wani iri yakeji zuciyarsa nayi be zataba be nufaba seji yayi anacewa Allah ya yarda aure ya dauru tsakani nabil sani da shatuwa umaru jikar iya ikwan Allah Akan sadaki nera dubu dari biyu lakadan ba ajalanba
kafin nabil yagama mamaki se jiyayi abokansa Yan tsokana sun dagashi sama suna tayashi murna suna ta Masa dariyar mugunta da tsokana
Megari ne yashiga yafasawa iya angama daura auran tafito ita da amarya zasu tafi Abuja haka mahaifiyar shatuwa tana hawaye taiwa yarta nasiha du da tasan bawani dauka zatayiba Haka aka fito da amarya shatuwa aka sata amota tare da iya akatafi
Baffah ya dada bawa kawayan shatuwa hakuri Akan abinda yafaru tsakaninsu da nabil yakuma musu alkawarin zuwa ganin gidan shatuwa in komai yanutsa hakama yabawa suwaiba mahaifiyar shatuwa hakuri tayi hakuri itama zata tagano inda yarta take in ankwana biyu Haka faffah yakama hannun nabil yasashi amota tare da tawagarsa ta Yan fati suka dunguma zuwa Abuja raka ango da amarya
Hajiya Fatima da alhaji sani sunacan basusan meyake faruwaba faffah ne yakira Amina yayar nabil yace Tai maza tataho gidansu tajirasu komai dare sunanan tahuwa zebata wata Amana yakira Hajiya Fatima itama yace Mata tashirya gashinan tare da Baki abinnan da takira tafada Masa komai yakankama Dan Haka tashirya gasunan sauran bayani se yazo ya tambayeta sani dansa nagari tace eh yace to du sujirashi gasunan
Sedare suka Isa Abuja zokiga zare Ido wajan iya da shatuwa sunga birni ko Ina da hasken wutar nepa kamar ba dareba ga dankara dankaran gidaje agarin anazuwa gidan su nabil Nan kallo yakoma sama iya dada zare Ido take saboda ganin dankareran gidan Dan baffah Haka aka bude musu gate motocinsu suka shige wajan fitowa amota ansha fama da iya cewa tayi bazata fitoba ayanke Mata Kai abinda yadada Bata tsoro ganin sojoji da bindigogi ahannunsu tadada tsurewa Dakar Amina tazo ta lanlabata tashiga
Baffah godiya yayiwa tawagar abokan nabil sannan kowa yashige gidansu sukayi sallama da ango mijin amarya shatuwa
Baffah Kama hannu nabil yayi zuwa cikin gidan da sallama ya shiga afalo yasamu hajiya Fatima da alhaji sani da su iya waje yasamu yazauna ya zaunar da nabil kusa dshi baffah yafara mgn yai sallama yace to sani da Fatima kubude kunnanku kuji me nazo dashi musamman Kai sani Dan nasan daga gunka matsalar take Nan yaimusu bayanin abinda yafaru tindaga zuwan nabil ma,agai har daura auransa da akayi da shatuwa wannan da kuke gani me karaya ahannu itace amaryar tashi Kuma itace Wanda ya karya din itakuma wannan tsohuwar itace iya kakar shatuwa tazo taga inda jikarta zata zauna yanzu amarya zata zauna a bangaran nabil cakin gidannan Kuma adakin nabil har se tawarke sannan acikin gidajanka kabasu Daya sutare acan Dan Haka ga amananan ankawo muku ta Yar mutane kuji tsoran Allah kukula da ita kamar yanda zaku kula da danku nabil
MINISTER yace baffah meyasa kahada wannan auran kafasan nabil wlh baze taba yarda da wannan Yar kauyanba Kuma nasan nabil basanta zeyiba Kuma baffah na sanka Baka tambayi nabil ko yana san ta ko baya san ta kawai ka yanke hukunci ne ka aura Masa ita wlh daga ganin yarinyarnan Bata da kunya Kuma bazasu zauna lfyba ko ta ilimin nasan nabil yafita da komai kagan tafa yarinya kamar aljana se zarzare Ido take tin da suka shigo ko ita kakar tata Naga se wani huhura hanci take tana wani zarzarewa mutane Ido wlh in har akabar nabil da yarinyarnan ancuceshi Kai nabil kana santa ko baka Santa kafada kowa yaji Dan Allah baffah inyace bayaso kabarshi yasaketa kowa yahuta Dan wannan aljanar yarinyar ba ajinsa bace
