Dan Minister 1 Complete Hausa Novel

Author :  Mrs Nashe Category :  Love

Chapter   8 / 12

21K to 24K   out of 35K words

ta kwana aciki ammafa du da nace yanzu in ta min lefi na Dena kulata ammafa du ranar da ta kaini bango nako gaji da abinda take min wlh se na bata mamaki itama kija Mata kunne tanena shiga har kata

Shuru Hajiya Fatima tayi azuciyarta tace alhamdulillah komai yakusa zuwa karshe insha allahu

Yace mommy yanaga kinyi shuru ko abinda nace be mikiba

Tace yamin Mana nabil bakomai kana kwana adaya dakin Allah yaimaka albarka Allah yadada shiryamin Kai itama shatuwa Zan sameta nai Mata fada sosai akanka Suma su Amina du za su Dena yima abinda suke maka maza tashi Kai wanka muje muci abinci tare

Dadine yakamashi yahau murna yace ngd mommy wlh yau kin sani farinciki Ashe dai kina Sona da gaske bandaki yashige yana ta fara,a yau mommy Bata Bata Mai raiba

Yau shatin shatuwa biyu agidan minister bakaramin hakuri nabil yakeyi da itaba ko Hajiya Fatima shedace gawata tsanarta minister da nabil suke dada nunawa Hajiya Fatima Jin dadinta yanzu nabil bayashiga harkar shatuwa tin ranar da tamai nasiha akanta shine bekara kulata sunyi fadaba yadan rage kadan daga cikin halayanshi ko Yan aikin gidan suma sunsan nabil yacanja Akan da har mamaki suke itadai Hajiya Fatima har yanzu tana kai kukanta awajan Allah akan Allah yadada shirya Mata shi yakuma dedaita tsakaninsu da shatuwa Dan in nabil yafara San shatuwa minister ze hakura da akidar da yasawa ransa Akan shatuwa Amina ma na iya yinta Kan shatuwa Babu lefi tadan rage wani abin Hajiya Fatima Kiran yaranta na kasar waje tayi taimusu nasiha Akan nabil su jashi ajiki sosai Dan yacire zargin da yakeyi akansu amina ma yanzu tadage wajan Jan nabil ajiki tana nuna kulawarta akansa tahaka itama take samu take bashi shawarwari cikin dabara Kuma alhamdulillah Yana dauka hakan yasa Hajiya Fatima cikin farinciki du wannan bidirin minister be saniba musamman ma kwanannan da aiyuka sukai,mai yawa nabil yanzu Yana Jin dadin yanda Yan uwasa Mata da mahaifiyarsa suke nunamasa so da kulawa basa Kuma numa suna kinshi saboda halayanshi

yaune baffah yazo da me gyaran karaya Dan yaga ya hannun shatuwa ko ta warke Kuma shima yaga irin zaman shatuwa da nabil me gyara yakunce daurin da ke hannun shatuwa alhamdulillah gyara ya gyaru dayake me dorin kwararrene

baffah yakebe da Hajiya Fatima da Amina Akan yaji Yaya zaman nabil da shatuwa da Kuma halayansu ko sun gyaru su Hajiya Fatima sun Masa bayani Akan nasarorin da aka samu baffah yaji Dadi sosai se dai sum masa bayani har yanzu shatuwa Bata Dena tsokanar nabil ba Dan Haka yakara jamata kunne ta dena yakuma ji Dadi da akasamu yanzu tanajin mgnar Amina shi Kuma nabil najin mgnar Hajiya Fatima

Baffah bayan ya sallami me gyaran karaya shi be tafiba se da yajira dansa minister yadawo wajan yamma sosai yadawo se dadandare suka samu Zama tare yace to sani nadawo Akan bakata na acikin gidajanka kazabi Daya kabawa nabil yatare da matarsa Kuma gobe gobe nakeso subar gidannan tinda matarsa ta warke su koma saban gidansu Dan su samu fahimtar juna sosai Kuma du wani Kayan dakin shatuwa Kaine nake so kadau nauyi gaba,daya saboda Kaine yanzu ubanta Kuma befi karfinkaba Dan Haka bazan bar garinnan ba se Naga sun tare Naga gidan da suke ciki

