Babu a idanta burinta kawai itama ta rama abinda yai mata jitayi takara tsanar nabil azuciyarta takuma dau alkawarin se ta dau fansa itama se tabashi wahala
Amina bangaran nabil tamai da shatuwa ta zaunar da ita itama Zama tayi kusa da ita tace haba shatuwa yakike,yin Haka bakiji fadan da baffah yai mikiba ko in har bakya,bin abinda baffah da mommy zasu fada miki Zan Dena kulaki Nima tinda nasan Nima bazakiji nawaba yanzu Dan Allah wace irin kwalliyace wannan afuskarki karki Kuma mu anan ba a irin wannan kwalliyar in kayi mahaukaciya za a dauki mace Zan koya Miki irin kwalliyar da Zaki nayi afuskarki Kar na karaji kin kula nabil Kuma kome zemiki Kar ki kulashi mijin,kine
Shatuwa tace to aini tin Ina yarinya baamin Abu ban ramaba in ban ramaba har bacci kasawa nake Kuma Iya tace karnabi fadan da baffah yai min Dan shima dandaudun baji zeyiba Kuma Ni iya itama tamin fada irin nata Kuma Ni Dole nabi fadan da iyata Tai min Kuma nata fadan yafi tinda cewa tayi du abinda yaimin narama Kar na raga mishi tace bashi da mutunci Kuma Ni gaskiya bazan iya kin bin mgnar iya ba kowadai acikinku zanji nashi in yamin Kuma Zan na aiki da kowanne kiyi hakuri Ina sanki karki Dena zuwa wajena Dan Allah
Shuru Amina tayi se da tagama tinani sannan tace naji shatuwa Allah yashiryeku se mgnar kirki kin iyako
Baki tawashe tace eh na iya sosai makuwa
Tace to zaayo Miki siyaiyar du abinda yadace na Kayan abinci in kin warke in Zaki koma saban gidanku ke da nabil se kifara girki yanzu anan mommy ce zatana sawa ana kawo Miki har kiwarke yanzu kije ki wanke fuskarnan Taki kiyi alwala kiyi sallah naji ankira Nima Bari naje nayi
Nabil dakin alhaji sani yashiga yaje yakwanta Dan shi abin ya zamemishi kamar Al,Ada in aka batamishi Rai dakin mahaifinshi yake zuwa ya kwanta ko yashiga yazauna har yahuce Zama yayi Kan kujerar da ke dakin se furzar da numfashi yake afili yace senayi maganinki yarinya yanda in kin ganni ko gaba zakina guduwa
Minister ne yashigo dakin Yana ganin nabil yasan ranshi abace yake dasauri yakarasa wajansa yace Kai dawa nabil badan tin abinda baffah yai maka bane kake fishi baka huceba nacema ai Zan rarrashi baffah yahakura ka saketa har mazagai zanje na rokeshi jira nake akwana biyu tukunna Nima kaina wlh basan yarinyar nakeba gakuma wannan maramuncin tsohuwar Nan tata ai Dole murabu da mugun iri nidai nafadama kaganawa yarinyar azaba karka taba raga Mata da kanta zataje tasamu baffah tace yasa ka saketa kome Tai maka karka barta kai Mata abinda yafi Wanda tai maka kaji ni nasaka
Nabil yace ai du abinda kace,min nayi du senayi daddy har dama Kari yanzu yanzu kaga me ta min mommy ce ta hanani hukuntata da se ta Raina kanta
Minister yace kamin dedai Dana Ni wlh narasa me hajiya Fatima take nufi da Kai kullin Bata goyan bayan abinda kake yi Ni ma kaina mijinta Bata goyan bayana yanzu abinda nake so da Kai ka kwanta ka huta kafin zuwa anjima in kanasan kudi ma ka iba in katashi
Minister wajan hajiya Fatima yaje ya sameta yace Fatima yanzu Dan Allah meyake da munki kekuma haka kike bakya kishin danki da mijinki kowama yatakasu badamuwarki bane Ina Yar sadakar da akabawa nabal dan kaniyarta nemanta nake me nabil yai Mata tabata Masa Rai ke Kuma da yake basan Dan naki kike ba shine Kika hanashi ya daketa ko kefa Naga alama kamar kina goyan bayan auran da baffah yaiwa nabil Anya kuwa basa hannunki aciki nifa nafara zarginki Dan ke basan nabil kike ba