Nabil yace daddy bakinciki ya hanani mgn tin daga lokacin da yake hada auran nakasa cewa komai Dan ganin komai nake kamar amafarki Ni abinda yafi konamin Rai wai a cikin aljihuna baffah yaciri kudi yabiya sadakin wannan mahaukaciyar yarinyar wlh daddy nakuma tsanar mace arayuwata Mata sun yimin abinda bazan taba mantawaba natsani yarinyarnan ranar da nafara ganinta na tabata ta zamemin Bala,I ta zamemin alakakai arayuwa Wai yau mace akakawo gidanmu azaman matata inba Wanda ya haifi ubanaba waye zemin Haka na barshi ban dau matakiba aduniyarnan bazan taba san taba Kai bama itaba du wata mace wlh na tsanesu illa uwata da Yan uwana Mata sune kawai ban tsana Suma sun Zama Dolene awajena daddy yau baffah ya kunyatani Wai Ni nabil nine baffah yasa aka dinga daukana agaban yarana da abokaina da wayannan mahaukatan yaran cancak kamar wani yaro anasawa amota ana ta rikeni Wai Kar na gudu Ni baffah yaiwa auran Dole dabaka ta da hankalinkaba baffah saboda Ni har abada bazanyi aureba Dan ko anyimin bani aka daura waba mommy da daddy ka daurawa aurannan ko Kuma kanka ka daurawa tin amazagai nakeso nai kuka ko naji Dadi azuciyata Amma nakasa Daddy zuciyata zata fashe in har aka barni da mace azaman matata faffah Zan hutar da Kai Zan saketa yanzu Ni nabal sani Zan
Kafin yakarasa iya tace wlh karma kafara baka Isa kamayar min da jika bazawaraba inaji Ina gani da ban yarda da auranba Amma yanzu na yarda da auran shatuwa da Kai Kuma wannan ikirarin da kayi na ka tsani du wata mace wlh kajawa kanka Zama daram Kai da shatuwa Dan Haka ka karya min jika bass kamar kasamu rake to karike wlh baka karya banzaba se nasa shatuwa tarama Kuma ko ban sataba nasan shatuwa Yar halakce Ni tagado zata rama Kuma wlh da Wasa ka tabamin jika se narama Mata itama Kuma kafin natafi Sena Mata nasiha akanka du abinda Kai Mata tarama Kar ta barka kana kiramin jika mahaukaciya kaifa me kala biyu Dan Allah jibeka ko gashin kanka abin kallone jibi wani wando Rabin duwawu du awaje ana ganin wandanka naciki jibi wasu uban sarkoki awuyanka sunfi kala biyar jibi yatsun hannunka zobunan da suke hannunka dubi shigar taka babu ta arziki da ubanka yake Kiran jikata Yar Kauye me kirar aljanu Kai kumafa me kirar me za a kiraka me kirar aljani ifiritu Zan kiraka ko dandaudu ko me tabin hankali da ubanka yake cewa jikata ba ta da ilimi indai irin ilimin kane wlh gara ta zauna Haka da Wanda na koya Mata jikata ba jahila bace Dan Ni Nan nice na ke koya Mata karatu har me kwanciyar tsakar daki du na koya Mata kai Kuma na dawo wajanka sani kake kowa wlh inkai Wasa Zan tsinkeka da Mari Dan Naga baka da mutunci tinda nashigo Naga kana harararmu kaganni Nan wlh shegen karfine da Ni bankiba daga Kai har Dan nake mu daku Dan jina ne ke dakaukau saboda karfi Kuma Nima nayi alkawarin senayi zaman Yan bori Akan kafar danka tinda ya karya min jika Kuma wlh ko yasaki jikata Bata sakuba Zama daram Dan Bazata koma mazagai ana kiranta da bazawara da kuke kiramin jika Yar Kauye kowa asalinsa Kauye Dan kwal ubanka daga Ina ubanka yake in ba da ga kauyenba anzo birni anyi kudin Alla ya Isa anci burudi da shayi da abin Yan gayu an manta da kauye usuman kajawa danka da jikanka kunne wlh Basu sanni bane labarina sukeji Zan gwada musu halina in suka kaini bango