Gumine yafara ketuwa minister yace baffah Daman da gaske kake ba anan gidan zasu zaunaba yanzu in na basu wani gidan nasan me zatayiwa nabil na cutarwa ga wannan kakar tata Mara mutunci Kuma ai yarinyar tana da uba ai shine ze Mata kayan daki wlh Ni da nabil na Santa ko nawane Zan iya kashe Mata Amma gaskiya yanzu ubanta yai mata

Baffah yace Kai wato har yanzu baka sadudaba baka yarda da kandaraba shifa aure nufin Allah ne Dan Haka kabi ahankali ba aja da irin aurannan Dan bakasan me Allah yake nufiba akan nabil da shatuwa Dan Haka Kar na kara jin ka kushe Masa Mata da zaman auransu Kuma dolene kayi abinda nace ko ranka yabaci ba zanbar garinnanba se Naga komai yayi dedai yanda nake so

Haka minister ya yarda badan ransa yaso ba gari na wayewa minister yakai baffah gidan da yaginawa nabil tin kan yagama makaranta Daman ya ajje gidanne amatsayin Daya daga cikin manyan kyautintika da ze Masa ranar auransa gidane nagani na fada ankashe nera wajan ginashi haka minister yazubawa shatuwa da nabil dukiya ko Mai na zamani me tsada yazuba musu Amma Yana bakincikin ba matar da nabil ke so bace zatayi rayuwa agidan baffah yayi faranciki da yaga bajintar da minister yayi

su Amina ne Yan raka amarya gidanta aikuwa taci gyara Amina da Hajiya Fatima sunyi kokari Dan ko mahaifiyata se dai haka wajan gyarata Dan su sun san da mgnar tarewar Dan Haka tin kan lokacin yazo sukai Mata du abinda yadace na gyara

ango nabil be San da mgnar tarewaba se yau da aka,kai shatuwa baffah da Hajiya Fatima suka zaunar da shi suna Masa nasiha me ratsa zuciya akan zaman aure da kula da matarsa suka Kuma Gaya Masa yau zebar gidan yakoma saban gida yaso yaki yarda Amma da yatina da kukan farinciki da Hajiya Fatima tayi akansa na yafara Jin mgnarta se jikinshi yamutu Kuma gashi yanzu Yana Jin dadin Zama da ita da Yan uwansa Dan Haka yace to baffah da mommy du naji Kuma zanyi aiki da abinda kukace Amma baffah yarinyar na kaini bango sosai wlh darajar mommy takeci Kai Mata fada tadena Kar na fusata Dan bazatai kyauba in da ta daddy zanbi da tini tana gadan asibiti

Baffah yace karka damu du nasan komai Kuma na Mata fada bazata kumaba har Yan aiki du sani yazuba muku Allah yai,muku albarka tashi muje Ni zanma rakiya har gidanka daga Nan Ni zan shige garinmu in da nafi wayo kaga Kenan nine babban abokinka na rakoka saban gidanka

Dariya dukansu sukasa Hajiya Fatima da baffah sunji Dadi sosai da nabil be yimusu kardamaba Akan abinda suka fadamasa yabasu mamaki sosai haka baffah yarakashi har gida yahadasu yai musu nasiha sannan yashige mazagai

Minister besan nabil ya yarda da mgnar tarewarsu ba yasan nabil ba ze yardaba murna yai tayi yasan in nabil yaki yarda Dole baffah yahakura da mgnar Dan Haka ko mgnar bewa nabil ba yai ficewarsa wajan mitin se bayan dawowarshi yake tambayar Ina nabil Hajiya Fatima take gayamasa ai nabil yatare a saban gidanshi baffah nema yarakashi wajan matarsa ran minister yadada baci Dan bahaka yasoba mamaki yafara yaakai nabil Yayarda Kuma ko kiransa beyi yagaya masaba

Bayan tafiyar baffah kallan kallo suka tsaya yiwa juna shatuwa harararshi Tai tayi da murguda Baki shi abinma dariya yafara bashi kwafa yaja me karfi sannan yatashi yashige dakin da yake azaman nasa itama dakin da aka nuna Mata azaman nata tashige da kudiri kala kala aranta