Dariya hajiya Fatima tayi tace gaskiya girma yafadi Alhaji abin naka dada cigaba yake yanzu Kai bakaji kunyaba da kazo kana kunfar Baki akan yarannan gaskiya kaiwa kanka fada saboda gaba Kar aji kunya Ni wanka Zan shiga kaga tafiyata Dan kome Zan tsaya cemaka ba shiga kunnanka zeyiba bakaji na baffah ba bare Kuma nawa Kai da danka Allah yaganar da ku
Dare nayi lokacin kwanciya bacci yayi nabil yafito daga wajan minister yazo shigewa yaga shatuwa da Hajiya Fatima afalo suna Hira ko kwallan inda suke beyiba yashige yana Jin abinda zewa shatuwa in ta kuskura ta shigo bangaransa Yana shiga yakarewa ko Ina na wajan kwallo afili yace Allah ya temakeki yarinya Baku batamin waje naba yau da kinga rashin mutunci Ina jira yau Naga a Ina Zaki kwana dakinshi yashiga yaje yayi wanka yayi Shirin kwanciya bacci kwanciyarsa yayi hankali kwsnce
Bacci yafara ibanshi yaji ana buga kofa kamar zaa balla can Kuma yaji muryar shatuwa na mgn ka budemin kofa wlh ko na hanaka bacci wlh Babu inda zanje na kwanta se awannan dakin kafuto ka barmin dakina Ni karka samin kazanta adaki
Dataga baze fitoba fita tayi taje kicin ta dauko ludayin miyi tazo tahau yin kida da kofar dakin da nabil yake ciki akulle tacika ko Ina da karar kidan Amma can da taga bemataba tahau Waka dandudu matamaza meshigar Mata rabi aljani rabi mutun anji kunya me zamanman wando me wuya du sarka me fanti agashi me tafiyar Yan kaciya
Kidan da take be batawa nabil Rai sosaiba se Wannan Wakar da take Masa ai awani zabure yaduro daga Kan gado yahau neman abin da ze zaneta dashi dube dube yafara yagano belit dinshi yadauka yanufi kofar dakin yabude cikin bacinrai yayo kanta ze daketa itakuma Daman ta shiryawa hakan tasan yanzu ta tunzuroshi ransa yabaci Dan ta fahimta bayasan tana kiranshi da sunayan banza da Kuma wakar da takemai Dan taga ransa yabaci ranar da tasa kawayanta sukai Masa Waka tana ganin yabude kofar yayo kanta zefara zuba Mata ajiki Tai maza ta bude ledar dake hannunta ta Hura Masa kararar da Tai alkawari se tasamasa ajiki shi da minister in har shima be Dena yiwa iya rashin mutunci ba tindaga can takwaso shi agidan megari da zasu taho Abuja takwayi saa ta fesamai da yawa yashiga jikinshi sosai Kuma du dukan da ze Kai Mata baya samunta kaucewa take suna ta zagaya falan wajan nashi intaga ze cimmata ya sameta se Tai maza ta tura kujera wajan da yake shikuma seyai tsalle ya tsallake
Tace lokaci kadan nabaka zakayi sanyine yau zamuga ainahin rawar dandaudu me tafiyar Yan kaciya ai kowa yaci tuwo Dani Miya yasha yanda ka karyamin hannu nasha azaba wlh kaima se kasha tawa wahalar yau se kayi kwanan zaune yanzu muka Fara wasan muzuba mugani Waze gaji tsakanin Ni da Kai bawai bakasan mataba aikuwa zakaga aikin Mata ka kirani Yar Kauye to ga aikin Yar kauyenan kafara gani Dan yanzu nafara ban Fara komai ba Ina da salo kala kala kuma du se ka shasu gobema ka kara shiga gonata
Allah yabawa nabil sai,a yakama shatuwa yadaga hannu kenan ze zuba Mata belit din yaji lokaci Daya kamar anzuba Masa wani mahaukacin kaikayi ai besan lokacin da yasaki hannun shatuwa ba yatsaya Yana daurewa ai tin Yana daurewa besan sanda yafara tsalleba Yana Susa Yana tsalle Yana zagaye falan Yana Hawa Kan kujerun wajan ai besan lokacin da yacire rigar jikinshiba yafara ihu Yana Kiran daddy