Kafin baffah yai mgn MINISTER yace lanlai tsohuwar Nan daga ganinta Bata da mutunci Ni kike gayawa wannan mgnar lanlai in baaraba aura nabil da wannan yarinyar ba wlh kashemi Dana zakuyi ke da jikarki yanda kike San jikarki Haka Nima nake san Dana nabil Ni Kuma azamana na mahaifin nabil bangoyi auran nabil da jikarkiba Dole ya saketa Kuma Nima zanwa Dana nasiha in jikarki tamasa rashin kunya yarama Kar ya barta nama San Dana nabil shima Dan halakne ze Rama kakuma balballata Ni nasaka kaji nabil wlh wuya kadai se tasa jikarki ta gudu ji wani suna Wai shatuwa ko dadin ji Babu Dan Allah baffah karka Hana nabil sakin yarinyarnan wlh ke tsohuwa karki Kara kiran Dana Dan kwal uba nagaya Miki
Kafin kowa yayi mgn shatuwa tatakarkara takurma wani uban ihu se da nabil ya toshe kunnansa tace nashiga uku Ni yanzu ma nagane me ake nufi tin amazagai ban ganeba se yanzu har fadan da babarmu taimin Wai nabi mijina Ni du ban ganeba Ashe Wai aure akaimin iya kina Ina aka auramin wannan dandaudun Mata matamazan aka auramin iya Kika Bari haka tafaru Daman shi abbah ba Sona yakeba neman Kai yake Dani su megari ma Haka du basa Sona Wai ma Kuna nufin anan garin Zan zauna billahillazi ba Zan iyaba tinda muka shigo garin Banga gonakiba Kuma Ni bazan iya rayuwa Babu dawa da gonaki Babu kawayena Kai dandaudu wayacema Ina sanka Allah yakiyaye na auri rabi mutun rabi aljani yanda baka Sona Nima bana sanka yanda ka tsaneni Nima na tsaneka Kuma nadau alwashi se narama abinda kami wlh bazan taba hakuraba bakasan shatuwa jikar iya ikwan Allah ba
Nabil yace nashiga uku kaina zefashe Dan Allah baffah kakawo karshan rigimar Nan Dan Allah badan niba kaji tausayi na baffah karabani da mahaukayar Nan wlh na tsaneta ko ganinta banaso nayi karka min Haka Dan Allah baffah Kai mgn kayi shuru tin dazu
nabil yaje yarike wa baffah kafa
Baffah yace nabil wlh wlh wlh kaji na rantse har sau uku aure ya dauru Babu me Rabashi se Allah tinda shine komai yake hannunsa Amma wani Dan Adam wlh be Isa yaraba auranka da shatuwa ba Babu shi Kuma baayishiba Kai da ubanka kubude kunnanku kuji Ni Ni usuman mahaifin sani Kaka awajanka nabil in har ka kuskure ko da Wasa kasaki shatuwa wlh wlh wlh Sena tsinewa ubanka sani yabi duniya ya lalace Kuma bani bashi har abada kuma nacireshi acikin yarana gabadaya in kanasan ubanka kabar mgnar raba aure ko mgnar saki in Kuma bakasan ubanka gafili ga medoki ka saketa kaga aiki da cikawa Kai da ubanka me daurema gindi naji kana gigin ambatan saki wlh daga yanzu mgnar tafita bakinka gaba daya Kai da shatuwa mutu karaba Kai zaka binneta ko ita ta binneka kace katsani du wata mace ko to ga macenan ku zauna gida daya tare in kaso Dan Allah kamutu tana warkewa zaku bar gidannan Kai yanda kakeji da rashin mutunci hakama shatuwa takeji dshi ga tanan ku kashe junanku daga ita har Kai da kuke cewa ba kwasan juna aure dai ya dauru Babu batun rabuwa kuje Kai da ita ku koyi San junanku Kai sani shawara ta rage taka kace bakasan wannan auran ko to kaiwa danka fada yazauna da matarsa lfy ko kabi San danka ya saketa Ni Kuma mahaifinka na tsine maka
Gaba daya Kan MINISTER ya daure wani uban gumine yake ta ketomai ajiki du sanyin esin da ke falan Amma yajike da gumi se gogewa yake jiyayi gaba daya ya tsani shatuwa arayuwarshi da kakarta iya yanzu ya zeyi tinda har baffah Yana Kiran ze tsine Masa Akan wannan aljanar yarinyar Baki narawa yafara mgn yace Dan Allah baffah bekai hakaba Amma Ni da zakabi tatawa da kasa nabil yasa