Amina ta nemi malama mace me koyawa shatuwa karatu na boko da arabiya gidan Amina malamar take zuwa kullin Amina take sa ake kawo shatuwa gidanta ana koya Mata karatu da abubuwa da dama na rayuwa Amina tayimakin kokarin shatuwa na yanda ana koya Mata Abu take rikewa ban garan girkima Babu lefi tana Mai da Kai wajan koya

yanzu Babu lefi ta rage tsokanar nabil ba kamar Daba Amma har yanzu in tana jin tsokana tana tsokanoshi sedai shi yanzu yanayi ne kamar be gantaba rashin tsorone na shatuwa Amma yanda yanzu nabil yake hade Mata fuska Babu alamun Wasa ko faa,a a fuskarshi Dan karfin Hali irin na shatuwa Haka take tsokanarsa shikuma da kudirin da yayanke akanta na yin maganinta ko da sau dayane

Yau iya ce taje har gida tasamu baffah ta tubure masa Akan se ya kawota wajan shatuwa in bahakaba ta kaishi Kara wajan hukuma akan yakai jikarta garin Yan gayu gidan Miss Miss yasiyar da ita

Tace usuman tinda jikata tatafi Basu taba kawota ganin gidaba Kuma naba aminaina labarin kalar garin da danka da jikanka ke Zama da kalar gidan da suake ciki Dunn Basu labari shine suka fadamin danka na yankankai Kuma na yarda da maganar su Dan inba hakaba ta Ina ze Tara wannan uban kudin sun tambayeni aikin me yake Acan na gaya musu mukamin Kiran mage gwaunati tabashi ko acanma garin miss miss ake kiransa da shi Dan Haka yau wlh bazan yi hakuriba se munje tare da Kai na gano ta ashiryena nataho kaga har da kayana nataho Dan Haka daga Nan se gidan miss miss Dan tinda naji shuru nasan dandaudu da miss miss sun karasa min ita ta karasa mgnar da Kuka

Shi baffah dariya ma ta bashi yace iya ikwan Allah sarka me rikicin gangan kakar nabil da shatuwa sirika awajan alhaji sani me mukamin Miss Miss Nima na dan taba yakuma sa dariya to kiyi shuru ki Dena kuka Bari nasa wani daga cikin jikokinmu ya kaimu amotar,sa Amma aminannan naki sun iya Baki shawara me Kyau Ni Dan Allah kiyimin shuru tin da mun fito waje Kar ki taramin jamaar gari ga motanan shiga mutafi

Se da iya taga da gaske wajan shatuwa za a kaita sannan ta Dena kuka da ruwan masifa daga bayama baccine ya kwasheta amotar kafin sukai baccinta Tasha har da munshari baffah shi dai dariya yake ta mata seda suka Kai Abuja baffah ya tasheta

yace munzo tashi mu shiga

Baki ta washe tafito suka shiga gidan minister baffah yasa aka Fara kaisu

minister na zaune aharabar gidan Yana Shan iska Babu zata Babu tsammani yaga baffah da iya ko kadan be yi murna da zuwan iya ba Rai yahade yai kamar be gantaba baffah kadai ya gaisar

Aikuwa dawa Allah yahadata inba Shiba tace ai Dole ka dauke Kai kayi kamar baka ganniba ka hade Rai tinda kun siyarmin da jikata kun kara Akan kudin da kuke dashi Ina Dan kwal uban Dan naka me zamanman wando me gashi kala biyu muje ku kaini inda kuka sai da ta na karbo jikata in bahakaba na tara muku mutane wlh

Shadai baffah na gefe beyi mgnba

Ana Haka Hajiya Fatima tafito saboda Jin hayaniyar da taji taganin iyace da minister tace ashedai kunnena be jiyomin karyaba Daman nace iyace dasauri takarasa wajan tahau bawa iya hakuri tace haba iya Dan Allah kiyi hakuri be Kai hakaba Yan zudai shatuwa kike San gani ko

Iya tace indai suna da gaskiya anunamin ita Dan naji usuman nace min wai shatuwa Bata gidannan Ni ko saurararshi ma banyiba Dan nasan me ze fadamin an sai da shatuwa Dan Haka Ni ko cikin gidanku bazan shigaba se ankaini na karbo jikata in yaso shi Miss Miss din yasan yanda zeyi yamai da musu da kudinsu tinda bani naciba

Hajiya Fatima tace ikwan Allah Yanzu Dan Allah inba rigima irin takiba iya Wai shatuwa kike nufi alhaji da nabil sun sayar da ita se kace wata Yartsana Kinga muje ga direba can nasa ya kaiki gidan shatuwa ki ganta tananan lfy Ni Zan shigar Miki da Kayan