Me shatuwa zatayi inba dariyaba har da kwanciya yanda taga yanayi yake dada Bata dariya Waka tahau yi masa asosa asosa asosa Babu ciwo cinnaka ya cijeshi asosa Masa asaso waiyo Allah asosa kaga yanda zaka nayi in kanaso kadena Jin kaikaiyin kaga yanda ake agarinmu du yanda nayi kayi
Ai dasauri ya yarda da abinda tace danshi Yama manta fadan da sukeyi Dan azabar kaikaiyin da yake ji rawa tafara tana juyi tana wakar asosa shikuma bawan Allah Dan azaba rawar yake yi da wakar bill hakki yanda taga yake rawar dariya take tayi Dan mugunta dogwan wandanma shima cireshi yayi yakoma dagashi se gajeran wando
Tace zuba dagudu katafi wajan su mommy ka nuna musu kafin kaje zaka Dena ji
aikuwa yace to Ina hanyar
tace kaganta Nan
Aikuwa yazuba da wani mahaukacin gudu yafice
Shatuwa takuma fashewa da dariya tace kadan kagani in dai nice yanzu kaga Ni se naje nai baccina hankali kwance Kai Kuma ka kwana azaune
Tashige daki Tai kwanciyarta tahau bacci cikin kwanciyar hankali
Litantafaina da na rubuta kamar haka
*HADARIN So*
*'YAR KWALLIYA*
*NAFI GANE ARO*
*HEDAYA IKIRARI*
*TALLAFEE*
New writer's
Hakan Take
*Husba'ahfama* 鉂ゐ煈�
*'YAR KWALLIYA* 馃コ馃拑
👝👝👝👝👝👝👝👝👝👝
👠👠👠👠👠👠👠👠👠
👝👝👝👝👝👝👝👝
👠👠👠👠👠👠👠
👝👝👝👝👝👝
👠👠👠👠👠
👝👝👝👝
👠👠👠
👝👝
👠
💄💅 *DAN MINISTER* 💅💄
🦚🦚
Written by *Husba'ahfama*
*IG officiall_husba'ahfama*
Facebook *Real Husba'ahfama*
Follow me on Wattpad *@ Real Husba'ahfama*
11-12
Yan aikin gidan du Wanda yaga nabil yataho dagudu bakaya ajikinshi Suma se su zuba da gudu kowa na neman wajan buya tindaga bakin kofa yake kwallah Kiran daddy mommy kufuto Zan mutu dagudu yakarasa shigowa minister najin Kiran da nabil yake musu yafito hankali atashe yanda yaga nabil shima abin yabashi tsoro ga jikin nabil du yatashi yayi kamar kurajene yafito Masa abinka da farin mutun
cikin tashin hankali minister yace me yasameka nashiga uku nabil karka tafi ka barni zanshiga mugun hali Nima za a iya rasani waye yaima wannan abin Haka Hajiya fito kiga me yasamu danmu kifito ki temakeni zanrasa farincikina
Hajiya Fatima itama cikin tashin hankali ta karaso wajan tace mekuma yafaru da,dandarannan me zangani haka nabil tsaya nagani
Dakyar tasamu yatsaya tagani lokaci daya tagane meye ajikin nabil ahankali tace wlh nasan kece shatuwa kece Zaki iya zubawa nabil karara ajiki Daman shine abinda kikayi dako tin daga mazagai Allah yashiryeku ku denawa junanku mugunta muje kafarayin wanka da ruwa mezafi tukunna Sena shafama magani kai Kuma alhaji kayi hakuri ka kwantar da hankalinka yanzu ze denajin abinda yake ji
Nabil bemasan iyayan nashi na mgnba shi takansa yake Yana rokar Hajiya Fatima da minister su Sosa Masa da Kar Hajiya Fatima tasa minister yakama hannun nabil aka kaishi bandaki aka hada Masa ruwan zafi yasamu yashiga yai wanka Yana fitowa Hajiya Fatima tasa ya shafe ko Ina na jikinshi da manja sannan yaji dadin jikin nashi kaikaiyin yadena besan sanda baccin wahala ya kwasheshiba ranar dai be kwana awajansaba se awajan su Hajiya Fatima yakwana adaki Daya daga cikin na Yan uwanshi Mata da aka ware musu kafin safiya zazzabi me zafi yarufeshi se da aka Kira Dr yazo ya dubashi hankalin minister Kuma in yayi dubu yatashi Dan,so Babu lfy ko abincin kirki yakasa ci Yana ta lfyar nabil dinsa
Shatuwa kuwa batasan ya nabil yakareba da ta sashi yafita baccinta Tasha har gari yawaye ita Tama manta da babinsa saboda burinta yacika tafara bashi wahala