Iya CE tataso tazo gaban MINISTER tace au baka sadudaba ko bakayi sanyiba du da dokar da ubanka yasa maka ko tu Bari kaga tinda kaki jin mgnar ubanka Ni Bari na fara wankeka da Mari tukunna
hannu tadaga zata mareshi kafin hannunta ya Kai fuskar MINISTER nabil yayi kukan kura yataso cikin fishi yarike hannun iya jikinshi se tsuma yake Dan masifa da bacin Rai da yake cin ransa yace ke tsohuwa ki nutsu kishiga taitayinki kafin na koya Miki hankali uban nawa Zaki Mara haba zance kike wlh Ina gani ki mararmin ubana Ina wajen Ashe ban haifuba ko da Wasa Kar ki Kuma gigin daga hannu da sunan mararmin uba kema inaga ban karyakin bane Dan Haka kikaki yin sanyi har kike cewa Zaki ramawa jikarki Nima se kin karyani ko ta Bari kiji somin tabi hannunta ya matse da karfi iya tasaki Kara Dan azaba Kuma ki jawa jikarki kunne tashiga hankalinta da Ni takuma iya bakinta in bahaba Zan canja Mata kamanni ke ko kunya bakijiba ubana na MINISTER kidaga hannu Zaki mareshi kin san waye shi a kasarnan Kinkuwa San me mukamin MINISTER na man fetir yake nufi koni DAN MINISTER kin Isa kisa hannu ki mareni bare ubana dada matsa hannun iya yayi takuwa da wata karar me karfi
Haba wa cikin fishi shatuwa tataso tararumi wata kwalbar fulawa da ke gefen TV zata kwadawa nabil tana jefuwa cikin zafin nama MINISTER yataso yatare Dan karya samu nabil seji akai kau agoshin MINISTER lokaci daya jini yaballe Yana zuba agishin sa ran nabil dada baci yayi jiyayi zuciyarshi zata fashe Daya hannunsa yasa yadafe kirjinsa jiyayi jiri na ibansa lokaci daya idansa yakada yayi jajir besan lokacin da yasaki hannun iyaba shima yafara neman abinda ze kwadawa shatuwa da besamuba idanshi yarufe yayi kan iya yabi ze daka azaman shatuwa ihu iya tafara tana neman dauki Dan nabil yayi Bali,in Bata tsoro dagudu Tai bayan kujerar da baffah yake azaune
tana cewa nashiga uku yau Naga ikwan Allah usuman Daman Haka jikanka yake ka hadashi aure da jikata ko dai shima Yana shaye shayennan na zamani da matasa keyi wannan wanna kalar aurene Kai nifa sirikarkace jikata kake aure usuman zefa lahantani kanaji kana gani in wannan zakin yai wasan kura Dani wlh ragargazani zeyi
Tsawa baffah ya dakawa nabil ya tsashi tsaye yace Kai karka yonan ko dawasa bare har kakuma tabata kaikuma sani kadan kagani ku bacemin dagani afalannan Kai da danka zamuyi Zama na musamman Ni da Kai sani kekuma shatuwa bakiga me kikaiwa sirikinkiba ko Baki San uban mijinki bane
Shatuwa tace Ni bashi nai niyar samuba wannan dandaudun nai niyar jifa shikuma yatare Masa na fasa Masa goshi ban saniba tsautsayine se hakuri Kai Kuma wlh Sena zubar maka da jini tukunna zakasan nice shatuwa
MINISTER hannun nabil yakama suka bar falan Yana tafe Yana masifa
Du wanna ruwan masifar da akeyi hajiya Fatima da Amina na wajan sun kasa mgn se Ido da dariya da mamaki
Baffah yace Amina jeki Basu wajan kwana Kan gobe bangaran nabil Zaki kaisu kimusu du abinda yadace ko abinci Basu ciba du kibasu suci in kin Gama dsu kizo nabaki Amana ke da mahaifiyarki kinji Yar albarka
Tace to baffah suka fice zuwa bangaran nabil
Hajiya Fatima tace baffah yau naci dariya Naga ikwan Allah