Baffah yace Ni nasha ciki Fatima se kun shigo in kingama raban rigimar iya kushigo tare ta huta

Ai baffah nashi iya tadada burkicewa dole hajiya Fatima tasa direba yakaita gidan shatuwa

Hajiya Fatima nashiga ciki bayan sun gaisa da baffah yake tambayarta ina it's

Tace ai Taki yarda mu shigo tare Dole se da nasa direba yakaita gidan nabil taga shatuwa

Baffah yace Fatima kinyi ganganci kin sanfa halin iya in nabil nagida se tayi abinda Dole se ya kulata danma ansamu yanzu yadan yi sanyi Dole yanzu mubi bayansu tinda bamu San me ze faruba

Hajiya Fatima hijabi tadauko tasa suka fito ita da baffah zuwa gidan nabil baffah kallan inda minister yake zaune yayi ze Masa mgn sun tafi gidan nabil se yaga Babu minister awajan zamansa

Baffah yace to shikuma sani Ina yaje Fatima ko dai yashiga ciki ne

Hajiya Fatima tace aa baya ciki Dan Banga shigarshi a

Hajiya Fatima direba takira take tambayarsa ko yaga minister

direban yace ai hajiya naji Yana cewa Musa direba yakaishi gidan yallabai nabil

Salati hajiya Fatima tafara tace shikenan baffah za akuma yakin badar alhaji yabi bayan iya kenan

Baffah yace Daman abinda nake gudu Kenan muyi maza mu karasa Kan ta kwabe

Hajiya Fatima tace ai nima se nakira Amina munhadu Acan Dan itace me iyawa da shatuwa yanzu

Kiran Amina hajiya Fatima tayi awaya tace Mata su hadu agidan nabil Amina tayi mamaki tinani tafara ko lfy

Direban na Kai iya gidan nabil tinda ga kofar shiga falansu tafara Jiyo muryar shatuwa tana ihu da kara nabil ne yamurde Mata kunne tana ta Kara Dan azaba yau takaishi bango Dole se da yakulata Miyar kubewa tayi tazubo akwano tataho falo da ita Dan tsokana nabil na zaune Kan kujera Yana kallo tazo ta juyemai miyar ajiki shikuma saboda bacin Rai ya kwace kwanan yai cilli da sauran miyar da tarage akwanan tazube awajan kofar shigowa Dan bacin Rai nabil yarasa wana hukunci ze Mata Yana rike da kunnanta yaki yasaki Daya hannun yasa ya dauketa da Mari har sau uku zafin Marin yadada gigita shatuwa takurma wani mahaukacin ihu

Tace waiyo iya ze kasheni kizo ki temakeni

Habawa iya najin Haka tace Ashe gara da nazo dawuri da ban zoba da ankashemin ke

dube dube tafara aharabar gidan wata doguwar sanda tagani ta dauka tashiga gidan da ita Allah yasa ta kula da miyar da ke zube akofar falan Amma Bata kula da sauran da ya ballatsu acikin falan du yabata waje dadama lokacin da tashigo lokacin shatuwa tasamu takwaci kanta daga wajan nabil tazuba dagudu shikuma nabil wayar T.V yacira yabita da ita ze zaneta zagaya falan suka hauyi dagudu ga shatuwa da shegen gudun tsiya kamar taci kafar kare

Ai iya itama Babu Bata lokaci tashigarwa shatuwa tabi bayan nabil da gudu abin dariya gudun nata saboda tsufa dakyar take gudu tana bin bayan nabil da sanda zata kwala Masa shikuma nabil bema San iya na binshiba Dan be kula da itaba daga shi har shatuwa Babu Wanda yakula da shigowar iya

Dedai Nan motar minister tashigo gidan nabil ihun shatuwa da iyi yajiyo ai ko motar bebari ta tsayaba yafito yashiga cikin falan cikin zafin nama Yana masifa shikenan sun hadu zasu kashemin Dana kwaya Daya da nake dshi namiji

ai kokarasa sauran mgnar da ke bakinshi beyiba yasa kafarsa cikin falan Kan miyar kubewar da su nabil suka zubar minister Babu zato Babu tsammani yaji anyi sama da shi andawo dshi kasa damm Dan azaba minister Kara yasaki yayi yayi yatashi tsaye yaje ya temaki nabil amma yakasa ashe yazamu gocewar kashin hannun shi na hagu ga Kuma yatsun kafarshi guda biyu da sukaji targade