Nabil da yatashi da safe tinanin abinda yafaru jiya tsakaninshi da shatuwa yafara afili yace tambas itace silar komai jiya aikuwa Zan yi maganinta Nima baffah baffah ka hadani da wahala tindaga ranar da na hadu da annobar yarinyarnan shikenan komai nawa yafara samun matsala kullin bana cikin farinciki saboda ita dolenema nabar garin gaba Daya
Hajiya Fatima ce tashigo tasamu nabil tace nabil katashi yajikin naka
Yace da sauki mommy
Tace to alhamdulillah nabil yau sonake nabaka shawara da Kuma Yar nasiha Zan maka nabil wacece mahaifiyarka
Yace mommy wace irin tambayace wannan kece mahaifiyata bani da wata bayan ke kece dai bakya Sona bansan meyasaba Kuma wlh abin na damuna sosai Naga ke da su anty Amina bakwa fada kina sansu sosai kodan Ni ba mace bace ko Danni namijine bansaniba mommy abokaina in naji suna hira atsakaninsu suna fadin abinda iyayansu Mata suke musu kuma suke nuna musu so da gata har mamaki nake mommy meyasa Ni du bana samu daga wajanki kecefa daya daga cikin wayanda sukasa na tsani mace aduniya bazan boye mikiba kecema mace ta farko da tasa min akidar kin du wata mace saboda kece Kika haifeni Amma baka nunamin so kamar yanda daddy yake nunamin ke kullin cikin yimin fada da hantara kikemin ko Abu daddy yai min na kudi ko na siyaiya se kinmai fada ko Ni kinmin Kuma Naga bakyawa Yan uwana Mata da Suma kekika haifesu Kuma in sone Ni yadace kifi so saboda da nine auta saboda naji ance anfisan auta Anfi Kuma nuna Masa so amma ni meyasa du bana samu daga wajanki se wajan daddy kullin daddy ne ke sani farinciki kekuma kece mesani bacin Rai Dan Haka nasawa kaina akidar kin du wata mace saboda uwar da tahaifenima ta nunamin tsana Bata sona to wace macace zata Soni Kuma du da tsanar da nayiwa du wata mace narasa meyasa ke nakasa tsanarki azuciyarta na gwada na gwada Amma nakasa tsanar taki suma Yan uwana Mata na gwada na tsanesu Amma Suma nakasa tsanar tasu du da Suma basona sukeba kullin cikin kina da tsanata suke mommy irin abinda kike min Suma shi suke min natashi Babu kauna tsakanina da uwata da Yan uwana Mata me yasa meyasa mommy wlh Ina sanki azamanki na mahaifiyata innaTina da Ni bakya Sona acikin yaran da Kika haifa kinsan irin kukan da nakeyi
Kasa karasa mgnar yayi yafashe da kuka kamar karamin yaro itama kukan tasa taje ta rungumeshi tana rarrashinsa har tasamu yafara shuru tinani ta fara azuciyarta tafara mgn tace gaskiya Nima Ina da lefi babba dolene nai kokarin gyara komai Dan na samu ka gyaru Allah sarki Ashe yanajin zafin abinda nake Masa nikuma Allah yagani Dan yagyaru neke Masa wasu abubuwan dolene najaka ajiki sosai nabil Dina har kagane Nima ina sanka alhamdulillah Allah nagode ma da kafara ansar addu'a ta Akan nabil saura alhaji sautin kukan sane ya dawo da ita daga tinanin da takeyi
Cikin karfin Hali tace ya Isa Haka Mana haba nabil Dina Ina kataba jin uwa ta haifi danta tace bataso se dai taki halinsa wlh nabil ni kuwace me sanka kasan yanda nake ji araina saboda rashin jituwar da take tsakanina da Kai Sam Babu jituwa da fahinta tsakanina da Kai kaki ka gane abinda kake yi ba Abu bane me Kyau wlh kullin mutane na kuka da Kai da rashin mutuncinka da iko da takama irin naka du ba Abu bane mekyau du bana so kake yinshi kuma ko na maka nasihah bajina kakeba kasan ya uwa takeji in taga danta nayin Abu mara kyau kasan