Baffah yace rabu da su Ina sane nahada aurannan insha Allahu shine silar shuryuwar nibil da sani Dan Allah kiga abin kunyar da sani da iya suka yi gaban yarannan memakwan suyi musu nasiha suhada kansu su zauna lfy Sema dada Bata abin sukayi kowa nawa nashi muguwar huduba Akan zaman auransu sani idansa yarufe San dansa yake du mgnar da tafito daga bakinshi fada yake Haka iya San jikarta itama yarufe Mata Ido du abinda yafito daga bakinta fada take Fatima ke da Amina ga amananan nabaku na shatuwa ku temaka ku gyarata ku wayar da ita asata amakaranta in tawaye itace zata gyara nabil Kuma itace zata cusawa nabil Santa azuciyarshi da San Du wata ya mace azuciyarshi takuma nuna Masa darajar mace da mutuncinta awajanshi da kansa ze sauka daga Kan akidarsa ta kin Mata yakuma so shatuwa ammafa se anyi Dan karamin yaki sosai agidan nabil Kuma fa se kunyi hakuri da halayan shatuwa Dan yarinyar bataji Kuma Bata da tsoro ko kadan Dan Haka na hadata da nabil zata iya da shi rashin tsorantane yasa na hadata da shi Dan Naga nabil na da wata baiwa kusan kowa tsoransa yake tin da Kika kirani awaya Kika fadamin halin da nabil ke ciki nake ta tinanin matar da Zan zaba Masa Kuma Sega wannan abin yafaru tsakanin sa da shatuwa da Kuma kalaman da naji yanayi Kan mace yasa na hada wannan auran Allah yasa kin fahinceni Fatima
Hajiya Fatima tace nagane baffah Kuma naji dadin hadinnan Allah yabamu ikwan rike amanar Yar mutane yanzu inda matsalar take awajan alhaji take Dan shima yadace yaba da gudun mawa wajan hada Kan shatuwa da nabil Amna se gashi shima bayasan auran saboda dansa bayaso kasanshi du abinda nabil keso shi yakeso in da nabil yace Yana Santa shima alhaji ze sota yagoyi bayan auran Amma yanzu tashin farko kaga me yafaru da idanka Ni nataba ganin wannan Bala,in ranar da aka kawo amarya akwashi wannan ruwan masifar haka memakwan ayi farin ciki se abin yakoma bacin Rai Allah ya kyauta
Baffah yace rabu da shi se gone zamu hadu da sani yanzu zanje na kwanta gobe in Allah ya kaimu zamu karasa yanda zaayi Dan gobe in komai yalafa zamu koma Ni da iya
Kai 馃ぃ馃ぃ Yan DAN MINISTER fans ku da kuke tashirin zuwa biki kunga yanda aka kwashe ranar da aka Kai amarya shatuwa to Ina Kuma ga ranar da ake Shan biki Ashe zakusha raban fada tsakanin iya da MINISTFR da shatuwa da Nabil馃ぃ se kunzo
su hasana lawan
da su maman munur
da su shafa Umar
da Aisha ummu Minal
da hajiya Rashida
maman Abdulhakim
Yar mulki
maman Haifa
Amina isima il
maman baby
ummu hasim
maman kairat zariya
maman yaseer
momin twins daweesu novel grp ayishat daweesu novel grp
Asha biki lfy nidai Ina daga gefe馃ぃ
Ngd sosai Yan DAN MINISTER fans grp da irin ruwan shirhin da kikaimin tin daga ranar da nafara DAN MINISTER zuwa yanzu
da sauran grp grp da sunayansu na manta godiya nake Allah yabar zumunci da du wayanda na manta sunansu Dan Allah kuyi hakuri ngd sosai Allah yabar so da kauna
Bana turawa ta PC Dan Allah kuyi hakuri
New writer's
Hakan Take
*Husba'ahfama* 鉂ゐ煈�
*'YAR KWALLIYA* 馃コ馃拑
馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹
馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼
馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹
馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼
馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹馃憹
馃憼馃憼馃憼馃憼馃憼
馃憹馃憹馃憹馃憹
馃憼馃憼馃憼
馃憹馃憹
馃憼
馃拕馃拝 *DAN MINISTER* 馃拝馃拕
馃馃
Written by *Husba'ahfama*
*IG officiall_husba'ahfama*
Facebook *Real Husba'ahfama*
Follow me on Wattpad *@ Real Husba'ahfama*
7-8
Adaran aka Kira Dr yazo yaduba MINISTER yaimasa dinki nabil ma se da Dr ya dubashi har