Su nabil gudu suke suna ta zagaya falan iya na ta binsu abaya taga minister azaune ai bashiri tayi kansa

tace au Ashe kana gidan kana gani me zamanman wando ze kashemin jika bakayi mgn ba kaiwa danka mgn yabar min jikata Kar yakuma sata Kuka au baza kayi mgn ba ko to Bari nafara kwadamaka inkaji zafi kayi mgn

takarkarewa tayi tadaga sandar sama ta sakarwa minister ita abaya Kara me karfi minister yasaki Dan Safi

tace Kai Mai mgn yabarta ko na karama

minister mgnar ma yakasa dada daga sandar tayi takuma sakar Masa abaya

ai besan sanda yace nabil kabar Mata jikarta Dan Allah kayi hakuri zata karya min baya matarnan shegen karfin tsiyane da ita

Karar shatuwa du tacika falan shi nabil ma bejiba be kula da minister ba har yanzu bare iya dagudu sukayo wajan su iya alokacin Nabil yasamu yafara zubawa shatuwa bulalar ajiki saura kadan ayi tafiyar ruwa da iya nabil Ido yarufe yazubawa iya wannan wayar T.V itama ajiki lokaci guda iya tacika wajan da Kara Dan tsabar rudewa rasa inda zata shiga tayi Kai kanta wajansu takuma yi wajan guduwa yakuma dagawa yazubawa iya ajiki shi du ya dauka shatuwa yake zanewa saboda idanshi yarufe da zafi yakuma ruda iya tai hanyar waje dagudu tsutsayi Tai Kan cikin miyar kubewar Nan se jitayi anyi sama da ita tadawo kasa rimm wani marayan ihu tasaki ko mutsin kirki takasa tana kwance male,male cikin miyar kubewa garama minister shi yayi karfin Hali azaune yake Yana jinyar kanshi

Ana Haka motar su baffah da Amina tashigo gidan ihun da sukaji nafitowa daga cikin gidan gamasu aiki du awaje sunyi jugum,jugum suna,jin abinda ke faruwa aminace Tai saurin shiga ciki taci Karo da iya da minister ahanya

ihu tasaki tace su mommy kuzo kuga ikwan Allah yau abin nayine gasu iya da daddy anshemesu kushigo ahankali yau abin yayi zafi miyar danyan kubewace azube duka afalan

Cikin dabara suka samu suka shigo wajan dakar suka rabasu suka rabu Hajiya Fatima tarike hannun nabil Taki sakinshi Amina itakuma tarike shatuwa jansu sukayi suka zaunar da su Akan kujera Suma suka zauna

Kuka Hajiya Fatima tasa tace nabil kakaryamin alkawari ko yanzu kunga danyan aikin da kukayi ku kalli iya da alhaji du kun dokesu da bamuzoba kashe kanku zakuyi da Allah be kawomuba

Se lokacin nabil yaga minister da iya Hakuri Nabil yai tabawa Hajiya Fatima kukan da take Yana dada tadamai hankali Yana dada Jin tsanar shatuwa aransa

Shatuwa tace lah iya yaushe kikazo har da daddy

Baffah yace yimin sharu ta Ina zakusan sun zo kun shiga filin dambe Ni yanzu babu wata nasiha da Zan Kuma muku Dan ko karatune yaci ace kun dauka Dan Haka nagama yanke hukuncin abinda yadace Dan Haka yau nayarda iya muzo tare da ita taga jikarta Ashe daraban abinda ze faru Kenan

Yakalli su minister da har yanzu sun kasa motsi yanzu ai kunga abinda nake gudar muku gakunan da alama du kanku kunji ciwo ajiki kadan ma Kuka gani Kar kuyiwa kanku fada Kar kuyi kokari kuhada Kan yarannan se ku tashi mutafi gida

Iya tace wlh usuman karfin siyane da jikanka Ina ganinshi kamar kajin turawa bawani karfi zeyiba Ashe ba daganan takeba Kai me zamanman wando me ka dinga shaudamin ajiki wace irin bulala kayi anfani da ita ta fashe da Kuka

Amina dariya takewa iya

MINISTER Dakar aka kamashi yatashi tsaye akasashi amota iya Kuma aminace

8 / 12