ya nake ji in na saka ahanyar gyara kaki ji nabil meyasa kana Jin mgnar mahaifinka amma Ni Kuma baka Jin tawa mgnar ai yadace Kai Mana adalci Ni da mahaifinka in kaji tashi mgnar Nima kaji tawa Kuma ka zauna kayi tinani da mgnta da ta mahaifinka wancece zata saka ahanya ma daidaiciya daga yau ka zauna kana tinani in na fadama mgn Kai bani bama har su baffah du Wanda yaima nasiha kana Zama kana nazari akai kaji Kuma nabil du Wanda yaima nasiha wlh masoyin,kane ba makiyinkaba daga Ni har Yan uwanka Mata wlh du muna sanka muna kaunarka ka canja kagani daga yau kaga in bakaji dadin Zama da muba Kuma zaka gane mune masoyanka na ainahi shima alhaji bawai nace baya sankaba aa Amma San da yake maka yasa idansa yarufe baya gayama gaskiya kome kayi Wanda ba dedaiba se dai yagoyi bayanka baze taba yima fadaba Dan ka gyara Kuma har ga Allah ba gata yake nunamaba nabil kullalin burina Naga ka gyaru kazama kamilin mutun Wanda kowa Zena alfahari da Kai Kuma kowa Yana yabanka baka tabayin tinani kaga yanda kowa yake tsoranka Kuma abayan idanka kasan zagi da tsinuwar da kake Sha awajan mutane musamman talakawa ko ga Yan aikin gidannan baka yimusu adalci kana wulakantasu kana cimusu mutunci Dan kawai Allah yamaka arziki sukuma suna Zama karkashinku karfa ka manta du kanmu dayane Allahne ya yomu yanzu in har kana sona kamar yanda kace to kana jin mgnta Nima kamar yanda kake Jin ta mahaifinka kaji Allah yasa du kaji abinda nace daga yau in dai zaka na Jin mgnta mun koma kamar abokai zakaga gatan da Zan na nunama Kai Sema kafi samun gata Akan sauran abokanka yanzu nice abokiyar shawararka Dana Allah yai maka albarka ai du kajini ko
Yace eh mommy to kiyi hakuri daga yau na Dena du wani abinda ba kyaso in dai Nima Zaki Soni kamar yanda kowace uwa take San danta Ni kullin burina da tinanina Naga Nima kina nunamin gata da kulawa kamar sauran Yan uwana yanzu me kikeso na Dena kuma ki fadamin wlh Zan Dena
Hawayan farincikine yafara zuba a idanta hajiya Fatima kuka me karfi tasaki Dan murna
Dasauri yaje yahau goge Mata hawaye Yana rarrashinta shima Yana hawaye yace mommy kina dagamin hankali Dan Allah kiyi shuru wlh indai nine nadena
Tace nabil kasan kukan me nakeyi kukan farin ciki nake yau Allah yaamshi addu'ar da nakeyi akanka safe dare cikin dare kullin se na Hana idona bacci Ina rokwan Allah Akan yashirya,min Kai Kuma kullin ban finda Raiba nasan Allah me amsa addu'ar bayinsane musamman addu'ar uwa Akan danta yanzu Ni Akan tsakaninka da shatuwa nake so kudena fada sonake kadena kulata kome Tai maka karka daga Ido ka kalleta bare har Kai Mata mgn Kaine mijinta baasan megida da kula matarsa suna raba abin kunyaba kaga yanzu raini na neman shiga tsakaninka da ita Dan baka Kama girmanka
Kuma kabi nasihar da baffah yake maka se Kuma Kan Yan aikin gidannan Suma ka Dena musu abinda kake musu ka Dena takura musu
Yace to mommy du Zan Dena ko ban Dena dukaba Zan Dena wasu daga ciki in har Zakiji Dadi aranki ki dena min abinda kike min du Zan Dena Amma gaskiya nifa wannan yarinyar bana Santa kema kin sani yarinyar kina ganin abinda take min Bata da kunya Kuma Ni gaskiya bazan iya kwana da ita daki dayaba Dan lokacin da Zan karkaryata ma bazan saniba Kuma gashi kince na,Dena kulata in ta batamin Rai se dai in nakoma dakin da ke kusa da ita tinda da komai adakin shima Dan Ni bazan iya komawa dakin da