata kyakkyawar fuskarta tace"

Kiyi dariyanki kawai afili.

Dariya afia tayi tana fara cin pasta salad tace"

Sorry babe Zaki sabane ahankali.

Suna gama cin abincin suka koma daki farhat na Taya NURU fahimtar karatun da akayo Mata afia na dariyansu har lokacin sallan la'asar yayi sukai sallah me karatun addinsu yazo Maheer asim suka fito zuwa libry inda acan yake musu karatun.

Sai dare bayan tagama komai ta kwanta tafara tunanin gobe ya zata Kaya Mata a makarantar Kuma da haka bacci ya dauketa asuba nayi ta farka tayi sallah ta tadasu sukai sallah itakuma tahau ayyukan data Saba tareda Shirin abincin farhat qarfe bakwai tayi wanka tazo tasake tadasu bacci sukai dakin farhat akai wanka ta shiryata cikin school wear itama tadawo daki tashirya qarfe takwas suka gama Shirin suka zauna cin abinci 8:10 driver yadaukesu yakai kowacce makarantarta ya ajiye.

Yauma kusan abin da wuya Amma dai sbd saka Rai sai Bata damuba Kamar jiyan data dawo gidama haka afia ta ajeta tana sake maimaita Mata karatun tun Bata ganewa har abin yafara warware Mata tana ganewa har a school dinma sbd kusan tafi kowa girma acikin makarantar Dan kaman primary ce afia kuwa kaman a secondary take ita.

Tun karatu nabata wahala sbd rashin sabo da nauyin da yake Mata hartazo tafara ganewa ta maida himma sosai tareda nacewa karatu saigashi yanzu batajin wahalarsa Sam ahaka har lokacin exams yayi cikin ikon Allah kuwa taci exams din suka Bata Daman wucewa makarantarsu afia Amma aji daya maimakon aji uku da afia take wato last year dinta wadda daga ita sai University.

Dan hutun dasuka samu yabata Daman waya da iyayenta a waya ta hanyar jekadi Wanda yasake faranta rayuwarta tareda sake kwantar Mata da hankali musamman dataji meryam da padima wadda yanzu ruwan soyayyarsu da amed yafara neman qafewa sbd wasu abubuwan.

A 'yan kwanakin dad dinsu afia na gida Dan haka yanzu ta daina fitowa iyakacin hayaniyarsu a dakinsu ne kokuma a dakin farhat dasuke Zane zanen drowings sbd farhat na tsananin son Zane.

Wanka tafito bataga afia data Bari tana waya da mahaifiyar dad dinsuba ta nufi gaban mirror tana goge jikinta da ruwa ke gangarowa sbd tsantsin fatarta tana duba lokaci tasan suna can sama gurin dad dinsu ta shirya cikin doguwar riga straight designer ta _Alexender McQueen_ wadda taje straight ajikinta ta dauro wata hula Mara nauyi da Bata rufe kanta dukaba sbd tai Mata kadan ta fito ta nufi kicin Dan kamawasu Fana aikin abincin dare.

Sanin suna palon sama tareda dad dinsu yasa tabiyo ta babban Palo sbd hango kaman mum Sarah a palon.

Shigowa tayi gabaki daya palon hankalinta na kan hanyar shigowa da aka bude wani kyakkyawa yashigo sanye da suits farare tsayawa tayi cak tsakiyar palon tana dauke Kai daga kallonsa shikuwa cikin wani irin kyakkyawan murmushi yake kallonta cikeda mamakin wacece wanna agidan yabude Baki zaiyi magana sukaji taku abayansu cikin nutsuwa da Kamala

Da sauri ta juyo daidai Yana isowa daf saura kadan kirjinta ya daki nasa tayi saurin durqusawa qasa zuciyar ta harba da qarfi

Shikuwa kanta dake qasa ya kalla kadan da fararen idanuwansa kafin ya raba ya wuce Jin muryan farhat daga bayansu tana ihun ganin _IMRAN_ NURU na ganin hakan ta miqe da sauri tabar gurin numfashin na kasa daidaituwa dole daki Takoma Dan bazata iya zuwa kicin ahakaba zuciyarta na irin wannan harbawan sbd tsoro

Shikuwa Imran bayan NURUn yabi da kallo cikin basarwa da ya kamo farhat dake tsallan murnar ganinsa tana cewa"

Uncle Imran yaushe kadawo?

MALEEK ya kalla cikin shiga nutsuwa da wani irin kwaijininsa daya cika idanuwansa yace"

Barka da yamma MALEEK.

Zama yayi a kujeransa da Babu me zama Yana amsawa ahankali tareda miqa Masa hannu ya miqo Masa takardun

6 / 37